Skip to content
Part 28 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

A daidai lokacin da Ado ke ta faman wasa min garin nasu na bude ido tarwai, wai domin in ga abinda yake gaya min din, tunda an yi sa’a farin wata ya haske ko ina. Ban ga komai ba in ban da dogayen bishiyoyin da ya ce min na kuka ne, sai ko filayen da yake ta nuna min yana fadin duk nan da ki ke gani ba jeji ba ne, gonaki ne na mutane. Bari damuna ta zauna sosai ki ga abin mamaki, a zuciyata na ce ka gani dai.

Shi garin Dabai gari ne da yayi sa’a babbar hanya ta ratsa shi, ta ko ina kin ga wannan hanyar da muka biyo’ai kin ga garuruwan da muka baro a bayanmu, to nan gabanmu in ta wuce Dabai zata wuce, mararrabar Danja ta tafi har Hunkuiyi taje Basawa ta isa Zariya, kin ga ta tafi har Kaduna kenan.

In kuwa a mararrabar Danja ki ka tsaya ki ka bi hanyar da tayi dama, to za ki isa kauyen Dan Mai gunta ki wuce kije har Danjan, in kuma ki ka nufi hagu to zaki je garuruwan Kudan daga nan kije har Makarfi in ki ka fada babban titi ma sai ya maida ke har Kano, ita ce ma hanyar da yan kasuwanmu suka fi amfani da ita.”

Ya sake kallona cikin murmushi yana fadin “Ba za ki gane dadin Dabai da karamcin mutanenta ba sai na gaya miki cewar mutanen da suka san Dabai din da irin halinta suna yi mata kirari da cewar ce Dabai dabaibaye bako, maida bako dan gida ya manta garinsu, ta magaji mai alamar samu.

Ban taba tankawa Ado maganganunshi ba tunda muka baro gida, don haka wannan ma ban amsa ba, na dai san kawai yana son garin nasu da kuma jihar tasu ta Katsina don yanzun nan ne zan ji ya ce wa Mallam Haruna a’a ai mu nan Katsina babu wannan, to ban tsananta jin mamakin shi ba, don kuwa nima ina son jihata ta Bauchi da garinmu na Giyade da kuma unguwarmu ta Nasarawa Jahun.

“Rage tafiya sosai Mallam Haruna ka kuma sanyawa na baya alamar barin hanya nan gabanka kadan ta gefen damanka akwai hanyar da ta shiga ciki, ita za ka bi.” “Yan daidaikun mutane ne a waje saboda dare ya riga yayi nisa, amma mafi yawancinsu Ado yana shaida su alamar dai bai taba rabuwa da al’amuran garin nasu ba.

“Bi ta nan gefen kayi dama sosai, akwai katuwar bishiyar kuka, ta gefen ta zaka wuce ka yi yamma irin bayanin da Ado ya rinka yi kenan har muka iso inda yace to, ga Masallaci can fari nan kawai zaka tsaya.

Muna tsayawa Mallam Haruna yayi murmushi ya ce, “Kai Mallam Ado kasan garin nan Ado ya taya shi murmushin ya ce, garina ne fa, ga ruwa nan a randa ga bandaki can gefe in zaka taba ruwa bari mu shiga in fiddo maka da abinci.”

Mallam Haruna yayi maZa ya ce, kai ai ni a koshe nake, a dai bani wurin kwanciya kawai.

Ado yasa hannu ya dauki jaka guda daya dakke bayan motar ya rataya akan kafadar na kuma san da ita kadai ya iso garin ya tasa ni a gaba muka nufi cikin gidan, muna fita daga zauren wanda babba ne sosai ga kuma wani daki a cikin shi.

Sai ga wani shamaki da ya shiga tsakanin mutanen zauren da ganin cikin gida daga bayan shamakin hanyoyi ne da suka nufi sasan da ke gidan, gaskiya ne girman gidan su Ado ya wuce a tsaya yin bayani.

To Kinga ga hanyar sasansu nan, wancan sasan Baba Halliru ne shi da ‘ya’yanshi wancan na Baba Ubangida shima shi da nashi ya’yan wancan nasu Baba Tukur ne shima da nashi iyalin mu dai je kawai yanzu ba za ki gane komai ba sai an kwana biya kin gane kan gidan da mutanen ciki tukuna. A zuciyata nace hu’un.

