Skip to content
Part 15 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Aka dan yi dariya saboda rahar da tayi, Baba Yahya ya ce, Inna bakar nan fa gida ta dauko Innar giyade tayi shiru cikin yanayin murmushi don kuwa kowa yasan Babana kama da mahaifiyarshi yake yi. Baba Yahya ya soma magana cikin farin ciki alamar shi kam ya gamsu da hukuncin da ta zartar, ya ce to ba zan ba Alh. Abba ita ba, Inna Ahmad zan baiwa Aliya don shi ne saurayi a cikinsu, ta ce wannan kuma kai ta shafa.

Gambo ma nasan ta dan samu sassaucin damuwarta, sai dai kuma nasan babu yanda za’ayi taji dadin hada ni da Ado da za’ayi, don haka sai nayi maza na nuna mata murnata a zahiri na ce ai shi kenan ma Gambo tunda gashi daga Salisusun har Ahmad  duka naki ne, ka kuma da Aliya za’a ba su, Gambo tayi magana cikin natsuwa tana kallona cikin wani yanayi ta ce min, to amma ke fa? Ki auri wannan yaron? Kin ga zan samu natsuwa cikin zuciyata? Ai da Atika ko Aliyan aka ba shi, ai da gangan Mama take yin abin da take yi, bakin ciki take so ta sani na ce uh’uh Gambo kar kiyi maganar nan har wani ya ji ni da su Atika da Aliya duk daya ne a wurinki, kuma gara ni in auri Ado da su su aure shi saboda ni ce babba ban da haka ma kuma nafi su sabuwa da wahalar Mama, don haka gara ni din kiyi hakuri kar kuma ki nuna baki gamsu da abinda tayin ba, dukkanmu naki ne Gambo dukkanmu kuma daya ne sannan wadanda za’a basun suma naki ne.

Ta ce, “Haka ne, Allah na gode maka ni da nake ta fatan ko ke kadai in samu ayi auren ki gashi a sanadin auren naki ‘yan uwanki ma duka sun samu auren, Allah Ubangiji ya yi miki albarka, ya kuma rufa miki asiri, nayi murmushi na ce amin Gambo.

Na sake maida kunnuwana can tsakar gida inda nake jiwo Hajiyar giyade tana sakin maganganu masu zafi, saboda hakan ne yasa ka zubawa ‘yarku mai yaji ido tana zaune a gida? Baba Yahya yai shiru kamar ruwa ya cinye shi. Can anjima ya soma magana saboda yasan shirun da tayi alama ne na wai shi take sauraro, ya ce to Gambo in na ce komai na gani sai nayi magana ba fa ba jituwa zamu yi da shi na gaya miki abinda ya faru sanda nazo da maganar yaran nan da aka kawo min labarin abinda suke yi zuwa nayi da karfina don musan matakin da zamu dauka a kan su tun abin bai yi nisa ba sai uwar su ta ci mutuncina a gabanshi ta ce wai duk tsiyata dole in ga ‘ya’yanta in kuma hakura da su tunda an riga an haife su ba kuma zai yiwu in dunkule su in maida su inda suka fito ba.

Hajiyar Giyade ta ce, to kayi hakuri, ni da kaina na baka hakuri in cin mutunci tayi kuwa to ba kai tayi wa ba kanta tayi wa, gyara kayanka kam ai baya zama sauke mu raba, ba ga ta nan gasu ba, ko ni din nan da ban san shaye-shayensu na zamani ba ina ganinsu na gaya musu kai ba sigari kadai suke sha ba suka ce shi kadai ne nace to bai karbe su ba, su daina don duk sun rine sun zama wani iri.

Sannan ko ba komai wadannan yaran su Salisusu ai sa’o’insu ne shi Baba ma ya girme shi to ba gashi nan ba ya natsu ya zama babba har ga aure zai yi su wake ta tasu? Dama shi mutum in yayi kos din iya shege ai in ya rika sai ya koma yiwa kanshi, don haka ba don su taimake ni kasa a mayar da wannan yarinyar dakinta.

Ya ce to Gambo, yanzu in na tashi daga nan zan tafi can gidan mijin nata in neme shi muyi magana in yaso da daddare sai in turo masu maida ita su maida ita, ta ce mishi to, tayi tasa mishi albarka Babana kuwa tayi mishi tas. Ba akan komai ba sai akan irin mu’amallarshi da Baba Yahaya ta ce shi kadai ya rike abotar da don ta Babana da tuni sun rabu.

