Da sauri Mama ta tambaye shi to don me zaka fadi haka shi ba wanta ba ne? Ya ce wanta ne Mama amma ita din matar aure ce, shi auren kuma Amana ne, daga nan kuma zuwa ranar da zan ce bana yin shi to zan tsare wannan Amanar, don haka kar ya fara yin hakan kawai, kalaman na Ado da yanayin da fuskarshi ta nuna yasa daga Mama har Ibrahim jikinsu yayi sanyi, a hankali ta matso kusa da shi tana tambayar shi anya Adamu ba suyi maka komai ba?
Anya ba dandani haukaci aka sa maka ba? Tsoro fa nake ji kar su juyar min da kai, su kwace ka, dubi yanda ranka ya baci akan al’amarin ta wai har ni ka ke wa fada?
Ya ce, Babu mai kwace miki ni Mama, kuma ni ba a kanta raina yake baci ba, aurena da yake kanta ne ba zan iya yin hakurin da za’a wulakanta min shi ba, ace Ibrahim ya kama matar da aurena yake kanta Mama don a bugeta? To me ya hana shi ni ya buge ni? Ni fa inda ana mutunta min aurena to da watakila sai ayi a gama komai cikin hanzari, in ta yi laifi a matsayinta na matar aure a gaya min a ga abin da zan yi, ba a dauko bulala ace za ayi mata duka ba, wannan wulakanta min aure ne.
Hukuncin hukuntata nawa ne nima kuma na iya dukanta tunda kema kin ce an gaya miki sau biyu ina mata duka a zuwan da tayi, har ki ka kara jaddada min in ci gaba da haka, don kar ta ce zata raina ni na ce miki a’a ba zan bar ta ta raina ni ba, ai da gaske nake yi ba zan barta ta raina ni ba, haka kema ba zan barta ta raina ki ba, to amma kuma ba zan bar wani itama ya wulakantata ko ya hanata ‘yancinta na matar aure ba, ba kuma don ita ba sai don aurena da yake kanta.
Mama ta rasa yanda zata yi da wannan curarren bayani nashi na ba don ni ba don auren shi yake yi, ya saki auren kuma ya ki ya ce sai an yi laifin da ya dace ayi sakin ko kuma a saurari zuwan kwanaki casa’in din da aka ambata tun farko.
A haka Mama ta hakura ta tafi gida bayan ya yi mata alkawarin yana idar da Sallar Isha’i zai shigo ya same ta don su kara tattaunawa. Mama tana barin gidan ya kalle ni fuskarshi a daure ya ce min, ke haka ake yi? In an zo za’a buge ki ba za ki yi maza ki shiga dakinki ko kicin ki kulle kanki ba har kafin in dawo sai kiyi waje da gudu? Kina da hankali kuwa? Ke kin san darajar kanki kuwa?
Hawaye suka soma zuba a idona, ya roki in mutunta shi nayi mishi hakan yanzu kuma ya zo zai yi min fada.
Yanayin fuskarshi ya dan sauya a hankali kuma ya soma yin magana, yi hakuri kar kiyi kuka nasan kin tsorata ne to amma ya kamata ki san kina da daraja jikinki ba jikin da ya dace ayi ta budewa ba ne wasu da ba su dace ba suna ganinshi, kishi mai yawa nake yi a kanki ban san dalili ba, da dai ace kin taba barina na taba ki ne to watakila da nima na yarda da maganar Maman cewar dandani haukaci aka yi min.
To ban dandani komai ba Humaira, kowa ya gane abinda nake ciki bare-bare nake yi akanki amma babu ruwanki, na ce akan aurenka dai, yayi maza ya ce eh akan aurena, to amma waye auren nawa? Ban tanka mishi ba, shima ya kawar da zancen ta hanyar tambayata yanzu nan har yau ma ba za ki yi girki ba?
