Skip to content
Part 29 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

A firgice na kwallara kara saboda zafin da naji, na kuma yi maza na kame bakina nayi shiru saboda tunawar da nayi cewar a bakon wuri muke ko kuma ni din ni bakuwa ce.

Daga cikin dakin Baba Tanimu da ke makwabtaka da namun naji an yi gyaran murya alamar dai yin kashedi.

Ado ya hakura ya gyara ya kwanta, ni kuwa naci gaba da zama a kan katifar ina kukan sharbe tare da shisshika a hankali sai dai shi Ado shiru kawai yayi amma yana ji na.

Ana cikin haka wani irin hadari ya taso mai matsanancin iska da guguwa da rugugi mai tsananinn firgitarwa har wani bai iya cin motsin wanda suke tare, sai in yayi motsi ne da karfi nayi maza na gyara na kwanta da nufin yin shiru kamar yanda shima Adon yayi, sai kawai naga ya juyo gare ni.

“Kin fasa kukanne?” Nayi kamar ban ji shi ba, Ni fa yau ba zan iya irin kwanan da muka yi jiya ba.” Ya miko hannu zai taba ni, nayi maza na ce mishi “Gaskiya ni fa ba zama nazo yi ba, ko da ina da kudin mota da tafiyata nayi.”

Ina gama fadin hakan ya cafke ni, bai saurari ihun da nake yi mishi ba saboda yasan ba zai kai ga kunnen Baba Tanimu ba. Sabuwar iskar da ke kadawa ga tsawa da rugugi, watakila ma ya dade yana baccin shi, gane hakanne yasa ni barin ihun na koma yi mishi bayani.

“Ni gaskiya tun da muka zo fa cikina yana ciwo, ban gaya maka ba ne kawai.” Bai saurara ba.

Na kwana da matsanancin ciwon cikin da yayi dalilin da na kwana ina murkususu daga kan katifa in koma kasa, na rasa in da zan sa kaina in ji dadi, nayi kuka har na hakura nayi shiru.

Ado yayi nadamar abin da ya faru tsakanina dashi, yayi nadamar tilasta min da yayi a haka muka kwana daga ni har shi babu wanda ya samu runtsawa.

Ana fitowa daga sallar Asuba muka kama hanya zuwa asibiti da ni dashi da Yaya Jafaru da Ruwailah, saboda tun dare ya shaidawa Baba Tanimu halin da nake ciki, tun daren kuma Yaya Jafarun yayiwo aron mota wurin wani abokinshi don ma Baba Tanimu ya hana tafiyar daren ne ya ce a hakura ayi sallah tukunna.

Asibitin Malunfashi ya kai mu, shi ne wai yafi girma a nan kusa, gwajin farko da Likitan tayi min tayi bayanin ciki ne ya lalace ya fita daga cikin mahaifa, sai dai bai shiga ya fadi ba, saboda haka zasu wanke shi ya fita don in ba haka zan yi ta wahala da shi kafin ya kai ga fita.

To amma me ya kawo haka Likita? Ado ya bukaci sani, tayi ta lissafo dalilai ciki har da tafiya mai tsanani ko kuma bacin rai ko aiki mai wahala shi yasa yawanci muke hana mata masu karamin ciki ko kuma cikin da ya riga ya kai watanni bakwai yin irin wadannan abubuwan, ku kuma maza muke rokonku da ku rinka tausaya musu.

Daga Ado har Yaya Jafaru da Ruwailah sun gamsu da jawabin nata.

Aka yi min wankin ciki aka sallamo mu bayan La’asar, duk da Ado yaso a bar ni in kwana wai a kara kulawa dani sosai aka ce babu gado.

Mun iso gida gab da magriba, kai tsaye dakin Goggo Ayalle aka kai ni, wacce ta yi fada mai tsanani akan wankin cikin da taji an yi min, ina dalili yarinya ko haihuwar fari bata yi ba za aje ana kakaba mata karfen nasara a ciki? Da da ni akaje ai da ban bari anyi hakan ba.

Gaba daya hankalin Ado yayi matukar tashi da abin da ya farun, ina jin Baba Tanimu da daddare yana ta ba shi hakuri, ita rayuwa fa haka take, a kullum mutumin kirki ba ya zama ba tare da ana jarraba shi ba, ba ka fita daga cikin wannan ba ga kuma wannan ya sake zuwa.

