Dama kin yi hankali kin yi karatun ta natsu ki gane bata kanki da bakin kishin gidanku ya kamata kiyi ba ta wadannan yaran ya kamata kiyi ki tsaya kiyi musu tarbiya ki tsaya musu da addu’a, Ubangiji ya raya miki su ya kuma basu mazan da za su rike su.
Shima wannan yaron Mallam yana nan yana jiran shi don Alhaji Yahaya yaje yaga yawa Mallam irin bakaken maganganun da ya rinka gasawa mijinki sakaryar yarinya kawai shashasha mara wayo.
In sake jin kin kai wata magana can gidanku za ki gamu da ni, in kina da matsala ki kai wurin Mallam Yahaya tunda ba shi da wani daban a cikinku, ta tashi ta fita ta bar Inna tana ta faman kuka, nima jikina yayi sanyi.
Can cikin zuciyata na dan ji tausayin Baba karo na farko da na ji hakan a game da shi, ko wadanne irin bakaken maganganu Alhaji Mai kudin ya yi ta gasa mishi oho.
A wannan lokacin sai na samu kaina da jin tausayin Babana, maimakon tsananin jin z afin shi da da nake yi, a yanzu sai na gane ma fi yawancin abubuwan da suke faruwa a gidanmu ba sonsu yake yi ba, illa iyaka dai ba shi da yanda zai yi an riga an sha gabanta.
Ta haka sai na koyi daina ganin anyi abu in gayawa Inna in ta ganan wa kanta kuma in bata hakuri in naga da Babana a cikin abin kuma in ce mata kar kiyi fada dashi Inna daina gasa mishi maganar da zata bata mishi rai.
Kinga dai kin hana shi hirar dakin Mama ya daina duk da tsananin hakan a wurin shi tunda kina jin irin habaice-habaicen da take yi. To kyale shi haka komai yayi, kiyi hakuri ta ce min to.
Ta haka sai Inna ta rike kwanakin girkin ta guda biyu sune nata in ta shige su zata yi komai don farantawa mijinta in ta fita kuma bata sake daga ido ta kalli Baba balle har ta gane wane abin haushin yayi?
Gashi tunda muka yi wannan tsiyar da Zubaida tana shakkar gaya wa Inna magana, sai dai kuma wani abin can daban, don haka har yanzu Mama bata gamsu ba daina zuwa hira dakinta ran girkin Innata ba karamin tayar mata da hankali ya yi ba.
Ban san yanda aka yi ba sai kawai gani nayi Babana ya sake taso ni a gaba kan maganar gaida Zubaida, Inna ta ce min rinka gaishe ta na ce mata to. Kullum zan tsaya a kofar dakinta in gaishe ta ko kuma a tsakar gida, wata ran ta amsa wataran tayi kamar bata ji ba.
Rannan na fito daga dakinmu da safe naga Mama da Babanmu akan katuwar tabarma sun hadu har da Zuwaira suna karyawa. Na tsuguna na gaishe su dukansu har na mike zan tafi sai Mama ta ce. “Humaira mai gaisuwa yau da yake da Babanku a wuri ita ma Zubaida ta ci arzikinshi an gaishe ta.”
Nan da nan Babana ya tunzuro ai bata gaishe ta ko? Mama ta ce uhun to ai gata nan kusa da kai menene na tambayata ni? Ya juya wajen Zubaida da tanbayar ta gyada kai ta ce mishi eh.
Nan da nan ya shiga banbami yana fadin za ki gani zan nuna miki duk abinda ki ke yi ina kyale ki ina yin hakanne kawai don kaina ba don tsoron wani ba, ba kuma wani ne yake sa ni nake yin abinda nake yin ba, don na ji ana cewa wai ni bana amfani da ra’ayina sai na wanda aka tsara min.
Akan gaida Zubaida ne aka kafa min dokar da ta hana ni zuwa Makaranta gaba daya tun daga ta boko har zuwa ta allo saboda wai ina karasawa can gidan su Innata wai kuma a can dinne ake koya min mugayen halayen da kullum nake fitowa da sababbi.
