Skip to content
Part 19 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Can cikin zuciyata na sake tunawa da Anti Ramla da irin yanda ta rinka jaddada min cewar kar in yarda in bar Ado ya taba budurcina tunda dai na riga na ce ba sonshi nake yi ba, ba zan zauna dashi ba sannan suma mun riga mun san ba da manufar suka karbi auren nasu ba, aure ne kawai suka yi da nufin bata suna don kawai a maida budurwa ta zama bazawara.

A wannan lokacin ban yi tunanin wani abu ne mai tsanani ba yin hakan, musamman da yake nasan babu wata alaka dake shiga tsakanina dashi, to ashe wai ba haka ba ne, ban san dalili ba ban san abinda yasa ya matsa ya takura rayuwarshi kan sai lalle ya taba ni ba, don ya cika burin Mama ne ko kuwa dai da gaske son nawa ya soma yi kamar yanda yake yawan nanata min? Na sake zurfafa cikin wani tunani don in tantance tsakanin son da Ado yace yana yi min da kuma sha’awa kamar yanda Anti Ramlah ta taba yi min bayanin su ban iya gane komai ba illa iyaka dai nasan ko ma wanne yake yi min a cikin biyun to ya soma kanshi cikin fitina don kuwa yayi matukar takura kanshi barci yayi matukar yin karanci a gare shi.

Kallo daya zaka yi mishi ka gane walwalarshi ta ragu, gashi kuma rama ta bayyana a fuskarshi.

Ina cikin wannan zaman sai ga Sa’adatu ta shigo rungume da wata katuwar leda, na tabbatar Ado ne ya aiko ta sai da ta shiga daki ta ajiye sannan ta fito ta gaishe ni ta mike zata tafi, nayi maza na ce mata zo mana Sa’adatu, ni hayaniyar me jiya na rinka ji tana tashi a cikin gidanmu?

A hankali ta ce min, Anti Zubaida ce suke fada da Mama, shi ne Anti Suwaiba ta shigan wa Maman da sauri na ce mata Mama kuma? Ta ce min eh, nayi maza na ce mata me ya hada su Sa’adatu? Ta ce ban sani ba amma dai na ji tana cewa Gambo wai Mama macuciya ce tayi karyar ta bar mata ko menene? Ni ban gane ba, cikin zuciyata na gane da magana bai wuce Zubaida ta gane Mama irin rashin adalcin ta ba.

Na yi murmushi kafin na sake kallon Sa’adatu na ce mata, yanzu kuma Zubaidan tana magana da Gambo ne? Ta ce, eh daga kwana ukun can ne take samun Gambo in ta ganta a kicin tayi ta mata magana ita kuwa sai ta ce mata ai zaman aure sai an hada shi da hakuri, nayi dariya na ce Gambo kenan ki ce ina gaishe ta in wankin ya hadu ta baki ki kawo min ta ce to ta tafi.

Ruwa ya dan fara saukowa sanda Ado ya shigo gida ga dukkan alamu kuma ranshi a bace yake duk da shi din ba mai yawan fushi ba ne, na kuwa gane hakan ne ta dalilin yawan bakaken maganganun da nake gaya mishi don wai in tabbatar mishi da kiyayyar da ke tsakanina dashi.

Shi kuwa maimakon ya bata rai sai ya ce min ai shi auren namu ba yin shi aka yi a dalilin so ko amincewa ba anyi shi ne kawai bisa ka’ida ta rabo da kuma kaddara, don babu wanda yasan menene a tsakanin, don haka mu baiwa juna lokaci kawai.

Tashi nayi na bi bayan Ado, zuwa cikin dakin duk da lokacin da ya shigo bai ma kalle ni ba balle ya yi min wata magana, ina shiga dakin nayi mishi sannu don dai in samu ya saki jiki in tambaye shi abinda nake son sani. Ni me ya hada Mama ne kuma da wannan yarinyar Zubaida?

Yayi maza yayi min wani lalataccen kallo kafin ya tambaye ni, to ina ruwanki? Hakan da yayi, ya yi matukar bata min rai, amma sai na danne na ce Mama kenan, ai munafurcinta da sharrinta da mugun abin ta da iya…ban kai ga karshen maganar ba na ji caraf Ado ya cukume ni ya shake da hannunshi, za ki zage ta ne a gabana? Kina nufin ke din rashin kunyarki har ta kai ki kalli idona ki zageta? Ya sake ni ya tsare ni da idanuwanshi wata kila don ganin na shiga mutsu-mutsun kokarin kwatar kaina saboda wahala, kina nufin don kin zama matata sai ki zagi Mama akan idona ina kallonki?”

Duk da ban wastsake daga wahalar shakar da ya yi min ba, ban yarda nayi shiru ba sai da na ce mishi ai ni ba matarka bace ba kuma zan yarda in zama ba, bai kula ni ba ya wuce ya shiga cikin daki ya barni a nan ina kuka sai da ya sake fitowa falon na gane wanka yayi.

