LITTAFI NA UKU
Tuni zuciyata ta tsayar min da cewar ba zan bi Ado ba, don kuwa na gane zabin da zai fi dacewa da ni shi ne zabi na zama da Mahaifiyata da dangina, ba zai yiwu in tafi in bar Gambota cikin bacin rai da bakin ciki da damuwa da kewa mara misaltuwa ba.
Kowa yasan Gambota, yasan babu abinda take so irina. Shi da kanshi Ado ya tabbatar min da cewar tsananin son da Gambon take yi min ne ya sanyata saurin yafe mishi laifukan da yayi mata a baya, kafin auren namu.
Ta kuma yi gaggawan maida shi da a wurinta, ta hanyar kyautata mu’amalla a tsakaninsu, ta girmama al’amarinshi ta hanyar ba ni umarni na in kyautata mishi.
To in kuwa har haka ne shi da kanshi yasan wannan, to ai shima bai kamata ya zartar min da hukuncin tafiya kauye ba, in dai ba hakan yana cikin ajandar su ba ne shi da Mama. Tunda dama da gayya Marnan ta zabe shi ta ce a ba shi ni.
Don haka ban yarda da su yarda na dari bisa dari ba, don haka ba zan bishi ba, zan zabi zaman gidanmu ne in rabu da shi yayi tafiyarshi, in rabu dashi in rabu da fitinar Mama, ba zan taba yarda soyayyarshi ta wata uku da yaudare ni ba in rabu da Gambota, in rabu da ita cikin kunci da bakin ciki bayan nasan soyayyar da take yi min ita ce ta gaskiya, ita ce ta asali, ita ce wacce bata karewa saboda babu algus ko wani magudi a cikin ta, don ba yi min ita take yi don taga wani abin sha’awa a gare ni ba.
Ado kuwa fa? In ma har da gasken ne yana sona, to ya fara son nawa ne a daidai lokacin da watan amfanina ya kama a wurinshi, ya fara sona ne a daidai lokacin da aka bashi shawarar karbar aurena tunda tun zuwana gidanshi sau daya ban ga wata alamma da ta nuna yana nufin nuna min tsana ko kiyayya ba.
Tun zuwana a cikin kokarin shawo kaina yake, don ya samu zaman lafiya da kyakkyawar mu’amallah a tare da ni, amma kafin wannan lokacin babu irin wannan mu’amallar a tsakaninmu, in kuwa haka ne to zan iya cewa da wata lagwada da ya hango wacce ya gane in yayi wasa ya rasata kanshi ya yi wa asara.
Ta hanyar tsiya da nuna fin karfi kuma yasan ba zai taba samunta ba, tunda ni da shi ai kar-ta-san-kar ne, ya sanni na san shi, don haka yayi gaggawar watsar da makaman fada ya nemi hanya ta rarrashi da kyautatawa ba gare ni ni kadai ba, har da ita me haifiyata da kuma sauran dangina.
In kuma har nace Ado ya canza ra’ayin shi ne a kaina ya janye daga taimakon ‘yar uwarshi kishi ta hanyar wulakantata don su kara sanya mahaifiyata cikin karin bakin ciki kan wanda suka saba Sanya ta? To ba sakarci yayi ba, don kuwa nasan maza da yawa za su iya yin irin nashin a kaina, tunda ko da ban taba daukan kaina na jefa cikin kyawawan matan da kyansu ya kai ya kawo ba, saboda ganin kyawawan yan uwana da nake tare da Su, su Aliya da Atika, wadanda su din dukkansu farare ne so, ga su kuma da dogon gashi tunda su kama da Gambota suka yi.
Na sani tun ina yarinya ‘yar karama nasha jin Gambor tawa tana gaya min cewar ba fin ki komai suka yi ba, ai bakar fata ba muni ba ne, Babanku ai kyakkyawan mutum ne, ban kara yarda da hakan ba sai da na girma na zama cikakkiyar budurwa, na ganni a tsaye sanbal har ban bukatar sanya dogayen takalma, saboda tsayin nawa ya ishe ni.
Sai dai kawai in yi hakan wani lokaci don nishadi, ga ni da kyawawan idanuwa masu tsananin fari da wadatacciyar girar ido da gashin idon, sannan ni din ba ‘yar siririya ba ce, ina kuma da cikakken kirji gami da damammen ciki da ya Sanya kudurina ya samu damar fitowa, gashin kaina ba mai tsayi ba ne, amma a cike yake gashi kuma da laushi.
