Skip to content
Part 22 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Har Asuba tayi ban iya daina kukan da nake yi ba, saboda dalilai guda biyu, na farko dai in ma Mama taci galaba a kan Ado ta tilasta shi sakina in zama karamar bazawara kamar yan’dda dama can tayi buri tunda nasan tana da karfi akan al’amarinshi, ko kuma aurena dashi ya ci gaba kamar yadda ya kwana yana yi min alkawarin in kwantar da hankalina in saki zuciyata muyi zamanmu lafiya babu abinda zai samu aurenmu.

Babu mai sa shi ya rabu dani ya kuma godewa Gambo da ta sanya ni nayi mishi alherin da nayi mishi, to in auren namu ya ci gaba da akan son ran Mama ba tunda nasan ba za ta taba son zamana da dan uwanta tunda tun asali ma ba don a zaunan ta sa shi yin auren ba, zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin da nake bukatar samu a rayuwar aure na ko kuwa na rinka zama cikin fitinar Mama kenan tayi min ta yi wa mahaifiyata?

Shi kuwa Ado wanda ya kwana cikin matsanancin farin ciki gani yake yi tanfar matsananciyar wahalar da na gamu da ita a wurin shi ne ta sanya ni kukan da nima na kwana ina yi, don haka ya kwana yana rarrashi da ban baki da fadin kalamai masu nauyi tare da alkawarin zai tabbatar min da cewar shi din namiji ne.

Na idar da Sallah kenan sai ga Hajiyar Giyade ta shigo, na tabbatar Ado ne ya turo ta, kai lalle Ado namiji ne ko ya ya aka yi yaje gaban Hajiya yayi mata wannan bayanin? Oho. Cikin zuciyata ne kawai nayi wannan tunanin, oh’oh sannu Humaira sannu kin ji? Sannu Aishatu sannu da hakuri kin ji? Allah dai yayi miki albarka, ya kuma kara rufa wa uwarku asiri ku dukanku ukun, haka aka yi haka nan aka same ku lafiya lafiya sai alheri.”

Sunkuyar da kaina kasa nayi ban iya ce mata komai ba, saboda tsananin kunya ai ma kin yi kokari kin taimaki kanki kin yi abin da ya dace ayi miki, to amma duk da haka sake shiga ki kara wani wankan don ki kara gasa jikinki sosai, ban yi musu da ita ba.

Ado ya shiga kai-kawo da hidimomi iri-iri ko kunyar su Hajiyar Giyade da Hajiya ‘Yar dubu da suka zo gidan baya yi, wai har hira yake yi da su Hajiya ‘Yardubu ta kalle ni ina makure wuri daya saboda zuciyata ta ki yi min dadi, ta ki yarda da cewar in sake ta tayi walwala taji dadin al’amuranta, musamman da yake na jiwo maganganun da Mama ta gayawa Ado sanda ya shiga wurinta da safe bayan Hajiyar Giyade tazo wurina saboda akwai hadakar bango tsakanin cikin dakina da nata.

Amma wai sai Hajiya ‘yardubu ta kalle ni ta ce min oh’oh mahakurci dai mawadaci, wannan fa shine wai komai wayon amarya a sha manta, to yau dai Adamu ya zama miji karya kuma ta kare.

Kuka sosai na kama yi ita kuwa Hajiyar Giyade ta soma yi mata magana Hajiya ke dai munin nan naki bai da wani dadi, zo ki tafi gidanki kije wurin naki mijin ki bar min Aishana ta huta, karyarta bata wani kare ba me akai kuma da maza, da za ki ce mata wani karya ya kare?”

To haka al’amarin ya zama, shiryawata da Ado sai ta haifar da al’amura masu yawa a ta bangarena dashi dai sai nake ganin tanfar ba a taba son wata ‘ya mace kwatankwacin irin son da Ado ke nuna yana yi min ba, ko kuma don ban taba sanin yanda son yake ba ne, ban kuma taba yin dacen ganin wacce ake son ba ne? oho.

A tsakaninshi da Mama kuma abin ya kara cabewa har ya shiga zullumin shiga cikin gida da dai ace yasan in bai shiga ba ita ba zata zo ba to da ya rinka dadewa bai shiga don maganganun ba su da dadi, to ka’ida ne kullum sai ta shigo da safe da daddare sannan a gabana ma gaya mishi take yi ba fa a kanta muka soma ganin yarinya takai budurcinta ba, duk ‘ya’yan dakina da kake gani ‘yanmata aka same su yauwa ba sabon ba ka taba mace ka haukace.

To wannan ma har wata mata ce da za’a rude akanta? Yayin da itama Mama take wannan tashin hankali itama Gambo nata sha’anin take yi, aike biyu tayi tana tambayar Ado ya bada lokacin da ya ga ya dace azo ayi min jere a sanya min kayana don mu ma mu ji dadin zama a inda muke, shi kuwa sai yayi murmushi ya ce a gayawa Gambo tayi hakuri kawai ta huta ai shi din mace ya nema ya kuma samu an bashi, don haka ya gode da alherin da aka yi mishi maganar kaya kuwa a bar su ba shi da bukatarsu wadanda aka kawo mishi sanda aka kawo mishi matar shi sun ishe shi.

