Gambo ta ce uh’uhun abin tausayi yana zaman zamanshi dai aka tsoma shi cikin wannan fitinar da ba a sa shi wannan auren ba ai da yana nan yana harkokinshi da ya saba cikin kwanciyar hankali, kema da yanzu kina naki dakin, shiru nayi ban ce mata komai ba.
Sa’adatu ce ta shigo gida da gudu rungume da katuwar Jakar da kayana yake ciki wanda kayana ne na gida da kayan da nayi biki da su a ciki don tun ina gida nake amfani da Jakar. Hajiya Kubra ce ta bani ita, tana ajiye Jakar a tsakar falon Gambo ta sake komawa da gudu na jawo Jakar kusa da ni nasa hannu na bude ta ina dubawa duk wani abu nawa da naje gidan da shi da wanda ya saya min da kanshi ya tattara min ya saka a ciki har da akwatin sarkokina don dama yasan in da nake boye su, na mika wa Gambo akwatin sarkokin tare da yi mata bayani gabadaya kayana ne Ado ya tattara ya aiko min da su.
Ta dan yi shiru cikin tunani kafin zuwa can ta ce duk abinda ya yi niyyar zartarwa don ya samar wa kanshi kwanciyar hankali da ya rasa muna yi mishi addu’a ta fatan alheri ba kuma zamu ji zafin shi ba. Cikin zuciyata na ce itama Gambo ta hango abinda na hango kenan, cewar Ado zai hakura da aurena ne yasa ya tsintsinto kayana ya aiko min dasu.
Muna cikin haka sai ga Sa’adatu tana shigo da kayan kallon shi da ya saya bayan auren mu a dalilin Mama ta ci gadon nashi na samartaka, Gambo tayi maza ta ce a’a wannan ai ba nan za ki kawo ba can dakin Mama za ki kai mishi, ta ce a’a nawa ne bani ya ce yayi in sa a dakinmu in rinka kallo. Da sauri Gambo ta ce a’a shi da yake cikin wannan hali yayi kyauta da kaya mai daraja haka?
Na ce, a’a Gambo bashi ya bata ba? Ta ce to ina yake yanzu? Ta ce na dai ganshi ya baiwa Yaya Ibrahim makullan gidan ya ce wai yaba Mama shi kuma ya hau mashin ya tafi.
Gambo ta sake cewa kai wannan al’amari yakai inda ya kai, yaron nan yana cikin wani hali kuyi mishi addu’a. Sa’adatu ta ce wa Gambo shima ya ce in gaya miki kiyi hakuri kuma kiyi mishi addu’a ta ce to ni me yayi min ma? Nan da nan kuma ta shiga jero addu’o’in da yace tayi mishin, zuwa can kuma ban san tunanin da tayi ba sai naji ta ce ni in da zai samu ya kama muku haya a wani wuri ai da nasa an gyara muku gidan ba kadan ba ta shiga bani labarin irin gadaje da kujerun waje da Alhaji Abba yasa ake kawowa Hajiya Kubra wai don itama ta rinka juya kudi a hannunta.
Gambo tana fadin haka sai zuciyata ta shiga raya min irin kayataccen gidan da zata shirya mana in har Ado ya kama mana haya da zai yi hakan kuwa ko da wane irin dadi zamu ji ni da shi oho?
Washegari da safe ne Ado ya sake zuwa unguwar har ya shigo gida sai da ya fara shiga wajen Babana ya gaishe shi sannan ya shiga ya gaida Mama ya fito zai shigo wurinmu ina jin Mama tana ce mishi ai na dauka ba za ka sake shigowa gidan ba ne saboda an kwace maka Gambo Majandi, in kuma baka daina shigowa kana shiga wannan dakin ba to zan sa mai gidan ya hana ka shiga mishi gida, ban ji ya ce mata komai ba.