Tsakanin gobe da jibi ne fa naji Baba ya ce wai Hajiyar Giyade zata tafi, da sauri na ce mishi kai? Ya ce, uhun, dama zata yi ta zama ne? Na dan kalle shi kadan kafin na kawar da kaina gefe, wani lokaci na kan ji kamar in saki jiki kawai da Ado muyi zamanmu, to amma in nayi wani tunanin sai kuma in ga to ai zan iya sakin jikin nawa dashi muzo muna cikin zaman kwanaki casa’in su cika ace min ki tafi aure ya kare, in akayi haka wa aka cuta? Ni tunda ni ce zan rasa wani abu shi bai rasa komai ba, to in kuma ma ba ace min in tafi ba zama da Ado yana nufin ci gaba da zama cikin ukubar Mama da wulakantawarta, don haka sai in ga to gara min kawai in ci gaba da jajircewa har lokacin rabuwarmu tazo in je in yi aurena na ‘yanci da mutuntawa da ganin darajar mahaifiyata.
Na shiga kicin da nufin yin girki karo na farko a rayuwar aurena ni da Ado cikin kwanaki goma shataran da muka yi tare saboda in yi girkin da zan aikawa kakata Mahaifiyar Baba abincina don kar ta tafi bata taba cin girkina saboda na yarda da maganar da Ado ya gaya min cewar yawan rai ne ya sata ganin auren nawa, don shekaru tamanin da hudu ke gare ta, bai kamata in bari ta tafi bata dandani girkin nawa ba, tun da ban san randa zata sake zuwa ba.
Na fara shirye-shiryen dora girkin kenan bayan na gama tsabtace wurin, sai Ado ya leko cikin natsuwa ya ce min ko za ki yi ne har da mai babban allo? Ban tanka ba ya juya ya tafi, ga dukkan alamu dai ya ji dadin ganina a kicin din, shawarar da ya bayar ta sanya ni fadada girkin sosai. Tuwon semobita nayi miyar kuka don a sanina tuwo shi ne abincin da yafi dadi yafi saukin ci a wurin Hajiyar Giyade, to ko shima mai babban allon yasha gaya min cewar a dole yake cin wani abinci matukar ba tuwo ba ne.
Na kammala komai ya kuma yi dadi sosai, don wadatattun kaji na zuba a cikin miyar ina tunanin idan na gama in aika a gayawa Gambo ta bani inda zan zuba abincin sai ga Ado ya shigo da su food flask har guda uku da wasu kwanukan silber masu murfi masu kyau set biyu da dinner set guda daya.
Nasa hannu na karbi wasu, wasu kuma shi da kanshi ya shigo ya ajiye su ya kuma koma gefe ya tsaya yana kallon yanda nake malmala tuwon ina nade shi cikin leda ina ajiyewa cikin food flask da kwanukan da ya kawo. Wannan na waye? Ya bukaci sani ba tare da na kalle shi ba na ce mishi nasu Yaya Ibrahim, to wannan fa? Ya sake nuna wani, na gaya mishi na ce na Baba ga na Hajiyar Giyade da na gidan mai babban allo da ka ce a sa.
To na Gambo da Mama fa? Na ce ai wannan da na ce na Baba ne malmalar ciki na da yawa duk mai so sai ya diba, ya ce to ya yi ina gama zuba miya nasa manshanu da yaji, Ado ya juya zai kira Yaya Ibrahim ya daukan musu nayi maza nace mishi a’a bari shi zan je in kai musu jin haka da yayi ya sa shi diban kwanukan a hannunshi yaje har dakinsu ya kai musu. Cikin zuciyata ni kam ina jin takaicin yanda Ado ke tafiyar da su Ibrahim duk da dai shi din kanin mahaifiyarsu ne, to amma kuma na sani in banda su din sun lalata kansu da shaye-shaye da kin karatu da zaman rashin sana’a babu yanda za’ayi ya rinka yi musu haka. Koda yake akwai adawa mai yawa a gidanmu tsakanin ‘ya’yan wannan dakin da na wannan wanda nake ganin kamar Mama ce tayi dalilin aukuwar hakan, ko da yake dai Maman da kuma Babana suna fadin cewa wai Gambo ta ce tayi sanadin faruwar komai to amma kuma hakan ba zai hana zuciyata sa min cewar Baba da Ibrahim dama duk wani da da Mama ta haifa ‘yan uwana ne ba don haka ina jin ciwon rashin kintsuwarsu musamman da yake ‘ya’yan abokan Babana da yawa sun yi gaba sun bar su na kuma san Babana baya jin dadin hakan, iyaka dai ya kama bakinshi ya yi shiru ya zuba ido kamar yanda nasan shima Adon a farkon al’amarin nasu bai dauki al’amarin nasu da sauki ba.