Can gefe ya koma ya zauna kan kujerar dake wurin sannan ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya soma cewa ai na riga na roke ki cewar ko bamu mutunta juna ba a zaman da zamu yi to mu mutunta auren dake tsakaninmu, mu kuma girmama shi, mutunta aure da girmama shi yana nufin mutuntu ta, duk wani abin da ke bukatar mutunci da ke zagaye da shi haka nan a girmama duk wani abinda ke bukatar girmamawan dake tare dashi Mama ai uwa ce a wurinki aurena da ke kuma ya sake maida ita surukarki sannan ni bani da wata wacce ta fita mahaifiyata ta rasu ita ce uwata ba zan iya ba ba kuma zan yarda ba ki rainata ina gani balle har rainin ya kai ga zagi ina ji, na ce eh ai shi yasa nima nace maka ba zan iya zama da kai ba don nafi bukatar auren mutumin da zaiga girma da mutuncin Mahaifiyarta ba.

Ai ni ban raina Gambo ba ban kuma taba yi mata wani abu wanda yake na raini ko rashin mutunci ba in ke kin dauka a haka to ita Gambo na gode bata dauka a hakan ba domin ranar da na fara shiga dakinta na gaishe ta na roke ta ta yafe min abubuwan da suka faru a baya a tsakanina da ita na kuskure ta ce ban mata komai ba, kuma a tsakanina da ke da ki ke ganin nayi matana kamar yanda nima zuciyata ta ki yarda da cewar ban yi matana ba, sai na roke ki ki bani dama irin wanda ta bani kiyi min adalci irin wanda ita din tayi min, ki kuma yarda da yawan ce mikin da nake yi cewar ni din namiji ne ma’ana zan iya juyawa a kowane lokaci daga wani matsayi in koma wani, ban ce mishi komai ba.

Kwanaki biyu a jere harkokinshi kawai yake yi bai kula ni akan wani abu ba, iyaka dai nasan yasa min ido mai yawa kan al’adar da nake yi, ya kuma hana kawo min abincin da ake yi daga cikin gida, wai na riga na fara girkina duk kuma da ba yin girkin nake yi ba.

Rannan ya shigo gida bayan sallar Isha’i, tuni nima na riga nayi sallata na hau kan katifa nayi kwanciyata naja bargo na kululluba zuwa zan ya shigo rike da leda a hannunshi abinda za’aci ya kawo har kin kwanta ne? Na ce mishi eh, tashi kici naman nan tunda duminshi kar yayi sanyi nace ai na koshi, ya ce to ba laifi, kin yi wanka ne kin yi sallah?

Nayi shiru kamar ban jishi ba, ya ce ba kya jina ne? Ko ba na ce bana so in yi tayin magana kina jina kina kin amsawa ba? Kinyi wankan al’ada? Na ce ba yau na ke yi ba, ya ce to ban yarda ba ki tashi kiyi yanzu, na ce ha a nuka ake yi ba sai ta dauke ake yin wanka ba? Ya ce ko ta dauke ko bata dauke ba yanzu za ki yi wankan wacce irin al’ada ce haka har kwana shida? Tashi kiyi wanka kawai ko kuma in ganta da idona kamar yanda rannan na ganta.

Rikici mai yawa ne ya faru tsakanina da Ado saboda kokarin da nayi wajen ganin na hana shi ganin abinda yake son ganin kallona yayi, ya yi murmushi bayan ya tabbatarwa kanshi da abinda yake son tabbatarwar, nayi matukar tsorata da abinda ke shirin faruwa na takura na maku re a jikin ban go a daidai lokacin da na daga ido na kalle shi naga abinda yake yi tsoro ya sake kama ni hawaye suka soma zuba daga idanuna, bai fasa abinda yake yi ba sabanin sauran kwanakin da suka gabata da in ya ganni ina kuka yake hakura ya kyale ni, kayi hakuri kar ka taba ni.

Nayi maganar cikin wata irin murya da ta riga ta tsorata da abinda ke shirin samunta kiyi hakuri ki bar ni in taba ki, ya fadi hakan a daidai lokacin da ya miko hannayenshi a gare ni, kuka sosai na soma yi mishi ina rokonshi yayi min adalci kar ya tilasta ni yin abin da bana so yayi murmushi ya ce babu komai don na tilasta ki tunda na riga na gane ke din baki da ra’ayi baki da wani abin da ki ke yi don kanki, kina bin umarnin da ake baki ne.

Kin kuma san ba zai yiwu ni dake mu hadu muna bin umarnin wani mutum wanda shi a gidan shi yake nashi zaman auren lafiya duk irin nashi mas’alolin amma mu a namu gidan yayi uwa yayi makarbiya wajen ganin bamu zauna lafiya ba, tuni na bar kukan da na ke yi na koma sauraron kalaman Ado saboda na kara tsorata da kalaman nashi, ai nayi hakuri na kuma tilasta zuciyata yin hakuri akan dole saboda na dauka ra’ayinki ne ki ki yarda da ni ki ki bani hadin kai a duk lokacin da na nemi kiyi min hakan.

