Tuni dama Mama ta riga ta yada rashin jituwar dake tsakaninta da Ado, bata bar shi ya zama sirri ba a tsakaninsu, don haka kowa yasan da maganar, ta dauka hakan zai zamo tozartawa ga shi Adon ko kuma Gambota ace ta mallake mata kani ta rabata dashi, ta sani ba kanta ta jawa magana ba, don kuwa mutanen da suka santa suka san komai na sirrin zaman gidanmu da dalilin da ya sata tasa Ado aurena sai albarka suke sawa Adon suna fadin mun gode mishi kaga min jarumin yaro ai gara da yayi mata haka.
Wannan magana da ta riga ta bayyana kowa ya san da ita yasa dawowar Habiba gida ya zamo abin gulma abin tattaunawa a tsakanin mutane wasu ma fadi suke yi to ai gashi nan tana kokarin fidda wata ga tata nan an korota.
Baba Yahya da kanshi ya nemi wani abokinshi ya dauki Habiba a motarshi suka je har gidan don maida ita dakinta, daga nan su baiwa uwar mijin hakuri, tunda dai an yi sa’a hutu suka bayar basu furta kalmar saki ba.
Amma uwar mijin Habiba tayi kememe ta kekasa kasa ta ce ai tunda da bata hutun nan sai tayi shi in dai ba sun gwammace auren ya mutu ba ne, tunda dai ai sun san ‘yarsu zata gidan wasu, amma basu tsaya suka yi mata tarbiya ba.
Shi kuwa uban mijin da suka koma ta wurinshi ko zai yi halin maza ya ce a’a tunda an riga an kawo ta to shi kenan iyaka dai a kwabe ta don gaba kar ta kara sai yace tunda hukuncin da Hajiya ta zartar kenan sai dai ayi hakuri aje kawai in lokacin yayi a dawo da ita.
Wurin Ado naji labarin saboda abinda aka yin yayi matukar bata mishi rai, ni kam murmushi na dan yi can cikin zuciyata dai cewa nayi ashe dai ba Babana kadai aka yi wa irin wannan kamun kazar kukun ba.
Duk da irin hidima da dawainiyar da nake yi da Habiba saboda tausayinta da nake ji gashi kuma na gane dan karamin ciki ne da ita komai bata nake yi ko ba ta zo ba in aike mata dashi don nasan tana bukatar kulawa ta musamman amma bata gamsu ba haka Mama gabadaya jin haushina suke yi tanfar dai ni naje na fito da ita daga gidan mijin nata.
Kullum dai ta shigo dakina sai ta zagi dakin sannan shigarshi babu ka’idar sallama a wurinta, sau biyu tana samuna kan shimfida tare da mijina amma hakan bai hanata shigan mana daki babu sallama ba. In kuma abu ta gani ko na diban mata sai tasa hannu ta kwashe sauran.
Rannan dai abin nata ya ishe ni ta shigo falo babu sallama bata ganni ba ta biyo ni can cikin daki bayan kuma tasan Ado yana gida muna tare a ciki, don haka na kalle ta na ce mata “Habiba kar ki sake shigo min daki babu sallama, bana so kuma in kin yi sallamar ma ban yarda dan baki ganni ba ki biyo ni cikin dakina, don kuwa wurin sirrina ne ni da mijina.”
Sai da tayi wa dakin kallon banza sannan ta tambaye ni, me ye a cikin wannan sukurkutaccen dakin naki da babu komai a ciki sai ‘yan tarkacen kujerun da?” Na ce ai ba kayan daki ne aure ba, Habiba da sune to da tuni anyi nasarar korata daga gidan da kuma ba a koro wasu daga nasu gidajen ba, don haka aure daban kaya daban in ana maganar aure kuwa to miji shi ne maganar in aka yi dacen samun shi to shi kenan zance ya kare.
