Skip to content
Part 20 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ina cikin haka naji kamar an yi min magana, a firgice na ce iye, na’am? A hankali ya bude baki ya ce min yi maza ki kulle kofa kar Mama ta shigo ta same ki, da gudu naje na kulle kofar na dawo na durkusa a gaban Ado, kuka sosai nake yi yayin da shi kuma yake kwance bai motsa ba lokacin ne na gane tsoratar da nayi ne ya hanani gane ya farfado, tun sanda na ji atishawa da hamdala sai nayi zaton ko daga wani wuri ne.

Muna cikin haka na ji isowar Mama tana fadin “Lallai yau za’ayi wacce za’ayi, bude min kofar in ga abin da yake ciki in bai tashi ba ai sai dai in hada su za’ayi a hada su gaba daya in kuma nayi sa’a ya tashi to uwata zata ci gari na wayewa kuma zan tattara ta koma dakin uwarta.” Gwam-gwan-gwan, duka suke yi da iyakacin karfin su nayi matukar tsorata don ji nake yi tamfar zasu balla kofar su shigo, don haka na tsallaka can bayan katifar na makure.

Ado ya tashi zaune nayi matukar kara tsorata saboda ganin da nayi tanfar zai bude kofar ne saboda yawan kiran da Mama ke mishi “Adamu! Adamu!! In kana nan amsa mana in ji ka.” Cikin karfin hali ya ce, “Lafiyata kalau Mama, je ki gida kawai sai da safe.” Da kyar ta hakura ta tafi saboda ganin da tayi ya ki yarda da bude kofar.

Har gari ya waye ban tashi daga inda nake takuren ba, yayin da shi kuma Ado ya koma falo ya zauna ban san me yake yi ba sai da na ji an yi kiran Sallar farko ban ga shigowarshi don yin alwala ba, lokacin ne na mike da kyar na tashi saboda ciwon da jikina nima ke yi min na leka shi yana zaune ne kan kujera ya kuma kwantar da kanshi akan masagalin kujerar ya kuma dora hannayenshi duka biyu a kan nashi alamar dai ya addabe shi da ciwo.

Durkusawa nayi da gwiwoyina duka biyu na ce mishi “kayi hakurin abin da nayi maka.” Da iyakacin gaskiyata hakurin kawai nake bashi ba tare da wani tunani ba, don na riga na tsorata na kuma yi nadamar daukan wannan mummunan shawara da nayi, na yi amfani da ita da Ado bai farfado ba to da wanne hali zan shiga? Ba abinda Mama zata yi ne matsala ta ba, girman laifin ne na tsorata dashi.

“Kayi hakuri.” Bai amsa ba, bai kuma motsa ba daga yanayin kwanciyar tashi, shiga Masallaci da ya ji anyi shi ne abinda yayi dalilin mikewar shi ya nufi bandaki sai da yayi wanka sannan yayi alwala ya fito yayi raka’atil fijr, sannan yayi sallar Asuba ya idar yana jan carbi nima na idar na shafa fatiha sannan na kalle shi na sake ce mishi “kayi hakuri ka ji?” bai kula ni ba.

Aka soma buga kofa da karfi kamar na jiya da daddare, gwan-gwam-gwan. Ya mike ya bude, Mama ta shigo da damarar gyale a kugunta rike kuma da sharbebiyar dorina a hannunta, nayi maza naja can baya na makure a jikin bango sai faman kaduwa nake yi, don in ta soma dukana yau ban san wanda zai kwace ni ba, tunda shima Adon bai huce ba daga mummunan abinda nayi mishi.

Yau za ki gamu da ni, yau za ki san bakko miya ce in ma uwa ki ce ta turo ki ku kashe min shi to zaku san karya ku ke yi yau zan yi maganinki ke da iyayenki masu koya miki mugun abu.”

Me ya faru Mama? ya yi maganar cikin natsuwa, ta dago ido ta kalle shi kamar zata yi mishi magana sai kuma ta fasa, watakila don ganin da tayi tanfar bata lokacinta zata yi, don haka ta zabura ta dago bulalar da niyyar sharba min, ni kuma na takure ina sauraron ta inda zan ji saukarta, sai kawai na ji shiru.

