Skip to content
Part 34 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Tun daga nesa dai na hango buhun shinkafar da Ado ya kawo a kwance a kasa, ga kwandon tumatur, attaruhu, albasa da tattasai, ga galan din man gyada da ledar maggi da su kori da sauran kayan hadin da ya san ina amfani da su.

Ina dosar wurin naji matan gidan suna Shewa suna fadin “Lalle yau za’ayi sha’ani shinkafa? Matar so zata yi girki, Ruwaila kuwa sai cewa tayi mutanen birni ne yaushe za su je suna taba dawa? Ai sai mu.

Nayi kamar ban ji su ba, na gaishe su suka amsa na wuce naje na kawar dá buhun naja shi na jingine shi, na kama sharan wurin na share shi tas na kwashe tokar da take murhu.

Naje na debo itace na kawo wurin, ban ankara ba sai kawai naga gaba daya sun sulale sun watse sun barni ni kadai a wurin ko wanda zan yi wa tambaya in wani abu ya daure min kai babu.

Na leka tukwanen da zan yi amfani da su babu wanda aka wanke gaba daya kayan wanke-wanken yana tare a bakin rijiya, randunan da ake tara Ruwan girkin ma babu komai a ciki.

Don haka na tafi wurin Ruwailah tunda ita ce ta riga kowa karbana a gidan sannan kusancin da ke tsakanina da ita ma yafi yawa.

Cikin natsuwa na kalle ta na ce mata babu ruwa a randunan kuma ina so ki hada min itacen murhun don wutar ta kama sosai.

Sai kawai naga ta zuba min ido tana kallona cikin wani yanayi “dama kin mike kin yi aikinki tunda kema ba taimakon wasu kike yi ba.

Ai ba zai yiwu kema ki ce sai an taimake ki ba, in zaman jikin miji ne babu mijin da baya so á zauna mishi sai dai in bai samu ba ya hakura.

Don babu wata matar da mijinta ba ya sonta, tunda duk daya muke amfanin da ki ke yi wa mijinki shi nake yiwa nawa mijin, shi ko wace mace ma take yi wa nata kin gane?

Na ce mata eh, na juya na tafi, na nufi bakin rijiya tana fadin au, tafiya ki ka yi tun ban gama yi miki bayanin ba? Ban sake sauraronta ba.

Na dauki guga na jefa cikin rijiya da nufin debo ruwan da zan yi aikin da shi, sai ga Ado ya shigo wurin, abin da ban taba ganin yayi ba tun zuwanmu, tun da yasan wurin zaman mata ne.

“Ke me ki ke yi a wurin nan? tambayar da ya soma yi min kenan, ban iya amsawa ba saboda in na ce zan y1 magana zan yi kuka.

Ajiye gugar ki tashi a wurin, na ci gaba da jawo gugar, tunda na riga na cikota da ruwa ga nauyi. Ajiyeta kuma yana nufin ta koma cikin rijiyar.

Ganin da yayi ban ajiyeta ba ya sanya shi Rarasowa wurin yasa hannu ya karbeta daga gare ni, wannan rijiyar da ba a ganin cikinta ne za ki zo kina jan ruwa a ciki?”

Ya dangwarar da gugan a kasa ruwan da na jawo din ya kife, ya wuce ya fita. Ina tsaye ina tunanin abinda zan yi sai naji wata a cikin matan da şuke dakin Ruwailah tana ce mata wai fa matan so zasu yi girki a gidan nan maza sai zirga-zirga’suke yi.

Ta ce, ai zai ga tsiya ai sai dai ya cire rigarshi yayi mata girkin, haba ina amfanin namiji ya susuce ya zama ‘Mijin Ta Ce’ kamar Ado ya laface akan wannan yarinyar ya záma sai yadda tayi dashi, wai har yana cewa suna aka tara.

To da me tafi wata? Gabadaya suka kwashe da dariya suna fadin to shi ba tashin ya sani ba.

Taja wani mummunan tsaki da ke kara baiyanar da tsananin bacin ranta, ai ni da su ne a gidan nan zasu ga tsiya, zan ga yadda za’ayi suji dadin zaman, sai dai in zasu tattara su koma in da suka fito, ko da yake dai can din ma koro su ita Hajjyar tayi.