A fusace tace mijin da kike gadara da shi din dai ai kawunmu ne kuma kema dolenki sai kin fito, na ce oho kin dai riga ni fitowar sannan ko Kawunki ne ba mijin ba ne tunda ba za ki yi abinda nake yi dashi ba, don haka kar in sake ganin kin zo kin daukar mun wani abu ba ki sanar da ni ba.
Kin kuwa san duk yanda ki ka kai da gadara da abinshi saboda kusancin da ke tsakaninku, baki kaini ba, tunda kin sha fado mana daki babu sallama, kina ganin mu a shimfida guda daya, ko ba haka ba? Gidan Kawu ai ba abin gadara ba ne gidan miji shi ne abin gadara ba ki ga ni daga shigowana sai nayi kane-kane na kankane komai ba? Na wuce zan kai abinda na kwace a hannun nata kicin in ajiye.
Ado ya leko daga daki “Ke Humaira menene haka? Maida mata dasu, na ce to na kawo na bata ta karba ta fita ta tafi sai kuma gata ta dawo ta dangwarar mun da su ta juya ta tafi tana maganganu kici ki kara kece bakuwar dadi na ce eh ni ce bakuwar su na kuma gode da na yi sa’a na samu a gidan mijina.”
Nayi ta zuba ido ko zan ga Mama ta shigo da bulala ko kuma ta turo a kira mata Ado don ya amsa tambayoyi kan abinda ya faru tsakanina da Habiban, ban ji ba, a zuciyata na ce ta hakura kenan, sai da na gama abincin dare na aike musu da shi naga an dawo min da abincin gaba dayan shi wai in ji Mama ace min bata so in hada duka in cinye ita tun kafin asan za’a haifi uwata ta same ta ne a duniya tana cin abinci, abincin ma kuma mai dadi tunda ita tuni tun da dadewa a cikin rufin asirinta take raye.
Na kalli Suwaiba da ta rattaba min bayanin nayi murmushi da gangan na kalle ta na ce mata Kawu mijina ne ina kuma son shi kamar kamar in yi ya ya? Ni kadai nasan yanda nake jin shi a cikin raina, don haka babu wani abin da wani nashi zai yi min in ji takaici, balle Mama wacce uwata ce sannan da umarninta ne aka yi min wannan aure mai dadi ki bata hakuri kafin in zo da kaina in ba ta.
Ta juya ta tafi ga alama kuma ta gane gatsen da nayi mata, na sake zuba idon ganin Mama ta shigo bata shigo ba. Cikin zuciyata nace in ma dai sabanin Mama da Ado yayi tsananin da ta fita harkarshi, to kuwa tana nan tana shirya abinda take shiryawa.
Ko da yake dai a yanzu itama tana da matsalolin da suke kewaye da ita, ga Suwaiba da aka ki karbar aurenta daga dalilin daguwa ga Habiba an ce ta dawo gida ta kara koyon hankalin zama da manya, ga Zubaida da yanzu ta watse musu kusan kullum sai ka ji ta tana zuba rashin kunya a cikin gida wai da Mama take yi daga baya kuma ka ji fadan ya rikida ya koma tsakaninta da su Habiban.
Ga al’amarin su Yaya Ibrahim da ya riga ya baiyana har duk mutanen unguwa sun gane kusan kullum sai wani dattijo mai mutunci cikin mutanen dake ganin bari su bada hakkin makwabtaka yayi sallama da Babana akan su yana tambayar shi anya Alhaji haka za’ayi ta zubawa yaran nan ido ba za a dauki matakin da ya dace ba?
Ga Anti Sha’awa daga zuwan Amarya kuma wai komai ya susuce mata, bini-bini sai ka ganta a gida ita da ‘ya’yanta wai tayi yaji saboda wai mijin yana nuna bambanci a zahiri, sai Maman ta kwabeta ta ce mata ta koma dakinta kawai taje ta duba taga irin matakin da ya dace ta dauka saboda a yanzu ba zai yiwu tazo ta zauna a gida ba, tunda ga Hajiyar Giyade ga kuma maganar Suwaiba da Habiba.