Muna dosan sasan da ya ce min shi ne nasan ya kwala sallama sai kawai naji wata murya ta amsa daga cikin wani daki tana kuma tambayar Adamu ne a cikin tsohon daren nan? Yayi murmushi ya ce mishi eh Baba, mutumin da Ado ya kira da sunan Baba ya fito rike da sanda a hannunshi ba dai don tsufa ba kam sai dai ko don wani dalili don da karfinshi na ganshi.

Yana ganina yasa hannu ya rufe baki nuna alamar mamaki da wannan yarinyar ku ke tàfe? Ya ce mishi eh Baba, sannu da zuwa Aishatu, nima nayi ta amsawa don girmamawa.

Kaga halin mata ba? Sufa babu wani babba babu yaro a cikinsu, in ka biye musu kunya za su ba ka. Ado yayi murmushi ya ce, me ya faru Baba? Ya ce to ai uwar taku bata nan tana can taje Kauyensu na Tukunya zata kwana saboda yau ana kamun wata jikar su, in ban da rashin hankali irin nata da nima na biye ta shi babba yana yin nesa da wurinshi ne tunda ya san yana da baya da yawa.

Ado ya ce, ai babu komai Baba, Baba yaja tsaki ya ce, in ban da lalura irin ta girma me za’ayi da zaman mace daya ne?

Ado ya sake wani murmushin ya ce ai Humairah ba gobe zata tafi ba, ba kuma jibi ba, zata dawo ta same ta babu damuwa, ya ce au to shi kenan amma ai ba dai haka aka so ba.

Makullin dakin nan a kusa yake ni ko Baba? Baba yayi maza ya ce, eh ai cikinshi nake wuni tunda sorona ya fadi, ya ce haka ne fa Baba an gaya min soronka ya fadi ya bude dakin muka shiga, komai a gyare yake a kintse, dakin yasha leda ga katifa timemiya a shimfide ga kujerar kwanciya can gefe akwati ne shi mai kyau a rufe na tabbatar komai na cikin dakin na Ado ne.

Muna shiga ya sauke jakar kafadar shi ya bude ta ya fiddo fitilar chaji da batir ya kunnata ko ina ya dauki haske sosai.

A to, tunda ka ki ka sanya mana wutar lantarki a gida mu ma mu rinka ganin haske irin naka na birni, ai ka rinka yawo da fitila a Jaka, wata mata ce da ta ja ta tsaya a bakin kofa tayi wannan maganar tana ganin dakin ya gauraye da haske kuma ta karasa shigowa cikin dakin ta durkusa kamar wata karamar yarinya.

Da gefen ido Adon ya harareta ya ce, mijinki fa me ya hana shi jawowa? Tayi murmushi tare da langabar da kai ta ce waiyo bai da shi ne, ya ce eh bai da shi, amma ai a hakan yake iya karo aure ko? Ta sake wani murmushin kafin ta sake cewa waiyo!! Wannan ai rabo ne.

Ado yayi maza ya ce, haka ne. Tayi maza ta kalle ni cikin fara’a, kin ga rabu da mijinki kin ji ke dai sannu da zuwa abinki na ce mata yauwa, na kuma fara gaisheta saboda ganin zata iya girmana da shekarun da suka kai tara ko ma goma.

Kai mata ruwa kafin ki fara tambayar mutane abin da za su ci don ke aikinki kenan tayi maza ta sake langwabewa ta ce ehhhyi, ni ai cin ne sna’ata, sai in ga kamar kowa ma haka yake. Yayi maza ya girgiza kai ya ce a’a ke kadai ce, ta ce au to, to na ji to ku da wanne ku ke farawa? Ya ce wanka don ba ki iya karbar baki ba ne yasa ba ki gane hakan ba, ta ce au to to naji zan gyara ko da yake dai munan da yake mu yan kauye ne ci ne gaba da wanka ya ce, eh to ai kin san mu ‘yan birni ne, ta ce haka ne.