Ga shi bakar fatar tawa tasha gyara saboda Gambo bata yarda in shafa wani mai ba tare da ta zauna tayi mishi hadi na musamman ba, ba wai don fatar ta canza daga launinta na bakin ba, a’a sai dai don ta kara laushi tayi kyau.
Sannan kuma ga ni ma’abeciyar tsabta da kamshi a kowane lokaci, sai nake ganin tamfar wadannan dalilai su ne suka janye Ado suka yi dalilin da suka hana shi jarumtakar ci gaba da taimakon ‘yar uwar tashi fadan kishin kamar yadda ya saba, sai yaga maimakon yayi hakan a karshe ya rasa ni, gara mishi ya rike auren shi in yaso ko ma menene zai biyo baya bai damu ba.
To in kuwa haka ne, ai son nashi yana da dalili, sabanin na Gambo da shi makaho ne, yin shi kawai take yi sona kawai take yi a kowane hali nake kuma ba za ta daina ba, don haka ba zan bar ta in bi wani Ado ba.
Haka nan don nace ba zan bishin ba, ba wani laifi nayi ba, zai je ya samu wata a gaba. Sannan cikin dangin shi zai koma ban da haka ma juna biyu ne da ni, zan haifan mishi da ko ‘ya yazo ya dauka, wannan ba karamar riba ba ce a wurinshi.
Sannan zai tafi ne tare da iliminshi da yayi arnfani da dukiyar ubana ya nema, ai ko da ya dawo mishi da abubuwan shi da ke wurinshi bai dawo mishi da ilimin ba, ya rike wannan balle ace shima ya ajiye Babana ya samu ya rabawa nashi ya’yan da sakarci ya hana su yin karatu.
Don haka ba zan bishi ba, ko don in dandana mishi bakin cikin rasa ni bayan ya soni ba zan bishi ba, tunda bai so ni a lokacin da ya dace ya sonin ba, ya so ni ne bayan ya taimaki ‘yar uwarshi sun gallawa Gambo, sun gana mata azaba ita da ‘ya’yanta.
Ya so ni ne bayan na gama wahala a hannun Mama, na gama azabtuwa da azabar dukanta, bai so ni a lokacin da nake bukatar taimako ya taimake ni ba, don haka ba zan bishi ba. Sannan na riga na sani ko ban bishi ba ba zai sake zama tare da Mama ba har yayi mata irin biyayyar da yayi mata ba a baya, don kuwa ya riga ya kamu da sona matsanancin son da ya ba shi dama da kuzarin iya yin fito-na-fito da ita kaina. Don haka ko don in dandana musu wannan takaicin dukan su ba zan bi shi ba.
Ina cikin wannan zancen zucin, kalaman Mama suka katse ni, suka dawo da natsuwata ga kallo da sauraron abinda ke faruwa a tsakar gidan namu.
Daga ido nayi na kalli Ado a dalilin jin irin kalaman da Mama ke yi mishi.
A durkushe yake irin durkuson da yafi kama da ace dan kiris mutum yake jira ya ruga a guje, makwal wuyanshi sai kai kawo yake yi a tsakanin wuyanshi, yayin da idanuwanshi suke kaina ko Rifta su baya yi.
“Dama ka hakura ka fidda ranka a kanta, ka kwantar da hankalinka ka samu natsuwa da yafi maka, don kuwa ba za ta bi ka kauye ba, uwarta ma ba za ta yarda ka daukan mata ita ka kaita kauye ba.
Sun dai cuce ka ne kawai suka yi maka irin surkulle-surkullensu da tsatsube-tsatsuben su suka mallake ka suka yi maka dandani-haukaci, saboda sun san baka taba sanin mace ba sai akan yarsu, don haka suka kidimaka, to ba ita kadai ba ce a haka. Kar kaga kamar ba za ka sake samun irinta ba, dubu suna nan kamarta wasu ma sun fita da yawa ma kuwa.”
Baba Yahya ya kalli Mama cikin wani irin yanayi da yafi kama da na jin kunyar kalaman nata, ya ce “Ke Madajan wadanne irin kalamai ne wadannan ki ke furtawa a cikin mutane na rashin mutunci da rashin ganin girman mutane?”