A duk lokacin da na tuna Mama da irin iko da gadaran da ta gwada na ganawa wanda bata so azabar yunwa da ta wulakanci da duka sai in ji kamar zan ji dadin abubuwan da suke faruwa da ita, wanda nasan mafi yawancin mutane dariya suke yi mata sai dai kuma in na tuna ‘yan uwana ne sannan Babana ba jin dadin hakan yake yi ba sia in ji tausayi ya kama ni, in ce ina ma dai a kanta abin yake faruwa ba akan ‘ya’yanta ba.
Rannan Ado ya dawo gida bayan Azahar, cefane ya sake kawowa mai yawa sosai da sauri na fito daga daki na karbe shi guda daya, dayan kuwa kin bani yayi yace muje in kai miki wannan. Muna tafiya yana tambayata sau nawa ki ka yi aman bayan fitana?
Na ce, a’a ban ma sake ba ina jin fa dama tin nan ne ya daga min hankali don nafi son da safe insha kunun gyada da alala, ya ce to ki jika gero mana, na ce to ko kuma in ce Gambo tayi min kullin, ya ce a’a ina dalili baki taimake ta kin yi mata ba sai ki sa ta aiki? Ban yi magana ba na soma fiddo cefanen don in san irin adanar da zan yi mishi, tunda ko jiya yazo da wani sai na ji ya ce min za ki yi miyar ne ta soyu da kyau ta yanda zata dade bata yi komai ba, ta Haiyar Giyade ce gobe zata tafi.
Da sauri na dago kai na kalle shi, tafiya zata yi? Ya ce ina laifi goben ta ce watanninta uku kenan a gidan, na ce sai tayi ai kwanci tashi babu wuya, amma kuma har na soma kewarta tun kafin ta tafin. Ya ce, to ko zan je ne in gaya mata ta hakura ta bar tafiyar sai kin haihu an yi suna tukunna? Shiru nayi ban amsa mishi ba saboda ina jin kunyar irin wannan zolayar da yake yi min.
Da wuri sosai na gama aikina na kawo mishi ya gani, ya ce min to sai ki shirya in anyi Sallah sai muje tare kiyi mata sallama, na ce to. Cikin zuciyata ina murna zan shiga gidanmu har inga Gambota, bayan kwanaki tamanin ban ganta ba, duk da ga ni gata saboda bata shigo ba nima bai bar ni na shiga ba. A wani gefen kuma ina fargabar ganin Mama saboda mun yi kwanaki ba mu sa juna a ido ba.
Wanka nayi sosai na dau kwalliya mai kyau sai sheki nake yi ina daukar ido, doguwar riga ce a jikina ta shadda gown shep dinta yayi matukar fitar da surata da kyau ga dinkinta yayi matukar kwanciya. Ado ne ya saya min shaddojin guda biyu ya bayar aka dinka min su, na sanya kananan ‘yan kunne da abin wuyansu wadanda suma shi ya saya min su a dalilin sha’awar da suka bashi sai dai a hannuna ne na sanya wara-waran daham da zobunansu na kuma daura wani dan siririn agogo da zoben G.L, suma kyautar Adon ne.
Ya kalle ni cikin wani yanayi da na tabbatar nayi matukar burge shi, ya ce “Ba za ki fesa turare ba ne? Ai gida kawai zamu shiga.’ Na ce ‘uh’uhn bana son turaren na jikinka ya ishe mu, bai ce min komai ba in ban da kallona da ya sake yi.
“Dan kawo min turame biyu cikin kayan aurenki aro.” Nayi murmushi na ce, zan fa dunka su, ya ce eh na ji kawo min dai, naje na kawo mishi akwatin ya zubawa zannuwan ido yana kallonsu, babu wata atamfa a ciki da ta wuce dubu daya da dari biyar, ni nafi zaton ma zannuwan da dangin uban Ado suka zo dasu daga kauye ne na gudummuwa Mama ta zuba a cikin akwatin ta dora sabulai da man shafawa ta bayar.