Ko ba a gaya min ba ni na san Mama ce tasa aka hana ni zuwa Makaranta daga baya ma aka ce an cire ni don dama tunda muka zo aji biyar muka yi jarrabawar kwalifayin aka ce ni kadai ce naci, ni kadai ce Gwamnatin jiha zata biyawa jarrabawar (WAEC) da (NECO), su su Habiba da Suwaiba sai dai in iyayensu sun matsu da su rubuta su su biya musu ko kuma su sake maimaitawa zuwa badi.
Ta sanyawa karatun nawa kahon zuka ta tsani ganin na shirya zan tafi Makaranta tunda su su Habiba sun daina zuwa sun ce son kai aka yi musu saboda Malaman namu sun san Mallam mai babban allo.
In tsaya cewa nayi bakin cikin hana ni karatuna ma bata lokaci ne kawai tunda ina son yin shi Inna ma tana so in yi gashi yazo karshe aji shida nake.
Inna ta kalle ni ta ce, to ke ki rinka sammakon zuwa gaishe ta a gabanshi mana don ya yarda kina gaishetan, ya barki ki rinka zuwa karatunki. Na ce ba zan sake gaishe ta ba Inna ya hana ni yin karatu don na daina gaida ita in rayu cikin jahilci shi kenan ina ce sai bukatarshi ta biya.
Tayi maza ta ce hauka kike yi ne da kike gaya mishi irin wadannan maganganun, naja bakina nayi shiru illa iyaka ban iya hana hawayen da ke zuba gudu a idanuna ba, Inna tayi tayi in canza daga matakan da na dauka na daina gaida Zubaida har Maman ma sai in jera kwana biyu ni ba ta ga idona ba.
Rannan ina jin ta tana cewa wata kawarta muu ai ta riga ta rika, kin san ita ‘ya mace in ta riga ta dandani gardin namiji to shi kenan rashin kunyarta sai ta buwaya.
Kawar tata tayi dariya ta ce, Mama kenan wannan wani namiji ta sani? Rashin kunyar ‘ya’yan yau dai kawai, da in suka riga suka fara girma sia kaga kamar menene? Balle wannan ja’irar yarinyar da kullum ka ganta ka ra kyau take yi tanfar wata mai rikida.
Ai da gani ake tanfar kannenta za su fita, amma kin gani da yake dai kawai shi mai kyau to Allah ke ganin dama ya yi shi, ga kuma uwa uba tsabta da iya kwalliya.
Mama ta ce uh, ai ku ku ke kara zugata amma in ba zuga ba to wa tafi kyau cikin yaran gidan? Nan in da kike ganinta ma lakaci guda daya bata dashi in dai na kirki ne to ina kyau yake?
Abinda kullum ake yi min gori dashi kenan rashin saurayi shekaruna goma sha bakwai a dunmiya amma ban taba saurayi ba ko a gida ko a hanya wani bai taba tsare ni ya ce min ke ‘yanmata ji mana, wa sunanki, sonki nake yi ba a taba yi min hakan ba sai dai in ga sa’annina da ma wadanda ba su kai ni ba da yawa ma nafi su kwalliya dama kayan kwalliyar don ni din ma’abociyar ado ce da kuma kayan adon saboda Hajiya Kubra da dangin Inna da suka maida sai min kayan kwalliya tanfar ni kadai ke gare su.
Ko da Babana ya daina hirar dare a dakin Mama ran girkin Innata hakan ba yana nufin babu matsala ba ne, a’a suna nan birjik basa ma lissafuwa, babba daga ciki dai akwai mindira mana abincin da Mama ke yi kusan kullum a cikin neman abin da zamu ci Inna take.
Babu kuma halin Mama ta dora tukunya itama ta dora ba ma zai yiwu ba, don haka sai dai ayi ta kame-kame, gashi kuma wai Mama ta ce sun yafewa Babana hidimar kanana-kananan abin bukata na gida dangin su omo, sabulun wanka da na wanki.
Man shafawa har su kayan Sallar yara saboda wai hidima da nauyi sun yi mishi yawa, kowa ya yi wa ‘ya’yanshi kan hakanne yasa Inna ta ce to ko za a rinka yin wadataccen abincin da yara zasu rinka koshi.
