Salatin shi na jiwo da karfi tare da jan tsaki mai tsananin karfi, kafin ya soma fadin “Kai wannan fitina da yawa take, ni Surajo naga abin da ya ishe ni, kin gani Fatima, tun dai ni a wurinki na gajiya ba kya ganin kokarina bare alherina komai nawa a raine yake a wurinki, bani da fita a wurinki ba ni da shi a gun danginki kiin zo kin same ni cikin iyalina kin takura mana kin tasa mu a gaba da dokoki komai aka yi ki ce baki yarda ba kin watsa min hadin kan gida kin raba min kan ‘ya’yana sannan a hakan baki gamsu ba.
To in kin ga har yanzu kina da matsala to za ki koma gidanku ne kawai, donni na gaji na gaji abin ya ishe ni haka. Ya balle kofar ya fita cikin daren har ya isa dakin shi bai daina mita da fadin maganganu ba.
Inna ta mike tana hada kaya a cikin daren nan fito na same ta tana yi tana kuka watakila yau ma so take ta tafi ban sani ba, tana ganina ta soma share hawayenta na ce mata kar ki tafi Inna, za ki je gida ne ki haihu a can?
Kin san dai in kin tafi yanzu ba bin ki zai yi ba, ‘yan uwanki kuma ba za su dawo da ke ba, kiyi hakuri ki daina gaya mishi damuwarki kiyi mishi shiru kawai, ba ke ma kina da abinda kike shiryawa ba? Ta gyada kai nuna alamar eh, na sake ce mata to kiyi hakuri ta ce min to.
Na koma dakinmu na kwanta cikin zuciyata tunani nake yi burin Inna bai wuce ta yi ta hakurin zaman gidanmu har zuwa lokacin da zata ga an yi aurena, in yaso sai ta tafi, ita a ganinta don ta bar su Atika ba komai ba ne don su basu da irin matsalar take ganin ni ina da ita.
To amma yaushe? Yaushe za’ayi auren nawa tunda ni ko saurayi guda daya ban taba yi ba, ban taba samun saurayin da ya kalle ni ya ce min ke ‘yanmata ji mana, me sunanki? Ni fa sonki nake yi ba balle a ce an zo kofar gidanmu ana kirana balle har a biyo ni da wani dan hasafi kamar yanda kullum nake ganin ana yi wa su Habiba a kowane lokaci naga Mama tana nuna wa Inna irin hasafi da ake yi wa su Habiba wanda a ciki zanga har da sabulayen wanka da na wanki har ma da su omo sai in ji zuciyata tana cewa ina ma nima in samu saurayin da zai rinka yi min irin wannan kyautar da Innata ta huta da tara wankin da take yi tunda nasan tara wankin yana cikin lissafin damuwoyinta.
Amma Mama sai ta nuna mata ta kwashe su duka ta yi tafiyarta da su ba za ta bata ko kwalli daya ta ce ta wanke kayan kannen su Habiba ba, duk da addu’o’in alherin da take yi musu in ta ganni tanfar dai wacce ake yi wa kwalele.
Rannan cikin dare Inna ta haihu yau ma da namiji muka sake samu ni da ita mun yi murna Baba karami shima ya samu dan uwa sai da na tayata ta yanke wa yaron cibiya ta yi mishi addu’o’i ta nade shi a zani ta bani shi na kwantar dashi na juye mata ruwa taje wanka na dawo na nade ledar da ta shimfida ta haihu akai na goge komai na gyara shi tsaf.
Na kawo mata ruwa don ta wanke shi ta kalle ni ta ce min wanke shi ki koya nace ah Inna ai ba zan iya ba ta ce koyi na zauna na wanke shi tsaf ina yi ina canza mishi ruwa har sau uku da na gama na shafa mishi man da muke shafawa na kuma sanya mishi riga cikin rigunan Baba karamin da Inna ta adana don shi kam bai samu an sai mishi komai ba.
Na kalle ta na ce, mata to me za ki ci? Ta ce babu komai ai bana jin yunwa tausayinta ya yi matukar kama ni don na riga na saba ganinta tana cin abinci da na sha mai yawa idan ta haihu sanin da tayi ba mu da komai a dakin shi ne ya sanyata ce min ba ta jin yunwa.
Naje na tsiyayo ruwan dumi a flask na sa mata suger kadan da lipton na kawo na bata ta karba ta kwankwada, ta ce min to sannu je ki ki gaya musu na ce to naje na kwankwasawa Mama kofa.
Babana ya fito daga dakin Zubaida saboda jin kwankwasa kofar da nake yi, yaya lafiya? Na ce mishi Inna ta haihu, Mama ma ta bude ta haihu ne ko zata haihu? Na ce mata a’a ta haihu ne.”
Ita da Babana suka yi hanzarin shiga dakin na tsaya a tsakar gida sai da naga sun fito daga dakin sannan na shiga.
