Skip to content
Part 16 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Washegari ranar Lahadi rannan wuni muka yi daga ni sai kawayena sai dangin su Mama da suke shigowa jifa-jifa ganin amarya sai ko ‘ya’yana su dake kai-kawo amma dangin Gambo babu wanda ya leko don su dama sun ce sun gama da gidanmu tun jiya sun dai zo sun sheda daurin aure, to yau za su yi hidimar su a tsakanin gidajen amaren su Atika da Aliya da kuma gidan mai babban allo, don su a wurin su shima Salisusu da ne saboda Baba Yahaya.

Har bayan Azahar ba a zo aka yi min jere ba, abincin ranar ma ba a kawo ba, watakila don sun leko sun ga angwaye sun kawo abin karyawa shi yasa ko suke zaton za su kawo na rana oho.

‘Yanmata suka nemo redio suka shiga sanya kaset suna cashewa, don su debewa kansu takaicin zaman shiru.

Sai bayan La’asar lokacinne naga ana shigowa da wasu katakwaye da ‘yan kujeru wadanda rabon da inga irin su tun a hotunan mutanen da, tunda nasan ko a kauye ba za ayi amfani da wadannan ba yanzun. Nan da nan masu jere suka yi jere suka gama ko awa daya basu cika ba suka yi tafiyarsu dama kuma ‘yan uwan Maman ne masu jeren.

Wajen karfe shida saura kwata na yamma sai ga Anti Ramla ta shigo tasha kwalliya tayi matukar yin kyau da kyar maganar take fitowa ga alama ba karamin jiki ta ji ba a bikin, menene wannan? Ta shiga waige-waige tana kara kallon dakin na ce mata kayan daki ne ta kwashe da dariya ta ce, kanta ta yiwa kuma ta muzanta tunda shi ne zai hau kai ya kwanta ko kuwa na ce mata eh.

Ta ce, kai baki ga gidan su Aliya ba da Atika, nayi murmushi na ce sun yi kyau ko? Ta ce ai ba a magana, Salisusu yana fadamar mada na ce sabon gidan Baba Yahaya kenan, ta ce eh to ita kuma Atika tana C.B.N Kuarters, Alhaji Abba ya baiwa Ahmad bari daya amaryar shi shima tana daya, na ce kai sun more gidaje, ta ce eh an kuma yi musu kaya, don ban da na Alhaji Abba shima Alhaji Babba yayi musu wasu gadaje da kujerun a zuciyata na ce Alhaji Maikudi kenan.

Labari sosai ta bani na irin hidimar da aka yi na bikin Atika da Aliya, nayi murna sosai don nasan Gambo tana cikin farin ciki. Daga baya ne kuma na ji  tausayi, sai dai maimakon in ji tausayin kaina tausayin Babana ne ya kama ni.

Gaba daya abokanshi a yanzu arzikinsu ya zarce nashi, saboda suna da tsayayyun ‘ya’yan da suka tallabawa neman arzikin su a lokacin da suka soma bukatar hakan saboda shekaru sun soma yi musu yawa. Shi kuwa bai samu nashin sun kintsa ba, balle shima suyi mishi irin wannan taimakon sai Ado.

Ado kuwa ta’adin da suke yi mishi shi da Mama yawanshi ba kadan ba ne.

“Tashi kiyi kwalliya ga wadannan kayan Hajiya Kubra ta ce in zo miki da su.” Na ce mata “To.” Sai da na sake wanka na zauna na sake shafa mai tana taya ni don mun riga munyi matukar shakuwa da ita, sannan na sanya sabbin under wears wadanda suma a cikin kayan tazo dasu na sanya kayana tare da ‘yankunne da abin wuya tare da wasu banguls din a hannuna su zobuna sai sheki nake yi ina daukan ido tanfar dai wata amaryar gaske.

