Ban san yadda aka yi ba sai kawai naga Hajiya Kubra tayi jifa da gyalen da take yafe dashi kan kace meye wannan tuni danbe mai tsanani ya kaure a tsakaninta da Mama, sai ji kake yi didim-didim-dididim!!
Don kuwa su dukkan su ma’abota kiba ne da kuma jin karfi, sai dai kan ka ce meye wannan Hajiya Kubra ta kai Mama kasa tim! Abinda ya firgita gidan gabadaya ni da kaina jikina rawa yake yi.
Habiba da ta kasa hakurin kayen da aka yi wa uwarsu, ta sunkuto tabarya da gudu tazo zata rafkawa Hajiya Kubra. . .