Skip to content
Part 35 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Wani farin Dattijo mai wadatar farin gashi a fuskarshi yana zaune kan farin buzunshi a gindin wata katuwar bishiya mai yawan gaske.

Yana rike da carbinshi a hannunshi yana ja, cikin natsuwa Ado ya kalle ni ya ce min, “Gidan Kawo’ kenan wannan da ki ke hange shi ne Baba Sambo.

Sanda mahaifina yake raye bai da wani Aminin da ya fi shi, kin kuma san an ce mu sadar da zumuncin iyayenmu ko bayan ba sa raye ko? Nayi maza na ce eh, haka ne.

Muka karasa gaban dattijon nan cikin yanayi na girmawa yana gane Ado ya gyara zamanshi cikin fara’a da murmushi, ya amsa sallamar da Adon yayi mishi, ya kuma shiga yi mana sannu da zuwa, Ado yana amsawa.

Can kusa dashi yaje ya tsuguna yayin da ni kuma na tsuguna daga baya, amma yana hangena tafin hannunshi ya dora akan Ado tanfar wani dan yaro a hakan yake yi mishi magana, da alamar dai akwai shakuwa da kulawa a tsakaninsu.

Wannan ita ce iyalintaka? Ya dago ido yana kallona cikin nuna alamar jin dadi, sannu kin ji yarinya, sannu Aishatu, sannu kin ji sannunku, Ubangiji yayi muku albarka, ya kuma jikan Mallam Sulaimanu.”

Ado yayi maza ya ce, “Amin Baba.” Ya ce, “Kar ayi wasa da yi mishi addu’a, amfanin barin da a duniya kenan, ka kuma san kai kadai ya bari.” Ado ya ce, haka ne Baba.

Muka dan yi hira, Ado ya ciro kudi ya bashi, ban san nawa ne ba, yayi tasa mishi albarka har nima yazo ya burga mashin din shi muka hau muka tafi.

Wata hanya ya biyo da ni da bangane ba, wasu gine-gine nake gani da ban taba ganinsu ba, nan kuma ina ne? nayi mishi tambayar cikin natsuwa ya ce min “Dabai mana Humaira, ban biyo da ke ta inda ki ka saba bi ba ne.”

Tuni na shagala ina kallon gidaje da layuka har da su kwalta a shimfide cikin unguwanni, ga rijiyoyin burtsatse a ko ina, na ce kai Kawu, Dabai din nan ma fa ba wani kauye ba ne, ai ban san haka take ba sai yau.

Dubi gidaje har da tunkunan ruwansu, ga titina ga fanfunan burtsatse birjik, ga lantarki har mutane da yawa sun sanya a gidajensu, mas’alar dai kawai ba ku da babbar kasuwa.

Wani irin lallausan murmushi Ado ya saki cikin natsuwa naji ya ce min, sannu. A hankali dai in nayi sa’a Dabai zata yi miki halin nata ta dabaibaye min ke, ta maida ke ‘yar gida har ki mance garinku.

Kin ga shi kenan sai muyi zamanmu mun huta da kowa sai in huta jin ana cewa an yi mafarkin anje gida an ga an canza kofar gidan ko anje gida anga Sa’adatu balle kuma aje ana mafarkin anje gida Baba yayi kora da sanda.

Tsuke fuska nayi na ce, ai ni ba zan taba mancewa da garinmu ba, kuma ma ai ta nan wurin ne in da ba kauyen ba ne ta can wurinku ku kauye ne?

Kan mu karasa gida muka yi fada da Ado, don haka nan da na ganshi ya kafe mashin din a kofar gida na ce ba zan sauko daga kai ba sai ya juya ya maida ni Tukunya kamar yanda yayi alkawarin kai ni.

Ya soma rarrashi yaga alamar ba zan yarda ba, sai kawai naji ya ce min, kine dai so ne kawai ki nuna wa mutanen da suke zaune gindin bishiyoyin can cewar eh da gaske ne kin fi karfina.