Mama tayi ta kuka tana fadin wai dama can Hajiyar Giyade ba sonta take yi ba, ita kuwa Hajiya ko kallonta bata yi ba balle ta damu da kukan da take yi.

Mama bata dauki cewar da Hajiyar Giyade tayi na a baiwa Ahmad da Salisusu Atika da Aliya da sauki ba, da farko tayi maganar kankantarsu da Babana ya gayawa Hajiyar Giyade sai ta ce ai ita sanda aka kaita gidansu shekarunta goma sha daya ne ba gata ba me ya same ta? To balle Aliya mai sha hudu a kaita dakinta kawai ta sake dawowa da maganar hidimar da za’ayin wai an riga anyi nisa babu su a ciki gashi ana matsalar kasuwa tunda kwanannan ma akayi wata asarar.

Don haka a dan daga nasu bikin don a samu a dan tanadan musu wani abu, da Babana ya sake yi mata wannan maganar sai ta ce mishi kira min iyayen yaran in ji ta bakinsu, Mama da Gambo suka zo Mama ta sake rattaba mata bayani da dalilan son dagawan da ta waiwayi Gambo sai ta ce ita ana ta ayi hidimar ba tare da su an sanya su cikin wadanda za’ayi wa sayayyar ba, tunda ba a faro dasu ba a daura musu aurensu kawai a kai su dakunan mazansu arzikin gidan miji ai yafi na gidan iyaye, don haka kar ayi musu komai ko da kuwa tabarma ce.

Gambor Giyade ta ce, na gode miki ‘yar nan, Allah dai yayi miki albarka, je ki abinki kin ji Gambo ta tashi ta tafi ta kalli Babana ta ce mishi kar kayi sayaiyar da su sun yafe a daura musu auren a kai su gidajensu tunda uwar suma ta ce bata son sayaiyar, don haka na umarce ka ka aurar mata da ‘ya’yanta in kuma bani ka ke nema da magana ba.

An maida Anti Sha’awa gidan mijinta ko kwana bakwai ba ayi ba sai ga goro an kawo wai na tarewar amaryarta rana ita yau. Hajiyar Giyade ta ce, uhun ka gani ba? Gajiya yayi da irin karantarku da kuke mishi, don haka zai yi wa kanshi maganin iya shegen ‘yarku ku kuma kun kama ta kun rike kuna jira sai yazo, to ba don Yahaya yaje ya bashi hakuri yasa an maida ita ba da amarya ta tare ita tana wurin yaji kaga kuma da girma ya fadi. Ko da yake yanzun ma dai sai dai ayi sha’ani.

Rannan Mama ta wuni tana zage-zage, tana fadin kaga min ja’iri mara mutunci bai da ko kwabo naja na tsaya na ce sai shi bayan ga mutanen da suka dace a ba su shi ne tun ba a gama fita daga zaman talaucin da ake yi ba zai kwaso wata tsiya ya kawowa mutane? Zubaida ta ce ai sai dai kar a kuma don wannan kam ya riga ya kwaso.

Gabadaya Babana hidimarshi da maganarshi ta zama ta hidimar bikin da ya sanya a gaba na ‘ya’yanshi mata guda biyar, ga kumadan shi na riko wato kanin matarshi Ado, wai shima shi ne mai yi mishi komai sadaki da zannuwan aure duka ina jin mama tana cewa wannan kudi da ka bayar na sayaiyar zannuwan auren Ado ai ba za su yi ba Alhaji, haka fa kayayyakin dakin yarannan da hikima na karasa yi musu sayaiyar. Gambo mai ‘ya’ya uku rus cikin lamarin ba a ko shawara da ita hankalinta kuma a kwance hidimarta kawai ta sanya a gaba.

Tuni tayi kasafi na abinda zata baiwa kowacce a cikinmu cikin ‘yan kudinta da cikinmu ya rage mata da suke wurin juyi. Sai dai ni kam ba kayan daki take shirin saya min ba, don Mama ta riga tayi furuci maganar kuma ta riga ta bayyana har mutane da yawa sunji ta cewar auren nawa da Ado za a yi shi na wata uku ne kawai, watanni ukun suna cika zai sako ni in dawo gida in yaso sai ya nemi wata kalleliyar yarinyar ya aura tunda ma ai kan  nawa auren ko me aka yi bai da asara don ko kwandalarshi ba zai kashe ba, Babana ne zai yi mishi komai.

