LITTAFI NA BIYU
Na daga ido na kalli Gambo da hankalinta in yai dubu duka ya tashi, na ce “A’a Gambo, to menene na wannan tashin hankalin? Mu bar mishi gidan mana ina ce shi kenan magana ta kare?”
Ta yi maza ta rike baki nuna girman lamarin, ta ce “Magana kuwa bata kare ba, yau in da ni kadai ya ce in bar mishi gida to da ta kwana gidan sauki, amma budurwa kamarki ace ta bar gidan ubanta a dalilin shi din da kan shi ya koreta ai ba karamin al’amari ba ne, bata suna ne ba kadan ba.
Sai ayi ta nanata zancen har ‘ya’ya da jikoki, don haka ina ganin dai to maimakon ayi haka bari in koma kawai in ce mishi ko shi din zai baki mijin da yaga ya dace tunda ai Mahaifinki ne uba kuma dama yana da wannan damar.”
Da sauri na ce mata, “A’a Gambo, a’a ni kam gara kawai ki bar ni in yi tafiyata ban san abinda na yi wa Baba ba ya tsane ni, ya tsani farin cikina.”
Ta yi maza ta daka min tsawa, ta hanyar fadin “Ke kama bakinki, kiyi shiru ba ka gaya wa Mahaifinka magana ko da kuwa me yayi maka?”
Na ce mata “Haba Gambo, in ban gaya wa Baba magana ba me zan yi ba shi ya ja ba? Tayi maza ta wafce min bakina da duka abinda ya yi dalilin dana soma kuka sosai.
Tun ina yin kukan tana kallona har ta gaji ta soma rarrashina, daga baya ma ta shiga taya ni kukan, muka yi har muka gaji muka yi shiru don kan mu.
Na fito tsakar gida zan yi mana wanke-wanke daga nan in yi wanki sai na ji muryar Anti Kaltume a falon Mama alamar tazo gidan kenan, dama kuma su din don sun zo wuni gida basa zuwa su gaida Gambo sai in ta ji muryarsu ne zata leka ta ce musu “A’a su Kaltume kun zo ne? Su ce mata eh, su gaisa.
In kuwa lokacin tafiyarsu ya yi to in dai ba tana tsakar gida ba ne sanda za su tafin tayi musu sallama to zata shafa ne kawai bata gansu ba sai ta gane sun tafi.
Na wanke kunfan hannuna na nufi dakin Mama da nufin gaida Anti Kaltume, don ita tana cikin ‘yan dama-daman ‘ya’yan Mama, tafi Anti Sha’awa yi min adalci sanda nake karama, sai kawai na ji ta itama tana cewa.
“Uh’uh Mama bar mata ‘yarta, taje can tayi sha’aninta ita da ‘ya’yanta, mu ma a nan muyi namu, ai ba a kwacewa uwa ‘ya’ya, Mama ko an kwace su zasu koma.”
“Ko zan bar mata sauran dai wannan kam zan tabbatar na rike ta a hannuna saboda in har na barta taje ta sake, to ba karamin iya shege zata yi ba.”
Na yi sallama na gaida Anti Kaltume, na dan yi ma danta da take goyo wasa itama kuma sai kallona take yi, tanfar dai wacce bata gama sanina ba, ‘yar gari wato kenan yanzu kin girma kin daina zuwa wurin mutane ko?
Na yi murmushi na ce, “Anti kenan, ban fa dade sosai ba ai ban kai wata biyu ba.” Ta miko min hannayenta duka biyu alamar dakuwa.
“Wata biyun ne ba ki dade ba? Ki zo kiyi min wanki kayan dattin ‘ya’yanki sun taru.” Na ce, “To Anti.” Na tashi na tafi. Ko kadan bana jin kyashin zuwa gidan Anti Kaltume in yi mata wanki ko ma wani aikin da yafi wankin wahala, saboda ita akwai hikima cikin lamarinta, tunda ta gane ina jin zafin zagin uwata da ake yi a gabana ta yi maza ta daina sabamin, Anti Sha’awa da sauran yaran.
