Skip to content
Part 2 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Shekaruna na kuruciya shekaru ne da ba zan iya furta komai ba game da Babana, don kuwa shekaru ne da nayi su cikin wani yanayi na fuskantar wasu al’amura da ko kadan bai dace yarinya mai shekaruna ta ma san su ba, balle ta fuskance su.

Kan kace meye wannan? Tuni ‘yan uwan Inna sun cika mana gida, su Inna Aisha, Inna Balki, Inna Hajara, gasu nan dai birjik, wasu na kuka wasu na sakin maganganu a tsakar gida don neman a tanka ayi wacce za’ayi, a wannan lokacin ne na fahimci lalle abinda ya farun ba mai sauki ba ne.

Tuni Mama ta bar tsakar gida ta koma falonta, ta kuma yi maza ta kame bakinta tayi shiru bata tankawa bakaken maganganun da wasun su suke saki ba, don tasan karonta dasu.

Ana cikin haka na sake jin sallamar Baba Yahaya a tsakar gidanmu, Hajiya Kubra tana jin sallamar tashi ta fito cikin hijabinta, cikin natsuwa ta nemi wuri ta zauna a kasa cikin ladabi ta gaishe shi, kafin ta soma yi mishi magana cikin yanayin girmamawa, na cewa Alhaji ya gaya maka ina nemanka ne saboda in bi umarnin da ka bani na duk abin da ya faru a cikin gidan nan, kai ne farkon wanda zan gayawa ba shi Alhajin ba.

Ina bin umarnin naka ne kamar yanda nake bin na Baba da ya hana ni fitar da Fadima daga dakinta ba da izinin mijinta ba.

Baba Yahaya ya gyada kai nuna alamar gamsuwa da maganar tata, kafin daga baya ya tambaye ta wani abin ya sake faruwa ne? ta ce “Eh to, ni kam ai ban san komai ba, tunda baya kai kara kan laifukan da ake yi mishin, sai dai yayi hukunci na ganin dama saboda ganin komai yayi yana sharewa kalau.

In ban da haka me Fadima zata yi wa mutum yayi mata irin abinda ake yi mata a gidan nan.” nan da nan ta shiga share hawaye tana fadin a rokan mun shi kawai ya bani ita muje gida, inna yi jinyarta ta warke masan abin da muke ciki.”

Ya dan yi shiru kadan kafin ya ce mata “Hajiya shi babba fa da hakuri aka san shi, kin kuma sani sarai ita mace komai gatanta bata da wata darajar da ta wuce ace a dakin aurenta take zaune.”

Ta ce mishi, “Haka ne.” Ya ce, “To ina dalili, shi Alhaji Surajo komai kankantar abinda ya faru a gidanshi tsakaninshi da yarinyar nan ba za ku bari maganar ta kare a tsakaninsu ba sai kun shiga? Sai kun yiwo gayya kun cika mishi gida?

In ita Gambo bata laifi ne? kuma don ‘yar gata ce a danginta da ke da Alhaji Maikudi sai ace ba shi da iko a kanta? Tuni Hajiya Kubra ta soma kuka sosai tana fyace majina, ta ce “In tayi laifi Alhaji sai ayi mata duka har da targade? Kuma menene laifin nata, ta ki yiwa matarshi aiki? Mai aiki na kawo mata ne?

Yanzu mu da ku ka auro wasu matan a bayan mu haka muke yi musu? Inna Hajara ta leko daga cikin dakin tana gaishe shi, sannu da zuwa Mallam, nan da nan ya daga ido ya kalle ta ya ce, ai kuma duk kun zo ne kuna ciki? To duk ku fito, koma ciki ki gaya musu nace duk ku fito ku bar gidan nan.

In na bar nan kuma zan je in gaya wa Mallam har da ku a rura wutar fitinar dake aukuwa a gidan nan.”

Nan da nan suka yi ta fitowa suna tafiya saboda sanin matsayin Baba Yahaya wurin Mallam mai babban allo, matsayin da tuni ya maida shi ya zama dan gida, kuma mu’amalla da shi a matsayin dan uwa.

Yana tsaye a wurin har suka gama wucewa bai kuma fasa fadan da yake yi musu ba, sai da yaga sun kare ne ya kalli Hajiya Kubra dake zaune a kasa cikin ladabi tana sauraronshi ya ce mata.