To kayi hakuri kar kuma ka ce zaka yi saurin gayawa iyayenta tunda ga irin rabuwar da ka ce kun yi dasu. Naji Ado ya ce, “A’a Baba, ba zan iya boyewa mahaifiyarta halin da take ciki ba, tun muna asibiti nayi waya na gaya mata, ban dai sake gayawa kowa ba; amma ita kam na gaya mata, ya ce to shi kenan tunda kaga hakan yafi.

Kwanana bakwai a dakin Goggo Ayalle tana ta faman tarairayata, Baba Tanimu kuma da su Baba ubangida suka yi ta bayar da kaji ana yankawa ana yi min farfesu, har ma cikin kajin Goggo ta cire wata yar budurwa da ta bata sha’awa ta ce ba za ta yankata ba, bar min ita zata yi in yi iri.

A zuciyata na ce, uhun ni kam ai ba.zama nazo

yi ba.

A wadannan kwanakin babu wata mu’aallar arziki tsakanina da Ado, ko gaisuwarshi ban cika amsawa ba. A cikin kwanakin ne kuma na lura ya daina zama a gida tun bayan fitan da suka yi da Baba Tanimu ba a sake wayar gari na ganshi a gidan da safe ba sai gab da Azahar, ana yi sallar La’asar kuma zai sake fita sai kusan faduwar rana

ya dawo.

Ban san ina yake zuwa ba, ban kuma tambaye shi ba don a yanzu ko kallon shi bana yi, fatana da tattalina bai wuce in samu kudin mota ba in kama hanya in yi tafiyata.

Rannan ya dawo kusan Azahar ya shigo dakin na Goggo, duk da yana ganin naji sauki har ma nayi kyan gani, sai ya tambaye ni ya ya jikin naki dai Humaira? A lalace na ce mishi da sauki, ya kalle ni cikin natsuwa.

“Amma kin ga yayi miki daidai a hakan da kike yi Humaira? Kina mu’amallah da kowa lafiya amma ni da na kawo ki babu?” Na kalle shi a sakarce na ce mishi, “To ka maida ni mana in da ka dauko nin.” Ya ce, to babu laifi ya wuce ya fita.

Ran da na cika kwana goma rannan Baba Tanimu yasa Goggo ta sani na koma dakin namu, ita kam taso ne a bar ni in yi arba’in.

Zaman da na yi a dakin Goggo ya sani fahimtar gidan sosai da kuma mutanen gidan.

Sassa guda hudu da ke gidan suna karkashin dattawa hudu ne wadanda su ne asalin yayan maigidan su kuma dukan su uba daya ne ya haife su, amma uwa daban-daban, babban cikinsu shine Baba ubangida sai Baba Halliru sai Baba Tanimu kafin Baba Tukur shi ne karaminsu.

A duka sassan nan guda hudu akwai iyalai musu yawa su dattawan gidan kuma suma suna da nasu matan, Baba Ubangida shi ne mai mata Goggo Turai wacce take sana’ar kokon safe, Baba Halliru shi ne mai Goggo Jaku ita kuma tana furar sayarwa mai dadi Baba Tanimu Goggo Ayalle ita kosai take yi itama da safe.

Sai Baba Tukur, shi kuma tashi matar ita ce Goggo ‘yar neto ita kuma tana gaudan sayarwa. A kowane sassa na gidan akwai yaran mata masu yawa saboda kusan duk ‘ya’yan gidan maza masu aure ne wadan da basu yi ba ‘yan kadan ne mafi yawancin masu auren kuma mata bibiyu ke gare su masu dai-dai din basu da yawa, kamar ma ba su dade da yin nasu auren sosai ba.

Yanda duk tsofaffin gidan ke da sana’o’insu haka suma yaran matan gidan suke da nasu sana’o’in tun daga mangyada, manja, gyadar miya, maggi, gishiri, Alala, dan wake, gasu nan dai birjik. Wasu har dinki wasu kuma har aikatau da su wanki amma dai kowa da abin da yake yi gwargwadon karin injin shi.

Kiwo kuwa a gidan ba a magana duk yawan Tumaki da Awaki da Kajin kuma abin mamakin shi ne kowa yána shaida nashi.