Gambo ta amsa sallamar da yayi ya shigo suna gaisawa naji tana tambayar shi lafiya dai ko? Ya ce kalau Gambo, na dan yi zirga-zirga ne saboda in warware wasu abubuwa wasu kuma in kammala su, na kuma gama shi ne nazo in yi miki bayani, ta ce mishi to, daga ni har ita muka shiga sauraro don mun fi zaton takardar sakin aurena ya kawo min, sai na ji ya ce akwai wasu sharudda da kwanaki aka sanya min akan aurena ban sani ba ko rashin cika su ne yasa Baba ya baiwa Humaira umarnin dawowa gidan don haka na tsaya naga na cika su.
Gambo tayi shiru alamar shi take sauraro shima kuma da yake yasan hakan sai kawai ya ci gaba da yi mata bayani na farko akwai maganar gida cewar in bar shi na biyu akwai jarin Mama da nake juyawa sai na uku shi ne in fita gabadaya daga cikin kasuwancin Baba. Gambo ta ce tow, ya ce to wadannan din duka na shirya yin su don haka ne ma naje nayi wa Baba Yahaya bayanin komai ya kuma ce min in zo yana zuwa in na zo din kuma kafin ya iso to in shaidawa Liman da Malam Harisu makwabcinmu don su zo su taya shi zama shaida na zan mayar musu da abinda suka nemi in mayar musu don suma su bani matata da suka karba.
Gambo ta sake cewa haka ne, ya ce to bayan wannan ma Gambo akwai gidajena guda biyu da nake karbar hayarsu da bus da take yi min zirga-zirga ina kuma da shago da ake yin dikin a ciki shi wannan shagon nawa ne da kudina na gado na saye shi na kuma zuba kekunan, Musa ne yake lura da komai nashi, don shima gwanin tela ne ban kuma taba samun matsala da shi ba, yasan komai nawa na gaya mishi abinda ya saba bani ya rinka kawo miki ki rinka sayen sabulun wankin yara, su kuma gidajen da motar zan mayar wa Baba da abinshi don a cikin dukiyarshi na saya.
Gambo tayi maza ta ce a’ah to in kayi haka kai kuma fa? Ba wahala kayi wa dukiyar ba, ka kuma yi tattali? Ya c eh, amma ban same su ta hanyar da ta dace ba, don haka zan mayar mishi zan je in nemi nawa ni dai in suka yarda muka rabu lafiya dasu suka bani matata na tafi da ita to shi kenan komai mai sauki ne, sai da tayi tayi mishi addu’a da godiya kan alherin da yayi mata sai ta ce mishi to in ka dauki matarka ina za ku koma?
Sai da ya dan yi shiru tanfar dai nauyin abinda zai gaya matan yake ji zuwa can sai naji ya ce mata kauyenmu zan koma, da gudu na fito daga dakin da nake kwance ina rike da dankwalina a hannuna durkusawa nayi da gwiwoyina biyu a kasa na ce mishi kauye? Bai kalle ni ba bai tsaya amsa maganar da nayi mishi ba sai kawai ya ci gaba da yiwa Gambo bayani, dangin mahaifina mutane ne masu karamci da zumunci, na kuma yi miki alkawarin matukar ina raye cikin lafiyata to ba zan bar Humaira ta shiga cikin matsalar da zata dame ta ba, don haka na roke ki ki kara yin hakuri ki kuma yafe min abubuwan da nayi miki.
Cikin wata irin murya mai rauni naji Gambon tana ce mishi to amma kai ma na roke ka kayi hakuri ka fara tafiya tukuna in yaso daga baya sai kazo ka dauketa.
Maimakon ya ce wa Gambo to sai kawai naji ya ce mata a’a Gambo, ai in nayi haka ya zama min kenan tanfar na rasa komai bayan kuma don in same ta ita kadai dinne yasa na bayar da komai din da nake da shi saboda haka zan tasa ta a gaba ne mu tafi. Ina jin ya fadi haka ban jira amsar da Gambo zata bashi ba sai na ce mishi a’a babu wani kauye da zan bika mu tafi, ban taba zuwa kauye nayi kwanakin da suka wuce guda bakwai ba, bana iyawa. Sai kuma haka kawai in bika can in zauna? Ba a can aka haife ni ba mahaifiyata ma ba a kauye aka haife ta ba.