“Kiyi hakuri Hajiya, kiyi hakuri na kuma roke ki kar kije ki ce zaki gazawa Alhaji Maikudi munin al’amarin tunda shima bai san hakurin ba.”

Gambo dake da ‘ya’ya mata hudu a jere, Kubra in aka barku ke da mijinki kuka yi yanda kuke so din kun yi mata adalci? Ai ke uwa ce ba sai na tsaya yi miki dogon bayani ba, kin san komai zai yiwu ne ku kaita inda zaku mantar da ita wadannan ‘ya’yan nata?

Kin fi kowa sanin ba zai yiwu ba, to kiyi hakuri kawai ki kuma rinka kwabarta duk da kin ki yarda da cewar ‘yarki mai laifi ce, amma hakan ba zai sa kuma kullum ki rinka goyon bayanta ba, don gyara kayanka Kubra ba fa ya zama sauke mu raba, haka nan kana kin naka ne don duniya taso maka shi.

Ta ce, “To Alhaji na gode, Allah ya saka da alheri.” Ya ce, “Amin.” Ya wuce ya fita ita kuma ta koma dakin Innarta, ta gyara abubuwan da suke bukatar gyara, duk da watsewar da dangin Inna suka yi aka bar Hajiya Kubra ita kadai, Mama ta kama kanta sosai tana can wurinta ta kame daga yawan zirga-zirga balle aje ga sakin maganganun da ta maida yin hakan dabi’arta ta kullum.

Ana cikin haka ne Baba Yahaya ya sake dawowa tare da wata Dattijuwa Sidiya, kowa ya santa ita da mijinta gyaran targade da karaya suke yi ita ya kawo ta shiga ta gyarawa Inna targaden da Babana yayi mata ta fito ya maida ita.

Rannan a gidanmu Hajiya Kubra ta wuni sai da tayi sallar Magariba aka zo aka dauke ta, Inna ma ta wuni a kwance ga dukkan alamu kuma lafiyarta ta rasa shi yasa ta wuni a kwance nima na wuni rannan ina hidimar dakinmu bata yi ta addabata da yawan aike ba balle aje ga tabkata da dukan da aka saba yi min kullum.

Washegari da sassafe sai ga Baba Yahaya da Alhaji Mai kudi, ga dukkan alamu kuma daga Masallaci suke tunda su din makwabtan juna ne, unguwarsu daya can suke wajen Makama New Adtention. Baba Yahaya ne ya fara shigowa gidan, Babana ya fito daga falon Mama wanda dama nan ne wurin zamanshi ko da kuwa shi din a dakinta yake.

“Sannu da zuwa Alhaji.” Baba Yahaya ya amsa kafin ya ce mishi “Ni da Alhaji Mai kudi ne.” Nan da nan yanayin Baba ya sauya, ya ce “To bari in bude muku falona mana.” Ya ce mishi “A’a, izini ya ce in zo in rokar mishi a wurinka yana so zai shigo ya duba Gambo.”

“To, to ai shi kenan.” Baba ya sake fadi cikin wani yanayi ya kuma wuce ya shiga wurinshi.

Har tsakar gidanmu Alhaji Mai kudi ya shigo, Innata ta fito ta durkusa tana gaishe shi, bai wani tsaya wajen amsa gaisuwar tata ba, zuba mata ido ya yi yana kallonta.

“Sannu Fadima, sannu kin ji. Sannu da kokari.”

Shi kuwa Baba Yahaya yana gefe yana kallon shi, shiga cikin Gambo ta mike ta koma ciki suka kama hanyar fita waje, yana cewa.

“Baba Yahaya ba ka yi min adalci ba Alhaji, ka zalunce ni ka sani na kawo yarinyar nan in da ba za a yi mata adalci ba, bayan kasan komai amma duk da haka kaje ka hada ni da Mahaifina.

To nima na ce ban yafe  ba, ku hadu ku rufe ni da duka tunda itama abinda ta fada kenan aka yi mata wannan zaluncin.”

Baba Yahaya ya ce, “To naji muje.” Ya tasa shi a gaba suka fita.