Kin ga sai suma su yarda da magánar da matan cikin gida suke yadawa cewar ni din Mijin Ta Ce ne, ban sani ba ko Ado ya gane irin dukan da wannan kalmar ke yi wa zuciyata ne in an fade ta yasa ya gaya min hakan, don a firgice na sauko daga kan mashin din na shige cikin gida, naje na tsaye bakin kofa ina jiran yazo ya bude min in shiga.

Sai dai a gidan ban yarda kun zauna  lafiya ba, saboda na riga na gaji da yanda yake tsattsare ni yana kokarin hana ni mu’amallah da kowa da kowa, har da mutanen da nake tare dasu, wadanda matan yan uwanshi ne.

Muna cikin wannan rikicin, Ado ya samu aikin koyarwa a Makarantar Secondaryn yammata ta DANJA’, shi kenan sai murnan samun aiki yasa muka shirya.

A farkon samun aikin murna nayi ba kadan ba, saboda ni da shi addu’a sosai muka yi akan aikin, saboda irin bayanin da ya rinka yi min cewar, aikin koyarwar shi ne aikin da yafi so a wannan lokacin, saboda irin alherin da ke cikinshi.

Za ka koyar da yara mutanen da suke sune za su girma, su zama al’uma ta gama shi a wurinshi babu wani aiki da yafi koyarwa dadi, da kuma muhimmanci aikin ne mai lokaci ga kuma. Lokuta daban-daban na hutu wanda zaka iya aiwatar da wasu l’amuran naka da basu shafi Makaranta ba a lokacin.

Koda dai a wannan lokacin da muke ciki, ba wani muhimmanci hukuma da wasu Jama’ar gari suke baiwa Malami ba, shi a wurinshi darajar Malami ba sai wani ya ce gata ba, tunda Ubangiji da kansa ya girmama shi.

Irin wadannan kalaman nashi ne suka kara cusa min son aikin nashi, amma yana farawa ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba na gane ba sakandaren ‘yanmata ba ne ta kamata a tura min mijin mawa ba.

Don ba a je ko ina ba na soma gani wasikun yanmata da hotunansu a cikin Jakarshi ga waya akai-akai, ga text na kalamai masu dadi irin ma wadanda ban taba jin su ba.

A farkon al’aarin yana rarrashina ya gaya min kalamai masu dadi da yake rage min bacin raina, amma daga baya sai kawai ya daku wai shi ba zai dauwama kan rarashi da ban baki kan matsala guda daya ba.

Don haka hanya mafi sauki ta neman zaman lafiya kawai in daina yi mishi bincike in daina taba mishi jakarshi ta zuwa aiki da kuna wayarshi in ban taba su ba ai ba zan ga abinda ke ciki ba.

Kan ka ce me ye wannan kuma sai ya fito da wata ka’ida ta cewar, wai shi din tafiya tana yi mishi yawa, kullum sai yaje Danja yayi aiki ya dawo Dabai.

Don haka ba zai juri hakan ba, wahala tana yi mishi yawa, maimakon ace kullum yana zirga-zirga kan hanya da safe da yamma zai maida tafiyar tashi ta za a ranar Litinin da safe.

Ba zai dawo ranar ba sai ya kwana ya bada darussanshi na ranar kala ta in an tashi sai ya dawo ya kwana a gida, sai washegari aba ya koma da safe ya kwana ranar ya wayi gari a can Alhamis in ba shi da wani darasi na ranar Juma’a to ranar zai dawo.

Ba zai sake komawa ba sai ranar Litinin in kuma yana da shi Juma’a to sai in yi hakuri sai Juma’ar zai dawo.

A farkon bayanin nashi banga wani abin damuwa a ciki ba don yayi min bayani sosai kan wahalar zirga-zirga a hanya amma yana fara aiwatar da abin a haka mutanen gida suka gane shi kenan sai aka soma kace-nace.