Ado ya tashi ya fita saboda jin sallamar Baba Yahaya, ya barni a nan ina durkushe ban gama lissafa mishi abinda na fara ba, yana barin dakin Gambo ta kalle ni ta ce kauye kuma? Wannan wace irin fitina ce? Maimakon ta saurari amsar da zan bata tunda naga kamar tayi min tambaya ne sai kawai naga ta rushe da kuka, kuka kuwa mai tsanani irin wanda ban saba ganin tana yi ba.
A tsakar gidanmu gabadaya mutanen da Ado ya nema sun hallara ana zazzaune har da Babana wanda yasha mur sosai don nuna alamar babu wasa, Mama ma tana gefe tun kafin a kira ta ta fito ta zauna. Liman yayi addu’a ta fatan a dace da duk abin da za’ayi ya zaman ya zamo shi ne mafi alheri kuma ayi komai lafiya a tashi lafiya aka shafa da amin.
Baba Yahya ya kalli Ado ya ce, to me ya faru ne Ado? Ado ya gyara ya soma rattabo bayani tun farko yanda aka yi Mama tasa shi karbar aurena al’amuran da suka yi ta faruwa bayan auren da sharuddan da ta sanya mishi na cewar za su faru in har ya ce zai ci gaba da zama da ni da kuma yanda Babana ya kira mu muka zo ya ce ni in shiga dakin uwata shima ya shiga na tashi uwar shi kenan ya raba aure, magana ta kare. Kowa yaje ya rike tashi.
Ya ce, to shi ne nace watakila rashin cika wadancan sharudda da aka gaya min ne yasa aka zartar min da wannan hukunci, don haka na kira ku saboda ku shaida zan cika sharuddan dan nima a bani matata in tafi da ita, kowa ya yi shiru yana sauraron abin mamakin da Ado ya rattaba yayin da shi kuma Babana ya shiga fadin lalle kai din nan butulu ne ban sani ba, Mama kuwa kuka ta kama yi tana fadin wai bata taba zaton Ado zai kulla mata sharrin da ya kulla mata ba.
Liman ya katse su ta hanyar cewa, to amma wannan lamari da ban mamaki yake, ashe ba ni da Alhaji Yahaya ba ne muka je ba da hakuri don iyayen mijin ‘yar uwarta su barta ta koma dakinta ta zauna suka ki muka dawo muna bacin rai da bakin cikin wulakancin da aka yi mana na kin yarda ta koma ba?
Baba Yahya ya ce eh, to shi ne kuma kai da kanka kake cewa a dawo maka da wannan ka raba auren Alhaji a ina ne uba ya samu ikon kwace ‘yarshi daga wurin mijinta, alhalin ba mijin ne yace baya yi ba, ai daga fadin ka bayar an ce an karba to baka da sauran iko, kai Ado kana son matarka ka kuma shirya cika sharuddan duk tsananinsu don a baka ita? Cikin ladabi ya ce eh Mallam, to kawo su.
Ado ya shiga mika takardu yana bayani har da na gidajen nashi da motar ya ce ita kamma direban ya ce min ya kawo ta suka ce eh mun ganta bayanin kudi a banki da na hannun mutane da wanda su kuma ake bin su bashi duk ya bayar. Mallam Harisu ya ce amma Alhaji yanda yaron nan yasan komai na kasuwar nan taka da kuma dawo da wannan dukiya da yayi wacce da can baka san da ita ba baka ga kamar ka yafe mishi ka bashi matarshi suci gaba da zamansu kaima kuci gaba da harkokinku bai fiye maka ba? Tunda kowa ya san shi ya san shi ne a tare da kai babu kuma wanda bai san jarumtakar shi ba yana rabuwa da kai fa wasu a kasuwar a kuma kusa da kai za su kwace maka shi ba kuma zaka ji dadin hakan ba, kan Babana ya bude baki yayi magana sai Mama tayi caraf ta ce, to ya tafi mana da can da babu shi Alhaji bai nemi kudinshi ya samu ba?