Ina fitowa daga dakin naji Anti Kaltume tana sake cewa, “Ba fa zai iya da ita ba Mama, wahala kawai za a sha ki bar mata ita suje can su karata, in taso uwarta ba laifi tayi ba, mu ma duk muna sonki.”
Mama tayi maza ta daka mata tsawa “Tafi can shashasha, duk ‘ya’yana sun goyi bayan abinda na shirya sai ke saboda ke dama dole ce tasa kika yarda na haife ki in ban da haka da can wurin su kika fado wani so kike yi min?”
Komawa nayi dakinmu wurin Gambo don ya zama min dole in zaiyane wa Gambo irin maganganun da nake ji tunda ga irin furucin da Babana yayi na in fidda miji cikin kwanaki uku ko kuma mu bar mishi gida.
Gambo ta kalle ni cikin nutsuwa ta ce min, “Haka ne?” na ce mata “Eh.” Ta ce, “To babu laifi.” Tasa hannu ta dauki wayarta ta soma magana da Mamanta Hajiya Kubra, izini take so ta neman mata wurin Babanta don ta koma gida.
“Me ya yi zafi haka?” Ta kwashe bayani duka tayi mata, ta ce, “To zan yi mishi bayani in ji abin da zai ce, amma kafin nan sai ki sanar da Mallam Yahaya don kar ayi abin da zai ce ba a sanar da shi ba.” Ta ce, “To.”
Suna gama maganar, Gambo tayi fulashin din Baba Yahaya, ya kirata shima tayi mishi bayani, ya ce “To ai ba za’a bar gida akan maganar fitar da miji ba, ta fitar mana.”
Gambo ta gaya mishi gaskiya ai ni din bani da kowa ga kuma maganar da Ado ya yi wa abokinshi da kuma wadanda Mama ke ta fadi.”
Ya dan yi tsaki ya ce, “Bana son ki da irin wadannan maganganun Fatima, bana so in ace ance-ance yana fitowa daga bakinki.” Ta ce mishi “To.”
Rannan da daddare sai ga Jamilu dan Amaryar Hajiya Hairan yazo har cikin dakinmu ya shigo ya durkusa ya gaida Gambo, ya ce mata ni da Yaya ne, Gambo ta ce wannan yaron?” yayi maza ya ce, eh, ta ce to ina yake, ya shigo mana.” Ya ce, a’a yana waje yace ne wai in shigo in kira mishi Humaira.
Daga ni har Gambo kallon juna muka yi, don mun gane ma’anar kiran, Baba Yahaya ne ya turo babban dan shi sa’an Ibrahim dan Mama na biyu, don shi manyan ‘ya’yan mata ne Salisu su wanda Hajiya Hairan ke kira yaron nan, har su Gambo duk suke taya ta shine dan shi namiji babba yazo neman aure na.
Salisu yana daya daga cikin yaran da kullum Babana ke bada labarin natsuwarsu a duk lokacin da takaicin Baba da Ibrahim ya cika mishi ciki, yana shekarar karshe ne a karatun da yake yi kan harkokin kasuwanci a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, wato (A.T.B.U).
Sannan babu inda Baba Yahaya baya tura shi kan harkokin shi, sannan shine yake tafiyar da al’amuran gidansu gaba daya, in dai akan yara ne da yake su gidan su babu ruwansu da ‘ya’yan wannan dakin da na wancan gabadaya abin da suka sani shi ne ubansu daya to magana ta kare.
Bare-bare sosai muka kama yi ni da Gambo muna murna da farin ciki, yau na yi saurayi nima gashi an zo ana kirana. To shirya mana ki tafi yana jiranki kuma, na dan yi murmushi nan take kuma kunya ta kama ni.
Hijabin dana cire da nayi sallah kawai na sake maidawa na fita.
Yana tsaye a kofar gidanmu daga can gefe tanfar dai wani bako, na dan matsa kamar zan karasa kusa dashi na kuma kasa, saboda kunya da kuma jin nauyi.
Ya dan zuba min ido kadan cikin yanayin murmushi, shima dai kunyar yake ji ban fa taba zuwa tadi ba, ‘yammata na gaya min yanda ake yi in an zo.