Mama tayi maza ta waiwaya don ganin abinda ya rike mata bulalarta ta baya, taga Ado a tsaye da bakin bulalar a hannunshi, sake min bulalata, tayi mishi maganar cikin tsawa, nan da nan yayi hakan tare da fadin na sake Mama, amma kiyi hakuri kar ki ce za ki taba ta, ai in mun yi fada ba rama min zaki yi ba, nima da kaina in kin bar ni zan rama ai ba fin karfina tayi ba.

Ran Mama ya kai matuka wajen baci, da ta gane ba zai barta ta buge ni ba, ta shiga zage-zage tana hadawa har da shi a ciki, kiyi hakuri Mama, kar ka sake bani hakuri, tayi maganar cikin tsawa da fusata, kiyi hakuri Mama, ya sake bata hakuri. A hankali kuma cikin natsuwa da nuna ladabi har ta dan sassauto tayi kamar zata juya ta fita, muje gida yanzu ina zuwa Mama, kamar ta yarda zata yi hakan sai kawai naga ta juyo da iyakacin karfinta ta daga dorina zata sharba min, da sauri ya sake kama dorinar ya rike, ta sake juyowa tana kallon shi cikin karin fusata, zaka rike min bulalar ne kuma? Cikin natsuwa ya sake ce mata, mace a gidan mijinta Mama ya kamata ace tana da ‘yancin walawa, hukuncinta ya zamo a hannun mijinta ne kawai ba wai duk wani wanda ta yyiwa wani abu sai kawai ya zaro bulala ya ce zai buge ta ba, ba tare da ya sanar da mijin ta ba.

To ai nan ba gidan ka bane, balle ka ce na mijinta ne, cikin hanzari ya ce haka ne. Mama ta ci gaba da maganganu gidan mijina ne ni naga dama kai da ita ku ke zaune a gidan ita din kuma ni naga dama ne na ce a baka ita ko nawa ka kashe a cikin hidimar auren?

Ya ce, babu, ta ce to babu inda zani yau sai ka rubuta takarda ka sake ta tukunna tunda dama komai akan alkawari muka yi shi da kai, ya ce haka ne to kije gida ina zuwa. Ta sake fadin babu inda za ni ai gidan mijina ne in naga dama na ce a nan dakin zan kwana kana da yanda zaka yi dani ne? A hankali cikin natsuwa ya ce mata babu, ya waiwayo ya kalle ni a inda nake takure ya ce min shiga ciki.

Nayi maza na tashi na shige cikin na bar shi a nan don yin hakan ya fiye min sauki akan zaman da nake yi a cikinsu, ina ganin abinda ke faruwa. Ina so tabar min gidan a yanzu tunda na mijina ne, ya ce ai na ji Mama, amma na roki arzikin ki dan yi hakuri kadan ki dan saurare ni ba wani lokaci mai tsawo zata dauka a cikin gidan ba.

Mama tasa kai ta fita, shima Ado ya koma ya zauna akan kujera, ni kuma ina can cikin daki makure wuri daya, kirjina sai faman bugawa yake yi bal-bal-bal saboda ban taba ganin abinda ya firgita ni irin na jiya da yau ba, Ado da Mama suna kace-nace bayan kowa yasan kullum Ado akan bin umarnin Mama yake.

Wajen karfe takwas da rabi na ganshi yana shiri kamar in tambaye shi ina za shi? Sai kuma na fasa, saboda yanda fuskarshi take daure gashi kuma dama ban saba yi mishi irin wadannan tambayoyin ba. Yana fita daga gidan na koma can cikin daki na zauna ina tunanin in yanzu Mama ta shigo ko ya ya zan yi da ita? Oho.