Wannan neman kudi da yake yi mishi ma ai neman kudi ne na kashe mu raba, Baba Yahaya ya ce eh da ki ka sa shi yin hakan ba in ba haka ba a ina ki ka samu wannan dukiya da ya dawo miki da ita? Me ki ke dashi? Ko kina so ne in tuna miki da…da sauri Liman ya ce a’a Alhaji kai kuma me ya kaika yin haka? Baba Yahaya ya ce abin bakin ciki ne da matar nan Mallam, gaba daya ta hana gidan nan zama lafiya, ka duba yanda aka yi da dalilin da yasa ta kulla wannan aure da kuma abin ya juya ta inda bata zata ba maimakon tayi nadama kan muguntarta tayi ta istigafari sai kuma ta tasa dan uwanta a gaba da masifa, to za ki rasa shi za kuma kiyi kuskure don shi ne komai na hidimar gidanku ke da mijinki.
A wurinka ba, kai kake ganin hakan ai ku ku ka shiga tsakanina dashi, Baba Yahya ya ce to ai shi kenan kai Ado a ina ka samu inda zaka koma din? Ado ya sunkuyar da kai kasa ya ce can nake so in koma wurin dangin ubana, yana fadin haka Mama ta kyalkyale da dariya ta ce kauye kenan? Ai da can din kuka fi dacewa.
Gabadaya wurin yayi tsit saboda babu wanda ya zaci Ado kauye zai ce zai kai ni, shiru aka yi na wani lokaci mai tsawo kafin Mallam Harisu ya gyara zama ya ce wa Ado, ka gani Ado in wani abu irin wannan ya faru hakuri ake yi a kwantar da hankali a natsu kafin a san kuma inda za’a fuskanta.
Kai yaro ne mai natsuwa da girmama na gaba da kai, kowa ya sanka saboda kana da kwarjinin jama’a ka iya zama da su lafiya, kayi karatu.” Baba Yahaya yayi maza ya ce mishi ai digiri biyu ne da shi a yanzu, da sauri Mallam Harisu ya ce to ka gani? Babu wani dalilin da zai sa don wannan abin ya faru ka ce zaka bar birni ka koma kauye. A nan ma za ka yi harkokinka zaka samu kuma abokan harkar. Za kuma ka nemi aiki ai kayi ilimi shi kauyen nan da ka ke gani ka riga ka baro shi da dadewa ba iya zaman cikin shi zaka yi ba, don ka riga ka manta da rayuwar can duk da dai nasan kana yawan zuwa to sannan ita Humaira fa bata san kauye ba kar ka manta da wannan.
Gaba daya aka sake yin shiru na wani tsawon lokaci saboda Ado ya ki tanka maganar da Mallam Harisu yayi mishi, sai Baba Yahaya ya kawar da shirun da tanbayar cewa to ko kuma zaka fara tafiya ne kai kadai ka barta a nan sai kaje ka gano yanda zaman naku zai yiwu in yaso sai ka dawo ka dauke ta?
A hankali ya ce, a’a Baba, nafi so in tafi da ita, nafi so a bani ita, watakila taurin kan Ado ne ya fusata Babana ko kuma yawan tsakin da Mama ke ja ne oho. Don jin shi kawai aka yi ya kama fada yana fadin babu in da zaka tafi min da ‘ya ai bamu yi da kai akan in anyi auren kauye za ka dauke ta ka kaita ba, shi kuma Liman ya ce a’a wannan kuma ai ba magana ba ne shi dai a roke shi cikin biyu yayi daya, ko dai shi ya fara zuwa kafin ya dawo su tafi tare ko kuma kai Alhaji Yahaya ka yarda ka bashi aron wurin zama da shago a kasuwa tunda mun san duk abinda yake hannunshi ne ya kawo.”
