Skip to content
Part 12 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Nasiru yayi dariya ya ce, wannan shi ne zance ka dai yi ne don ka ji ta bakinta tun yaushe ne ma aka daina yin sadaka da ‘yanmata balle kuma irin wannan mai tsadar.”

Ado ya ce, in na dai an daina yin sadaka da ‘yanmata to wannan kam zan iya sa wa a baka ita, in kuma kana musu to zuba ido kawai kaga abin mamaki.

Wucewa nayi na tafi zuciyata a cike da bacin rai mai tsanani a dalilin jin maganganun cin zarafi da Ado yayi min a gaban abokinshi babu abinda yafi komai kara min bacin ran kuma irin sanin da nayi cewar duk maganganun nashi akan gaskiya suke.

Bani da saurayi su Habiba da Suwaiba an kawo sadakin aurensu sannan shi din da zai nishadi ya ce wa Mama yana son a baiwa Nasiru abokinshi ni, ina ganin babu abinda zai hana ayi hakan tunda shi ne Mama, Mama kuma ita ce Babana.

Har na isa gidan mai babban allo ban gama wastsakewa daga wannan bacin ran ban gama wastsakewa ba sai dai ina shiga wajen shi na soma murmushi a dalilin son da yake yi min, ina isa gabanshi bacin raina yake gushewa.

Fura na samu yana sha, don haka na zauna muka sha tare ina mitar babu sugar ni ya barni in sa kodan kadanne shi kuwa yana fadin ai ba zai yiwu ba don ba zan bar ki ki bata min ita ba sai dai in ki kawo wani abin in diban miki naki sai ki sa duk abinnda kike son sakawa, na ce a’a tare da kai zan sha ya ce to kuwa sai kisha mara sugar.

Ya gama shan furar yana kallona ina karasa, sahan wacce ya bar min sai naga yayi murmushi na ce mishi menene Mallam? Ya ce kallonki kawai nake yi ina tunaninki sai aukin kwalliya da iya lankwasa amma har yanzu ban taba ganin wani yazo ya gaishe ni ba a cewar ke kika turo shi na ce azo a gaishe kan?

Yayi maza ya ce zan kosa mana Aisha in ta samu aka kan dake din ai zata samu dan wani saukin. Na ce uh ni in ban da saboda Inna da kuma gorin da ake yi min mafa Mallam ni auren nan ba wani son shi nake yi ba.

Ya dan gyara zama kadan ya ce aure kuwa ai abin so ne Aishatu, Ibada ne kuma rufin asiri ne ina ce kina karanta surorin da na ce miki kullum? Na ce eh Mallam kullum sai na karanta (Yasin) in karanta (Arrahaman) in karanta (Waki’a) sannan in karanta (mulk).

Yayi murmushi ya ce, madallah ashe kokari ne da ke to rinka hadawa da (La haula wala kuwata) kafa casa’in da tara take yi karami daga cikin magungunan nata shi ne bakin ciki na ce to Mallam na gode, muka dan yi hira na mike na ce mishi bari in shiga ciki in gaishe su don in zo in tafi ya ce min to.

Na gama abinda zan yi a cikin gida na dawo wurin mai babban allo zan yi mishi sallama sai na same shi tare da Alhaji Abba, wasa dani da yake yi tun ina ‘yar karamata ya sani sakewa nima nake wasan dashi a matsayin ‘yar Inna da dan kawu don shi ya ce Inna uwa ce ba ‘ya ko kanwa ba.

Na kalle shi cikin murmushi na ce, ah, ka ce ka ji nazo ne ka biyo ni? Ya yi wata irin dariya kafin ya kalli mai babban allo ya ce ni Mallam in ce ko dai wannan irin kwalliya da ake tsalawa tana biyan kudin sabulu?

Mallam yayi dariya ya ce, to ina fa na sani tunda ni har yanzu ban gani a kasa ba, ya kyalkyale da dariya jin dadin abin da Mallam din ya fada, ya ce to ko dai ni zan soma zuwa gaishe kan ne kawai Mallam don ka gani a kasan? Mallam ya ce a to ga ka nan ai ga ta ku kuka san saura.

Alhaji Abba ya kalle ni cikin yanayin murmushi da zolaya ya ce, Yaya ko zan fito ne kawai muyi ‘yar gida ko kuwa Mallam? Mallam ya sake cewa, ato, ai ga ka nan ga ta nayi murmushi na ce sha kurumin ka ni na da ka ke kallona  gal a leda zan aura.

Mai babban allo ya ce uhun’uhun ka ji sakarcin nata ba? Da wani gal a leda da ya wuce wanda zai rike auren yaga darajar iyayenki? Ban kula zancen na mai babban allo ba don naga zancen yana nema yayi nisa. Un, ban kudin mota Mallam ni zan koma gida don Babana ya ce kar in yi yamma sosai.

Eh, ai yana da gaskiya Mallam yashiga dube-dube yana kokarin tattaro duk kudinshi ya bani kamar yanda ya saba yi kullum.

