Skip to content
Part 17 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ban taba zaton zai iya yi min hakan ba, don haka a kidime na kurma mishi ihu, yanda Sa’adatu tayi tsalle tayi waje a tsorace tun saukar marin da ta gani haka shima ya mike ya tsallake komai ya fita ya bar min dakin bai sha kunun ba.

Hannu biyu na saka na rungume fuskata tare da shafa inda ‘yan yatsunshi suka kwanta a gefen fuskata, can cikin zuciyata kuma fadi nake yi lalle mutumin nan ba karamin artabu zamu yi dashi ba. Ya mare ni a gaban kanwata saboda baya tsoron kowa? Tafdijam, na sake jinjina abinda yayin cikin zuciyata, bai wani dade ba ya dawo fuskarshi a daure sosai nima na daure tawa fiye da tashi ya ajiye kayan da ya shigo dasu kayan tea ne da kayayyakin amfani dangin su sabulu da omo da izal gami da detol.

Sai kuma wani yaro da ya biyo shi da katon din ruwan eba ya karbi tare da fadin yauwa Sadiku ko ba Sadiku sunanka ba? Yayi tambayar ta hanyar nuna alamar wasa ga yaron, ya bude food flask din ya dunbuzo kosai ya cika wa yaron nan hannu dashi sannan ya zauna yana karyawa sai da ya gama ya shiga ya shirya ya yi kwanciyarshi, sannan ya fito.

Kwana uku a jere bana magana da Ado, bana ko kallon inda yake shima baya shiga harkata, zaman a haka ya dan fi min dadi da sauki fiye da ranar kwananmu na farko, don haka na kudurawa raina ci gaba da daina kula shi.

Rannan ya dawo da yamma yayi min sallama ban amsa ba, ya nemi wuri ya zauna maimakon yayi abinda yake gabanshi kamar yanda yake yi a sauran kwanakin, sai ya ce min gaba a Musulunci kwana uku ne, in ya wuce haka ya zama haramun, don haka wacce muke yi wa juna yau ta kare, na kawo karshenta ta hanyar ce miki Assalamu alaikum” nayi shiru ban amsa ba ya ce min ko ki amsa ko kar ki amsa wannan ke ta shafa, ya ci gaba da al’amuranshi.

Ganewan da nayi cewar ba zai yarda gabar ta ci gaba ba yasa da aka aiko Baba Karami ya kawo mana abincin dare don Sa’adatu bata yarda ta sake shigowa gidan ba, tunda taga marin da yayi. Ina bude abincin naga irin salon da aka yi na bude baki zan sake jera mishi wasu bakaken maganganu saboda in samu mu dora akan na da, sai ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min, kina so ki sha wahala kenan, in ki ka ce za ki rinka gaya min magana ai ba auren ‘yan iska nayi ba, ba kuma auren nayi a bisa wata mummunar manufa ba balle in zuba miki ido ki rinka zagina, ko ki bari ne girma da arziki ko ki ji a jikinki.”

Shiru nayi na kame bakina saboda na gane idan na ce sai na fadi abinda nayi nufin fadan, to lalle kuwa da gaske zan ji a jikin, don ban ga alamar abin zai tsaya ga mari kawai ba.

Ban sani ba ko shirun da nayi ne ya dan bashi wata dama ta tambayata dazu naga fura da nono a frizer, a ina ki ka samu? Ban kalle shi ba na ce mai babban allo ne ya bayar aka kawo min, to dan dama min mana insha, yanayin da yayi maganar a ciki yasa na debo na zo na dama na mika mishi.

Sai da ya kusa shanyewa na tuna ban sa mishi sugar ba, nayi maza naje na dauko kwalbar sugar na kawo mishi tare da gaya mishi cewar kayi hakuri ban sa sugar ba, na riga na saba da shan furar mai babban allo, ya ce eh ai hakan ma dadi ne da ita na ce uh na ki yarda maganar ta kara nisa.

Rannan na kwana bakwai a gidan Ado, a lissafi ne kawai suke guda bakwai, amma a tsanani sun fi kama da watanni. A daddafe muka kai wadannan kwanakin, shi din bai yi gaba ba a kaina ba sai dai da gani har shi mun kai wani hali na tsananin wahala da galabaita.

Ni dai ina cikin wani hali na tsananin ciwon jiki a dalilin wasan mugunta da wani lokaci yake yi min, ga kuma tsananin ciwon kai saboda rashin samun barci. Yayin da shi kuma Ado yake kwana zirga-zirgar shan kanwa da su andur leber sold.

Kwana muke wani yanayi mara dadi, amma gari na wayewa sai ya maiyace ya maida komai ba komai ba ya ci gaba da murmushin shi, ya shirya da safe zai fita har ya gama komai sai ya waiwayo ya kalle ni ya ce min “Anya kina da kirki kuwa Humaira? Nayi maza na ce mishi ba ni da shi, ya ce to da alama kam amma in ban da haka yau kwanaki bakwai a nan gidan ga Hajiyar Giyade a cikin gida bata taba shigowa wurinki ba kema ba ki neme ta ba, sannan baki taba diban ko da ruwan gidanki ne a kofi ki ka aike mata da shi ba. Anya! Bakya lura ki ga kamar sa’a kika yi tayi yawan ran da taga aurenki? Sannan in kika yi sakacinda ta tafi ba ta ci abincinki ba sai yaushe kike ganin zata dawo taci? Yaushe? Jibi ko gata ko badi?