Na taya shi murmushin da yake yi na ce mishi “Ai nima ban taba tadin ba.” Yayi dariya cikin wani yanayi da na san dariyar rinjayarshi tayi, ya ce, “Au to shi kenan ki ce min mu duka sabbi ne, na sake taya shi wani murmushin na ce mishi eh, mu duka sabbin ne.
Ya ce, to kin gani Humaira dama can mu ‘yan uwan juna ne, ko da Baba bai turo ni yau ba ma aka daura mana aure aka kawo min ke ai ina zaman kamar zamanmu lafiya zamu yi, to zamu ce auren dole aka yi mana?
Na ce, a’a ai ma ba irin tarbiyar da aka yi mana ba kenan.” Yayi maza ya ce “Yauwa, Humaira to na gode miki da ki ka san hakan, to in je in ce wa Baba dai ba matsala kenan?
Na yi murmushi na ce mishi, eh, babu matsala ya ce to shi kenan, yasa hannu a aljihun shi ya miko kudi zai bani na ce mishi a’a, ai tsakaninmu babu haka, ba sai ka bani kudi ba, sai da ya kalli kudin dake rike a hannun nashi ya saki wani lallausan murmushi kafin ya ce min.
Da dai ace kudina nayi nufin yi miki kyautar da su ki ka fadi haka to da sai in mayar dasu kawai cikin aljihuna in tafi, to amma kudin Inna ne addu’a kuma mai yawa tayi musu kafin ta bani su.
Na shiga dakinta zan yi mata sallama sanda zan taho nan sai ta dauko su ta bani na ce mata a’a Inna Baba ma ya bani kudin ya ce in rike na ce mishi don kudin da zan yi mata kyauta ina da su ba sai ya bani ba, sai ta ce min sa hannu biyu ka karbi wadannan nawa ne in kaje su nake so ka bata.
Don haka sa hannu biyu ki karbe su daga hannun surukarki suka fitom hannu biyu na saka na karbe su tare kuma da yi mishi godiya mai yawa.
Habiba ta zo wucewa zata shiga gida, ga alama itama daga wurin saurayinta ta fito, duk da Salisu ba bakonta ba ne sun kuma gaisa dashi amma bai hanata waiwayowa bayan ta wuce.
A cikin gida Gambo ta daure fuska bata so karbar kudinshi da nayi ba, don haka nayi mata bayani, tayi murmushi ta ce, to miko min su nan in adana su don basa cikin ire-iren kudin da kike sayo sabulun wanka da na wanki.”
Rannan kwana muka yi ni da Gambo muna kus-kus-kus din mu cikin farin ciki da jin dadi, hirar abotar Babana da Baba Yahaya Gambo ke yi min, tana kara gaya min cewar shi kadai ne abokin Babana tun suna yara da ya ki yarda suyi batawar da zasu rabu ko ya zo gida an yi kaca-kaca bai hana shi kuma gobe ya sake dawowa.
Har irin tsayuwar da yayi kan neman auirenta sai da ta gaya min da ta gama kuma sai ta ce to gashi yau daga kai mishi wannan magana ya turo dan shi kan maganar aurenki, yanda ya rufa min asiri shima Ubangiji ya rufa mishi, na ce amin Gambo.
Abin mamaki gari na wayewa sai ga Alhaji Tijjani makwabcin Alhaji Mai kudi shi da Limamin unguwar su sun zo wurin Babana wai sun zo ne a madadin Alhaji Mai kudi don su nemar wa Alhaji Abba izinin aurena wai da Hajiya Kubra ta yi wa Alhaji Mai kudi bayanin abin da Gambo take ciki da wa’adin da Babana ya bayar lokacin uma Alhaji Abban yaje gidan sia ya roki mahaifinshi ya turo a tambayar mishi izinin auren nawa. Shi yana sona.”
Gambo tayi dariyar jin dadi, farin ciki mai yawa ya kama ta, ta daga hannu sama tayi ta addu’a da ta gama sai ta waiwayo ta kalle ni ta ce min “Amma fa ba zaki canza wannan yaron ba don Alhaji Abba yazo ba duk da shi din dan uwana ne amma kuma akwai mutunci da ganin girma mai yawa tsakaninmu da Mallam Yahaya, da kuma hajiya Hairan don haka kan Salisusu kawai za ki tsaya, na ce mata to Gambo.