Sai da ta gama feshe ni da turare ta ko’ina sannan ta kalle ni tayi murmushin gamsuwa ta mike tsaye da nufin tafiya nima na mike tsaye da nufin yi mata taku zuwa kofar daki, waiwayowa tayi cikin natsuwa kafin ta ce min “Kai kin yi kyau Humaira, kuma ke din amarya ce ta sosai da sosai, sannan angon ki ma ango ne na gaske abu guda daya da ya rage ku shi ne baku da hadadden gida baku kuma da kayan alatu amma wannan duk ba komai ba ne in har kun yarda zaku mallakawa junanku kawunanku zaku more aurenku a haka.”

Nayi maza na ce, “Haba Anti Ramla, yaya kike irin wannan maganar kamar ba ki san komai ba?” Ta dan yi murmushi tare da tabe baki ta ce, “Nasan komai Humaira, amma dai kuma nayi miki sha’awar yaron ne very handsome kuma very gentle.” Na ce, a hakan ko? Ta ce, eh, na ce to sumu-sumu kasau ne kin ji, in kin san abinda ya yi wa Gambo da wanda yake yiwa Babana za ki san ko yaya yake ni din ba ni da bukatarshi ba kuma zan bukace shi ba.

Ta ce, “To shi kenan abinda ki ka gani dai tunda mai daki ai shi yasan inda ke yi masa yoyo. Amma dai in har kin san baki da bukatarshi din da gaske to ki rike budurcinki kar ki bar shi ya taba don shi din shi ne komai din mu.”

Na ce mata, “To.” Ta tafi tana jaddada min, kar fa in yi sakarcin da zai cuce ni tunda ga abinda uwar goyonshi ma take  fada, cewar auren nasu na kwana casa’in ne, na ce mata yauwa ko nan aka tsaya zaki gane ba wani abin da zan yi dashi, tayi maza ta ce haka to amma fa sai kin yi jarumtaka mai yawa don su din ba wani kirki ne da su ba, haka nan kunyarsu ma ‘yar kankanuwa ce, na ce to.”

Na juya zuwa can cikin daki, cikin zuciyata ina tunanin yanda za’ayi Ado ya ce yana son wani abu daga gare ni, kai haba shima ba zai fara ba zai jira ne kawai wa’adin kwana casa’in din da Mama ta dibar mishi su cika ya sallame ni, shi kenan burinsu ya cika na zama bazawara tunda ma ga irin lalataccen kayan da suka yi min, ba don ayi amfani da shi suka yi ba, abu mai dan fasali da yake cikin gidan to a kicin yake shi ne coler da frich sai ko frizer wadannan kuwa Baba Yahaya ne yayi mana dukkanmu.

Abokan ango suka rako angon don sayen baki, kayayyakin sayen baki sosai suka zo da shi, kawaye kuma suna fadin abin da za’a basu na sallamar kawaye suka kawo suka basu bayan an dan yi raha da barkwanci suka sallame su, suka tafi daga baya suma suka yi ‘yan nasihohinsa da addu’o’i, suka shafa. Ado ya yi musu rakiya ya dawo dakin.

Yana dawowa ya cire hularshi da babbar rigarshi ya jefar kan kujera guda daya ga alamar dama ya riga ya gaji da su, ya shiga bandaki ya gama abinda zai yi ya fito cikin natsuwa ya kalle ni.

“Dan tashi mana Amarya kiyi alwala don mu gabatar da Sallar nafila.” Lokacin ne na gane bayan wankan da yayi har da alwala ya dauro.

Ganin ban tanka mishi ba ya sanya shi tsayawa yi min bayani, akwai alheri mai yawa cikin irin wannan nafilar da aka kwadaitar da ma’aurata game da samunsu, na ce au haba? Yayi shiru yana kallona sai dai fara’arshi ta dan ragu, a lalace na ce mishi har da auren kwana casa’in cikin irin auren da ake yiwa wannan nafilar?

Yana daga tsayen ya ce min, “Ai lokaci ne zai bayyanar da wannan, don haka tashi kiyi alwala muyi sallar.” Na ce to ban yi niyya ba.” Yayi sallar nafila raka’a biyu ya dora shafa’i da wuturi akai ya yi addu’o’in shi ya shafa, sannan ya mike ya jawo ledar kayan ciye-ciye da suka zo da ita, ya matso kusa da ni.