Ado ya yarda da wannan ka’ida da Mama ta sanya mishi, ya kuma yi rantsuwar yi mata duk abin da take so akan auren dama kuma kowa yasan shi din mai yi mata biyayya ne.

Bisa wannan dalili ne Gambo da ‘yan uwanta suka tsaida shawarar ni kar a saya min komai na kayan daki ta saya min zinari tunda kadara ce ban da haka kuma zan yi kwalliya.

Kwanakin bikinmu sun matso gabadaya abinda yai saura bai wuce kwana bakwai ba, hidima ta riga ta soma kankama in Mama tayi sammako ta fita tun safe to bata dawowa sai dare, wai tana can wurin hidima. Gambo ma dai da bata zuwa ko’ina itama tata hidimar tayi nisa don Hajiya Kubra tana tsaye akan al’amarinta gashi kuma ta tsaya wajen ganin an hadawa Gambor gudumowa mai yawa shi kam Alhaji Abba ma shi ta dora wa hidimar gadaje da kujerun su Atika, don haka masu matukar kyau aka saya.

Rannan da hantsi na fita naje gidan Anti Ramla don ita tayi kirana wasu ‘yan dabaru wai take son koya min na yanda zan yi in zauna da Ado, tunda ga abinda ake cewa wai  auren na kwana casa’in ne tana gama gaya min abinda zata gaya min din nayi mata godiya na fito ba wani dadewa nayi ba da barin gida amma abin mamaki da yake an ce wai baya bata kadan sai nazo na samu yanayin da na bar gidanmu ya canza, ganin mutanen gidan nayi a tsaitsaye kowa sai zare ido yake yi yana rarraba su.

Da sauri naja na tsaya ina tambayarsu me ya faru? An yi wani abu ne?ko wani ya rasu ne? shiru sai kallona ake yi na ce ha’a to menene haka? Zan fara kuka don ban san me ya faru ba gashi kuma ban ga Babana a cikin gidan ba, sai kawai Zubaida ta ce min ba fa wani abu ba ne maneman Suwaiba ne suka tuiro wai a daga musu nasu bikin don ba su samu daki ba, shi ne da aka ce musu a’a bikin ya riga yazo kuma ba ita kadai ba ce don haka ba zai yiwu ba maganar dagawar shi ne suka ce to sun fasa auren.

A zuciyata na ce ina ma ni ce! Duk da irin rashin kyakkyawar mu’amallar da ke tsakanina da su ban ji dadin hakan ba, don haka sai na wuce naje na shiga dakin Mama don in yi magana da Suwaiba, kukan da take yi ya wuce gaban bayani, nayi kokarin rarrashinta, naga ba za ta gane ma ina magana ba, don haka na hakura na fito cikin zuciyata dai na ji tausayinta don ta riga tasa rai da yawa akan auren.

Can cikin zuciyata na ce, oh’oh ko menene mai dadi haka cikin auren da za’ayi mishi irin wannan son? Oho.

Ko kwana daya da faruwar abin bai cika ba sai kawai Mama ta soma yin waya tana gaya wa mutane cewar bikin babu shi kwata-kwata ma ba za ayi ba don ba zai yiwu ayi biki babu Suwaiba a ciki ba. Kan ka ce menene wannan sai ga Babana shima yana kokarin gamsar da Mahaifiyarshi dalilan da suka sa shi zai daga bikin zuwa wani lokaci gaba kadan, ita kuwa ta ce ina! Akan mutum daya sai a fasa bikin ‘yanmata hudu? Ba zai yiwu ba sai dai ko ita Suwaiba da uwarta su fito da wani mijin kafin ranar don a hada har da ita ko kuma ayi babu ita.

Hakan kuma aka yi ranar daurin aure yazo an kuma daura auren ‘yanmata guda hudu babu Suwaiba a ciki, don ita da Mama sun kasa fiddo da wani mijin ko da kuwa cikin ‘ya’yan dangi ne, a zuciyata na ce oh’oh wato Gambo dai ba karamin rufin asiri ke gare ta ba da aka bata wa’adin kwanaki uku in kawo miji aka kuma kawo har guda biyu da aka hana su ni kuma aka ba su kannena suka karba saboda ba donni da kannena dama za su yi auren ba don ita Gambon ce sanin halinta da suka yi mutuncinta da kuma hakurinta.