Alhaji Abba ya karkace yana kokarin cusa hannunshi cikin aljihun wandonshi, kyale ta kawai Mallam bari in karbe ka ba da kudin motar nan a yau tunda ga dukkan alamu ma na fika ganin kyan kwalliyar tata ta yau.

Ya zaro kudin da bai kirga ba ya miko min nasa hannu biyu na karba, bai bari ya ji godiyar da nake shirin yi mishi ba sai ya ce min cewar da ki ka yi ni ba gal a leda ba ne ba fa ba zai hana ni biyo ki gida don tadin ba, bari in yi kwaskwarima in zo ki gani ki ga yanda zan zo miki a wani santalelen saurayi za ki gane wannan katuwar rigar da nake sanye da ita, ita ce ta hana ki gane ni din na ma fiye miki gal a ledan ba.

Mai babban allo sai faman dariya yake yi yana fadin har da su kwaskwarima a ciki kenan, ka yarda kai din ba gal din ba ne tunda sai ka hada da kwaskwarima. Suna dariyarsu ni kuwa na sunkuya na tsince ‘yan kudin da Mallam ya riga ya fito dasu, shi kuma sai fadi yake ka ganta ko? Ba kaga irin halin nata ba sai ta hada har da nawan ta kwashe.

Na isa gida gaban Innata cikin farin cikin gamuwa da Alhaji Abba da nayi, tuni na man ce da takaicin maganganun banza da Ado yayi min sanda zan tafi, na samo mana kudi Inna na gamu da Alhaji Abba ina murmushi nayi mata bayanin komai na debo kudin daga cikin jakata, kin gansu?

Na nuna mata itama tayi murmushi ta shiga yi mishi addu’a na gama lissafa su dubu goma sha uku ne na sake wani murmushin na ce mai kudi ne Abba ko kirga su bai yi ba ya bani. Ta sake wani murmushin cikin jin dadi ta ce, eh ai shi arziki haka yake ba daga yawan shekaru ba ne kyauta ce kawai daga mai bayarwan na ce haka ne.

Na dunbazu wasu kudin na mike zan fita don na saba in mun samu kudi bani kawai Inna take yi ta ce in sayo mana abinda nasan shi ne muhimmi, ina za ki da wadannan kudin?

Cikin natsuwa tayi min tambayar na ce mata sabulun wanka da na wanki zan sayo mana masu yawa don su dade basu kare mana ba, sai ko biskit da indomie saboda su Baba karami ba ta yi magana ba shiru tayi alamar ta amince kenan, na wuce na fito da nufin sayo abinda zan je sayowa.

Sai kawai na hangi Ado a falon Mama sun hada kai suna kus, kus, kus, ga alama kuma basa son wani ya ai abinda suke tattaunawan, gabana ya yanke ya fadi kar dai maganar da Ado yayi dazu a waje mai kama da shakiyanci ne yake shirin mai da shi gaskiya?

Har naje na dawo ba su gama maganar ba, hankalina ya yi matukar tashi don kuwa nasan Mama da Ado za su iya yin komai a kaina, don Innata tayi bakin ciki, tunda sun riga sun tsarawa kansu cewar ni din bata hada ni da kowa ba cikin ‘ya’yanta.

Nan da nan hirarrakin Mama da kawayenta da nayi ta ji suka rinka dawo min, rokon da suke yi ta bar wa Innata ‘yarta kar ta sake jefa ta cikin wani bakin cikin, ko ba a gaya min ba kuma nasan ba kowa ba ce wannan ‘yar ni ce.

To ga Ado ga kuma abinda na ji ya fito daga bakinshi gashi kuma na gansu suna tattaunawa, irin tattaunawar da suka saba yi in suna shirin kulla wa Inna wata kullalliyar.

A dakinmu na rasa yanda zan yi in gaya wa Inna da nake ciki tunda ita kuma a yanzu damuwarta ta ragu in ma bata gushe duka ba ta samu abinda za ta baiwa ‘ya’yanta su ci gobe da jibi da gata da citta, don haka sai kawai na wuce naje na hau gado can cikin zuciyata ina tunanin me zan yi wa Ado?

Me zan yi mishi in nuna mishi cewar ni ma din ta Maman ta ce kowa ya ci tawo da ita miya yasha. A yanzu kam madan ni kam ina ganin kamar zuciyata ta kai wani matsayi da bata da wani wanda ta ki ta kuma tsana take jin zafin shi take neman samun damar daukan fansa a akan shi irin Ado.

Washegari da sassafe Innata ta amsa kiran da Babana yayi mata a dakin Mama a gaban kuma Maman har ma da Zubaida.

A gaban Maman kuma da Zubaidan ya baiwa Innata wa’adi na kwana uku wai in fiddo da miji ya hada mu da su Habiba yayi mana don ba zai yi auren Habiba da Suwaiba ya bar ni a cikin gidan ina zaune ina zubawa matanshi rashin mutunci ba.

In ma dai mu bi wannan umarnin da ya bayar ne na kawo mijin cikin kwanaki ukun da ya ambata ko kuma mu tattara mu bar mishi gidan.

Mu ci gaba cikin yardar Allah a littafi na biyu tare suka fito.

<< Mijin Ta Ce 10Mijin Ta Ce 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×