Gabadaya sassan nan guda hudu kuma akwai mace guda da take kamar ita ce shugabarsu a sassan Baba Tanimu dai Ruwailah ce matar Yaya Jafaru ta farko, a sasan Baba ubangida da kuma akwai Furera matar Yaya Baidu itama uwargida ce.

Sasan Baba Halliru akwai Gaje matar Yaya Jumare, itama uwargida sai sasan Baba Tukur nan kuma Tanbai matar Yaya Amiru akwai Uwale, itama uwargida, gabadaya wadannan matan hudu sun zo gidanne a kusan lokaci daya, ma’ana babu bambancin lokaci mai yawa a tsakanin aurarrakin nasu dukansu kuma suna da amare da kuma matan kannen miji.

Haka nan gaskiyar Mama ne gabadaya gidan tukunyar abincinsu na dare gabadaya ne da rana ne dai kowa zai yi abin da zai ci shi da iyalinshi a wurinshi amma na dare a hade yake duk kuma wanda ke da girkin ranar to shi ne mai ba da hatsin da za ayi amfani dashi dama duk abinda za a nema Goggo Ayalle kuma ta shaida min cewar in mace tayi girki sau daya to kwana ashirin da biyar take yi bata sake ba.

Ai kuwa kin ga dole suyi ta neman kudinsu tunda basu da wani aiki na ce haka ne, a zuciyata kuwa cewa nayi yaran mata ashirin da biyar kenan a gidan.

Muna nan zaune a dakinmu ni da Ado, zaman babu wani dadi. Kallon shi bana yi balle in san me yake ciki, shima baya takura min akan komai zuba min ido kawai yake yi babu abin da nake fata irin nera talatin-talatin din da Baba Tanimu yake bani kullum safiya, ya ce wai in sai abin da nake so in karya da shi da kuma ashirin-ashirin din kokon da Baba ubangida yake bani.

Ita kuma Goggo Turai ta ce kai haba, bakin wannan yarinyar dai ita kadai ace sai na amshi kudinta? Je ki ki rike kudinki kin ji? Don haka kunu da kosai ba saye nake yi ba, sai nake tara hamsin-hamsin din ina fata su ishe ni kudin motar tafiya gida in sulale in yi tafiyata.

Rannan na wuni ina murna na kirga kudina sun kai dubu daya har da dari daya ina lissafin kwanakin da suka saura kudina su gama cika sai kawai nazo zan ajiye wata nera hamsin din naga babu komai sai wata tsohuwar nera hamsin itama watakila bai ganta ba ne sanda ya kwashe su. Nayi kuka rannan har na gaji ban kuma iya cin komai ba saboda tsananin bacin rai.

Ado ya dawo gab da Azahar ya same ni a haka, ya juya ya fita bai zauna ba, bayan Sallar Isha’i ma ya shigo dakin da niyyar kwanciya ya same ni ina ta faman kuka, wuri ya nema ya zauna bayan yaje yayi wankanshi ya dawo.

Ban kalle shi ba balle in san me yake yi, sai naji yana magana alamar waya yake yi, gaisuwa ta ladabi da natsuwa naji shi yana yi, don haka na kasa kunne ko zan gane da wa yake maganar, sai naji yana cewa.

“Gaskiya Gambo na gaji da karyar da nake yi miki ne, cewar muna nan lafiya, a gaskiya ba hakan ba ne, ina jin salatin da Gambo ta soma yi, ban san me ta ce ishi ba, sai naji ya ce mata gata, nayi kamar ba zan karba ba sai naga to ni kuma a wa? Gambo ta ce, a bani waya in ki karba? Ina karbar wayar na kaita kunnena naji muryar Gambota gabana ya yanke ya fadi nan take na soma yi mata kuka bata yi min fada ba kamar yanda nayi zaton zata yi magana ta soma yi min cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Ban ji dadin yadda ki ke yi wa mijinki ba to da wanne zai ji? Da halin da yake ciki ko da rashin lafiyarki da yayi ta fama da ita? Ko da bacin ran abin da ki ke yi mishi? Matar kirki kuwa ai bata haka, ita takan taimaki mijinta ne a duk lokacin da tasan yana bukatar taimakonta, ta rufa mishi asiri a inda tasan yana bukatar rufin asirinta.