Anyi biki irin wanda ba’a zata ba, zan ma iya cewa ba a taba yin irin shi ba a unguwarmu gaba daya saboda ba Mama da Babana ne kadai tsaye akan bikin ba, balle don sunyi mishi saki lecece ya kasa yin armashi.

Baba Yahaya da Alhaji Maikudi sunyi wa bikin hidima ta ban mamaki dangin Gambo rannan basu wani saurari dokar Babana ta hana su zuwa mishi gida ba, tururuwa kawai suke yi suna shigowa Gambo tana can cikin dakinta ko ganinta ba’ayi.

Itama Mama danginta da kawayenta sun zo da yawa, to amma kuma ta riga taki bakin sai zage-zage da neme-nemen tashin hankali take yi, Inna Balki ta ce kar wanda ya kulata ai mu ba ma hidimar arziki muyi fada. Duk wani abin da suke bukata shigo dashi kawai suke yi ko loma daya na gidan basu nema ba balle aje ana bacin rai.

Ni kam nayi kwalliya ko in ce mun yi kwalliya don kuwa Atika da Aliya kayan aure aka yi musu tanfar ba za su kare ba, saboda yawa to amma kuma nima dama Gambota da Hajiya Kubra sunyi min tanadin kayan ado masu daraja, don haka ko kallon akwatin da Mama ta bayar guda daya na kayan aurena da zannuwa biyar a ciki babu wanda ya sake yi. Sai ma da Hajiya ‘Yardubu taga irin wulakancin da ake yi wa Akwatinne taja shi ta adana tana fadin “Wannan akwati fa ba shi ne auren ba, miji shi ne aure.

Gaba daya aka fara magana shima mijin ai ba auren yake nufi ba, Hajiya ba ki ji abinda suke fadi ba ne cewa a kwana casa’in zai kare? Tayi murmushi ta ce, to ko na kwana bakwai ne in ya zamo mai albarka ai shi kenan, ba dai an daura ba? Suka ce, “Eh” ta ce to ai shi kenan.”

Cikin kwanaki biyun da bikin ya kankama wato Juma’a da Asabar hidimar da aka yi ba karama ba ce, abin mamaki kuma shima Ado yayi hidima yayi ado yayi gayya, danginshi na uba da abokanshi masu yawa suka zo, kanin Mahaifinshi ne wai ya karbar mishi auren.

Ranar Asabar da daddare Amare gabadaya aka kai su gidan mazajensu, sai dai ni kam fita da ni kawai aka yi daga gidanmu aka sake shiga dani daya gidan namu.

Inna Balki tana zaune a gefena kan wata ‘yar tabarma da muka samu a shimfide don Mama bata sa anyi jere ba, ta ce sai gobe, sannan gabadaya kayan alatun da Ado ya kamata wurin shi da su ta kwashe wai sunzama nata tunda yayi aure. Ta dan faki idon mutanen dake cike a dakin ta matso da bakinta kusa da kunnena ta ce min, mijin naki fa dazu na ganshi da yazo angwanci santalelen saurayi ne, ina ganin maimakon fito-na-fito da rashin kirki ko za ki gwada yi mishi kirki ne? nayi maza na ce mata a’a bana son shi ba zan zauna dashi ba, ta gyada kai ta ce to shi kenan, amma baki ga kamar…kan ta gama nace mata bar shi kawai Inna ba zan iya zama dashi ba, ta ce to yanda  tayi dai muna miki addu’a na ce to na gode.

Wadannan suka kawo ni suna barin gidan abokan Ado suka shiga kai-kawo suna tambayar ‘yanmata, abinda suke bukatar a kawo musu.

Wata zakakura ta ce musu katifa don ba mu ga yanda za’ayi amarya ta kwanta kan wannan tsohuwar tabarma da aka yar a kasa ba, suka ce kin fadi gaskiya ‘yanmata, suka juya suka fita. Jimawa can sai gasu da katuwar katifar sunbuka sabuwa dal a cikin ledarta, har bargo shima sabo duniyar kule kan ka ce meye wannan sun wadata wurin da kayayyakin ciye-ciye da shaye-shaye iri-iri.

<< Mijin Ta Ce 14Mijin Ta Ce 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×