Ya samu wata a can kenan ya ajiye, nan da nan hirar gidan ta koma hirar mazan da ke ajiye mata a waje, wato matan banza.

Cabdi! Ai gara mana irin namu mazan da ke shigo mana da abokan zamanmu cikin gida su ci daga abinda muke ci, shi din kuma gashi nan a tsakaninmu ya dai ishemu muna kuma kallonshi.

Amma matan banza hidimar da ake yi musu ai ba irin ta nmatar gida ba ce, ga kuma ciwace-ciwacen nan na zamani.”

A wannan lokacin in na ce bana cikin tashin hankali to nayi wa kaina karya, gashi dai a wannan lokacin nayi matukar wadatuwa da abubuwan rayuwa, komai da Ado yasan zan bukata ko zai yi min amfani kawo min yake yi.

Albashinshi na farko ma da aka fara bashi saboda anyi mishi biyan na wata uku ne gabadaya kamar yadda all’adar aikin Gwammati take, kananan atamfofi masu saukin kudi masu kyau turmi goma ya saya min.

Ya bayar duka aka dinke min, dinki kuma mai kyau ga takalma da gyalulluka da under wears, a wannan lokacin kuma tuni ya canza min tsarin abincina, a kowane lokaci ban rabuwa da madarar fulani da shi yasan inda yake zuwa ya samo ta.

Ba na rabuwa da naman kaji, ba na rabuwa da kayayyakin itace dangin kankana, gwanda, inabi, lemo, ayaba, in zai kawo kumá masu kyau zai kawo min. gashi kua ya tsare mnin girkin gidan.

Kullum ya zagayo kaina ko baya nan Furerah zata yi don zai sa a kawo mata kudin cefanen ya ce tasa a sayo wanda ta mafi son hakan.

Jikina yayi matukar yin kyau saboda yana samun nau’o’in abincin da ya dace ya samu, amma na kasa yin kiba in maida jikina ya zama kamar asalin yadda nake kafin zuwan mu.

Sai ma kara ramewa nake yi saboda kullum a cikin fargaba nake. Ni kuma gashi duk da wadatar da Ado ya samu ban koyi adana ko kwabo a dakina ba, hamsin-hamsin din da su. Baba suke bani yana ganin sun taru zai sa hannu ya kwashe in ma bai diba ba in dai ana zaune kalau ni da kaina ma zan ce mishi ga su.

Sai a lokacin da raina ya soma baci ne zan rinka ganin ina ma adana abina nake yi da nayi amfani dasu na tafi gidanmu.

Rannan abin ya ishe ni, bakin cikin Ado yana nema ya maidani wata iri Alhamis ya zo bai dawo ba na zuba ido ban gan shi ba cikin zuciyata na ce to watakila sai Juma’a kenan.

Ya yi sammakon dawowa don wani lokaci yakan yi hakan sai kawai naga Bala da sassafe ya kawo min cefane wai a gaya min sai gobe zai dawo ya tsaya daurin auren Jalo.

A zuciyata na ce tafdijam! Wato ni babu abin da nasan darajarshi irin ciki, don haka cefane na gashi nan an kawo min babu fashi shi sai sanda yaga dama zai taho.

A cikin gida kuwa rannan maganar da su Ruwailah suka wuni suna yi kenan, amma akan wai ban da ni ake yin hirar ba tunda ni da ‘yan dakinta ma ba wata doguwar magana ke hada mu ba.

Don ko nayi musu a lalace suke amsa min, ko a yanzu da rashin Ado ke sani zaman cikin gidan wani lokaci da sauran mutanen gidan muke hira, amma yan dakinta ta hana su kula ni.

‘Ko da yake dai nima ko da baya nan din na tsare dokarshi ta shiga dakin mutane, bana shiga dakin kowa. Ina jin ta a gindin bishiya tana fadin au, to shi namiji don ka tsare shi ka hana shi yin aure ai ba wata birgewa ba ce.