Kusan sati biyu ne da faruwar abin da ya faru a tsakanina da Ado tun lokacin nan kuwa ban sake yarda ya taba ni ba, tun yana hakurin har dai na kure hakurin nashi, don haka akan dole jiya da daddare na hakura na kyale shi yayi yanda yaso, wanda ba ni da na ji a jikina ba shima yasan ba karamin takura nayi ba.

Amma duk da haka da gari ya waye na fito na kama ayyukana na gida, don dai in samar mishi da kwanciyar hankalin cewar bai kware ni ba, duk da ni kam nasan ya kware nin, ina sunkuye ina karasa wanke wurin da nayi wanke-wanke ban san hawa ba ban san sauka ba kamar daga sama sai kawai naji saukar bulala a jikina da iyakacin karfina na kurma ihu.

Ina daga ido naga Mama ne mai dukan, kuma na yanka da gudu na nufi dakina saboda neman mafaka, da saurinta ta biyo ni tana fadin “Ja’ira mai gadon raba zumunci, ai ni ba za a kawo min wannan iya shegen ba, a hanya muka gamu da Ado ya fito daga dakin cikin sauri daga shi sai gajeran wando Boders fari sol, hannu ya saka ya tare ni ya hana ni shiga dakin ya maida ni bayan shi na tsaya, me ya faru Mama?” yayi tambayar cikin natsuwa duk da dai fuskarshi ta riga ta baiyanar da motsuwar zuciyarshi.

“Kaga ja’iri mara kunya, a gabana ka ke taba ta?” Ta yi maza ta sake daga hannu zata sharbo min bulalar ya tare da hannunshi, “Matata ce ai Mama don na taba ta ba wani laifi nayi ba, sannan na fara gajiya Mama, zuciyata ba za ta iya ci gaba da daukar irin wannan abin ba, kin yi sammakon zuwa dukan yarinyar nan alhalin ba ki san yanayin da ta kwana a ciki ba, ko tana da lafiya ko bata da ita.”

“A’a karya kake yi gaya min dai abin da kake son gaya min din, ja’iri mara kunya mara mutunci akan wannan ja’irar yarinyar? Ai in ba hanzarin raba ku nayi ba to in ba sa’a nayi ba ina zaune ne kawai zanga ka rufe ni da duka.”

Ta sake sharbo bulalar ban san yanda aka yi ba sai kawai na ganta a hannun shi, “Haba Mama, wannan fa  bulalar doki ce kike duikanta da ita.” Ban ita nan.” Tayi mishi irin tsawar da bata taba yi mishi ba, a’a Mama ba zan baki wannan bulalar ki buge ta ba.

Bayan bata yi miki komai ba, in kuma tayi miki ma ai ni ya kamata ki gaya wa in yi mata nasiha sai in bata ji ba ne zan sake dubawa in ga wani matakin da zan dauka amma ba duka kan wannan ba, ai ba zai yiwu a buge ta tana budurwa sannan yanzu ma tana matar aure tana hidimar mijinta da daukar dawainiyar shi ace za a buge ta, ko nima da nake matsayin mijinta in tayi min laifi a yanzu hakuri zan yi tunda nima akwai abubuwan da nasan hakuri zata yi dani a kansu.

Ni ban taba ganin ana bin matar aure gidan mijinta a buge ta ba sai ita, gaskiya ni kar a sake yi min haka Mama, na roke ki don bana so.

Kasake Maman tayi tana kallon Ado, cikin kaduwa da mamaki. Ai in bar maka ita ta sangarce ta lalace kenan, tafi karfinka taje tana rabaka da ‘yan uwanka tunda su abinda suka fi iyawa kenan?

Ya ce, a’a ni ban san abinda suka fi iyawa ba, Mama na dai san hakkukuwana da ke kanta tana kokarin tsare min su, maganar zumunci kuma ba ita ce ta hada ni da su Ibrahim ba mata suka kawo Baba kuma ya ce bai yarda a rinka shigo mishi da matan banza cikin gidan shi ba.”

Kasake Mama tayi tana sauraron Ado cikin kaduwa da mamakin kalaman bakinshi, uh yanzu nasan kasan mace, tasa kai ta fita kamar ace tayi fushi zance ya kare amma ina?

Da daddare nayi wanka ina zaune gabanshi yana shafa min wani mai a tabon shatan dukan Maman da ke jikina, yana yi yana fadin nan da shekara guda in muna raye ba za ki ga tabo a jikinki ba Humaira, tunda ni me za ki yi min in buge ki? Ai in ma kin yi min laifin dukan to bai wuce in yi kamar zan kade miki kura da bakin rigata ba, tunda nasan ba za a dauki wani lokaci mai tsawo ba zan dawo miki da lalurata.