Zabo min guda biyu masu kyau a ciki, nasa hannu na zabo mishi su ya kuma gamsu da zaben da nayi mishin ya sake maida kallonshi kan abinda ya saura a ciki, dama zannuwan shida ne? Na ce a’a takwas dai kwanaki ba ka ari guda biyu ba?
Ya ce, af, haka aka yi to zuba min wadannan sabulan da man in hada mata, na ce to ai ka kwashewa Hajiyar Giyade kayan auren nawa. Ya ce eh ai ba kya son su, da kina son su da tuni kin dinka su kin saka, na ce to ai yanzu ina son su zan kuma dinka su in daura don ma dai ba ni da keke ne da da kaina zan dinka abina.
Bai amsa ba iyaka dai ya tasa ni a gaba muka fito, bayan yasa makulli ya kulle kofar dakinmu ya kuma sake kulle kofar gida. Na sake daga ido na kalle shi daidai sanda yake kulle kofar gidan, idanuwanmu suka hadu na dan kawar da kaina gefe ya ce, uh sai dai ki faki ido ki kallan mun kwalliyata amma ba ki san ki ce tayi miki ba, ban tanka mishi ba iyaka dai nasan yayi kyau ba kadan ba.
A tsakar gida Hajiyar Giyade tana alwala ta amsa sallamar da muka yi tare da yi mana oyoyo mai yawa, na ce hala Hajiya Sallar Isha’i zata yi? Ta ce uh’uh me zan zauna yi har yanzu ban yi Sallah ba? Alwalar kwanciya nayi, na ce to kwanciyar ma har da alwalarta? Ta ce eh, muka bi bayanta zuwa dakinta wanda dama shi ya fi kusa da kofar zauren gidanmu har muka shiga bata gama yi mana bayani kan muhimmacin wannan alwalar ba, muna zama kan shimfidar da tayi mana ta koma bakin gadonta ta zauna tana kallonmu.
Ni in ce ko dama iya shege ne kawai ya saki yin abinda kika yi ba kin auren kike yi ba? Na yamutsa fuska naki yin magana, yayin da Ado ya ke dariyar maganar tata da tambayar ta me kika gani Hajiya? Ta ce eh to abin ne nake kallon shi wani iri, ashe dama ana so ake kaiwa kasuwa, an je don iya shege har ana kwale miji da guduma, yanzu kuma sai naga ana ina aka saka dashi ba aso ko kuda ya sauka akan shi.
Ado ya kama dariya yayin da ni kuma na shiga shure-shure cikin yanayin shagwaba da jin kunya ina cewa ba na so Hajiya, ba na so.
Kin gani Hajiya za ki sa ta tayi shure-shure duk ta shure kwalliyarta ta lalace, yana maganar yana kallona cikin murmushi ga alama dadi ya kama shi an ce ina wai ina aka saka dashi, ai ni da cewa nayi Hajiya tafiya tun yanzu ba za ki bari sai wata daga cikin amaren ta sauka anyi suna kafin ki tafi ba?
Hajiyar Giyade ta kyalkyale da dariya ta ce, kai dai gaya min kawai in sani cewar taka amaryar tana kan hanya.’ Daure fuska sosai nayi naki kulawa da zancen nasu, iyaka dai na jawo kayan da muka zo mata da su na ajiye mata a gabanta na kuma ciro kudin da ya bani ya ce in bata na hada tayi ta godiya tana sa mana albarka, tayi man addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma zuriya mai albarka. Ado ya ce amin.
Ta mike ta debo wasu kayan tana nuna mana daga gidan Atika aka kawo su, nayi murna nayi musu addu’a na tashi na bar Ado yana sa hannu a aljihu alamar zai mata wata kyautar ta daban.
Ina barin dakin Hajiyar Giyade can wurin Mama na shiga, samun Babana da nayi a dakin baisa ta sake min fuska ta amsa gaisuwar da nake yi mata ba, shima Babana amsa gaisuwar tawa a yanayin kadaran-kadahan na dai san sau biyu na ganshi yana fakon idon Mama yana kallona.