Washegari da sassafe Hajiya Kubra ta iso gidan saboda aiken da aka yi musu cewar Inna ta haihu, a wannan haihuwar gaba daya dangin Inna babu wanda ya leko ta daga Hajiya Kubra sai ko Hajiya ‘Yar dubu, sau biyu ina jin Inna tana gayawa Babana cewar tana so a sanya mata sunan Babanta wato a yi wa Alhaji Mai kudi takwara, amma ranar sai kawai na ji Mama a tsakar gida tana fadin wai Ado aka yi wa takwara, don haka sunanshi Adam.
Ai kuwa dai Mama a irin hidima da dawainiyar da yake yi da gidan ai gara da ki ka sa aka yi mishi takwara, in ji Zubaida. Cikin zuciyata na rasa abinda zan ce iyaka dai sai naga kai ni kam babu ma dai abinda ya dace da ni illa in fidda raina kan tunanin aure da ma sha’awarshi.
Tunda ma na riga nayi sa’a bani da samarin tunda in dai ma aure irin na gidanmu ne nima haka za aje ayi min irin yanda nake ganin ana yi wa mahaifiyata, to ai ina ganin barinshi kawai shi ne zai fiye min sauki tunda bana ganin kamar zan iya irin hakurin da take yi.
Duk da bacin ran da na samu akan sunan da aka sanyawa yaron nayi wanka nayi kwalliya saboda Innan bata dauki sanya mishi sunan Ado da wani zafi ba, ta ce kowane mutum da sunanshi yake zuwa.
Da hantsi na fito bayan nayi kwalliya sosai don in ma muna rashin komai to ni kam bana rashin kayan kwalliya gidan Anti Ramla nayi nufin zuwa don babu wani abin armashi da na gani a sunan namu, sai nazo wucewa ta falon Mama karaf sai na ji tana ce wa manyan kawayenta da suka riga suka zo mata sunan, ai bata ga komai ba tukuna ai sai na nuna mata ni din ni ce ai sai na sata tayi nadamar auran mun miji da tayi.
Gabadaya suka kwashe da dariya cikin zuciyata na ce, oh’oh ko me zata yi wa Inna wanda ya zarce wanda take yi mata a yanzu oho? Tausayin Inna ya sake kama ni da na tuna duk da halin da take ciki bata nadamar auren Babana da tayi na kuma tabbatar a zuciyata ko ma me Mama zata yi ko tasa ayi mata ba za ta iya sata tayi nadamar da take cewa zata sa ta tayin ba.
Tunda ita da bakinta ta ce min bata nadamar aurenshi domin ta haife mu a tare dashi, don haka ta gamsu da koma menene.
To ban san me Mama ta fada musu ba, watakila don na shagala da tunani to amma na ji Hajiya Anwamu tana ce mata uh’uh Mama, uh’uh kar ki fara, kar kiyi wannan abinda kike shiryawa, ba don komai ba sai don kowa yasan wannan yarinyar ita ce uwarta.
Kinga kuwa tura in ta kai bango to bata cika dadi ba, ita kuwa wannan yarinya da kike kallonta yanda fa bata yi kama da uwarta a halitta ba haka nan ko kadan halinsu ba daya ba ne don haka kyale mata ‘yarta kawai ai kin samu ina laifi wata da nakuda wata da fadin sunan da?
Ban da haka ban da haka ko hana ‘yan uwan yarinyar nan zuwa in da take da kika yi ai ya ishe ta.
Ina fita waje Habiba da Suwaiba na gani suma sun sha kwalliya kamar in wuce su in yi tafiyata sai na tuna maganganun da na bar uwarsu tana fadi, don haka sai na matsa kusa da su na same su.
Suwaiba dai tuni ta riga ta tsorata dani, don sau biyu ina yi mata dukan tsiya. Na isa wurin kenan sai na hango Ado yana fitowa daga cikin gidansu yasha kwalliya yayi matukar yin kyau, kallo daya nayi mishi na kawar da idona daga gare shi.
Na kalle su na ce musu, me na ji ku kuna fa da dazu? Habibna ta ce, abinda ki ka ji muna fadin shi… kan ta gama nayi maza na café bakin nata nufina wai in yi mata yanda itama da take yi min, sai Ado yayi maza ya karaso yana fadin.
“Kai, kai ku bari ku bari, ke fa fitinanniyar yarinya ce.” Yana maganar yana nuna ni da dan yatsa, na galla mishi harara na yi mishi wani lalataccen kallo na sama da kasa sai da na murguda mishi baki kafin na ce mishi dadin abin dai a gidan ubana nake fitinar duk iyayin mutum bai da yanda zai yi dani tunda shima zaman cin arziki yake yi.
Bina da kallo Ado ya yi, kallo kuwa mai tsananin cikin kaduwa da mamaki bai taba sanin zan iya yin abin da nayin ba. Nasa kai na wuce nayi tafiyata, daga shi har su Habiba babu wanda ya ce min kala.