Tana tayin maganganun bata san Ado ya shigo ba, yaran Almajirai ya kirawo ya kirawo guda biyu wadanda dama sanannu ne a gidan Hamza da Bala, ya nuna musu tarin wanke-wanken da aka tara ba ce musu su wanke su kuma debi ruwa su cika randuna suka ce mishi to.

Daga muryar da yayi ya kira Furera, shi ya fahimtar da Ruwailah mai rantsuwar Ado zai ga tsiyar da zata yi mishi tasan yana wurin nan da nan tayi tsit.

Furera ta fito tana gyara daurin dan kwalinta tana murmushi lafiya yau maigidan yake yawo a wurin da mata suke girki? Ko ba ya koshi ne?”

Bai saki fuska ba balle ya rama mata wasan da ta yi mishi, sai ya ce mata taimakona nake so kiyi ki hadawa Humaira wuta ki kuma tsaya ki kula da girkin ko ba za ki iya ba?

Da sauri ta ce, to me zai hana? Ya ce to na gode. Ya juya zai tafi tayi maza ta sake ce mishi in dama ba kana so ta zauna a wurin don ta ga aikin ba ne ai da tayi tafiyarta ma  za’ayi.

Ya sake cewa to na gode, ya wuce ya tafi, na tsaya zan taya Furerah aikin da ta runguma da hannu bibiyu zata yi, sai kawai ta kalle ni cikin murmushi ta ce ke tafi ki je wurin mijinki kin ji?

Kiran da Ado ya yi wa Furera ya danka mata aikina a hannunta ba karamin abu ba ne wurin Ruwailah, don a zahiri ne kawai suke abokan juna na kut-da-kut, amma a boye abokan adawa ne.

Don ita Furerah ma ita ce uwar dakin amaryar Ruwaila ban da haka kuma ita din bata yi zaton zai iya yin hakan ba, don ganin ba sasansu daya da Furare ba.

Sannan ita Ruwailah ban da zumuncin ita matar wanshi ne na sasa daya akwai kuma zumunci na jini, don haka ta dauka dole dai ita zai nema.

Ina tare da Ado a daki da daddare nayi mishi kwalliya da sabuwar rigar baccin da ya zo min da ita daga Zaria, sai kamshi nake yi, yayin da shi kuma yake zaune daga shi sai dogon wandonshi na Track Suit.

Yana tashe da laptob din shi Intenet ya shiga yana bincike kan noma irin na zamani, ni kuma ina kwance a gefenshi nayi filo da gefen cinyarshi ina kallon abin da yake yi.

Yana kuma kara yi min bayani kan abin da na tambaye shi, sai kawai Furera tayi sallama a bakin kofa, ya amsa ya ce mata shigo mana. Nayi maza na tashi na zauna na jawo dankwali ina daure kaina.

Suka gama gaisawa, sauran kayannan ne na kawo, ga shinkafa mudu zai kai bakwai nayi amfani da mudu ashirin da biyar ne ga… ya katse ta, je ki da su Furerah da rana sai ki girkawa yaran wurinki, tayi ta godiya ta tashi ta tafi.

Tana fita ya ture laptop din nashi gefe yasa hannu biyu ya jawo ni jikinshi, kin san yau kuwa yau wata uku daidai tun da ki ka yi rashin lafiyar nan.”

Dan langabe kai na yi nuna yanayin zolaya na ce mishi bana lissafi, ya dan rage fara’ar shi ya ce to ni ina yi wani lokaci kuma nakan tambayi kaina, to ko dai nayi kuskuren ne.

Kamar yadda Goggo ta ce, nayin da na bari aka yi miki wankin cikin? Nayi maza nace mishi baka yi ba ban yi ba? Na ce mishi eh, baka yi ba, lokaci ne kawai bai yi ba,

Kankame ni yayi da iyakacin karfinshi yana tambayata, to yaushe ne lokacin? Kin kuwa san haihuwar da aka yi wa Malla Haruna ta shekaranjiya, ita ce ta sha bakwai?