Muna cikin haka sai ga Mama ta shigo har can cikin dakin, tana ganinmu ta soma fadin uhun, ni fa nasan ba haka kawai kake yin abinda kake yin nan ba, don haka na yafe maka duk laifuffukan da kayi a sanadin zuwanta gidannan in ma hadin baki suka yi na su bata tsakanina da kai to ba su isa ba, ba za su raba mu ba.

Rubuta mata takardarta kawai in tasa ta a gaba in kai wa uwarta ita don in gaya mata gata nan na kashe wannan wutar aniyar kowa kuma ta bishi, kamar dai in ce amin sai na fasa saboda  Ado da kuma ita Mamar kanta don haka sai na fadi kawai a zuciyata.

Shiru Ado yayi yana jinta bai tanka ba tayi rarrashi da ban baki iri-iri bai motsa ba, da ta tunzura da shirun nashi sai ta ce mishi, amma dai ka san dagewa kan zama da itan yana nufin ne kayi zabi tsakanina da ita. Yin wannan zabin kuma ba karamin fitina zai zama maka ba, don zaka fita daga gidan nan zaka fita daga cikin harkokina, za kuma ka fita daga cikin dukiyar mijina da ka yi wa kane-kane, sannan ko kayi hakan zan kuma iya bi ta wata hanyar da zan rabaka da ita da karfi tunda in kai ban gaya maka ka ji ba shi uban ta ai zan gaya mishi ya ji. Ya ce mata haka ne.”

Muna cikin haka ne sai kawai ga Suwaiba ta shigo da gudu, “Mama wai ki zo da sauri ga Anti Habiba tazo.”

Suna barin dakin, Ado ya kalle ni cikin wani yanayi da yafi kama da na tausayin kai, cikin karfin hali ya tambaye ni in na ce miki ina sonki za ki gamsu? Da sauri don in kwantar mishi da hankali na ce mishi me zai hana? Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce, “Duk abubuwan jin dadin da nake ganin kamar yau ma za ki daure kiyi hakuri dani in same su sun rushe ko?

Nayi murmushi na ce, sai dai in kai ne baka so.” Ya saki wani lallausan murmushi ya ce, “Humaira in tambaye ki mana?” Na ce to, dama dai kayi sa’a in san amsar tambayar, kin taba sanin wani abin da yafi aure dadi? Nayi dariya na ce in dai auren na namiji ne kamar ka to ina ganin kamar babu. Dadi ya kama shi, ya jawo ni jikinsa.

Rannan kwana muka yi ni da Ado tanfar dai dama mu din ba bakin juna ba ne, tanfar kuma ya mance da kasadin da Mama ke yawan yi mishi na cewar tari mai karfi in kayi a wannan dakin ina jin shi, don haka babu wani abin da ku ke ciki wanda ban sani ba.

Harkar gabanshi ya yi, nima kuma ban takura mishi ba, saboda a yanzu nima ba zai yiwu in ce ba na sonshi ba, ban da haka kuma na riga na gane Gambo tana son auren namu a yanzu in kuwa haka ne to zan yi komai wajen ganin Mama bata kwacewa Gambo mijinta ta kuma sake hana ta jin dadin surukinta ba.

Washegari da safe Ado ne ya shiga gida don gaida iyayenmu, ya dawo yake gaya min cewar, kin ji ashe wai zuwan nan da Habiba tayi jiya uwar mijinta ce ta kora ta bayan mijin ya nada mata dukan tsiya, kuma don wulakanci baki ga doguwar wasikar da suka hado ta da ita ba, wai ta zauna a gida daga nan zuwa watanni uku don ta koyi tarbiyya.

Na kalli Ado kawai cikin zuciyata kamar in fadi wata magana sai kuma na tuna ba zai yarda in gayawa Mama wata magana ba, don haka naja bakina nayi shiru na buge da cewa kai abin bai yi dadi ba, yaushe aka yi auren da har za’ace a dawo gida ayi zaman wata uku?

Ya ce, to ai kin san bakinta itama kuma ba kunya ne da su ba, na dia ja bakina nayi shiru. Kiyi abin karyawa da ita na ce to. Tun daga lokacin ya zama min ka’ida Gambo yi girki bayan abincin da nake zubawa na cikin gidanmu zan kuma zuba na Habiba daban. Ado ne yasa ni yin hakan ga kuma kwanukan su Ibrahim safe, rana da dare, amma duk da haka ban fita ba a wurin Mama, wai ban sa mata nata kwanon daban ba, na sata a hadaka sai kace ni tawa uwar ba a hadakan na sakata ba.

Saboda gudun fitina, bayan kuma ni nasan zai yi wuya Gambo taje tana wani diban abincin da na aika dashi a kunya da kara irin nata ma ba za ta je tana yin hakan ba.

<< Mijin Ta Ce 21Mijin Ta Ce 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.