Skip to content
Part 1 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Humaira! Humaira!! Humaira!!! Bata jin wannan kiran ne ko kuwa?” daga can cikin gidanmu nake jiwo wadannan maganganun.

Abinda ya yi dalilin da na fasa shiga cikin gidan na kara ja da baya na tsaya ina sauraron mai maganar.

Cikin takaici da bacin rai na yadda ita kullum babu dama ta kira wani ta dan sa shi wani abu don ni ma na samu in huta komai sai dai ta kira Humaira.

Can cikin zuciyata na sake jan wani mummunan tsaki a daidai lokacin da haushinta ya sake kama ni a dalilin zuba wa kwanon dake hannuna ido da nayi, cikin takaici nace sai kace ba ita ta aiken ba, tun kafin in kai ga kawo mata aiken da tayi min din har ta mance tana sake nemana don ta sake aikena tanfar dai babu kowa a gidan sai ni.

Maimakon in hanzarta shiga cikin gida in kai mata aiken nata, musamman da yake ina jin yanda ta kasa daina kwala wa sunan nawa kira, sai kawai naja na tsaya cikin zauren na makale jikin bango ina sauraro tare da yin tsokaci kana wasu al’amura da suka addabi zuciyata.

Ko yaushe ne ni ma zan samu in dan huta in samu in rinka watayawa irin na sauran yaran gidanmu, in mallaki ‘yancin rayuwa irin na yanda nake ganin sauran ‘yan uwana suna dashi?

A kullum zuciyata ta dan samu wani sarari ko wata dama da zata yi min wata tambaya, to ba tayi yi min tambayar da ta wuce wadannan tambayoyin, yaushe ne ni ma zan huta? Yaushe ne ni ma zan samu ‘yancin rayuwa irin wacce sauran ‘yan uwana ke da ita?

A lokacin da nake yarinya ‘yar karama, na dauki halin da nake ciki na takura da kunci da rashin hutu tamkar hakan ya same ni ne a dalilin ni din ni ce karama cikin yaran da suka kai munzalin moro.

Don haka sai nayi ta fata da buri wadanda suke biye da ni su kawo sanda za su karbe ni, amma daga baya sai na gane a’a ba haka ba ne tunda ai akwai wasu kannen nawa da tazarar watanni goma ne kawai a tsakanina da su.

Kamar irin su Suwaiba, kuma su din ba ayi musu irin aiken nan da ake yi min na sayo min kuka, sayo min daddawa, sayo min kanwa, komai ma dai ba kuma wannan ne yafi komai bata min rai ba, sai irin wai ko a gida daya abubuwan da ake bukata suke to ba za a hada min aiken ba, sai na kawo daya a sake maida ni.

Duk a dalilin dai wai kar a ganni a zaune ina hutawa, ko sanda nake yarinya ‘yar karama wannan jeka-ka-dawon kan ci min rai, to balle yanzu da na soma sanin abinda ke min ciwo, ga kuma wasu kannen nawa da yawa da suka taso bayana wadanda su ba hakan ake yi musu ba, wadanda su suke ma da ‘yancin a aike su su ce ba za su ba.

Babana Malam Surajo mazaunin unguwar Jahun ne dake cikin jihar Bauchi, Jahun gaba take kadan da Nasarawa, in har ka biyo ne ta kofar Nasarawa ne, gabadaya ta nan kewayenmu har unguwannin dake kewaye damu mutane da yawa sun san shi, sun kuma san gidanmu.

Saboda kasancewar shi din a shekarun da suka gabata yana cikin ‘yan kasuwar da kasuwa ke kai musu, ko a yau din nan kuwa da ake fadin harka ta dan ja mishi baya yana cikin rufin asirinshi daidai gwargwado.

Sanda na soma wayo a gidanmu ina yarinyar karama, na bude ido ne na tarar da Babana da Matanshi na aure guda biyu, wato uwargida Hajiya Majadan wacce gaba daya gidan har mutanen unguwa ake kira Mama.

Sai kuma Innata wacce akan sakaya sunanta da nayi kokarin yi nasha tabka da bulala akan wai ni din fi’ili ne dani da kuma sanabe iri-iri don haka nima na hakura na shiga sahu wajen gantsara mata sunanta da ake kiranta dashi Gambo.

Mama ita ce uwargida a gidanmu, auren saurayi da budurwa aka yi musu ita da Babana, tana matukar jin dadi da kuma gadara da hakan, da kuma alfahari da uwargidancin nata.