Na ce, uhun! To sai me? ya zuba min ido yana kallona, ina sonki Humaira, ko ace dandani-haukaci ki ka yi min ko ace wani abu aka wanke aba ni nasha, ni na gode da hannuma ma in aka bani zan iya kaiwa bakina insha kin ji?

Ban tanka mishi ba, kiri-kiri a gidan nan Ruwailah tayi dalilin da aka radawa Ado sunan Mijin Ta Ce ai shi din ta ce ne wai bai da katabus sai yanda aka yi dashi.

Ado da nake ganinshi jarumi in na ce jarumi ina nufin akan komai ma shi din jarumin ne. wajen neman halal din shi wajen tsayuwa kan ra’ayinshi a gida ne kuwa ko a waje musamman ace ra’ayin nashi akan gidanshi ne.

Tunda nasan kullum nai ce nake bin umarninshi nake kuma barin ra’ayina in koma nashi don mu zauna lafiya amma wai shi ne Mijin Ta Ce, da zuciyata tayi kunci na tsunduma cikin tunani mai tsanani, saboda bakin cikin kira min jarumin mijina

MJIN-TA CE. Da tunani ya tsananta gare ni, sai na tunano Babana, na tuna marasa mutuncin unguwarmu har nuna mana gidanmu da dan yatsa suke yi suna fadin wai gidan mijin tace kenan, nace to ko dai shima ba mijin tacen ba ne sharri kawai ta kama ni a dalilin tausayin shi da yafi matukar kamani.

A hankali cikin zuciyata na shiga fita da addu’ar ina ma dai ya huce ya daina fushi dani, don wata rana in samu damar zuwa gabanshi don in roke shi gafara kan laifin da nayi mishi?

Tunda Furera ta karbe ni hidimar girkin abincin gida sai take ta kokarin sanya ni cikin al’amuranta misali haihuwa ko baki da suka dangance ta zata gaya min ta ce in gayawa maigida in ya bar ni sai muje tare don mu saba da jama’a tunda shi mutum shi ne babban arziki in bai bari ba babu damuwa in ce mata to.

Rannan kanwarta da suke ciki daya ta haihu tazo har dakina ta gaya min nace mata wanan kam dani za’aje tayi murna sosai.

Ado yana dawowa na bashi labari, ya ce to in lokacin ya matso sai ki tuna min, na ce to. In ka samu sarari sai ka saya min rigar yanmata in bata don mace aka haifa.

Ya ce min to, yana fita kuwa sai ga shi yazo min da riga mai kyau na kai mata tayi ta murna.

Tun ana jibi suna na tuna mishi ya ce to, ina ta murna nima zan fita unguwa tare da matan gida abinda ban taba yi ba ana gobe sunan ma na tuna mishi bai yi magana ba.

Washegarin suna ina gama aikina nayi wanka na zauna nayi shafa na gyara jikina, yayi tsaf sai kamshi nake yi na dako sabbin-under wears dina na Sanya tunda su kam ban taba rashinsu ba.

Duk rashin kudin Ado ba taba fashin sayen under wears rigunan bacci da man shafawa ba, ko turare.

Ina tashe da atanfata dana ciro don daurawa, cikin zuciyata ina tunanin Ado, tunda ya fita da safe bai dawo ba, gashi har rana ta fito, mutan gida kuma duk sunyi shirin tafiya baya nan, zuciyata ta raya min in har aka ce in fito ba dawo ba, tafiyata zan yi tunda ya san da maganar sanda na gaya mishin, kuma ba musu yayi ba.

Ina cikin wannan tunanin sa gashi ya shigo rike da leda mai dauke da robar yourgout da kuma fura a ciki.

Ungo dama in na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi, ko za kayi hakuri ne kawu duk sun riga sun gama shiri, ni kadai suke jira ka kuma san matan gidannan kara ce dasu, in hidimar mutum daya ta tashi sai kaga duk an dunguma an rufa mishi baya.

Ya ce, eh ai kirki ne da su, na ce eh, sai kawai naji ya ce min, amma ba da wadannan sabbin under wears din za ki ba ko? Wadannan ai kin san don kaina na saye su me yasa za ki bude su ba na nan?