“Sa hannu mu ci ko kin fi so in ba ki?” da sauri na kalle shi na ce mishi, kai kar fa ka ce zaka maida ni wata ‘yar yarinya karama, yayi maza ya ce haka ne ke a yau ba yarinya karama ba ce ya ture ledar can gefe ya fasa cin abin da ke ciki ya mike ya fita sai gashi ya dawo dakin daga shi sai wata lalausar rigar bacci da ya rike da belt dinta.

Gabana yayi mummunan faduwa, me wannan mutumin yake nufi? Nayi maza na mike tsaye ina ja da baya har na kai ga taba bango, zuba min ido yayi yana kallona kafin ya bude baki a hankali cikin natsuwa yana tambayata me ki ke yi haka kamar wata karamar yarinya? Nayi maza na ce mishi kar ka taba ni, kai ma kasan bai dace ka taba ni ba in har kana da gaskiya da adalci.

To in ba ni da gaskiya da adalci fa Humaira zan iya taba ki? Kasa bashi amsa nayi yayin da jikina kuma ya dauki rawa sosai saboda tsoratar da nayi dashi, don haka nan take na ji babu abin da nake son yi irin in yi kuka.

Kukan da yaga ina yi sosai-sosai ya sanya jikinshi ya dan yi sanyi, ya koma bakin gado da nufin zama yana taba gadon ya balle. Ado ya mike tsaye ya zuba wa gadon ido ya daga zanin gadon ya kalli katifar ya ce, “A’a kamar zai yi magana sai kuma naga ya kame bakinshi yayi shiru iyaka dai bai sake yin wani abu ko cewa komai ba sai bayan da ya gama fitar da gadon tare da ‘yar katifar dake kanshi, sannan ya dawo ya jawo katifar da muka kwana akai jiya ya kwantar yayi shimfida akai sannan ya sake kallona ya ce min.

“To zo ki kwanta.” Naci gaba da tsayuwar da nake yi, ya kalle ni ya ce min “Ai in ina so zan zo nan inda kike in dauke ki, don haka zo ki kwanta kawai ba zan taba ki ba, magana kawai zamu yi.”

Na dan taho a hankali jikina kuma a takure na dan dofanu gefen katifar yayin da shi kuma ya zauna a tsakiyarta ya baje kafafuwanshi ya zuba min ido yana kallona, menene matsalarki Humaira? Nayi maza na ce mishi bani da ita, ya ce to me yasa ba kya son in taba ki bayan kuma kin sani sarai tun jiya ke din a matsayin matata kike?

Na dago ido na kalle shi wasu sabbin hawayen suka sake zubowa sharrr daga idanuna na ce mishi na roke ka ko baka taba yiwa kowa adalci ba kayi wa wannan auren adalci, kar ka taba ni tunda kaima kasan komai.”

Ya ce, “Ban san komai ba, sai kin gaya min.”Na ce “Kaima kasan ba da gaske kake nufin zaman ba.”Ya ce, “Wannan kuma abinda ya shafe ni ne ni da zuciyata, abinda yake naki guda daya ne shi ne nayi miki umarni ki amsa, na ce ba zan iya ba.”

Ya ce, “To saboda me?” ban san yanda aka yi ba sai kawai naji bakina yana yi mishi lissafi “Saboda baka taba gaida Gambota ba, baka taba girmamata ba, baka taba daga ido ka kalle ta da nufin mutuntata ba, tsawon zaman ka da ita in ban da tattalin bacin ranta ya karu babu abinda ka rinka yi. Sai kuma ka taba mata ni?” Na sake dago ido na kalle shi hawaye suna gudu a idona shar-shar-shar cikin wani yanayi da yafi kama da na shanye halin da ake ciki, ko boyewa.

Ya ce, “To ai na ce miki ni din namiji ne.” Na tambaye shi me ake nufi da namiji? Ya ce min, jarumi, na ce tabbas na yarda kai din jarumi ne, na mike na bar mishi katifar na fito falon na hau kan ‘yar kujerar ulun da ke wurin na dan dofanu ban wani yi motsi mai karfi a kanta ba saboda tsoron kar itama ta wargaje kamar yanda naga gadonta ya yi.