Sai kawai naji sallamar Hajiyar Giyade da sauri na fita naje na tare ta, tana rike da food flask din da aka kai mata abinci a hannunta, nasa hannu na karbi food flask din tare da fadin, gani ga ki amma ba ki taba shigowa ba sai yau, don na kai miki tuwo kin ji miyar amayar mai zaki shi ne ki ka kawo min food flasks? To bari yau ma zan sake aiko miki da wani tuwon don gobe ma ki sake shigowa ki kawo min kwanon.

Tayi murmushi ta ce, oh’oh-oh’oh, ni ba don kwanonki na shigo ba, zuwa nayi don maigidan ya ce min in zo in zauna mishi a gidan kafin ya dawo.” Cikin zuciyata na gane abinda yasa Ado yin hakan, shima tsoro yake kar bayan shi Mama ta shigo ta same ni ni kadai.

Muna zaune da Hajiyar Giyade mu biyu hira muke yi bayan nayi mata abin karyawa ta karya ta koshi, sai sakucen hakoranta take yi da tsinken sakace a dalilin farfesun kaza da tasha, sanin da nayi cewar tun asalin dama can Hajiyar Giyade tana son Gambota tana kuma matukar sona ya sani sakin jiki da ita sosai, har na kwashe bayanin duk abin da ke tsakanina da Ado, da abin da ya faru daren jiya da abinda yasa ya turo ta taya ni hira duk na gaya mata, don kuwa neman abokin magana nake yi saboda damuwa tayi min yawa.

Hajiyar Giyade tayi min wani lalataccen kallo ta ce, to abinda ya rinka yi wa uwarki ba sa shi aka yi ba? Yanzu ma kuma za’a sa shi yayi ne? Ba gashi nan ba a yanzu kullum yana kai-kawo a tsakani kuma da ban sani ba ai nasan ba da gangan yake yin abinda yake yin ba, to kuma in ban da shirmenki da kayi cuta ka cuci abokin zamanka ai gara shi ya cuce ka, tunda babu wani abin da ba ayin sakayya akanshi musamman ma ace shi wannan abin kan lamarin aure ne. yanzu ace Gamborku bata soma ganin sakayya ba? Gamborku fa surukaye uku tayi rana daya, wane arziki ne ya wuce wannan? Kuma kana ganinta ma a cikin gidan ai kasan walwalarta ma ta dan sauya jinin jikinta ma ya soma dawo mata saboda wahalarta ta soma raguwa, gashi yanzu kullum zaka ganta a wadace cikin harka ni a zatona ma na ce ko mijinki ne oho, na ce anya shi ne kuwa surukayen nata wadancan din ai dukansu ‘ya’yanta ne, ta gyada kai ta ce oho ban sani ba, amma ina ganin mijinki ma yana cikin aini ba yarinya ba ce nace haka ne Hajiya.

Hajiyar Giyade ta gyara zama ta ce, to ko wannan tijara da ja’irar yarinyar nan mara kunya tayi wa Babanki da wannan mata shekaran jiya in ban da alhakin Gamborku da ya kama su me ya kawo hakan? Nayi maza na ballo barin goro na mika wa Hajiyar Giyade ta shiga goga shi a magogin goronta tana watsa shi a bakinta, ni kuma na kara mannewa da jikinta kafin na kara tambayarta ni me ya hada su ne Hajiya?

Ta ce, uhun in ban da iya shege menene wai kama su tayi suna yin wani abu ranar girkinta bayan kuma dama da nata girkin da natan duk ita kadai aka hadawa, na sunkuyar da kaina kasa cikin yanayin jin kunya, cikin zuciyata dai cewa nake yi lalle yarinyar nan da kafirin iya shege take, yanzunnan Babana ta yiwa irin wannan iya shegen? Ita kuwa Hajiyar Giyade babu ruwanta, sai bayanin ta take yi amma da maganar tazo wurina na gaya musu dukansu ita mijin nata na gaya musu dama gulma da munafurci ne ya saku yin hakan, don ku cutar da Binta, to gashi nan abin ya koma kanku.