Na daga ido na kalle shi ya bata rai sosai ji kuma irin kamshin da kike yi a haka ki ke shirin tafiya gidan sunan? Wannan ma ai rainin hankali ne cikin natsuwa da sanyin murya na ce kayi hakuri ka barni in tafi na yau, tunda nasa mata rai, in yaso na gobe ka hana ni.”

Ya ce, a haka a kamshin da kike yi? Ai alhaki ma sai yayi miki yawa, gara kawai ki sake wankan, na ce to. Ina cewa to din ya matso jikina, to zaki yi wanka mara dalili ne. Humaira bayan kin yi shafan nan mai kyau ai bari ki ga hikimar da za’ayi ai gara kawai a yi mai dalili sai kiyi kawai gabadaya kan nan ma kowa ya gama shirinshi maimakon kije kiyi ta jiransu.

Babu halin in ce zan yi musu dashi kan bukatar tashi sai ya ce kan tafiyar zan sabawa umarnin da yayi min, saboda haka nayi hanzarin sallama mishi kaina ban tsaya ja mishi rai ‘ba, don nima yayi saurin sallamata.

Sai dai abin takaicin shi ne, ina shiga hannun Ado na mance da komai, ya sanya ni ciki wani hali da ya kidimar dani, ya hanani tunani balle jin wani motsi.

Ban sake tunawa da komai ba balle in tuna a cikin sauri nake don kar in yarda in biye mishi, sai bayan da na ganshi kwance a gefena kokarin ne na tuna abin da ke gabana.

Zunbur nayi na mike cikin sauri na mufi bandaki nayi wanka da ruwan sanyi na zo ina shiri hankalina a tashe saboda shirun da gidan yayi min yayi yawa da sauri.

Na sanya kayana ba tare da na tsaya shafa ba na fita naje don in gani ko sun gaman suna jiraa nawa babu kowa a gidan gaba daya sasan babu kowa sai yar gidan Fureran budurwa Hasiya.

Na ce ke Hasiya tafiya suka yi basu gaya min ba? Ta ce sun gaya miki baki ji ba ne? Na ce sun gaya min wa ya gaya min? Ta ce ni ta aika sau biyu ina yi miki magana ba ki ba.

Na dawo daki raina a bace gululun bakin ciki sai yawo yake yi tsakanin wuyana da makogorona, na dawo daki har lokacin Ado yana nan a yanda na bar shi barci ma yake shirin yi bakin ciki da takaicinshi suka kama ni har ban san lokacin da na soma kuka ba.

Cikin sauri ya bude ido yana tambayata menene? Ban kula shi ba, balle in tsaya yi mishi magana ba ki da lafiya ne? Ban kula shi ba, menene ya same ki? Na ki yin magana har ya gaji ya dawo kan hanya sunyi gajin hakuri ne.

Haka suka tafi suka bar ki? Ban amsa ba yayi maza ya mike bari in yi wanka in zo in kai ki ke da kike da babur ma menene abin bacin rai a ciki?

Nayi shiri Ado ma ya shirya muka fita ya burga mashin na hau bayan shi muka kama hanya a yanda duk suke fada kauyen Tukunya kusa kwarai take da Dabai. Muna tafiya naga bamu je da wuri yanda nayi zato ba, na ce mishi har yanzu ba mu zo Tukunyar ba?

Yayi maza ya ce min Tukunya dama ki ka ce zamu? Nayi maza na ce, to da ina ka ji na ce? Ya ce Randa na ce, a’a ban da Tukunya akwai wani kauyen ma Randa ne a nan kusa? Ya ce min eh, na ce to ai Tukunya na ce maka ya ce, to ai Tukunya na ce maka ya ce to ai babu damuwa bari mu gaida wadannan sai muje Tukunyar na ce to.

Ya tsaida mashin din shi gaban wani gida mai tsananin tsabta ga ko’ina an dabe shi an kuma share shi gwanin sha’awa.

<< Mijin Ta Ce 33Mijin Ta Ce 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×