Skip to content
Part 32 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Yana kuma daidaitan lokacin tashin mu ne ya taso daga gonarshi ya biyo min ta makaranta mu dawo gida tare, da daddare in mun gama abinda muke yi kuma yana duba takarduna yaga aikin da aka yi mana ya yi min gyara kan abin da ban gane ba.

Zaman lafiyan da aka lura aka ga ya samu tsakaninà da mijina ne ya bayyana a cikin gida, wanda ban samu hakan ba sai da na yarda ni ce a kasa shi ne sama da ni, sai da na yarda da barin son raina na koma bin nashi, na koma karbar umarnin komai daga gare shi, na koma rayuwar yi nayi bari na bari ko da kuwa ina son barin ko kuma ina kin yin da aka ce in yin.

Misali, ko a cikin gida ina son shiga cikin mata ‘yan uwana in dan yi mu’amalla da su in dan ji dadi a raina, amma tunda yake min ya hana ni žaman gindin bishiya don hira, na ce mishi, to na kuma bari ko baya nan bana zuwa.

Tunda ya hana ni bin dakunan mutane matukar ba wani dalili mai kwari ne ya kai ni ba, na hakura na daina sai ko dakin Goggo Ayalle. Kullum ni kadai ce a wurina, in ba shi din yana gida bane kowane lokaci a cikin hidimarshi nake, tunda daga wankin yan suturunshi da adana su da tattalin abin da zai ci hakan kuma bai hana ni ba shi lokacina a duk lokacin da ya bukaci hakan.

Ana cikin hakanne kawai na soma jin maganganu suna yawa a cikin gida, wai ni din fin karfin shi nayi, bai da wani katabus bai iya yin komai sai abin da nasa shi, ko kuma na hana shi, wai ai tunda na iya raba shi da Hajiya Majadan duk alherin da tayi mishi, to babu wani wanda ba zan iya raba shi da shi ba.

Ina jin maganganun na gane daga inda suka fara fitowa, cikin zuciyata na ce don ta gane na daina daukan shawarwarinta ne, gara ita, nata mijin yana da irin wannan juriyar ni nawa in na ce zan yi mishi haka ba kwashewa kalau zan yi ba.

Na dai kudiri aniyar zama lafiya da kowa ba na son fitina, don kuwa nasan babu alheri a cikinta, tashin hankalin Mama kawai da ta tasa mu a gaba shi ne yayi dalilin barowar mu gida muka taho nan, to ta wadannan bataliya fa?

A wannan lokacin aka sake fito min da wata dabi’a, duk wacce zata yi wanka ko zata yi taya bahaya sai tazo wurina ta ce wai a nan zata yi.

Wuni suke yi suna layin shiga bayan gida, kuma duk yanda na kai da wanke shi sai sun bata shi yayi ta wari, wani lokaci har cikin daki, don tuni da nayi hakuri da su akan sabon halin nasa.

To Ado ya ce bai yarda in hana su, in gaya musu cewar shi din ya hana su shiga wannan bayan gidan ya ce in gaya musu su rinka wanke nasu, suna gyarawa don su rinka jin dadin shiga ko ni din da irin barin wannan din da kazanta da ba su zo sun shiga ba.

Ni kam ban iya gaya musu ba, ina jin kunya don mafi yawancinsu sun girme ni nesa ba kusa ba, shi kuma yana ganin wata tazo ta shiga ni yake balbalewa da fada, sai da nayi sa’a maganar ta kai ga Baba Tanimu.

Shi ne yayi kashedi mai kari kar ya sake ganin wata taje ta zaga a wurina baya son iya shege da neman magana.

A wannan lokacin har a gabana a kuma kan idona za a rinka tsaki ana cewa a hau, to namiji kuma, wacce bata san shi ba ai ita ce bata san shi ba, mu kan ai sun shamu mun ware, muna nan da ke za ki zo kina zubar mana da hawaye sanda zai yi miki halin nasu mu ce muma bamu sanki ba amarya muka sani.