Tun kafin Babana ya yi magana Mama tayi, Mama ta ce ai yanzu nan duk irin abincin da ake yi a gidan nan yara sun ce miki basa koshi? Tirkashi, ina yaran suke? Su zo nan su gaya min su wanene ba sa koshin?
Yanzu ashe a irin kokarin da Alhaji ke yi na ganin asiri ya ruhu har da wani mai korafi akan abinci? Baba ya ce, ai Binta kam akwai korafi akwai mita, akwai fitina. Ta dai ce ga abinda aka yi mata yauwa! Ko ga abinda ba ta yarda dashi ba uhun!
Mama ta ce, to kaga, maimakon suzo suna yawo dakai a gari suna bata maka suna tunda su zuriyarsu bata rufin asiri ba ne raba girkin nan kawai kowa ka ba shi nashi. Baba ya ce, a’a ai sai dai suyi abinda zasu yi amma ba zan raba girkin gidana ba.
Ta ce, ai kuwa da ka raban da yafi maka ni da Zubaida muna hade tunda ita ai ba mai matsala ba ce, tunda tazo gidannan ka ji tayi da wani in ban da su da suka matsa mata? Ya ce haka ne, ta ce to ware ka bamu namu itama ka bata nata taje tayi tayi tana baiwa ‘ya’yanta suna ci suna koshi.
A haka aka raba girkin gidanmu, Inna ita da ‘ya’yanta su kuma girkin su yana hade ita ce kuma mai yi tun daga ranar da aka raba girkin kuma ya zama komai Babana ya kawo tanfar wawashe shi ake yi.
Tun daga hatsi zuwa kayan hadin, Babana da komai suyo shi yake yi ya ajiye sai aka ba shi shawarar daina sayen komai wai ya rinka bada kudin kawai ya kuma yarda kudinsa biyun namu duk da ba ninka mu suka yi ba a yawa sai dai wai su din manya ne, a kullum aka bamu kudin namu sai mun zauna ni da Inna mun yi ta lissafin yanda zamu yi mu sarrafa su ta hanyar da za su ishe mu, amma ina!
Ta yanda duk muka juya su basa wuce abin karyawa sai ko kudin awon hatsi kudin cefane kullum sai ta nema ga sabulun wanka da wanki ga man shafawa duk wadannan al’amura da Mama ta kawo Babana sai ya mance da cewar ita manyan ‘ya’ya ke gare ta, ga kuma uwa uba kaninta akan dukiyarshi wanda kuma a cikinta suke yin komai.
Don haka maimakon Inna ta samu sauki sai ya zama kullum matsalolinta karuwa suke yi, kullum ka ganta a rame ramarta kullum kara yawa take yi.
Inna mai dabi’ar wanki kullum sai ta zama yanzu tarawa take yi sai randa ta samu omo ko sabulu tayi ban kuma san dalili ba, ko Baba ya gane a yanzu babu abinda Inna take so ne irin zaman gidan nashi.
Kusan kullum sai ka ji shi yana kafa mata wata sabuwar doka tare da fadin zaman nan fa ba dole ba ne in da takura a ciki a bar shi, tuni ya daina cin abincin da muke girkawa a dalilin wai bakin shi baya iya cin abinda bai da dandan.
Don haka kullum Mama ce mai ba shi abinci, zancen kar ya yi hira a dakin ta ma kuma duk bai taso ba.
Tuni ‘yan uwan Inna suka ja suka tsaya kan sai lalle ta fita ta bar gidan wai azabar da ake gana mata tayi yawa, in miji yana son mace ai duk yanda ya kai da tsoron wata matarshi bai yi mata irin wannan azabar.
Tashin hankalin da su Inna Balki yayinta mata suka zo gidan suka yi yasa Babana yin amfani da shawarar da Mama ta bashi na kai maganar gaban mai babban allo ko don ya jarraba dattakunshi ya gani tunda yayi alkawarin randa duk suka sake zuwa gidan aka yi fada dasu to zai haramta musu zuwa gidan.