To bari in samo ruwan zafi nan da nan ta fita, tana barin dakin ya daga ido ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min Ruwailah kenan, matar yaya Jafaru ce ai kin san yana yawan zuwa wurina, na gyada kai nuna alamar na gane shi, ya ce to shi ne babban wanmu a nan sasan shi ne dan Baba Tanimu na farko wanda yaje ya karbar min aurenki amma ai kin san ni ni kadai ne wurin mahafina ko?

Na girgiza kai a hankali, nuna alamar ban sani ba, ya ce to ni kadai ne. Ya ci gaba da abinda yake yi na kaye-kaye da gyare-gyare tanfar dai ba a cikin dare muka shiga dakin ba.

Ruwailah ta dawo da ruwan zafi a bokiti da wani kuma a flaks dinta da ta dauka a dakin, ga kuma wani kunshi cikin leda da ta ajiye a gefe, wai yana yi muku sannu da zuwa.

Ado ya yi tsaki ya ce, kai ke kan ba ki da kirki, yanzunnan sai da ki ka tashi bawan Allahn nan a cikin tsohon daren nan ki ka yi sanadin fitarshi waje? Ta ce, oh oh, ba ma a wurina yake ba, to amma da bai fitan ba da wa ya sauke maka mutumin da kazo dashi din?

Ado ya rike baki nuna’alamar mantuwa, ya ce na shagala ina kallon Humaira, kin san ni in ina tare da ita to sunana ne kadai ban iya mancewa da shi.

Ruwaila ta kyalkyale da dariya ta ce, ai kuwa dai ma kayi kokari tunda ba ka mancewa da sunan naka a nan sam.

Sabon soso da sabulu da brush da abin wanke baki da sabon tawul ya fiddo daga cikin jakar tashi ya miko min na karba nabi bayan Ruwailah da ta daukan min ruwan muka je ta nuna min ban dakin.

Na dawo daga wankan na samu kwanukan abinci iri-iri, ya kalle ni ya ce min wannan kunshin na gasasshen nama ne Yaya Jafaru ya sayo miki, ga furar da Baba ya bayar da nono Ruwailah ta dama miki, ga kuma tuwon dawa miyar kuka shima mai dumi ne ta dumamo da wanne za ki fara?

Na ce kowanne, ya kalli Ruwailah da ke ta faman bubbude min kowanne in gani ya ce mata ba kin gama naki ba, to kije mana kuma sai da safe, ta ce am wai jira nake yi ta gama mu tafi can wurina ta kwanta.

Yayi maza ya ce, wasa kenan, tabar dakin mijinta da mijin nata a ciki taje ta kwana a wannan tsohon dakin naki? Ta ce, to ai shi kenan sai da safe Amarya. Nayi murmushi na ce mata to ki huta gajiya.

Tana fita Ado ya kalle ni ya ce wannan atishawan da kike tayi fa don kin yi wanka a bayan gidan da babu rufi ne baki saba ba, ban amsa mishi ba amma cikin zuciyata nima na yarda hakanne don maimakon in ji dadin wankan da nayi sai naji kamar sanyi ya kama ni.

Naci tuwo sosai don yayi min dadi laushinshi da dankonshi yayi bambam da irin tuwon da na saba, nasha ruwan tea mai citta naci nama kadan na gyara na kwanta bayan na shafa mai nasa rigar baccina wanda itama shi yazo da ita.

Na kalle shi cikin natsuwa nayi mishi magana wanda tun fitowarmu ban yi mishi ba saboda na gane babu komai cikin jakar tashi in ban da kayayyakin amfanin da ya saya saboda ni na ce to da ban biyo ka ba fa yaya zaka yi da kayan nan?

Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, ban taba daukar za ki iya kin bina ba, na dauka ke ma kina  so na.

Muna kwance ni da Ado akan katifar yana gefenshi ina nawa sai dai mu dukanmu babu wanda ya samu yayi bacci, ya daga ido cikin natsuwa ya ce min Humairah ba ki ga kamar kasa yin baccin nan da muka yi alama ne na muna jin marmarin juna ba?

Nayi maza nace mishi, a’a bana ji ya sake daga ido ya kalle ni ya ce, to ai ni ina ji, nayi maza na tsuke fuska na ce mishi ba fa na zabi biyo ka da nufin in biyo ka ba ne.