Ta ce, “Ah’ah, bar ni kawai in gaya mishi gaskiya, in ya hadiyi zuciyata a kanta ya mutu ma to shi kadai ya yi wa kanshi asara, tunda uwarshi kam ai ta riga ta dade da mutuwa, ni kuma ya riga ya nuna min iyakata a kanta, ya watsa min kasa a ido, ya kunyata ni ya tozarta ni a gaban makiya kuma abokan gaba yasa su sun yi min dariya, to ai babu wani abu a tsakanina da shi a yanzu tunda an yi mishi ingiza mai kantu ruwa ya yarda.
Wai har ni ka ke dawowa da kayayyakina da suke wurinka akan wannan ja’irar yarinyar, shu’uma, yarinyar da kwanannan ta gama yi maka gori a kan kauyancinka, tana fadin ta godewa Ubangiji ita gidan ubanta gida ne mai albarka, kowa yazo cikinshi zai ci arziki ya koshi ya murje, ya goge, yasa sutura ya fita daga kauyancinshi.
In ba wanda ya san shi ba babu mai kallon shi ya gane ina ne asalin shi yake? Shi yasa ita ko bakunta bata barin gidan ubanta taje yi a na wasu.
Ba Humaira ba ce ta furta maka wadannan kalaman?” Ta zuba mishi ido tana kallonshi, sanin da nayi cewar gaskiya ne daga bakina maganganun suka fito yasa nima na zuba mata nawa idanuwan ina kallonta.
Tsana ne karara ya bayyana a idon Mama, zai yi wuya a yau in har da akwai sauran wani abu naso ko tausayi a tsakaninta da shi, to me yayi mata? Ko kuwa don kawai ta ce ya saki aurena ya ce a’a?
To in har haka ne yasa a yau Mama ta tsane shi to anya Mama tana yin so kuwa? Ko kuwa dai ita din takan so mutum ne kawai a gwargwadon irin amfanin da take yi da shi? Ai baka tozarta ni ba kanka ka tozarta ka tsiyata kanka don ka burgeta, ta ce zata bi ka ba kuma zata bi kan ba kai ne ka zabe ta ka bar ni, amma ita din ba za ta zabe ka ta bar uwarta ba, ko kuwa Humaira?
Ta juyo da kallonta gare ni, za ki iya yin rashin hankalin zaben namijin da ba shi da tabbas ki bar iyayenki uwa da uba tunda kin san su ba sa son tafiyar taki? Ado ai dan kauye ne, kauyen kuma babu wanda bai san shi ba, a nan sai ko ke din, sussuka ne da surfe gami da nika kafin aci abinci gidan su Ado kuma wani irin gida ne da girman shi ya hana shi yin fasali.
Don ko katangar arziki basu samu arzikin yi mishi ba, gasu da wani irin yawa mara sha’awa, sannan wai don rashin adalci duk mutanen gidan nan suna ci ne a tukunya guda daya mace daya kuma ke tuka shi, ko karya nayi nuku?
Ta zuba mishi ido tana kallonshi, ya girgiza kai a hankali cikin natsuwa nuna alamar ba karya tayi ba, gaskiya ta fada, ta gyada kai nuna alamar gamsuwa da amsar da ya ba yar tare da fadin kin ji ba? Shina ya ce ya karya nayi bà.
Kalaman batanci da tozartawa da Mama ke ta faman furtawa a kan Ado, anyi-anyi da ita kuma ta daina ta ki, sai suka sanya ni canza ra’ayina naga ko ba zan bishi ba to ba a gaban Mama kuma zan fadi hakan ba, tunda na gane abinda take son ji daga gare ni ke nan, don taji dadin tozarta shi ta yadda zai kunyata yayi bakin ciki.
Ke Hajiya da kin bar yarinyar nan ta zabi abinda ta zaba, don musan abinda muke ciki.” Bai sauraronta shirun nata ba balle ya gane tabi umarnin nashi ko bata bi ba? Ya dawo da zancen nashi gare ni.
“Ke Aisha wanne ki ka ga za ki yi? Za ki bi mijin naki ne ko ba za ki bishi ba?” Na daga ido cikin nutsuwa na kalli Mallam Harisu makwabcinmu da yayi min wannan tambayar, na ce mishi “Zan bi shi Baba.”