Yana zuwa kuwa ya zartar da wannan hukuncin har kuma akan Hajiya Kubra da take matsayin uwa rta, sai ta nemi izininshi gaba daya ‘yan uwan Inna suka dauke kafarsu suka kuma dauki mataki mai tsanani a kanta wai mijinta ya hana su zuwa wurinta.
Ita kuma tana zaune bata fito ba in ya soma daga baya ta koma amma dai sun san ta nuna rashin jin dadinta kan wulakancin da yayi musu, don haka duk wani taimako dake zuwa daga wurin ‘yan uwanta ya katse, ba sa ma zuwa balle su ga halin da take ciki.
Ita kuma dama ba zuwa take yi ba, balle kuma yanzu da haka ta faru ko ta tambaye shi zuwa wurinsu sau ashirin baya bari in yaga zata matsa ma sai ya ce da izinina dai na hana in kuma kin ga za ki da naki izinin shi kenan.”
Mallam mai babban allo ne kawai yake dan kewayo mu yazo mana da dan abin hasafi har ma ya bamu kudi sai ko Baba Yahaya.
Burin Inna a wannan lokacin bai wuce taga an yi aurena ba, tana gidan kullum ta kan gaya min in Allah yasa naga an yi bikinki lafiya to zan koma gidanmu zan koma wurin iyayena da dangina ba zan iya rayuwa babu su ba, in na ce to Inna su kuma su Atika fa? Sai ta ce uh’uh, su ko na bar su babu komai ba za su samu kansu cikin matsala mai yawa ba kamar ke, yanzu ina nan ma yaya? Balle kuma ace babu idona a kusa?”
A yanzu duniya tayi matukar yiwa Mama dadi sai wani irin kiba take karawa a daidai lokacin da Inna ke neman lami ta baiwa ‘ya’yanta ta dai samu suci su koshi kar su kwana da yunwa, wata rana bata samu.
Ita Mama ta daina cin naman saniya sai kaji saboda Ado ya karbe ta cefane, ita da bakinta naji ta tana gayawa kawayenta ai ita yanzu ta huta, Ado ke yi mata komai tun daga cefane zuwa sauran hidimominta ‘yan kudin da Alhaji ke bayarwa ajiye su kawai take yi saboda ba ni banin yara, ka’ida ne in sun miya da kaji da daddare to da safe kuma za su karya ne da farfesun kifi ko na bindi.
Gashi kuma ba za su zauna a falonta su karya ba sai ta ce wai ina dalili? Gara dai a baza katuwar tabarma a tsakar gida kowa ya baje, nan za su baje har da Babanmu da zai ga wucewar Sa’adatu ya dan gutsuro wani abu cikin abinda suke ci ya mika mata sai ta ce Alhaji kenan, to kasan abinda suka ci a dakinsu?
Ta manta cewar ko da ma me muke ci din muna da hakki cikin nasun tunda da kudin ubanmu ake yi, Ado bai da wata harka ko sana’ar da zai saman mishi kwabo in ban da zaman shagunan Babanmu da yake ji ko kuma zuwa mishi aika zuwa aikan da zai yi wuya ace sau goma ba a dawo an ce ga wani abin da ya samu kudin da aka yi akan da su ba.
Haka kuma dole Babana zai hakura don kar Mama ta tambaye shi Alhaji ba ka san asara ba ne? to wane bincike zaka tsaya yi a kanta in dai ba so ka ke kayi abinda zaka zobe ladanka ba?
Na tsani Ado, na tsani in daga ido in ganshi a cikin gidanmu gani nake tanfar har da shi cikin abubuwan da suka yi dalilin shigar mu da Innata cikin halin da muke ciki, gashi don raini da wulakanci sai ya shigo gida ya gaida Mama da Zubaida ya juya ya fita bai gaida Innata ba.
In har da wani abinda na ki na kuma tsana cikin zuciyata to bayan Mama kanin nata ne.
Rannan ina dakinmu a kwance cikin dare ban san Babana ya shigo dakin Inna ba, don a yanzu ranar da yaga dama ne kawai yake zuwa wurinta, ko da kuwa kwanan nata ne sai ya shige wurinshi yayi kwanciyarshi.