Cikin natsuwa ya ce min ai na sani, na sake tsuke fuska na ce, to ko da na biyo ka akan kuskuren ba zama zan yi ba, komawa zan yi. Ya sake cewa na sani, ya sake saurarawa ko zai ji zan sake fadin wata magana, sai yaga nayi shiru.

Sai naga yayi murmushi kafin ya ce min to amma ai ko za ki koman tunda ba ki kai ga tafiyar ba ai ina ganin ba zai hana in nace nayi marmarinki kiyi min yanda ki ka saba yi min bä ko kuwa. Nayi maza na kara tsuke fuska, kafin na ce mishi a’a, ya ce to shi kenan sai da safe.

Washegari tun safe Goggo Ayalle ta dawo gidan a dalilin aiken da Baba Tanimu yayi na a dauko ta, tana dawowa kuwa ta maida ni dakinta, wunin ranar har dare ban gane na gama gaisawa da mutanen gidan nan ba saboda yawansu.

Don haka kowa na gani kawai sabuwar gaisuwa nake yi mishi, sai in shi ne ya ce min ai dazu mun gaisa in ce mishi to.

Karba sosai Goggo Ayalle tayi min, ta yi ta ina taka saka dani, komai hannunta ya kai kan shi in dai ta daga taga naci ne miko min shi take yi, ungo ki ci, sai in ni ce naga zan kwari kaina in ce mata na koshi.

Sau goma kuma in ta kalle ni zata yi murmushi ta ce, oh haka rabo yake har da rabon aurenki cikin al’amuran da suka kai Adamu garin nan suka zaunar dashi, kin san shi rabo ba karamin al’amari ba ne.

Sai kawai nima in taya ta murmushin da take yin sai dai ban ce mata komai, can anjima kuma sai ka ji tana sake tambayata in ce ko dai manyan duka lafiya? In sake cewa lafiyarsu kalau, tamfar dazu bata tambayí lafiyar tasu ba.

A haka muka wuni har dare ina idar da Sallar Isha’i ta kalle ni ta sake nuna min gadon da na wuni akai ta ce min hau kiyi barcinki ki huta gajiya, kar yan hiraa suce zasu dame ki, na ce to. Na sake dalewa gadon nayi kwanciyata, zuwa can naji Ado yana kirana, nayi kamar ban ji shi ba, ya matso kusa da kofar Goggo yana tambayarta.

“Goggo Humaira tana kusa ne?”

Goggon tayi maza ta sauka daga nata gadon ta leka tana tambayarshi wani abu ka ke so ne Adamu? Ya ce a’a Goggo, sai da safe. Abin da kawai ya fada kenan sai na jiwo Baba Tanimu daga dakinshi yana fadin “Yau ga wani al’amari, wannan fa shi ne girman kwabo.

An girma ba ayi hankali ba, yaro yana kwalawa matarshi kira kina ji tayi shiru ba kiyi mata magana ba, ya taso yazo har kofar dakinki yana tanbayarki ita kin ce wai in wani abu yake so ya gaya miki, to in ita yake so fa?

Na ce in yana da bukatarta ne ma ya gaya miki? Goggo tayi maza ta ce au, to ai bangane ba ne. Ke Aisha tashi-tashi je ki maza mijinki yana kiranki.”

A kan dole ta fito da ni daga dikin na shiga dakinmu na samu Ado yana zaran jiran shigowan nawa, gasasshiyar kaza ne a gabanshi, a gefenta kuma flaks ne na ruwan zafi, ban kalle shi ba na wuce na hau katifa nayi kwanciyata, ya biyo ni da kallo fuskarshi ta bayyanar da rashin jin dadin shi kan yanda nayi.

Yayi karfin hali ya hadiye fushinshi tashi mana Humairaa nayi kamar ban ji ba, yayi tayi min magana nayi shiru kamar ba dani yake yi ba, ke ni fa kin san bana son irin wannau wulakancin na ayi tayi miki magana kina yin banza da mutane, ban tanka mishi ba, ban san yanda aka yi ba sai kawai naji ya cafko hannuna ya murde.

<< Mijin Ta Ce 27Mijin Ta Ce 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×