Baba Yahaya yayi maza ya ce har kayan zan sa a bashi in yi mishi lamuni ai duk an san shi, da Liman ya waiwayi Ado don jin abinda ya zaba sai ya shiga basu hakuri yana fadin shi a yanzu zai fi son a bashi matarshi ya tafi da ita wurin dangin ubanshi. Baba Yahaya ya ce to ina ganin tunda yarinyar nan itama tana da hankalinta da wayonta a kira ta tazo nan muji ra’ayinta, in ta yarda zata bi ka kauyen shi kenan, amma in bata yarda ba ba za mu tilastata ba, Babana yayi maza ya ce bin shi kuma yana nufin ta tafi kenan ba za ta sake dawowa ba.
Ado ya daga ido ya kalli Baba Yahya cikin natsuwa da ladabi yayin da tsoro ya baiyana karara a idonshi ya ce mishi na roke ka Baba kar ka bata zabi akan aurena, don zata ji tsoron maganar da Baba yayi mata.
Baba Yahaya ya ce ba zabi ba ne hakkinta zamu bata in ta ce zata bi ka shi kenan, amma in ta ce ba za ta bi ka ba ba zamu sa ta ba, domin ya kamata ace kaima kayi sassauci akan tafiyar taka tunda mun maka alkawura mun baka zabi mun kuma roke ka a matsayinmu na wadanda suka haife ka, amma ba ka yarda ba, to hakan ba yana nufin ita din zamu tirsasata ba ne.
Mama tayi dariya tare da gyada kai ta ce ai gara dai kuma ku gani wai shi nan a dole shi mai taurin kai ne.
Fitowa nayi a daki a dalilin kiran da aka yi min har kafin fitowar tawa kuma Gambo bata daina kukan da take yi ba, tana fadin kauye kuma? Haba wane irin kauyea? Na durkusa a kasa da gwiwoyina duka biyu cikin sauraron abinda Baba Yahya zai gaya min, zuba min ido yayi yana kallona cikin wani yanayi da yake baiyanar da tausayin shi a gare ni, ni ba ki da lafiya ne ma ko Humaira? Na ce mishi eh Baba, sai da ya kara daukan wani lokaci mai tsawo cikin nazari da tunani kafin ya daure ya ce min to Humaira kin dai ji duk abinda muke ciki da mijinki, amma a yanzu zabin ya rage naki, za ki bishi ku koma can kauyen nasu? In za ki bi shi to babu laifi ba zamu hana ki ba, domin aure ne shi kuma aure babu inda ba ya kai ‘ya mace, sannan mijinki yaron kirki ne jarumi kuma mai neman na kanshi, ni nafi kyautata kyakkyawan zato a gare shi, in kuma kika ce ba za ki bishi ba to babu mai sa ki saboda mu din iyayenki ne zamu yi miki adalci baki san komai ba game da rayuwar kauye a dauke ki a kai ki can ki koma da zama ba zai zamo mai sauki ba a gare ki.
Don haka me kika ga ni, za ki ko ba za ki ba? Ya waiwaya wurin sauran jama’ar da suke tare ya ce ko ba haka ba Jama’a? Suka yi maza suka ce wannan shi ne gaskiya, ya sake waiwayowa ya kalle ni ya ce, To Humaira zabi yana wurinki, yi maza ki gaya mana wanda kika dauka don ki kawo mana karshen wannan kai kawo kin ga ai tun safe muke wurin nan ko kasuwa ba mu samu mun je ba.
Dago ido nayi da nufin baiwa Baba Yahya amsa sai ka rab idanuwana suka hadu da na Ado, ni yake kallo ko kibta idon nashi baya yi saboda tsananta kallon da yayi, makwalwuyanshi sai kai kawo yake yi alamar tsananin damuwa da alama kuma wata maganar yake son gaya min watakila da ya san zabin zai zo wurina da yayi hanzarin gaya min ita tausayinshi yayi matukar kama ni da na tuna kalmomin da ya furtawa Gambo cewar tafiya babu ni din zai zamo mishi tanfar ya rasa komai, gaskiya ne tafiya babu ni tanfar rasa komai ne a wurin Ado, tunda ya bayar da komai nashi to amma kuma anya tausayin hakan ya isa yasa in zabi Ado in bar kaina, da mahaifiyata? Anya tausayin nashi ya isa ya hana ni tausayin kaina da mahaifiyata?