Ba mu san yanda aka yi ba, sai kawai muka jiwo Mama tana sakin manya-manyan ashar a tsakar gida, tare da fadin “Lalle ana munafurci a garin nan, jiya yaron nan Salisusu yazo yau kuma ga wadannan sun zo, to raba musu ita biyu za ayi kenan ko?’
Mama wai fa don ace tayi farin jini ne, in ji Habiba. Mama taja tsaki ta ce, farin jinin gidan uwar wa? A yanzu ko Samari goma aka turo mata rana daya ai an yi aikin banza tunda dai turo su aka yi, ban da haka kuma shekara nawa aka yi a gidan nan ana hidimar arziki a kanku ina nunawa uwarta bata taba cewa ga nata ba?
Magana kamar wasa, Mama ta shiga kai-kawo mai tsanani, kowane lokaci tana tashe da Babana tana gaya mishi abinda take gaya mishi, sai dai kuma babu wanda yasan me take fadan sai su biyun suka san abinda suke yi.
Aike akan aike daga gidan Baba Yahaya da kuma Alhaji Mai kudi, Babana ya ki ya tanka, rannan Baba Yahaya yazo da kanshi a tsakar gida ya samu Babana, don haka shima a tsakar gidan ya zauna sai da ya gaisa da duk mutanen gidan kowacce ta nufi dkainta, sannan ya kalli Babana ya ce mishi.
“Wurin ka fa nazo kan maganar yaran nan.”
Baba ya gyara zama ya daure fuska alamar rashin wasa kafin ya ce, “Ina sauraronka.” Baba Yahaya yayi kamar bai gane abinda yayin ba, ya ce mishi an turo mutane wurin ka daga wurina da kuma wurin Alhaji Mai kudi da fari ka ce a saurare ka don zaka yi shawara tukunna akai, daga baya kuma da aka sake turowa sai ka ce wai saboda ka raba fada a tsakaninsu duka ka zartar da hukuncin yi mata miji kai da kanka.
Wanene mijin da ka zaban matan? Ai mu dukan mu muna da ‘yancin ka gaya mana don mu ma iyayenta ne ba kai kadai ke da ita ba, kuma kasan zaka iya zar tar da wannan hukuncin a kanta ma Alhaji menene na bata wa’adi har kana cewa in ba haka ba ita da uwarta su bar maka gida?”
Maganganu masu yawa Baba Yahaya ya yi ta sakewa Babana, ya kuma ja ya tsaya akan ba zai bar gidan ba, sai Babana ya gaya mishi mijin da zai ba ni, da Babana ya ga da iyakacin gaskiyarshi yake yi, gashi kuma tuni ya riga ya amba ci ranar bikin matsowa kuma take yi, sai yaga to bari kawai ya fede komai ya ji ya huta da boye-boyen da yake yi.
Ina daga daki nayi kasake ina sauraron in ji ya ce Nasiru ne abokin Ado, na kuma zuba wa Gambo ido ina kallon irin sauraron da take yi, daga tsakar gida sai kawai na ji ya ce, wai Ado ne.
A daidai lokacin da Baba Yahaya ke tambayar shi Ado? Ita Gambo rafka salati tayi yayin da ni kuma na kurma musu ihu ina daga cikin daki.
Baba Yahaya ya ce, “wannan kuwa shi ne zance, me ka ke so ka yi wa Binta ne Alhaji? Ai kuma dai ba zai yiwu ba don ba zan kyale ka ba saboda kowa yasan in da maganar taka ta dosa da kuma abin da yasa kayi ta.
Tuntuni Ado yana gidan nan bai ce yana sonta ba, ba ka yi niyyar ba shi ita ba har ka zartar musu da hukuncin bar maka gida, sai da aka ga masu son aurenta sun zo na gaskiya sai kuma a koma a cuno maka shi ace ka bashi ita don a samu a yi ta sa uwarta bakin ciki? To kun yi kadan.
Ya tashi ya fita a fusace, Mama ta bishi da kallo kafin taja wani mummunan tsaki daga baya kuma ta saki wani lallausan murmushi ta ci gaba da abinda take yi.