Rashin jituwa mai tsanani ne ya nemi shiga tsakanin Alhaji Mai Kudi da Alhaji Yahaya wadanda ban da ‘yan uwantakan da Mallam Mai babban allo ya hada a tsakaninsu su din makwabtan juna ne a unguwa daya sannan a kasuwama shagunansu kusan wuri daya suke.

Alhaji Mai kudi yaja ya tsaya kan bai duba kusanci da zumuncin da ke tsakaninsu ba, yasa Mahaifinshi ya tilasta shi bada kanwarshi ‘yar karamar yarinya a inda yasan ba za ayi mata adalci ba, saboda ya fifita son amininshi a kanshi, sai da mai babban allo ya tsawatar.

Tun daga wannan lokaci Mama ta shiga sakin maganganu masu zafi a tsakar gida saboda ta gane Babana ya dauki matakin daina yin duka ko da ta kai mishi karar Innata sai dai kawai ya yi magana da fatar baki, abinda ita kuma ba haka taso ba, tunda ita ka’idar ta ne kullum sai taje ta ce mishi  ga abin da aka yi.

Ko kadan Mama ba ta so Babana ya dauki irin matakin da Babana ya dauka ba na kamewa daga yin duka don kuwa kusan kullum sai na jita tana yada magana a tsakar gida.

“Ni fa kar mutum yaga wasu guntayen iyayenshi marasa girma da sanin darajar Surukuta sun zo sun yi wa Alhaji burga ya tsorata yayi zaton ko ni ma a tsoracen nake.”

Ta tabe baki ta ce, “Ko kadan ni din nan a gidana rashin jini ne rashin tsagawa, baka shiga sabgata ba ba ruwana da kai, amma kana doso ni da rashin mutuncinka, to kama ka zan yi in nada maka dukan tsiya  ba mai Kudi ba ko mai dala ne ina daidai dashi duk da a gaban Innata take furta irin wadannan kalaman, ta kuma san da ita take yi bata daga ido ta kalle ta ba, balle ta tanka mata.

Amma duk da haka wai bata tsira rannan akan ruwan bunu ruwan tin da babu komai cikin shi sai ganyen tea. Mama ta ce, “Wai Innata ta kwashe wa ‘ya’yanta ita ta basu dan kankani.

Nan da nan kuwa ta shiga zage-zage, Babana ya leko yana tambayarta “Menene ya faru ne?” Ta galla mishi uwar harara ta ce, “Ai don ka ji ina cewa zan bata kashi ne yasa ka zaburowa ka fito kana tambayata?

To ai ko kana tsaye zan yi hakan, don na gaji da irin cin kashin da ake yi min a cikin  gidannan, zan yi in gani ko nima za’ayi min irin wuju-wujun da aka yi ta yi da kai.” Ta zubawa Inna ido tana mata kallo irin na wulakanci.

“Ke nan ga ‘yar gwal ko? Ki zo gidan mutane kina musu rashin kunya da rashin mutunci saboda iyayenki, ba su yi miki tarbiya ba in an taba shi su ce za suyi wa mutane iskanci, to ni ba Alhaji ba ce babu ruwana da iya shegensu maganinki zan yi ba Mai Kudi ba, aje a turo min mai babban allo in ya tashi zuwa kuma kar ya zo da allon katako ya zo dana karfe.

Inna ta kasa hakuri ta ce, “A’a me iyayena suka yi miki? In dai akan wannan ruwan tin ne gashi nan na juye miki.”

Garin juye ruwan ti wani ya dallu a kafar Mama, nan da nan ta kara fusata wai Inna ta kona ta, ta shiga dura wa iyayenta ashar. Inna ta juya ta nufi dakinta tana fadin “kiyi ta zage-zagenki ni kam ai kowa ya ji abinda kike fada yasan bada iyayena mike yi ba, tunda kowa yasan su yasan su din ba mutanen banza ba ne.”

Abinda kawai ta fadi kenan Mama ta bita ta jawo ta tana tambayarta su waye ne na  banzan? Bata kai ga bata amsa ba ta rufe ta da duk ta turmushe ta a kasa ta hau kanta ta danne tana ta faman naushinta da kyar Babana ya samu ya dagata a kanta, ya kaita dakinta tana ta faman huci tana zage-zage.