Zan ma iya cewa a wurin Mama, gani take tanfar duk wata mata da ba auren saurayi da budurwa suka yi da mijinta ba, to gani take tanfar auren matar ba wani aure ba ne na sosai, in ma ‘ya’ya ta haifa to ‘ya’yan da ta haifan sun fi kama da gasu nan dai gasu nan, amma ba wani ‘ya’ya masu ‘yanci ba.

Watakila hakan ne ma dalilin da yasa a lokacin da ‘ya’yanta mata suka zama ‘yanmata suka kawo munzalin aure ta kasa ta tsare, tayi kememe ta ki yarda da mutanen da Babana ya kawo su aure su.

Dalili, wai su din masu mata ne ‘ya’yanta ba za suje suyi bautar ‘ya’yan wasu ba, samari gal a leda zasu aura, don haka akan dole Babana ya yarda Kaza taja Zakara.

Ya daurawa ‘ya’yanshi Anti Sha’awa da Anti Kaltume aure da samarin da uwarsu take so. A kullum Mama cewa take yi da kaje ka samu ai gara a zo a same ka, duk tsiya an zo an same ka a gidanka da ‘ya’yanka da mijinka ai babu wata tsiya da za a kawo maka, dole kuma abi tsarin da a ka zo aka same ka akai, tunda dai mijinka ne, gidanka ne, to wane fi’ili za a kawo maka?

Mama mata ce mai nuna isa da gadara ga kuma mulki, zai yi wuya kwarai rana ta fito har ta kai ga komawa ga Ubangijinta baka ji ta tana yi wa kanta kirari ba, kusan kullum sai ta fada, “Alhaji mijina ne, auren saurayi da budurwa aka yi mana ni da shi, aurenmu aure ne na soyayya babu wani abin shi da ban sani ba, haka shima nawa.

Aurenshi nayi tun bai da ko kwabo tun ‘yan wandunan sakawanshi basu wuce guda biyu ba nake tare da abina, don haka babu wata matar da zata shigo min gida a dalilin ita da iyayenta sun hangi arziki da rufin asiri ta ce zata kawo min wani fi’ili.

Ba zai yiwu ba, ba zan yarda ba, shima maigidan ba samun shiga za’ayi ba a wurinshi, yauwa duk wacce ta hango min mijina tayi sha’awar shigowa taci arzikin da ta hanga to zata zo ne tayi zaman hakuri, in har ta matsu da zaman in kuwa ba ta matsu ba sai tayi gaba kamar yanda wasu da yawa suka yi da suka gane ba za su iya ba.”

Duk wadannan kalamai na Mama da takan furta kamar wasa kamar shakiyanci da iyakacin gaskiyarta take yin su, haka nan kuma al’amarin yake a hakan kuma ake zaune babu musu ko jayayya kan maganganun nata.

Babana ba ya iya musu da Mama, baya jayayya da ita kullum a to yake a wurinta, gashi kuma tayi sa’a yana matukar gudun bacin ranta kan abin da take so kuma to kullum zai iya sakin ra’ayinshi ya koma nata don neman zaman lafiya.

Dan karamin misali kuma shi ne, yanda ya hakura da bayar da auren ‘ya’yanshi Sha’awa da Anti Kaltume ga mutanen da yake ganin sune suka dace ya bada su ga wadanda Mama take so, duk kuma da gabadaya ‘yan uwanshi da aminanshi ba su so yayi hakan ba.

Innata da ke zaune da Mama da mijinta kuwa hakuri take  yi, hakurin kuma ba kadan ba, don kuwa in ban da tana da tsayayyun iyaye wadanda suke da tasiri mai karfi a kanta da bata iya yin shi ba.

Ita Innan ‘yar gata ce ta kin karawa a gidan su Yayu ne da ita maza da mata masu yawa, gashi kuma dukkansu ji da ita suke yi ‘yar auta ce wurin mahaifinsu Mallam Mai Babban Allo a wurin mahaifiyarta kuwa ma ita kadai ce mace.

Kyakkyawa ce kwarai, a lokacin da tayi ‘yanmatancinta babu wanda bai san da labarin kyanta ba, musamman ma a unguwarsu ta kofar Dumi, unguwar da a farkon auren Babana da Mama a can suka zauna da ya gina gidanshi na farko a Jahun, shi ne ya taso ya dawo nan kafin daga bisani ya gina gidan da muke ciki a yanzu, wanda manne yake da tsohon gidan namu.