Kusan kullum sai an ce min an ga Ado gidan Mallam Korau yaje tadi, rannan dai na daure na samu Adon na tambaye shi cikin natsuwa na ce mishi ni da gaske ne wai kana neman yar gidan Mallam Korau?

Bai wani kalle ni sosai ba ya ce min menene in ina neman nata? Na ce a’a na dai tambaya ne kawai don in sani ya ce ba uwardakinki ce ta gayamiki ba, ai ba zata yi miki karya ba, watakila dai kina ganin ne tanfar gonar tawa ba, za ta rike min ku ku biyun ba ko?

Ban sake ce wa Ado komai ba, amma wani irin al’amari ne naji ya taso min ya tokare ni a kirji, wani irin nauyi ya saukar min a kirjin, zuciyata tayi matukar kunci, karo na farko da naji irin wannan abin a tare da ni.

Kishi mai tsanani ne ya kama ni, na tabbatar wa kaina da cewar aiki ne babba a kaina, in har ya tabbata Ado auren nan zai yi tun daga wannan lokacin na soma sa ido akan lokutan fitanshi da kuma na dawowanshi tare da tunanin a wane lokacin yake zuwa wurin nata?

Zuciyata ta soma raya min cewar watakila daga yin sallar Isha’i ne tunda kullum bai dawowa gida bayan Isha in sai yayi zama na awa daya da minti goma sha biyar ko kuma da minti talatin.

A farko ya ce min yana zaman yin karatu ne wurin Limamin Masallacin unguwar, na kuma yarda. To yanzu kam na gane ba gaskiya ba ne, loba ni kawai yake yi, tadin shi yake zuwa.

Don haka rannan da zai fita Masallaci don sallar Isha’i; na ce mishi in an yi sallar Isha’i ka shigo gida don ban yarda da wannan munafukar makarantar taka ba, babu kowa a ciki sai kai kadai.

In ban da munafurci wane karatu ne ba za ayi shi ido na ganin ido ba, kullum sai dare yayi? Zuba min ido yayi yana kallona, a hankali ya bude baki ya ce min, makarantar tawa ce kuma munafuka yau Humaira? Nayi maza na ce mishi, eh, kana nema ne ka maida ni wata yarinya ‘yar kankanuwa.

Ka shanya ni a gida da sunan kana wurin Mallam alhalin kai kana can ne wurin tadin ka.

Ya ce, To shi kenan, ke ba yarinya kankanuwa ba ce, tunda kin yi kokari kin gano ni, to amma ai kuma ina jin ban taba yi miki karyar zan zauna da ke ke kadai ba, balle ki ce na boye miki.

A kullum kuma ina kokarin gaya miki cewar ni din namiji ne, shi kuma namiji ai kin san mijin mata hudu ne.

Kalaman nashi suka kara fusata ni, na soma sake mishi maganganu masu zati, musamman ma da na tuna eh, gaskiya ne shi din kullum a cikin alkawarin zai nuna min shi namiji ne, wato dama abin da yake nufi kenan?

Ba mu gama fita daga cikin wannan maganar ba tunda bai yarda zai daina zaman waje bayan Sallar Isha’i ba, sai kawai na dauki wayar Ado ina bincike a cikinta.

Text din yammata na soma gani, yayi maza ya fige wayar daga hannuna, nan take kuma ya kama yi min fada “”Kina fa nemana da fitina, kina nema sai kin takura min, yaya ne haka? Ya ya za ki tsananta min bincike bayan kin san an hana? Na soma yi mishi kuka saboda a wannan lokacin na riga na gane gaskiya ne yana neman aure?

Kenan gaskiya ne duk wahalar gonar nan da yayi da juriya da taimakon da nayi tayi mishi kudin a dawainiyar aurenshi zasu tafi?