To amma kuma a ‘yan kwanakin nan sai na gane saki ake yi don naji wayar da ki ka amsa kwanci wanda a ciki ake jaddada miki kar ki yarda in taba budurcinki, to ai nawa ne, domin aurena ya bani shi ba zai yiwu ba kuna zuane a dakina a gidana kina bin umarnin wata naki sabanin.”

Na kawar da kai game da ke don ki fahinci cewar ba budurcinki nafi nema ba a yanzu abinda nafi nema shi ne fahimtar juna, tsakanina da ke don shi yafi komai a wurina, to amma tunda akwai wasu a bayan fage masu zuga ki to shi kenan na hakura da fahintar zan karbi budurcin in yaso sai fahintar ta biyo baya tunda na gane kin ki yarda mu fahinci junanne don kina ganin in anyi hakan akwai wani abinda zai biyo baya.

Gaba daya na firgita, hankalina kuma yayi matukar tashi da na gane Ado ya ji wayar da Anti Ramlah tayi min wacce na amsa a kicin ranar da nake yin abincin da aka kaiwa su Hajiyar Giyade, jikina yana rawa na ce mishi kayi hakuri, bai kalle ni ba ya ce min kema na roke ki kiyi hakuri yau kadai ai ni kin sha bani hakuri ina hakura, don haka nina yau na roke ki kiyi min hakuri.

Ganin da nayi Ado bai da shirin hakura nema ma yake yayi amfani da karfi wajen raba ni da budurcina sai naji gaba daya hankalina ya tashi, na shiga tunane-tunanen da neme-nemen hanyoyin da zan bi wajen ganin na kubutar da kaina daga gare shi, ina cikin hakanne wata shawara da Anti Ramla ta bani na kuma yi amfani da ita ta fado cikin raina.

Kar ka taba ni, kashedi mai karfi nayi mishi cikin tsananin firgita saboda na kai matuka wajen tsoron abinda zai faru in har bai yarda ya kyale nin ba, bai ji ba baya ma saurarona abinda ya sanya a gaba kawai yake shirin aiwatarwa. A kikdime cikin tsananin tsoro na shiga mika hannuna karkashin filo ina lalube kan ka ce meye wannan na jiwo motsin abinda na ke neman wanda na dade ina boye shi, saboda maganin bacin rana irin wannan na gwada fin karfi da nuna zalunci da rashin adalci a zahiri.

Ado bai ankara ba saboda hankalinshi ya riga ya tafi inda ya tafi, sanda na jawo abin daga karkashin filo na kuma takarkare da iyakacin karfina na kwantara mishi aka.

Sai da yayi tsalle kafin ya kai ga faduwa a kasa cikin wani irin sauti mai tsananin firgitarwa, yana faduwar ni kuma na koma na kwanta cikin tsananin gajiya sai haki nake yi, ina maida numfashi a dalilin ya riga ya gajiyar da ni. Ina kwancen ina tunanin in ya tashi me zai faru a tsakaninmu? Ina karawa gudumar da nayi dukan da ita riko mai karfi ta yanda in ya sake tasowa zan sake gunduma mishi ita akan nashi, sai kuma na ji shiru bai motsa ba, shirun yayi min yawa ta yanda har na kasa jurewa, na taso na leko don ganin wane hali yake ciki.

Yana kwance a kasa shame-shame babu alamar numfashi a tare dashi, a firgice sosai na soma kurma ihu da iyakacin karfina, ina fadin waiyo Ado, waiyo Kawu waiyo ka tashi ka zauna in ganka a zaune ka yafe min wannan muguntar da nayi maka.

Nan take wani tunani yazo min da gudu na shiga bayan gida, bokitin ruwan da na fara cin karo da shi, shi na fara jawowa ban yi tunanin yawan ruwan ba na kwara mishi shi gaba daya cikin tsananin firgitan da ban taba ganin wanda ya yi shi ba.

Wani irin firgitaccen motsi yayi da ya kara tsorata ni da gudu na balle kofarnayi waje naje ina dukan kofar su Yaya Ibrahim da kyar suka bude suka fito. Bayan sun tabbatar ba zan iya hangen abin da ke cikin dakin ba, ke menene haka? Yaya Ibrahim ne ya fara tambayata cikin tsananin kaduwa na ce musu Ado, ne ku zo ku ganshi Baba ya ce ka ji ‘yar iska wai Ado take ce mishi ko da yake shima maganinshi kenan muje suka taso ni a gaba zuwa dakin, suna ganin halin da yake ciki suka juya da gudu, Mama kawai, Mama kawai za ku kashe mata kaninta don kun ga yana ji da ita dama auren hadin baki ne, ni kam na takura wuri daya in ban da kuka babu abin da nake yi.

Suna barin dakin na fadi jikin Ado ina ta faman kuka ina rokonshi gafarar abinda nayi mishi, tsorona kar ya rasa rayuwarshi a sanadin abinda nayi mishi ne, ba tsoron abinda Mama za ta zo ta yi min ba.

<< Mijin Ta Ce 18Mijin Ta Ce 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×