Na sha jin shi yana kai kararsu wajen Baba kan suna shan wani abu bayan sigari, don haka ayi bincike a san abinda suke ciki don a san matakin da za’a dauka tun kafin abin yakai ga lalacewa. Daga ranar da na ji Mama tana tambayarshi ne a’a har da kai ma Ado da nake ganin kamar kai nawa ne zaka tsaya ka taya ni fada da masu neman kulla musu sharri don su hada su da mahaifinshi kuma kaima zaka shiga cikinsu?
Ai ba a haka, ai ban kawo ka don kai ka samu shiga a wurin ubansu su kuma ka shiga tsakaninsu dashi ka bata ba, matsayinka daban nasu ma daban su ‘ya’ya ne, ya ce haka ne Mama nayi kuskure kiyi hakuri daga ranar ne nasan ban sake jin bakin Ado yana magana kan abin da suke yi ba tun daga shaye-shayen, kin zuwa Makaranta, tarkacen abokai da kuma ‘yanmatan da suke kwasowa sai dai kuma a yanzu kam nasan ba ni kadai ce na gane matsayin da Ado ya ajiye su ba, nasan Mama ma ta gane na kuma tabbatar ta fini jin zafin hakan to amma kuma ban san yanda aka yi ba taja bakinta tayi shiru tana kallo.
Maimakon a wancan lokacin ne ya kamata tayi shiru ta bar Ado ya taya Babana sa ido akan ‘ya’yan nashi.
Ado ya sake shigowa kicin din yana tashe da Sa’adatu, “Nuna mata na Hajiyar Giyade in yaso na Baba da na mai babban allo sai ni in kai musu.” Na ce, “A’a in ka bar shi ma sai ta kai musu duka.” Ya ce, “To bari ni da kaina in tambaye ta don kar ki dora mata abin da ba za ta iya ba, za ki iya Sa’adatu?” Ta yi murmushi tare da gyada mishi kai alamar tasan wasa yake mata, cikin zuciyata nace kai yaro kenan, wai har ta saki jiki da Ado bayan tsawon rayuwarta bata taba ganin yana wata mu’amalla da ita ba in ban da a ‘yan kwanakin nan.
Sai da ta kai na Hajiyar Giyade ta dawo sannan na tambaye ta Babanmu yana ina ne ta ce dakin Mama, na ce to can za ki kai mishi, ta ce to.
Na kammala komai nayi wanka tare da yin kwalliya mai kyau ta hanyar gyaran jikina sosai, sai dai ban sanya wasu kaya masu yawa ba, doguwar riga ce kawai baka sai dai bata da nauyi ko kadan, duk abinda nake yi Ado bina kawai yake yi da kallo sai da yaga ya gama komai har na nufi katifata ina shirin kwanciya shi ne ya tambaye ni.
“Mu namu abincin fa, ba ki kawo mana ba kuma kina shirin kwanciya?’ Na ce, ai ba ka ce in yi da mu ba, wadanda ka ce in yi wa girkin su na yi wa.” Ya ce, to babu laifi.”
Na hau katifata na kwanta na jawo bargona mai laushi na ruhu yayin da Ado ke zaune kan kujerar ukun dake falo wacce a kwanan nan ya mayar wurin kwanciyarshi, ina jin shi yana daidaita tashar talabijin ta hanyar yin amfani da rimot kafin ya ji fitarshi kusan minti talatin kafin ya sake shigowa.