Hannu biyu na dora a kaina nayi kuka har na gaji bai yarda ya sake shigowa dakin ba.

Washegari tun safe na tattara na bar mishi wurin, na koma dakin Gogori Ayalle nayi kwanciyata, zuwanshi uku in dawo wurinmu zai zauna muyi magana ta gaskiya, ni da shi ban yarda ba.

Har kusan yamma ban koma ba, anyi sallar La’asar ya shigo ya zo ya same ni, “Zo muje kiyi mana girkin abinda zanmu ci mana Humaira, na ce mishi kaje ka kawo yar gidan Mallam Korau ta girka maka.

Ya zuba min ido yana kallona cikin natsuwa, kiyi hakuri mana Humairah na ba ki hakuri na kara ina ce ni duk girman laifin da ki ka yi min hakuri daya ki ke bani in ce na hakura?

Na daga ido na kalle shi, kayi min wulakanci akan wata ‘yar iska? Yayi murmushi, “To ai na ce kiyi hakuri.” Ban tanka mishi ba sai ya juya ya fita.

Bai wani dade ba ya sake juyowa zai dawo, sai kawai naji Ruwaila tana ce mishi, ai kai kuma yau taka ta same ka tunda ka yarda ka bata mata rai, baka da šauran zama lafiya tsugune ta kare maka tunda ka bari aka yi fushi da kai.

A zuciyata na ce, kai wasu da rashin zuciya suke, tanfar dai bata gane irin sharewar da Ado yayi mata ba kusan kowane lokacin a cikin nemanshi da magana take.

Sai kawai naji ya ce mata, eh ai ta isa ne kin san ni din a hannunta nake, wata matar don ta yi wa miji fushi ai shirme tayi, tunda wanda tayi domin shin ba zai kula ba, balle ya bi baya.

Abin da kawai ya fada kenan, tayi matukar fusata da maganar tashi ta shiga sakin maganganu, ai kai ma ba haka kawai ka ke wannan zaryar ba ka ke ganin a kanta zaka iya batawa da kowa, ai rashin imani suke gwadawa tunda abin da ba a sha suke wankewa suna ba ku.

Maimakon yayi shiru tunda ya ji inda ta maida zancen nata, sai naji ya ce, ni na yafe mata, ba kuma rashin Imani aka yi min ba, da bakina sai in yi yanda ake so tunda ai nawa ne.

A mafi yawancin lokaci, nakan hakura da abubuwa masu yawa sosai inyi ta hakuri dasu saboda sanin da nayi cewar gaba daya matan gidan nan idonsu a bude yake akan al’amarin zamanmu ni da mijina.

Tunda Ado da Ruwaila suka yi wadannan maganganun gashi dai a zahiri wàsa suka yi irin na matar wa da kuma kanin miji, amma can cikin al amarin nasu sun kulle wani abu Ruwaila dai sai nanata maganar yafi a kirga.

Ana cikin haka, rannan na amsa kiran da Goggo Ayalle tayi min da sassafe, Ado bai fita ba ya jira in je in dawo don ya ji kiran akan menene?

Me ta ce miki? Yayi min tambayar tare da bina da kallo zuwa in da na zauna.

A hankali cikin natsuwa don kar ya dauki maganar da tsanani nace mishi kan maganar girkin ne.

Wani lalataccen ashar ya wulwulo ya antakawa Ruwailah, zan sa kafar wando daya da matar nan, wai ita tana son takurá min ne ko?

Nayi maza na fara bashi hakuri, ba fa ita ba ce. Da sauri ya ce ke matsa can, ke me ki ka sani? To ka gani ma dai kawai ni kam kayi hakuri na gayawa Goggo zan karbi girkin.

Da sauri ya tambaye ni mene? Za ki karbi girki ki ka ce musu? To kje ki karba ta kuma kisan yadda zaki yi dasu ni babu ruwana.

