Skip to content
Part 27 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Wani irin gigitaccen mari ya dauke ni dashi, sai da naga waikiya ta haske ni gaba daya, Ado yayi maza ya kankame ni a jikinshi da sauri yana baiwa Baba Yahya hakuri.

“Kayi hakuri Baba, kayi hakuri.” Yana kuma tattare ni da fadinshi don gudun kur hannun Baba Yahyan ya sake kawowa gare ni, gigitaccen marin da Baba Yahya ya kifa min ya katse min komai, hatta kukan da na dade ina yi, na daina shi na koma zare ido saboda ban taba jin mari mai tsananin wannan ba.

Ado ya tasa ni a gaba, muna fita daga gida ina jin Baba Yahya yana fadin, “Ai ko za ki shide ba shure-shure ba sai ya tafi da ita, ai ba zai zabe ta ya bar ki ke da mijinki da duk abinda ki ke ganin kun mishi ya ce ita kadai yake so sannan ku hana shi ita ba, yana sonta tana son shi ke ki ka kulla auren da nufin sharri don ki cutar da ita, kisa shi ya wulakantata.

Amma’ abin mamaki sai gashi zaman da yayi da ita na kwanaki tamanin da bakwai kacala sun sa shi ya zabe ta ita kadai ya barku ke da mijinki da duk abin da kuke ganin kuna dashi.

A kofar gida Ado yana kokarin shigar da ni cikin motar da ke tsaye tana faman jiranshi wadda shatarta ya dauko, sai ga su Liman da Mallam Harisu, har da Baba Yahya sun fito. Mallam Harisu da Limar suka wuce, Baba Yahya yana yi musu godiya.

Shi kuwa Baba Yahya yazo ya tsaya jikin motar hannayenshi duka biyu ya saka cikin aljifayen shi ya fito da duk abinda ke ciki ya mikowa Ado tare da fadin sai kayi hakuri da wannan baka ba da lokacin da za’a yi maka shirin tafiyar taku ba.

Hannu biyu Ado ya saka ya karbi abin da aka bashin cikin ladabi na gode Baba, Ubangiji ya kara girma.”

Baba Yahya yana tsaye a kofar gidanmu har motarmu ta bace daga unguwarmu, Ado yana ganin motar ta bar kan titinan daga cikin gari ta fada kan babbar hanyar da ta nufi Kano ya saki wani irin sansanyar ajiyar zuciya tanfar dai da a tsorace yake, ko yana tunanin za’a biyo shi ko a tare shi a kwace ni.

Lokaci mai tsawo yana cikin wata irin matsananciyar natsuwa kafin daga bisani naga ya shafa fatiha, don haka na gane addu’a yayi yana shafa fatihan kuwa ya juyo gare ni, kamo ni yayi da hannayenshi duka biyu ya jawo ni ya kwantar da ni kan kirjinshi, ya kuma dora hannunshi guda daya a jikina don ýa tilasta ni kwanciya kan kirjin nashi.

Cikin natsuwa ya soma yi min magana. “Kin taba ganin wanda ya zabi yin aure ya tozarta? Ai abubuwa guda uku Aisha, Ubangiji ba ya tozarta mai yin su, alkawari ne ma yayi cewar zai taimaki mai yin su, na farko a cikin su shi ne aure, sai Jihadi sai kuma bawan da aka rubutawa biyan wata ka’ida don ya samu ‘yanci ya zama da, don haka babu abinda zai same ki sai alheri.

Wata irin tafiya muka Yi wacce bazan iya tsayawa ina bada labarinta ba saboda tsananinta, ya kai duk in da ya kai, daga ni har Ado babu wanda bai wahala ba, iyaka dai shi ya yi tashi wahalar ne cikin farin ciki da gamsuwar samun yanda yake so, babu kuma wata alama ta damuwa a fuskarshi, yayin da ni kuma nayi tawa wahalar cikin matsananciyar damuwa ga bacin rai ga ciwon ciki mai tsananin gaske.

Ado ya rarrashe ni ya gaya min duk wata magana da zai gaya min, har ya gaji yayi shiru ya zuba min ido, amma ban daina kukan da nake yi ba, babu abin da yafi damuna irin tafiyar da nayi na bar Gambota da na san haka zabin da zan yin zai zama da ban yi shi ba.

Na zabi bin Ado don in batawa Mama ita kadai rai daga baya in an tashi in sulale in yi tafiyata in ki komawa gidanmu, sai na tabbatar ya bar garin tunda nasan ba zai sake zama ba, gashi hakan ya jawo min al’amura masu tsananin gaske, na farko ya haddasa bacin rai mai tsanani tsakanin Babana da Amininshi Baba Yahya, a dalilin furta kalmomi masu zafi da Baban nawa ya fusata yayi tayi a kaina da mahaifiyata, da ma danginta gaba daya.