In ta san yana cikin tashin hankali kuma ta kwantar mishi da hankalinshi, sannan in ba ki sani ba wannan abin da kike yi ba shi kadai kike tozártawa ba har da ni, don kuwa kina kokarin nunawa wadanda basu sanni ba ne su san yadda nake tunda ai ita ‘ya wakiliya ce ta uwarta.

In kiyi halin kwarai ace kin samu tarbiyya gidan ku in baki yi ba a gane uwarki ba mutuniyar kirki ba ce kar in sake jin an ce min baki kyauta ba, in dai ba kina so raina ya baci da ke ba ne, tana fadin hakan ta kashe wayar.

Sunkuyar da kaina kasa nayi, nayi shiru ban iya cewa Ado komai ba, iyaka dai ranar mun kwana lafiya amma ko kusa da ni bai zo ba, balle ya ce zai taba ni, ina wurina yana nashi.

Washegari da Asuba yana idar da Sallah Asuba ya shigo ya tashe ni ya wuce ya fita, sai dai maimakon sai Azahar in ga ya dawo, wajen sha daya naga shigowarshi. Ya koma gefe yana cire ranbut din kafarshi da hand globe din hannunshi mahadin ranbut din.

Naji Baba Tanimu daga daki yana ce mishi “Ka dawo ne Adamu?” Ya ce mishi “Eh Baba, na dawo.” Ya ce “Sannu da kokari ka ji? Ubangiji ya yiwa kokarin ka albarka.” Yayi murmushi ya ce Amin Baba.” Ya shigo cikin dakin namu ya same ni ma Zaune.

Ya kalle ni yayi murmushi, ya ce to ko ke fa? Kin yi wankanki kinyi fes da ke, na sani ba kya jin dadin mu’amalla da kayan da ki ke amfani da su tunda sunyi miki karanci da yawa dogayen riguna biyu ne kawai, sai zanin da ki ka zo da shi a jikinki.

Kiyi min hakuri a yanzu, na katse shi ta hanyar fara gaishe shi, yana gama arnsa gaisuwar ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, samo min dumamen tuwo wurin Goggo Ayalle, na ce to, na tashi na tafi cikin zuciyata ina tunanin tun zuwanmu gidan kwanaki ashirin da daya da suka wuce ban taba lura da cin shi ko shanshi ba, ban kuma taba dora tukunya a murhu don yin girkin rana ba, tunda kowa yana abincin ranarshi.

Ni dai nasan duk abin da Goggo Ayalle zata ci zata bai haka nan ma Yaya Ruwailah tunda nima yanzu yayan nake kiranta.

Na dawo da kwano mai dauke da tuwon da aka dumama shi tare da miyar shi a wuri daya na ajiye mishi na koma gefe na zauna sai ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min baki bani cokali ba, nayí maza na kalle shi saboda sanin shi ba mai cin tuwo da cokali ba ne.

“Da cokali za ka ci?” Ya ce, “Eh, dashi na ke ci yanzu saboda hannun nawa ba na jin dadin cin tuwon da su.” “Me ya same su? mu gani.” Bai yi magana ba ya ware min tafin hannayen nashi.

Tsigar jikina tayi matukar tashi tayi wani yarrrr! hankalina yayi matukar tashi da yanda naga hannun Ado gaba daya hannun nashi bororo ne ya. duru ruwa, wani wurin ma ya fashe ya zamą miki babu dadin gani.

Fuskarta a yamutse saboda yanda hankalina yayi matukar tashi na tambaye shi me ka ke yi hannunka yayi haka? Shirun da yayi bai ban amsa ba yasa na sake tambayarshi Noma? Cikin nutsuwa ya kalle ni ya ce min, in nayi noma menene Humaira?

Ni ba namiji ba ne? Ni fa ba wannan ne wahala a wurina ba, wahala a wurina bai wuce ki ki yarda mu zauna lafiya ba, amma in za ki yarda mu zåunna lafiya ki gamsu da kokarina ki yarda da cewar in ban yi miki ba, ba ni da shi ne.

Kiyi min hakuri ai ba zan gane ina wahala ba sai in rinka ganin tamkar abin da ya dani a matsayina na namiji kawai nake yi in kuwa haka ne kin ga bai zamo min wahala ba.

<< Mijin Ta Ce 28Mijin Ta Ce 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×