Tunda na gane kin fi jin tsoronsu da ni, kin kuma fi jin maganarsu da tawa.

Kuka na soma yi mishi sosai da sosai, to ya ya zan yi? Iyayenmu ne in naji maganarsu ko naji tsoronsu nayi hakan ne saboda girma da darajarka a wurina ba zan iya jayaiya da su.

Goggo ta ce, “Ci gaba da kin shiga girkin nawa zai zamo sanadin da kowa zai iya warewa ya ce baya ciki, in nayi haka kuma ban kyauta musu ba, don wannan girkin nasu yana cikin alamomin hadin kan gidansu.

Gaba daya suna ci daga tukunya guda, to sai kuma in ce mata ba zan yi ba?

Shiru Ado yayi cikin nazari da tunani kafin jimawa can ya dago ido ya kalle ni ba za ki iya aikin ba Humaira ba, kuma zasu taya ki ba don wannan haduwar da ki ke ganin suna yi kowanne suna taya ‘yan group din su ne.

Ke kuma ba kya cikin na kowa, sannan cefanen gidan nan ba karamin abu ba ne, ni kuma a halin yanzu ba zan iya ba saboda a halin da nake ciki kina gani sarai kullum kara maneji nake yi.

Ban yi miki bayani ba ne, don,ba ki yi magana ba, ba ki kuma nuna min damuwar ki ba duk wani abin da nake kashewa yanzu ba nawa ba ne, rancensu nayi.

Hannu biyu na dora a kaina na ce rance? Bai kula ni ba sai yaci gaba, to zan rinka cin bashi ne ina yin cefanen da bai zaa min wajibi ba?

In suka yi hakuri ma ai nima ba zan bar abin haka kawai ba, tunda duk masu cin abincin nawa ne ba sai an ce min in yi ba.

Ni kam kuka na rinka yi saboda na tsani bashi, sai nake tankar shi ne karshen fitina tunda naji Mallam mai babban Allo yana yawan neman yin magana kan Hadisan da suka yi mini da gaggauta biyanshi in har mutu ya cika ana bin shi, kai ni kam ban son bashi.

Kukan da nake tayi yasa Ado tsayawa yi min bayani Ke bashin fa ba wanda za’a matsa min ba ne wurin Haruna naje na karba wannan abokin nawa da nace miki tare muka yi Secondary School.

Yana gamawa shi ayayenshi suka yi mishi aure, har na ce miki yanzu matanshi uku da ‘ya’ya birjik yana kuma ta hidimarshi.

Duk da Ado yasha bani labarin abokinshi Haruna na rowan bargo ban ji dadin bashin da yace min yaje ya karba a wurinshi ba da nayi tunani sosai ma sai na gane har ‘yan atamfofin Nicharm din da ya sayo min guda biyu yazo min dasu a dinke, wai in dan sabunta a kudin da ya rantan ya sayo min su.

Ke ba fa ni kadai ne nake cin bashi ba mutanen da yawa ana bin su bashin da bai dadi shi ne wanda ka karba bayan kasan baka da hanyar biya, ni kuwa ina da shi.

Damuwar da ya gani a tare da ni ce tasa shi yi min wannan bayanin, tabbacin da Ado ya bani na bashi da halin da zai yi cefanen gidan nan in girkin yazo kaina yayi matukar tayar min da hankali.

Duk da ni din ba mai yawan yin addu’a ba ce, sai na dukufa nayi ta karanta wata addu’a da mai babban allo ya bani ita, ya ce min addu’ar Nana Aisha’ ce (R.A) a kowanne lokaci.

Wani lokaci ma in na zauna ina yi na rinka kenan sai Ado ya gaji da ganina a zaune ya sure ya dora a katifa yana dariyar cewar da nayi mishi mai babban allo ya ce min mai yawan karanta addu’ar ba ya talauci.

<< Mijin Ta Ce 31Mijin Ta Ce 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×