Hakika nayi wauta mai tsanani da nayi nufin batawa Mama rai ba tare da na tunawa kaina cewar bacin ran Mama yana nufin ɓacin ran Babana ne ba, sannan hakan yayi sanadin da ni din zan bi Ado kauyensu alhalin m din ban san komai game da zaman kauye ba, ba kua duk wadannan ne suka fi kuntatawa zuciyata ba, irin tafiyar da nayi na bar Gambota, ko a wane hali take ciki ko a wane matsayi ta dauki tafiyar tawa? Wannan shi ne abinda yafi damuna.

Motar ta sake yin tsalle ta sake faduwa cikin wani ramin a karo na biyu, nima na sake yin maza na kankame marata da hannayena duka biyu tanfar dai yanda nayi a farkon fadawar nata, haba Malla Haruna a rinka kokarin kaucewa ramukan nan mana.

Mallam Haruna ya dan yi tsaki kadan alamar shi ma ba a son ranshi ba ne hanyoyin namu ne sai hakuri in ban da haka da gangan ai mutum ba zai rinka fadawa cikin ramukan ba don sukurkuta mishi motar za su yi babu halin kayi ƴar tafiya sau daya sau biyu sai ka raba abin da ka samu tare da makanikai.

Ni kam suna maganarsu ina jin su ina kankame da cikina ina sauraron abinda zai sake faruwa, tunda daga sanadin fadawa ramin farko ne cikina ya murda ya kama ciwon da nake ta fama da shi.

Da kaina na lallaba na sake jingina jikina a jikin Ado, maimakon jawo nin da yake yi ina ki saboda dunkulewar da naji marata tayi a wuri daya, da sauri Ado ya dora hannun shi a jikina ya kara tallabe ni na kwantar da kaina a kirjinshi ya cusa hancinshi da bakinshi a kan nawa ya dan sumbace shi kadan.

A hankali kuma cikin natsuwa da kuma sanyin murya ya soma yi min magana a hankali.

“Ina son ki Aisha.” karo na biyu kenan da na taba jin sunan nawa sak a bakin Ado kafin yau, bai taba ba da Humaira ya saba kirana, ban damu ba duk abin da za a fada a fada, in ma dandani haukaci aka yi min oho, ni kam ina so, ina sonki ban kuma zabe ki don in batawa wani rai ko don in ba wani haushi ba.

Ban zabe ki akan lalura ko akan kuskure ba, na zabe ki ne don ina sonki don na riga na gane rabuwa da ke ba zai haifar min da da mai ido ba, don haka na zabi rabuwa da komai da kuma kowa don in same ki ke kadai, don nasan abinda kawai zan yi kenan in samu kwanciyar hankali da nutsuwar da nake bukata.

Don haka ban ga dalilin wannan bakin cikin da ki ke tayi ba, in don tsoratarwar da aka yi tayi miki ne a kan kauye da kuma gidanmu ni din ai namiji ne Humaira, nayi miki alkawarin babu wata wahala da zata dunfaroni in barta takai ga taba min ke face sai nasa dantsena na tare miki ita.

Ai ban rabo ki da gidanku da iyayenki don in wahalar da ke ko don in zama sanadin wahalarki ba, na rabo ki da su ne don ina son rayuwa tare da ke, ina son ganinki a tare da ni, ina son mallakar jikin nan naki, tó a na menene za ki yi ta wannan bacin ran?

Ko kina so ne ki nuna min cewar ke din ba kya  so na? Ko kuma ba kya bukatata?

Tabbas na sani ba zan iya amsa wadannan tambayoyin na Ado da kalmar eh ba, in dai har gaskiya nake nufin fadi. To amma iyayena fa? Musamman ma Gambota, Gambo tana da girma da darajarsu da kullum mai babban allo yake gaya min da kashedin da yake yi min a kansu, na ba a karo tsakanin kwai da dutse.

Sai in ga don in zauna da su lafiya in rabu da su kuma lafiya zan iya hakura da duk wani abinda nake so amma ina amfanin wannan abin da ya faru tsakanina da su a yau? Na tafi Babana yana ta furta munanan kalamai a kaina, Gambo kuwa ko sallama bamu yi ba balle in san halin da take ciki, amma Ado wai kar in tsananta bakin ciki.

To me zan yi? dariya? Nan da nan naji haushin shi ya kama ni saboda ganin da nayi tanfar kanshi kawai yake so..

“Dan sha ruwan nan ki jika bakinki, in ma ba za ki ci wani abu ba kin ga ai tunda ki ka yi amái ba ki sake cin wani abu ba, na ce uh’uh.

Kalaman Ado a kowane lokaci na rarrashi ne da fadin maganganu masu dadi, don dai ya samu yaga hankalina ya kwanta, ni nasan babu abin da kalaman Baba zasu yi miki don kuwa baki yi mishi komai ba, fushi yayi da fushin wani, Gambo kuwa nasan ba za ta taba jin zafinki ba, balle tayi fushi da ke, balle har taje tana yi miki wasu munanan kalamai.

Nayi Imani a daidai wannan lokacin da take jin kalaman dan Baban yake fadi a kanmu ita tana yi mana addu’a ne tana neman mana kariya daga duk wani sharri ko wata fitina, tana kuma neman mana alheri wurin Ubangiji shi ne kuma abin da zai same mu Humaira.”