“Humaira!” Sau biyu ya kira ni kafin ya soma tambaya “Na dai san idonki biyu ba wani bacci kike yi ba, tunda da za ki ji motsina firgigit zaki yi ki tashi, ki fito nan muyi magana.” Na bi umarnin da ya bayar din ba tare da na yi magana ba, gasasshiyar kaza na samu ajiye a gabanshi.
“Zauna mu ci tunda ai ba zai yiwu ki kwana da yunwa ba ko?” na ce “Ai na koshi.” Ya yi maza ya dago kai ya kalle ni, kina nufin ke kin ci tuwon kenan ni kadai ne ba ki baiwa ba?’ Na ce, a’a ban ci ba, ya ce zauna muci. Yasa wuka ya raba kazar biyu ya turo min tawa yaja tashi nasa hannu zan dauka in tafi kamar yanda na saba yayi maza ya kama hannuna ya zaunar dani tare da fadin zauna a nan kici.
Ai magana na ce miki zamu yi ina zaune ina kallon shi yana cin tashi kazar har ya gama ya dora robar ruwan swan ya tashi yaje ya wanke hanunshi yayi brush sannan ya dawo ya zauna yana hamdala sai da ya dan dauki lokaci kadan kafin ya ce min ban fa shirya yin wasa da aurena ba Humaira, don haka ina ganin bai dace ace kina ta cutar da ni ba.
Cikin natsuwa na tambaye shi, cutarwar me nake yi maka? Ban wani tsaya dogon bayani ba sai ya ce min, kina cutar da ni mana, ai kema kinsan komai tunda ke ba yarinya ba ce ‘yar kankanuwa kin san abin da kike yi sarai, ban kalle shi ba na ce mishi to in ina cutar da kai ba sai ka maida ni in da ka dauko ni ba? Ko kuma na menene damuwar? Kaima dama auren kwana casa’in aka ce maka kayi, to in kayi na kwanaki sha tara ai ka kyautata baka yi ta wahalar da ni ba balle in yi ta cutar da kai tunda itama mai auren dama ta ce maka tuni ya riga ya ishe ta.”
A natse ya ce min, auren ai nawa ne kuma tun kwanakin baya sai na roke ki cewar in muna magana to ta rinka tsayawa a tsakaninmu mu biyu kar ta rinka shafar ko da na kasa damu ne, balle na sama damu, na ce to a ma daina yin magana mana a rinka kirgen kwanakin kawai zuwa lissafin casa’in din.”
Ya ce, a’a ba zan iya ba ba zai yiwu in yi ta zama da ke ina zuba miki ido kina zaune a gidana, nayi maza na daga ido na kalle shi na ce mishi gidanka? Yayi maza ya ce min eh, gidana ne, na yamutsa fuska na ce, wai….bai bari na gama maganar ba yayi maza ya katse ni ta hanyar tambayata wai me? Fadi in ji karasa abinda ki ke son fadan in dai har ke din mara kunyar gaske ce.”
Ban iya karasawan ba ta hanyar furta kalma sai dai kuma ban bar shi haka ba murguda mishi baki nayi, yayi maza ya cafke bakin nawa ya rike da ‘yan yatsunshi ya matse tare da fadin mara kunya kawai wacce bata san rarrashi da ban baki ba tafi gane ayi tsiya-tsiya da ita tukuna.
Washegari da sassafe ina zaune a tsakar gida ni kadai duk da matsanancin hadarin dake haduwa a garin wanda yayi dalilin tasowar iska mai tsanani cikin zuciyata tunani nake yi irin abinda ya faru tsakanina da Ado jiya da daddare, abin da na tabbatar kawia shi ne in ban da al’adar da ya gananwa idonshi a zahiri da babu abin da zai tsare shi daga yin abinda ya shirya din.