Ni kam ban yarda na tofa cikin wannan zancen ba, illa iyaka dai na amsa sallamar Hajiya ‘Yar dubu, itama rike take da food flask dina a hannunta na kalle ta nayi dariya nace, kema kwanona ki ka kawo min? ta ce, oh’oh, wane kwano ne zai fiddo ni a ruwan nan? Uwarki ce tayi wa Mallam waya ta ce mishi wai mijinki babu lafiya, gabana ya yanke ya fadi me Gambo ke nufi da wannan wayar da tayi kar dai itama zafina take ji?

Ina yake yanzu, ko yana ciki ne a kwance? Tayi tambayar bayan sun gama gaisawa da Hajiyar Giyade, sun yiwa juna ban gajiyar biki har tana fadin ai ban san kina nan ba Hajiya da na zo miki hira, Hajiyar Giyade ta ji dadin hakan da ta gaya mata ta kwashe zance duka ta yi wa Hajiya ‘Yar dubu, har da yiwa bayanin kwaskwarima na ce ah Hajiya…kan in fadi abinda zan fada Hajiya ‘Yar dubu ta daka min tsawa ke tafi can ki baiwa mutane wuri akan zai taba ki ne ki ka kwantara mishi karfe kina neman kashe shi?

To zauna ya bar ki ba shi kenan ba sai ki rinka jikawa kina sha ko ki kai inda za ki kai. Hajiyar Giyade ta ji takaicin maganar, ta ce a’a Hajiya wannan ai ba zancen da za ki yiwa yarinya ba ne, sai kiyi mata fada kawai irin wanda ya dace da ita.

Rannan cikin dare na yi wa Gambo waya don in gaisheta, bata dauka ba kamar yanda dama kullum nake mata washegari ma da sassafe na kira ta bata amsa ba, gashi kuma ina ji ta bugo waya ta gaida Ado da jikinshi, a zuciyata na ce ha’a to me na yi wa Gambo? Me babban allo yazo gaida Ado wai da jiki, ya gaya mishi gani nan zuwa zai turo ni don in gaishe shi amma naje zauren shima ban same shi ba ya tafi.

Na dawo daki na zauna zuciyata takai matuka wajen baci, me nayi musu? Me nayi kowa yake fushi da ni? Ban san yanda aka yi ba kawai naji hawaye suna zuba a idona, kuka na soma yi sosai.

Ado ya juyo ya kalle ni, me ya same ki Humaira? Me ya saki kuka kuma yanzu? Ko kuma kin tuna da irin takurawar da nake yi miki ne? Rarrashi da yake yi min ya sanya ni bude baki na ce mishi ban san dalili ba ne kowa sai jin haushina yake yi. A hankali ya ce min haba Humaira, kowa fa kika ce, kenan har da ni cikin masu jin haushin naki? Na gyada kaina nuna alamar eh har dashi.

Ya ce, uh’uh ni bana jin haushin ki,ina dai so ne kawai in dan rinka danne zuciyata ina yin hakuri kar in rinka yawan sakin jikina ta yanda zan yi tasa rai a kanki ina matsa miki tunda na gane da gaske kike yi ba kya son haka din.

Ban tankawa zancen nashi ba, iyaka dai na riga na sawa zuciyata wani al’amari tunda na gane har da Gambo cikin masu fushi da ni akan Ado, bata lura da irin tasa Ado a gaba da Mama tayi ba kan sai lalle Adon ya sake ni.

Kwana wajen hudu a jere daga wurin Gambo ake kawowa Ado abincin dare na kuwa gane hakanne a dalilin Sa’adatu da ke kawowa da ganin irin kwanukan da ake zubo mishin kuma kasan ba karamin girma Adon yake dashi ba a wurinshi, yana gama cin abincin in ya gama abin da zai yi zai dukunkune kan ‘yar kujerar da ke falon yayi kwanciyarshi iyaka dai bai cika yin wani barci ba, bini-bini kuma zan gan shi yana jika jar kanwa ko andre leber sold yana sha.

<< Mijin Ta Ce 19Mijin Ta Ce 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×