Ban dawo gidan ba sai da yamma, nazo na samu Hajiya Kubra tazo ta tafi ga kuma kayan da ta kawowa Inna zannuwan da ba su wuce goma ba, sai kayan jarirai babu wani yawa suma sai dai ta kawo mata kudi masu dan auki wai ta rike a hannunta saboda hidimar yara.
Tun ban gama zama ba Inna ta soma tambayata me yaron nan yayi miki kika zage shi? Na ce shi yazo ya gaya miki na zage shi? Ta ce a’a su Habiba ne suka gaya wa Mama shi ne ta ce min in gaya miki kar hakan ya sake faruwa.
Don haka kar ki sake, na ce an zagi Ado Inna suyi abinda za su yi an zage shi, Inna ta zuba min ido tana kallona zata yi min magana na ce mata kar kiyi min fada akan shi Inna ki bar ni kawai ‘yan abu kazan uba na sake mulmulo wani ashar din na antaka musu.
Shiru tayi tana bina da kallo saboda ita ba mai son tashin hankali ba ne, na nemi wuri nayi kwanciyata ba tare da da na gaya mata hirar da na ji Mama da kawayenta suna yi ba.
A yanzu Habiba ma shakkar haduwarmu wuri daya take yi, don ta gane babu abinda nake so irin danbe ya hada mu ta kuma riga ta tsorata da wadanda take ganin mayi, don haka ta daina shiga harkata balle aje ga tsokana.
Rannan mun hadu da Ado a wajen wani biki da abokan Baba suka hada ‘ya’yansu aure, don kara karfafa zumuncin da ke tsakaninsu, dukanmu mun je har da su Habiba mun kuma sha kwalliya don mu a gidanmu kwalliya muke har da ta gasa.
A yau din kuma na burge kwarai don har da zinari nayi adon saboda Hajiya Kubra ta dawo daga Ummara, don haka ta sayo min dan kunne da sarka har da zobe masu kyau da kuma girma kirar Dubai.
Cikin kudin Innata dake hannunta wanda take sawa ana juya musu, to Ado ma yana cikin abokan ango ya kuma sha kwalliya don ya iya sanya sutura mai tsada gashi kuma kwalliyar tana yi mishi kyau, don ya riga ya koshi ya zama saurayi mai kwarjini da nagarta.
Wata yarinya da muke tare da ita Sadiya ita ce ta ce lah, su Humaira ga kawunku sai da na waiwaya bayana muka hada ido dashi sannan na juyo na kalle ta ba kuma tare da na ji kunyar Habiba dake tsaye a gefenta ba, na ce mata uh’uh Sadiya ba kawuna ba dai kawun su Habiba ne, ai ni babu wani abin da ya hada ni da shi in ban da zaman cin arziki da yake yi a gidanmu.”
Sum-sum Sadiya tayi ta bar wurin don ta san Ado ya ji abin da na fada su kuma suna girmama shi saboda ya iya kama kanshi, ita kuwa Habiba ta kama fuskarta ta tsuke alamar rashin jin dadi, sai dai bata tanka ba.
Nima na ci gaba da harkokina, ana bude falo aka soma neman ‘yanmatan da za su taka rawa na fita, ba tare da na damu da tsayuwar Ado a wurin ba, don dai in nuna mishi bai da wata kima a wurina.
A wannan lokacin kusan kowane lokaci Mama bina da kallo take yi cikin takaici da kwafa ban dai san dalili ba ko tasa mata ‘ya’ya da nayi a gaba ne su Habiba da Suwaiba wadanda a baya suka yi matukar takurawa rayuwata tana kallo, oho.
Sati guda da gama bikin gidan su Sadiya ranar ma ranar wata Juma’a ce, nayi niyyar zuwa gidan Mallam mai babban allo wanda na dade ina nerman izinin zuwan wurin Babana bai bani ba sai yau. Don haka kwalliya sosai na yi na fito daga gida.
Ado da wani abokinshi Nasiru suna tsaye a inuwar bishiyar kofar gidan mu, ina jin sanda Nasiru ya cewa Ado kai kai kai yarinyar nan haka ta zama? Ado yayi maza ya kawar da kanshi can gefe ga barin kallona.
“Menene na wani kai kai kai? Sai ka ce ka ga wani abin da baka taba sani ba, in ka naso ka wai kayi magana shi ke nan dama ba wani saurayi ne da ita ba, ‘yan uwanta gaba daya sun samu manema har an kawo sadakinsu amma ita babu kowa babu wani malalacin.”
Nasiru ya ce, ai yarinyar ce kwarjini ne da ita gata bata bada fuska in ka dunfareta da nufin yi mata magana ma dole ka daina don gabanka faduwa zai rinka yi. Ya yi tsaki ya ce, ka zama ragon maza kenan, don haka tunda kana cikin wadanda take fadar wa da gaba to bari zan yi maka iso a cikin gidan in yaso ko baka zo tadi ba nasa a daura auren a kawo maka ita har gida sadaka.”