Da yawan mutanen da suka san Innata da irin gatancin dake gare ta suka kuma san halin zaman da take ciki a gidan namu kan ce wai har da rabon haihuwa cikin abinda ya zaunar da ita.

Mallam mai Babban Allo Malami ne mai karantatarwa yara da manya suna daukan karatu a wurin shi.

Yana da matanshi na aure guda biyu, Hajiya ‘yar dubu ita ce uwargida, ita ce kuma uwar manyan ‘ya’yan gidan gabadaya su Alhaji Maikudi, Alhaji Malam, Alhaji Kawu, Inna Aisha, Inna Hajara, gasu nan dai da yawa gaba dayansu sun girmi Innata nesa ba kusa ba, don ma ‘ya’yansu sune sa’o’inta wasu ma da yawa sun girme ta.

Saboda ita mahaifiyarta Hajiya Turai an bashi aurenta ne a shekarunshi na girma bayan rasuwar matarshi ta biyu ta rasu ita Hajiya Turai ‘ya’ya uku ne da ita Kawu Hassan da Husaini sai ko ita Gambonsu.

Matan Mallam mai babban allo zama suke yi na girma da mutunci ita Hajiya ‘yar Dubu ta kama girmanta itama Hajiya Turai tana kame da kanta tana kuma girmama Hajiya ‘yar  Dubu saboda ta girmama kanta shima Mallam yana iya kokarin shi wajen ganin gidanshi ya zauna lafiya.

Don haka sai komai ya tafi bai daya gabadaya ‘ya’yansu kuma suna girmama su saboda mahaifinsu yana da girma a wurinsu.

Tasowar da Innata tayi a cikin gidansu cikin wani yanayi na shagwaba mai tsanani saboda rashin kwabo da sangarcewa yasa Alhaji Maikudi yasa hannu ya dauke ta daga cikin gidan ya maida ita nashi gidan gaban matarshi Kubra wacce a lokacin take da ‘ya’yanta maza guda uku, wato Abdullahi da ake kira Abba sai kuma Auwal da Ahmad.

Ita kuwa Hajiya Kubra tayi mata riko na gaskiya da amana ta hanyar bayar da ingantacciyar tarbiya tare da sauran ‘ya’yanta wadanda suka girmi Innan da wasu masu yawa da suka biyo bayanta.

Inna ta taso cikin gidan Alhaji Maikudi tanfar ita ce babbar ‘yarshi mace, itama Baba take kiranshi tanfar dai shi ne ya haife ta, don haka daga baya ne kwarai da yawan ‘ya’yanshi dama sauran mutane suka san cewa ita din kanwarshi ce ba ‘yarshi ba.

A lokacin da ta zamo budurwa kuwa ba zai yiwu in kwatanta yanda ta zamo ba, don kuwa ba karamin gata Alhaji Maikudi ya nuna mata ba.

Manema sosai tayi duk da bai yarda ya bada damar aje gare ta ba, saboda jan da yayi ya tsaya kan cewar karatu zata yi.

Sai dai Mallam mai babban allo bai goyi bayan hakan ba, hasalima shi ne ya bada umarnin bayar da auranta ga Babana saboda kamun kafar da Baban nawa yayi da Almajirin mai babban allo Alhaji Yahaya, wanda shi kuma Aminin Babana ne, tare ma suka taso tun suna ‘yan yara.

Duk da bin umarni ne yasa Alhaji Maikudi aurar da Innata a wannan lokacin saboda kwata-kwata shekarunta goma sha biyar ne, gashi kuma gabadaya an san Mama da irin matan da ta kora a gidanmu da ma rade-raden da ake yi na fin karfin Maigidan da ake cewa tayi.

Kowa cewa yake yi zata ne kawai ta dawo ‘yar karamar yarinya zata yi mata sanadin zawarci bai hana Alh. Maikudi kashe dukiyarshi mai yawa wajen hidimar auren nata ba.

Inna ita kadai a gidanmu, dakunan kwana uku ke gare ta gami da makadeden falo mai dauke da toilet a cikin shi.

Hajiya Kubra ce taja ta tsaya kan sai an bata wannan wurin kafin ayi bikin, kasancewar gidan namu a lokacin sabo ne gashi kuma Babana yana matukar son auren, ga kuma sulalla a hannunshi, yasa yayi musu yanda suke so din duk da irin tashin hankalin da ya fuskanta daga wurin Mama.