Shiru nayi ban tanka mishi ba, shima bai matsa sai na bashi amsar ba, yasa kai ya fita yana fita sai ga Sa’adatu ta shiga da sauri na tare ta cikin farin ciki ina tambayarta me yasa ba kya shigowa Sa’adatu? Sa’adatu sai yau?”

A hankali ta ce, “Gambo ce ta hana ni, yanzu ma yaya Ado ne ya ce min kina nemana, da sauri na tambaye ta me yasa Gambo zata hana ki zuwa wurina? Ta ce na gaya mata kin zagi Yaya Ado shi kuma ya mare ki, shi ne ya ce to kar in sake shigo muku gidanku.”

Nayi kamar in sake tambayarta wani abu sai kuma dai na fasa a dalilin shekarun nata ba wasu masu yawa ba ne tara ne da ita. Na jawo kazar da Ado ya kawo min jiya da daddare ban ci ba, na tura mata tare da kayan tea.

“Zuba yanda ya yi miki ki sha Sa’adatu, yi nayi wai don in burge ta in yaso in ta gama sai in ce mata taje ta turo min su Baba Karami sai ta kalle ni ta ce min, na riga na koshi. Da sauri na ce mata, naman kaza ne fa Sa’adatu, don nasan ita din mai kwadayin naman ne sai ta ce eh na koshi ai muma muna dashi.”

Na ce, “To shi kenan Sa’adatu, ki gaida Gambon ko?” na ce mata “To.” Ta tashi ta tafi cikin zuciyata sai murna nake yi, Gambo ma al’amura sun fara canza mata, ko a ina take samun kudi yanzu? Tunda nasan dai duk abinda take dashi ta kashe sai kuma na tuna ai surukaye ne da ita ga Ahmad dan wanta ga Salisusu dan Baba Yahaya na kuma san dukansu zasu ji da ita.

Na fito tsakar gida sanye da doguwar shimi a jikina wacce ta dan fara jikewa kadan a dalilin wankin kayan su Baba Karami da na sa aka kawo min nayi shanya na ke yi a igiya yayin da su Baba da Ibrahim suke dakinsu suna sharholiyarsu tare da abokansu, sai ga Ado ya shigo rike da ledojin sayaiya biyu a hannunshi.

Yana ganina fuskarshi ta sauya ban ce miki a tsakar gida kisa gyale ko hijabi ba? Nayi shiru ban amsa mishi ba, ya sake yi min tambaya cikin tsawa, “kina so ne wani ya ganki a haka?” na ce, “A’a, to su waye za su ganni ba yayuna ba ne?”

Yayi maza ya cukume ni ya shake yana fadin “Har abokansu da suke cikin dakin ma yayunki ne?” Na yi shiru ina zaro ido cikin yanayin tsoro yana sakina ya nufi dakin su Baba ya daga labulen.

“Kai duk ku fito nan bana hana ku shigowa gidan nan kuna mana shaye-shayenku ba?” “A’a Kawu, sigari ne kawai.” Abokansu ne masu bashi amsa, daidai suna fitowa suna barin gidan sum-sum ya sake biyo ni daki bayan ya gama dasu ya same ni kwance a kan katifa ga cefane na kawo ki tashi kiyi girki, na ce ba zan yi ba na riga na fasa, ya ce kije kiyi ta fasawa. Ya juya ya fita.

Ado yayi matukar tasa Baba da Ibrahim tare da abokansu a gaba har sai da Mama tayi mishi magana akan su sai kuma ya sake dawowa kaina da wasu dokokin nashi masu tsananin bi.

Rannan ya dawo gida da rana T.B da kafet Plasma tare da rediyo C.D da kafet na tsakiyar daki alamar dai so yake ya dan gyara falon saboda rashin fasalin shi ya yi yawa, yana barin gidan sai ga Suwaiba ta shigo, bayan tunda aka yi bikinmu bata shigo min ba, amma kullum tana barin unguwar taje gidan Habiba.

Ban ji tayi min sallama ba, don haka na ci gaba da kwanciyata akan katifata a daki ba tare da na tanka mata ba, ta shiga kunne-kunne da jone-jone ina jin ta sai naji kawarta tana ce mata mun shigo gida babu sallama babu gaisuwa mun kama yiwa matar gida tabe-tabe.

Sai kawai naji Suwaiba tana ce mata, “to nata ne? na Kawunmu ne ba ki ji Mama ma tana cewa duk abinda zan taba a gidan in taba shi cikin gadara na Kawuna ne ba? Ita fa ga irin kayan da aka yi mata can.”