Rannan dai kusan kwana nayi idona biyu saboda tsoron Ado da abinda yake shirin yi abinda ban taba tsammanin hakan zai faru ba a tsakaninmu, to sai dai kuma shima Adon da baya cikin tsoron barazanata bana zaton ya runtsa, don ina ta jin motsinshi.

Ana kiran Sallar farko ya tashi ya shiga yayi wanka ya yi alwala ya fito falo inda nake “ki shiga kiyi wanka kiyi Sallah.” Ban amsa ba, ban kuma ki yin abin da ya ce in yin ba, saboda ciwon da jikina ke yi ga gajiyar biki ga kuma kwanan takura da nayi, ido kuma biyu da kamar nayi bacci ne ma to da da dan sauki.

Na idar da sallar Asuba na dan kishinfida gefen katifar ina sauraron shigowar Ado daga Masallaci, ban san yanda aka yi ba sai kawai na farka naga gari ya waye sosai, na mike na shiga bandaki don in rage nauyin dake marata, lokacin ne naga aikin da Ado ya yi ina bacci jarkoki cike da ruwa ga wata katuwar randa itama ya cikata da ruwa donni ko kayan aiki ba ayi min ba.

Mama ta ce, wai uwa ce mai yin wannan ita kuma Gambo bata yi ba, ta ce tunda ba da niyyar a zauna suka yi auren ba to babu abinda zata kai musu sai cin-cin da alkaki da kayan rabon da za’a baiwa iyayenshi wannan kam a wadace aka yi aka kuma basu suka tafi cikin murna.” Ta window nayi leke saboda jin maganar da Ado keyi shi da Baba ne a tsakar gida wai yatsa yake nunawa Baba alamar kashedi.

“Ba fa zan lamunci abinda ku ke yi a cikin gidannan ba kai da Ibrahim, saboda a yanzu ba ni da ku ba ne kawai, matata tana ciki.” Gabana ya yanke ya fadi da karfi saboda jin yanda ya ambaci matata din cikin wani yanayi.

Haushi da takaici ya kama ni, na yanda yake gwadawa Baba Isa da gadara, bayan kuma gidan ubanshi ne, a zuciyata na ce in ban da su Baba sun zama abin da suka zama yaushe za ace wanda yake zaman cin arziki a gidan ku zai yi muku haka? Ko da dai a matsayin Kawunsu yake ai da sai dai ayi zaman ganin darajar juna da mutuntawa.

Tsintsiyar zabori Ado ya saka ya wanke gidan gaba daya ya gyara duk wani abin da yake bukatar gyarawa, sannan ya shigo daki bai kalle ni ba ya ce min za ki rinka gaisawa da Baba da Ibrahim ne a matsayinsu na yayunki, amma ban yarda ki ga wani abokinsu ki gaishe shi ba, ban kuma yarda wani abu ya kai ki dakinsu ba ko menene shi.

Matukar kuma ba wani aiki za ki yi ba, to bana son zamanki a tsakar gida in kuma hakan ya kama to ki sa gyale ko hijabi ki rufe jikinki, na ce tafdijam gidan nan ai gidanmu ne ni da su kuma ‘yan uwan juna ne, ubanmu daya babu wani wanda zai zo ya saka mana dokoki don kawai yazo cin arziki ya samu shiga. Bai kula ni ba.

Ina zaune a falo shima ya fito falon a dalilin shigowar da Sa’adatu tayi ta kawo mana abin karyawa, Mama ce ta aiko ta dan kununa a kofi da kosai guda uku kanana a takarda nashi kuma a wani kyakkyawan food flask an cika shi tam ga yaji a gefe ga kuma kununshi a wani kyakkyawan jug tare da kofin diba asha, shima mai kyau.

Na kawar da kaina gefe na ce hu’un, ai Babana kam kirkinshi yana da yawa, kowa yazo cin arziki gidan shi zai ci ya koshi. Da sauri ya tambaye ni menene? Alamar bai ji abinda na fadin sosai ba, yana jin na soma kamo bayanin zan maimaita mishi sai kawai naji ya warware hannunshi ya wanke ni da mari.

<< Mijin Ta Ce 15Mijin Ta Ce 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×