In har baka hana shi ganin na banza ya ce yana so ba, ta tsirtar da yawu nuna alamar kyaa, ta ce ni a yadda nake da kyaman nan ai ba zan iya zama da manemin mata ba.

To me zan yi da shi? Ai komai zai bani gara ya bar shi ya tsare min mutuncin kanshi kawai yafi min, ni nayi sana’ata in nemi abin da zan rufawa kana asiri dashi.

Sannan abin tsiyar shi ne, sma kara kullewa a can tana karakwace maka shi. In a farko kana ganinshi şau uku a sat sai a koma biyu sai a koma daya wani satin ma sai ka ji shiru.

Ai gara a hada mu mu hudu a gida kishiya dai kowacce tazo Ubangiji zai bani hikima da basirar zama da ita, in ta kunso wani abin tsiyarta ma a wayi gari ya koma mata kanta ko ya kare tsakaninsu can musu ita da wanda ya kawo ta, aifa kam- aifa kam abin da yan amshin nata suke fadi kenan.

Rannan da daddare Gambo ce na runtsa ta karya na yi wa kaina. Washegari tun safe Ado ya dawo ya yi sa’a kuma a wurina yazo ya same ni ban riga na rufe na tati wurin hira ba.

Karbar da nayi mishi bata wani ba shi sha’awa ba baki da lafiya ne? na kalle shi da gefen ido na tambaye shi me ka gani? Yanayin ki ne na ganshi wani iri.

Na ce ta dauro ne ka ganshi a haka ka kuma san daurowa take yi a daure AIkali. Ya ce haka ne, to ga leda nan nazo da shi juye abin da ke ciki don ba zai juri zafi ba.

Na mike kamar zan juye abin da ke ledar na wuce na tafi tsakar gida abin ban sake dawowa dakin ba. A tsakar gidan kuma sai tambayeta ake yi ana fara’a ashe maigidan ya dawo?

In ce eh sai ace kai madallah, hannunshi da zuwa. Ina nan wurin a. zaune sai ga Ado ya shigo suka gaisa da matan duka ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min zo mana Hunmaira, na ce to.

Na tashi na bi bayan shi don komai yaya ba zan iya wulakanta mmijina a gaban wani ko wasu ba.

Muna shiga ya kalle ni ya daga ido ya kalli agogo sannan ya sake kallona ya ce min, kin ga wannan abinda ki ka yi min na farko kin yi min kuma na karshe kin gane? In dawo daga wani wuri baki karbe ni ba baki yi mi abida ya dace kiyi min ba.

Ki tafi ki bar ni awa guda minti sittin ina zaman Jiranki, na yau din ya zama na karshe kar ki sake. Na ce idan sake din me zai faru? Ko me zaka yi?

Ya ce to ki sake mana ba ga ki ba gani? Na juya da nufin sake fita, yayi maza ya kamo ni ya murde min hannu, nayi karfi hali ban yi irin ihun da nakan yi ba alamar na riga na saba da wannan wahalar.

Kar ki neme ai da fitina Humaira, ba na so. Yana ta nanata kalmar alamar bai son fadan da ya gane ina so muyi. A zuciyata na ce ya san ba shi da gaskiya.

In wani abu nayi miki a laifi ki gaya min bai zama min komai ba in ba ki hakuri ke kin san na saba hakan bani da wannan girman kan me nayi miki?

Kullum naje aiki na dawo sai kin yi min sanadin bacin rai?

Saboda kawai bana gida kina shiga cikin matan da suke cusa miki ra’ayin da ba naki ba suna koya miki abinda bai dace ba, wanda ban taba zaton zaki yi haka ba, ke da ki ka girma a gida irin naku ki ka yi karatun boko da na addini har yanzu ma kina yi.

Amma wai wadannan matan ne suke koya miki abinda za ki yi wa mijinki.

<< Mijin Ta Ce 34Mijin Ta Ce 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×