Ina jin haka nasan da hannun Mama cikin rashin mutuncin da tazo zata yi min, don kuwa ita dai nasan a yanzu tsorona take ji, a zuciyata nayi tunanin wata kila ta turo ta ne ta tsokane ni don muyi fada da ita ta fake da wannan tasa Ado ya sake ni, don kuwa ko shekaran jiya ta shigo har gidan har cikin nan falon na gaishe ta taki ta kula sai da Adon ya ce mata ana gaishe ki Mama sannan ta amsa.

Ina cikin daki ina jin ta tana tambayar shi anya muna nan akan alkawarinmu kuwa Adamu? Yayi murmushi ya ce, me ki ka gani Mama? Ta ce bare-baren da ka soma yi ne yake bani tsoro, ya sake kallonta cikin natsuwa ya ce mata, ai ba na bare-bare Mama, me ki ka ga nayi? Ta ce me ka ke zuwa yi dakin uwarta? Cikin natsuwa ya ce mata gaisuwa ce kawai Mama don akwai nauyi mai yawa ace ‘yarta tana gidan nan a matsayin matata amma ace ba na gaishe ta.”

“Matarka Ado? A gabana ka ke kiranta matarka? Kaga yanda kasa na ji faduwar gaba kuwa?” Ya yi maza ya shiga bata hakuri, yana fadin ya yi kuskure ba kuma zai sake ba, ya yi ta lallaba Mama tana ta faman tashin hankali da fadin wai ya wulakantata tunda ya kira ni matarshi a gabanta, da kyar ya samu ta hakura ya mike ya rakata har gida.

Don haka da na ji kalaman Suwaiba na gane turo ta aka yi sai na fito na same ta hannu na saka na kashe kallon na zare soket din na ce, ko na Kawunki ne na hana ai na mijina ne dakinmu daya ni dashi, shimfidar mu kuma daya ni dake wa yafi iko da kayanshi?”

Ta ce, “Au, kwana nawa zaki yi a gidan nashi? Ai za ki fito.” Na ce to ko zan fito dai ai an daura ya karba bai ce baya so ba, gashi kuma har yana zaryar gaida uwata.” Suwaiba tasa kuka ta fita wai nayi mata gori an ce ba a sonta.

Ban san yanda aka yi ba sai kawai na hango Mama tana shigowa gida da sharbebiyar dorina da gudu na fito daga dakin ban yarda ta ritsa ni a dakin ba. Muka shiga kai-kawon zagaye gida a kokarinta na son kama ni, ina yi kuma ina ihun wayyo Mama kiyi hakuri kar ki buge ni, ko zan samu makwabta su jiwo mu su kawo min agaji.

Ganin ba za ta iya kama ni ba yasa ta shiga kwalawa Ibrahim da ke gida kira wai yazo ya rike mata ni, da gudu na yanka nayi waje don nasan zai iya kama mata ni din don ta buge ni, karab muka hadu da Ado a zaure.

Lafiya? Da sauri ya tambaye ni bayan ya bude hannayenshi gaba daya ya tare hanyar da nake nufin wucewan, jikina yana rawa kamar yanda muryata ma take yi saboda na riga na tsorata, Mama ce tasa Yaya Ibrahim ya kama mata ni wai zata buge ni.

Shiru ya yi na wani dan lokaci nuna alamar nazari kafin ya bude baki cikin natsuwa ya ce min “To mu koma ciki.” Kuka na soma yi mishi saboda na riga na tsorata ba kuma na son gidan dama kuma a matukar takure nake.

“Kiyi hakuri mu koma cikin tare in kin yi min haka zan ji dadi don zanga kamar kin mutunta ni ne.” Mun juya zamu shiga cikin gidan muka ji Mama tana cewa Ibrahim ai ni na fasa kwana casa’in din ma da na diban mishi tunda tun ba aje ko’ina ba har ya fara canzawa, ni ina tunani kar ma dai washa-washan da nake ganin uwar a ciki kwanannan shi ne.

Tana ganin na shiga ta katse maganarta tana tambayarta ai dawowa kika yi? Ai kuwa za ki…bata gama ba Ado ya shigo, ni na dawo da ita Mama ai bai kamata ta fita ta bar gidan Babana nan ba nine nan na ce ta tafi taje duk inda zata auren nata ya ishe ni haka, ai rannan ma da nayi maka magana kan zaman naku ya ishe ni cewa kayo to ko za’a rabu da ita ai za’a rabun ne akan tayi laifi, ba haka kawai ba, to yau tayi sai ka sallame ta.

“Me tayi?” ya bukaci sanin cikin natsuwa, Mama ta kwashe bayanin da Suwaiba tayi mata ta gaya mishi. Ya ce, “Kiyi hakuri Mama, amma ya yi daidai ace an sake ta akan Suwaiba? Ni nafi so ki bari sai tayi wani abinda ya shafe ni ko ya shafe ki wanda kowa ya ji da ma yasan muna da hujja ba za’ayi ta zarginmu ana bata mana suna ba, amma Suwaiba ai kanwarta ce kuma ni Kawunta ne mutane ba za su gamsu da hukuncin saki akanta akan Suwaiba ba, sannan kai Ibrahim kar ka fara ace maka ka kama ta ka mata.’

<< Mijin Ta Ce 16Mijin Ta Ce 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×