Mun iso Kano ne misalin karfe shida da kwata, shirye-shiryen sallar magriba ake tayi don a wannan lokacin ita magriba din ana yinta ne shida da rabi a mafi yawancin wurare.

“Samu wuri mai kyau ka tsaya Mallam Haruna ka tsaya sai mun yi sallar magariba da isha mu wuce.”

Mallam Haruna yayi maza ya ce, “Kai a’a Mallam Ado, kar muyi haka don kuwa muna da sauran tafiya mai tsawo ban da haka ma ina ganin tamkar gara wannan hanyar da muka baro a bayanmu, kan wanda zamu hau nan gaba.”

Ado yayi murmushi ya ce, “Ina ganin dai ka dade ba ka je Katsina ba Mallam Haruna, in ba haka ba ai mu hanyoyinmu masu kyau ne.”

Kofar wani gida Ado ya kai ni, sai da yayi sallama da mai gidan suka gaisa sannan ya roke shi in shiga wurin iyalinshi in yi sallah, don a kan hanya muke, ya ce babu komai. Na shiga shi kuma ya koma sai da na idar da sallar naja carbina na jira nayi Isha’i bai dawo ba, na huta naji dadi sosai don ban saba irin wannan doguwar tafiyar ba, ban taba yin ta ba.

Iyakacina giyade, ban taba wuce nan ba, sai zuwa can maigidan ya shigo yana gayawa iyalinshi wadanda suka yi matukar karrama ni cewar bakuwar nan ta fito suka ce to, suka rako ni har kofar zaure suka miko min leda mai dauke da robar da suka cika min da kunun aya, nasa hannu biyu na karba nayi musu godiya.

Ado ya tasa ni a gaba zuwa in da motar mu take, ina shiga ciki na zauna ya miko min wasu kwayoyi guda biyu tare da kwalbar Coke ya ce “Karbi ki sha saboda aman da kike yi.” Ban yi mishi musu ba na karba nasha, ya fita akan zai maida kwalbar, bai dawo ba sai bayan minti ashirin da biyar. Mallam»Haruna yayi tsaki har ya gaji.

“Dabai fa mutumin nan ya ce zamu je, amma yake yi mana irin wannan bata lokacin.” Gabana ya yanke ya fadi jin sunan garin da Mallam Harunan ya ambata, ban taba jin sunan garin ba, iyaka kuma dai ban ce mishi komai ba, tunda ba abokin magana ba ne.

Ado ya dawo rike da ledoji guda biyu ya mika wa Mallam Haruna daya, ya ajiye mana daya Mallam Haruna ya karba yana godiya, yana ganin dankwaleliyar kazar da ke ledar tashi ya mance abin bacin ran da Adon yayi mishi, duk da tabbacin da Adon ya bani na ba zan sake yin amai ba komai naci, ban yarda naci koman ba, in ban da kunun ayan da mutanen nan suka bani wanda yayi min dadi ba kadan ba.

A wannan lokacin na dan samu natsuwa da kuma saukin da nayi bacci, watakila don sanyin dare da ya sauka watakila kuma don saukin aman da na samu, gashi har na samu nasha kunun aya ya zauna min.

Ban sha wahala ko naga tsananin tafiyar ba kamar yadda direban ke ta magana don kuwa na farka ne a inda naji Ado yana ce min “Kin farka a daidai Humaira, daga wannan garin da ki ka ga muna wucewa sai kauye guda daya ne a gabanmu (Tukunya) daga shi sai (Dabai).

Can baya kuwa in da muka baro, kin yi bacci ne a kusa da garin (Dayi) daga nan sai Malumfashi sai Kafur sai Sabuwar Kasa, sai Gozaki sai Dabai, to amma kin san akwai kananan kauyuka a tsakanin garuruwan sai a hankali za ki san su.”

A zuciyata na ce, in na zauna a garin kenan, don ni kam a zuciyata ina ganin tamkar babu abin da ya dace dani irin komawa gida in je in roki Babana da Gambota gafara kan bacin ran da na san na sanya su.

Ado ya saki wani lallausan murmushi bayan yayi ajiyar zuciya, tare da hamdala ga Ubangiji.

“Ga Dabai Humaira mun iso.” A hankali ya soma rada min a kunnena, bude ido ki ga garin mijinki Humairah gari da zai zamo shi ne garin ‘ya’yanki, ina son Dabai Humaira, ba wai don garina ba ne kawai, a’a mutanen garin mutane ne masu neman na kansu, masu karamci da ganin girman juna.

Mutanen Dabai jarumai ne manoma ne wasu da yawa kuma ‘yan kasuwa, in ta fannin ilimi ne kuwa muna da manyan Malaman addini a ta bangaren bokon ma ba a bar mu a baya ba, mutanen mu da yawa suna nan warwatse cikin ma’aikatun Gwamnati suna aiki tun daga Local Gobernmnent har zuwa State da kuma Federal.

<< Mijin Ta Ce 26Mijin Ta Ce 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×