“Haka kawai kaje ka dauko masifa ka kawo min cikin gida, ba dole in tsaya in yi maganinta ba, tunda kai ka kasa?” yana fitowa daga dakin Mama ya kai min maka, kafin ya daka min tsawar da ta katse min komai.

“Me aka yi da ki ke kur ma wannan ihun kina nema sai kin tara min Jama’ar unguwa a gidana?”

Shiru nayi na bi Babana da kallo har ya shiga wurin shi, an daki Innata an farfasa mata baki da hanci alhalin ba wani laifin ku zo ku gani tayi ba, amma ina kuka ya make ni ya ce, wai ba ayi komai ba.

A hankali na faki idon mutane na fita na bar gidan namu na taka da kafata na tafi har Makama edtention naje na gaya wa Hajiya Kubra abinda ya faru duka, ta ce “To babu laifi zauna ki karya kiyi wanka ki sauya kayan jikinki, sai ki koma gidanku.” Na ce mata “To.”

Ina dawowa gida na samu Inna cikin wani yanayi, ko dukan da Babana ya yi mata wanda gaba daya dangin Inna suka yi ta kai-kawo akai suna fadin maganganu bata ji jiki irin wannan ba, iyaka dai a wancan ta samu targade a hannu shima kuwa ta kare dukan da ya kawo mata ne da hannunta.

Cikin zuciyata na ce, “Wato dai da banbanci tsakanin dukan miji da kuma na kishiya?”

Ban san yanda aka yi ba, Baba Yahaya ya ji abin da ya farun da yamma sai gashi yazo gidan, don jin abinda ya faru. A gaban Babana Mama tayi wa Baba Yahaya wanki irin na babban bargo, ko dama can kuma nasan ta dade tana da cikinshi don ko maganarshi zata yi bata ambaton sunanshi sai dai ta ce mishi munafuki.

Haka bata zuwa hidimar gidanshi wai shi da matanshi sun ci amanarta, Baba Yahaya yana ganin haka ya juya ya fita ya bar gidan ya barta tana ta zage-zagenta, tana hadawa har da abokin nashi wato Baban namu, har tana ce mishi wai tunda shi ya kasa to ita zata yi mishi maganinsu.

Tana nan tana jiran zuwan Alhaji Mai kudi, zata nuna mishi bai da wayo, zata gaya mishi magana irin wacce bai taba ji ba, zai gane shi din kyalle shi kawai ake yi da wata tebar shi kamar kullin kayan wanki.”

Har Babana ya gaji yasa kai ya fita ya bar gidan Mama bata gaji tayi shiru ba, sai tambaya take yi a kanki na fara ganin kishiya? Guda nawa aka yi min? ke ce ta shida, ke ki ka fi kowa? Shafaffiya da mai, ki zo min gidana ki ce za ki gallabe ni, ke din banza!

Ai tunda abin ya zama haka, to za mu sa kafar wando daya tunda kuma na gano abin naku tsiya ne da kuma rainin hankali, to zan tasa ki a gaba zan ga yanda za’ayi kiyi zaman gidan nan, sai dai ko in shi mai kudin ne zai zo ya taya ki zaman ko?”

Ana cikin haka sai ga Hajiya Kubra ta shiga cikin gidan tana fadin, “Mama ja’ira Mama mara mutunci, Mama mai rashin kunyar karya, to don kin daki Fadima sia me? Sau nawa ki ka haife ta? Don kuma yi kanki don dan girman da take baki kina rainawa ya kara zubewa, hakan kuma ba zai hanata sake hada shimfida da mijinki ba, sai dai ma ta kara. Tsohuwar banza kawai mara mutunci.”

A fusace Mama ta fito  tana tambayarta “Ke ce ki ka zo baki turo Mai kudi ba?” Hajiya Kubra ta ce, “Ai sai kan abinda yafi karfina ne ki ke ganinshi yaje ke kuwa ni ce zan yi maganinki sakaryar banza wacce uwargidancinta bai amfani mijinta da komai ba sai karin fitina. Sakaryar tsohuwar da ta rasa masu zaunar da ita su gaya mata gaskiya.”

<< Mijin Ta Ce 1Mijin Ta Ce 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×