Su kuma su Hajiya Kubra da mijinta ba suyi kasa a gwiwa ba, suka shake mata wurin nata da kayayyakin alatu gami da gadaje irin na alfarma.

Alhaji Maikudi yana matukar sona a dalilin tsananin son Innata da yake yi, wasa dani yake yi irin wasan Jika da Kaka, don kuwa ya dage kan cewa Innata ‘yarshi ce, don haka sai na dade ban gane cewar ba shi ne mahaifinta ba, sai a wani lokaci da wani abu ya faru.

Rannan ne cikin dare na farka a daya dakin Inna damu ‘ya’yanta muke kwana a ciki sai na jiwo muryar Babana yana magana cikin yanayi mai karfi, alamar dai akwai bacin rai cikin maganar tashi.

Sannu a hankali da na saurari maganar tashi sai na gane tuhumar Innata yake yi yana tambayarta dalilin da yasa Mama tasa ta aiki bata yi ba?

Ban jin bayanin da Inna take yi mishi, don magana take yi a hankali cikin muryarta mai sanyi, sai daga baya da maganar tayi tsanani ne na jiwo ta tana cewa, to tunda kace ita bata karya me yasa in ta gaya maka magana ba zaka yi hukunci ba kawai sai kazo kana tuhumata?

Babana ya ce, ai haka ma za ki ce? Ta ce eh, saboda in ta riga ta fadi nata zancen ko na musa baka yarda.” Ya ce, “To kar kuma kice an zalunce ki.” Ta ce, “Uhun, zalunci kam ai a cikinshi nake raye, sai dai kuma na sani da sannu mai sakayya zai saka min, don kuwa ba zan yafe ba.”

Inna tana fadin haka naji saukan dukan Babana a jikinta, wai tayi musu Allah ya isa shi da Mama. Tuni jikina ya shiga rawa ina ta karkarwa akan gado na rasa yanda zan yi in taimaki Innata, tunda bayan saukar dukan farko da naji wasu masu yawa ma sun biyo bayan shi.

Nayi kamar in mike in fita falo don dai ya ji motsina ko zai saurara sai kuma na tuna da gaya mishin da Mama take yi wai ni din zamana a wannan dakin labe nake yi musu, komai suke yi shi da Innata ina jin su.

Don haka ya hana ni kwana a nan ya fito dani tsakar gida saboda tana son ganin ta rage karfin mu’amallar dake tsakanina da Mahaifiyata, wacce ta tabbatar cewar ni ce farin cikinta na wannan lokacin.

Bisa wannan dalili yasa nayi shiru, na sake komawa na kara labewa kan gadon namu sai dai hawaye da suke ta gudu kan kumatuna.

Ban san dalili ba, Inna ta ki kuka wanda in da tayin watakila da dukan da yayi matan bai yi tsanani haka ba, don watakila yaso tayi kururuwa ta yanda Mama zata yi abinda ke faruwa don tasan shi din yayi hukunci kan karar da ta kawo mishi.

Duk da Babana ya daina dukan nata, ban kuma ji wani motsinta ba, kwana nayi idona biyu ina kuka, don haka ina jin bude kofar da yayi ya fita sai nima nayi maza na diro daga kan gadonmu na fito na shiga wurin Inna don ganin halin da take ciki.

Cikin rawar jiki da rawar murya saboda kukan da nake yi na ce mata “Sannu Gambo.” Bata amsa min ba, sai ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min “Dauki Aliya da Sa’adatu ki dora su suyi fitsari ki wanke musu baki.”

Nayi maza na ce mata “To” naje nayi yanda tace din, har na idar da Sallah na zo na gaisheta bata motsa ba daga yanayin da na barta, ban dade da tsayawa a wurin ba sai kawai ga Hajiya Kubra ta shigo cikin zurmemen hijabinta.

Ga dukkan alamu daga idar da Sallahrta ta Asuba ta fito, ga alama kuma ita Innan ce tayi amfani da wayarta ta hannu ta kira ta.

“In ce ko dai lafiya Fadima?” sunan da take kiranta dashi kenan, ta ce “Eh, lafiya Umma.” Na durkusa na gaishe ta na juya na fita, musamman ma da yake ban ganta cikin yanayin fara’a da walwalar da na saba ganinta ba.

Don haka na koma dakinmu na zauna ina tunani, tunanin da zan iya.

Mijin Ta Ce 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×