Bin Ado kauye kenan yana nufin rayuwata ta shiga wani hali musamman ma da yake nasha jin mawakanmu na Hausa masu basira suna fadin wai kowa kaga ya bar birni ya koma kauye to wannan zaman duniya tasa ce ta gigita. Ban da wannan ma ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba, shigana cikin matsala yana nufin Gambo ma tana cikinta tsundum, na kuma sani da ita ce ta samu damar da aka bata irin wannan zabin da aka bani da tuni ta kawo karshen maganar ta hanyar fadin babu inda zani.
Wadannan dalilai sai suka sanya ni cikin wani hali na kai-kawo da bugun zuciya wanne zan zaba? Rufe ido zan yi in zabi kaina da kwanciyar hankalin Gambota in bar Ado da dan guntun kunyarshi da dan bacin ranshi ya kama hanya yayi tafiyarshi kauyensu ko kuwa? Tunda ai yayi kyakkyawar rayuwa babu ni, gabadaya son da yake tutiyar yana yi min kwata-kwatanta daga wata uku ne, a baya ni din ba komai ba ce a wurinshi, sannan dukiyar da yake ikirarin mayar wa don ya same ni na sani jarumta ne yin hakan, to amma kuma ai ta wani bangaren taimakon kanshi yayi tunda dama bata hanyar halal ya same ta ba, tana cikin asarorin karya da aka yi ta cewa Babana yayi.
Sannan ko Ado bai tafi da komai ba zai tafi da iliminshi wanda babu wanda ya isa ya kwace mishi shi digiri biyu kuma ke gare shi, sannan ban da wadannan dalilan duka bani da tabbacin cewar zan samu karbuwa wurin ‘yan uwan Ado da yake ikirarin maida ni cikinsu in suma suka zamo min kamar Mama fa yaya zan yi haka nan shi kanshi Ado wane tabbaci ke gare ni akan shi tunda tun ina ‘yar karamata nake jin iyayena mata suna fadin wai shi da namiji ba dan goyo ba ne, to musamman ma kuma wannan da shi da kanshi ne yake yi wa kanshi kirari da cewar shi din namiji ne.
Iyayena kuwa da dangina tuni suna sani zama da su yana nufin zan ci gaba da zamana a cikin gatana musamman Gambota wacce nasan babu wani wanda zai cike mata girbina balle ya debe mata kewata tun daga ranar da ta haife ni take sona kowa kuma ya san hakan, kowa ya bada wannan shaidar cewar Gambo bata taba son wani da kwatankwacin son da take yi min ba, haka nan zan ci gaba da rayuwa ta a birnin da na sani, birnin da aka haife ni, birnin da na rayu, zan ma iya komawa Makaranta in yi karatuna tunda ina da wannan burin.
Mama kuma in babu auren Ado a kaina ba za ta sake takura min ba don kuwa ba zan sake yarda ba saboda a yau kan ungulu ya riga ya waye dan auren nan da nayi na kwanaki tamanin da bakwai ba karamin bude min ido yayi ba.
Tuni zuciyata ta shiga kai-kawo mai tsanani na kasa gane menene abin yi? Wanne zan yi? Wane zan bari? Hankalina ya yi matukar tashi na rasa wanda zan zaba cikin biyun, Gambo da sauran dangi tare da Babana mai fadin bin Ado yana nufin na bar gidanshi kenan zan dauka in bar Ado?
Tunda shi Ado ai zai tafi da iliminshi ban da haka ma zan haifar mishi abinda yake cikina yazo ya dauka abin shi, ko kuwa Adon zan bi min soyayyar wata uku muje can kauyen nasu cikin danginshi mu yi zamanmu?
Duk yawan kirarin da yake yiwa kan shi na cewar shi din namiji ne, alhali kuma mu mata mun sha jin iyayenmu mata suna jaddada mana cewar shi namijin ba dan goyo ba ne…?
Mu hadu a littafi na uku jama’a don jin kafin nan in ku ne wanne zaku zaba cikin biyun?