Ina fadin hakaa dakin ya dauki kabbara mai karfi tare da hamdala, daga wurin Ado da Liman, Mama kuwa kurma ihu tayi da iya kacin karfinta, tamfar wacce wani mugun abu ya samu, tana fadin ita kam ta shiganga, to bara kada ta mutu ta bar rai a duniya, wayyo!! Ita Majadan an kwace mata dan uwanta an shiga tsakaninsu an rabata dashi, ina ma dai ace ta ji kashe din da wannan yarinyar tayi mata?
Baba Yahya ya ce, “Kaltume ba? Ni da kina ji da mugun nufi iri-iri da ba ki aiwatar da shi ba, amma ga ki nan ga irin abinda ki ke shukawa.”
Babana ya yi maza ya mike a fusace a’a Alhaji, kar ka ce zaka yi wa Mama baki, in dai akan wannan ja’irar yarinyar ne, ai gata nan ga wanda ta zaba din, ba dai a kanshi ta wulakanta ni ba? Na ce kar ta zabe shi ta zabe shi?
To in ta bi shi suka tafi ta tafi kenan har abada ba za ta sake tako min cikin gidana ba, kuma ma in naga dama inyi mata baki ta lalace tabi duniya, kowa ya huta, tunda ban ga amfaninta ba, tunda tasa Mama take irin wannan kukan.
Nima da iyakacin karfina na soma kuka ina birgima ina shure-shure, Babana zai yi min baki ina zan shiga ni ‘yasu? Hankalina yayi matukar tashi, na rasa in da zan sa kaina in ji dadi, na rasa wanda zan matsa kusa da shi in rada mishi cewar ni fa ba da gaske nake yi ba, zabin da nayi na cewar zan bi Ado nayi hakan ne kawai don in sanya Mama bacin rai, amma babu wanda zan iya fuskanta da maganar tawa ya saurareta.”
Gaba daya wuri ya hargitse, hankula sun kai matuka wajen tashi, Baba Yahya da Babana sai faman rirrike su ake yi saboda Babana ya koma taya Mama zagin Gambo da danginta da take yi, yana tayata kiransu munafukai masu raba dan uwa da dan uwa, shi kuma Baba Yahya yana rama musu. To ma na fasa tunda akan wannan..
Cikina ya bada wani irin sauti na kulułulu!!! Saboda tsoron kalmar da zai karasa zancen nashi da ita, sai naji ya katse zancen nashi ya ce, na fasa ba in da zata zabin da tayi zabin banza ne, ban yarda ba, ba za ta bishi ba, a zuciyata nace tafi nono fari,
Baba da haka kayi tun farko ma da ba a tsaya wannan kace-nacen din ba, tunda dai ni din ai mallakinka ce.
Zancen Baba Yahya ya katse ni da na ji yana fadin, wannan ai shi ne karya ba za ta zabi mijinta ka hana ta bibn shi ka kashe mata aure ba, saboda kawai matarka tana son ganin hakan, in zaurawa kake son gani a gidanka ai gasu nan ka samu.”
Mama ta sake kurma wani uban ihun, wai Baba Yahya ya yi wa ‘ya’yanta gori, bai saurare ta ba balle Babana, ganin shi kawai naga yayi ya damko hannuna yana jana zuwa inda Ado ke makure a jikin bango.
“Yau ka ce kana son tafiya da matarka?” Da sauri Ado ya ce mishi “Eh.” Baba yana jin haka yayi maza ya danka mishi ni a hannunshi, tare da fadin “Gata nan Ado na baka ita ku tafi, ka rike min ita amana ka sani iyayenta ma hakuri da su muke yi, to balle kuma ita yarinya ce yar karama.”
Ado yayi maza ya kama hannun nawa ya rike da iyakacin karfinshi, tamkar yana tsoron kar a kwace mishi ni.
“Wuce ku tafi.” Ya bani umarni mai karfi, daidai lokacin da Babana yake ta sakin wasu maganganu masu tsanani su Mallam Harisu suna ta faman bashi hakuri, na kalli Baba Yahya ina kuka, na ce mishi “Ba zan bi shi ba Baba, ba zan bishi ba, ni dama ba da gaske nake yi zan bi shi…”