Nan da nan na mike na canza zanin gadon da ke shinfide kan katifar na shimfida, wankakke, gogagge, na fesa freshner mai sanyin kamshi na kuma kunna turaren tsinke a bayan gida na jawo dan kofan tsaki gina na koma dakina na zauna ina jiran lokacin Sallar magrib tayi.
Cikin zuciyata dai bani da wata matsala illa jiran in gabatar da sallolina insha tea in kwanta tunda nasan ni da ganin Ado watakila sai gobe da yamma ko kuma ma ranar Allhamis.
Na idar da Sallar Isha’i na kulle kofata na dawo ina hada tea da zan sha kafin in kwanta tunda ban yi girki ba ban kuma aika an karbo min abincin gida ba sai naji ana taba kofa nayi maza naje na bude don ganin ko waye?
Sai naga Ado na kauce daga kofar ya shiga nayi mishi sannu da zuwa ya amsa da har kin rufe kofar ne? Na ce mishi eh, yana cire kayan jikinshi alamar wanka yake shirin yi yana tambaya ta me kika girka ne?
Cikin natsuwa na ce mishi ban yi girki ba saboda ban san zaka dawo ba, in ba zan dawo ba ba za ki girka abin da za ki ci ba? Kin ga irin ramar da ki ka yi kuwa? Ya maida rigarshi ya fita.
Tunda Ado ya dawo ranar Talata da yamma bai sake tafiya Danja ba yana gida bai kuma fita ko’ina in ba sallama aka yi dashi ba.
Zuwa nayi na gayawa Princepla da yake akwai fahinta a tsakanin na ce mishi akwai matsala a gidana, ya ce to in je ya bani wannan satin sai na roki wani Malami ya taimaka min da darussan nawa don kar yara su cutu.
Ya dago idanuwanshi ya kalle ni doon a kwance yake sanda yake maganar. Sai dai kuma gashi na dawon tun ba aje ko’ina ba har na gundure ki kin gaji dani ban tanka mishi ba don nasan me yake nufi. Tun daga wannan lokacin mu’amallar Gambo da
Ado tayi matukar karuwa, na kuwa gane hakan ne daga yawan kiranta da nake ganin yanayi, ba zai yiwu sai rikici ya taso min a gida in rinka kiranta tana kwantar min da fitinar ba.
Abinda ya gaya min kenan rannan da na ji su suna magana ban kula shi ba, na dai san kawai yana ganin girmanta da darajarta yana kuma girmamata da iyakacin gaskiyar shi. A wannan lokacin ne na gane gaba daya matan gidan bakin su daya ne haduwa suke yi suyi maganganinsu kan abinda ya shafe ni ni da Ado.
Illa iyaka kawai ita Furerah ta ki yarda ta daina karbar girkina tana yi saboda tana matukar amfana dashi. A zahiri kuma tana nuna ita babu ruwanta ni tata ce saboda alherin da nake yawan yi wa ya’yanta.
Don haka sai na hada su gabadaya nayi musu jumiah guda daya dukansu ina girmama su bana kuma jin zafinsu tunda na gane damuwarsu bata wuce ta kulawar da mijina yake da ni ba.
Ado bai daina zuwa Danja ya kwana ba na kuma cire raina a kan hakan randa yake gida ma mafi yawancin lokaci yakan raba dare ne biyu yana waje bai dawo bakuma damu ba duk da ‘yan maganganun da ake yi in an ganni, nasan yana wurin lambunshi yana lura da yanda ake ban ruwanshi.
Wani lokaci ya dawo ya samu ina zaman jiranshi, wani lokaci yazo ya samu nayi bacci, randa yaga zai tashen ya tashe ni in yi mishi abinda yake so in yi mishi.
Randa yaga zai hakura ya bar ni in yi barcina, shi yasa ma mafi yawancin lokaci in naji yana tayi min kashedin kar fa kiyi bacci ki jira ni ce mishi nake yi gara dai in ka dawo ka tashen, don ba zan iya wannan dogon hirar ba a wannan duhun ni kadai.
Yawan mitar da nake yi wa Ado akan duhu ya sanya shi yana fara diban labun nashi ya kashe kudi mai yawa ya sanya wutar lantarki a gidan gabadaya.
Ya kuma gyara katangar gidan yayi mata kofa daya, yayi wa zauren gidan kyakkyawan gyara, soronshi ya zauna daidai maimakon da da yake barazanar zubowa, amma bai yi musu gwaninta ba.
Su Ruwaila wai cewa suke yi aikin banza, tun lantarki yana sabo a Dabai ba a sanya mana shi ba sai yanzu da ya zama gidan kowa da shi, kuma dubi hanyoyin nan da muke samu muna shiga makwabta hankali a kwance wai don fitina yasa an toshe.
Yanzu babu halin ka fita sai ka nemi izini, kai zama da fitinannen mutu dai wuya ne dashi, sai kayi hakuri.
Ni kam tunda na gane mijina na kuma gane halinshi na gane yana sona yana girmama min mahaifiyata yana tattalin yan kannena sai na kudurawa kaina yin hakuri da shi da duk wani abin da ya shafe shi.
Ban ganin yayi wani abu in ce mishi don me? balle in je ina tambayarshi dalilin da yasa yayi har akai ga halin da zan ce ban yarda ba na daina.
Shi kuma in ya ga nayi mishi ba daidai ba ya kama zai yi fada tunda shi baya iya ganin an yi bai tanka ba sai in ba da hakuri ko da kuwa ina sane nayi don ya ji in da dadi.
Don haka yan uwanshi başa bata min rai komai suka yi min ban tankawa saboda na san fitinata da su ba za ta saman mishi farin ciki da kwanciyar hankali ba ni kuma abinda son ganin ya samu kenan.
Rannan na dauki wayar Ado na kira Gambo don mu gaisa, tunda zaman jiran fitowarshi daga wanka nake yi muna cikin hira Gambor take bani labarin anyi ruwan saman farko a Bauchi jiya.
Na yi kabbara cikin farin ciki tare da addu’ar Ubangiji ya sanya damunar ta zamo mai albarka, ta ce min to amin. Na ce shi kenan Gambo za ku dan samu saukin zafin nan da ake ta fama dashi ko ina.
Don mu ma nan din zafin ne, Gambo tayi murmushi ta ce to mu tun yaushe kuma muka huta da zafi? Nayi maza na ce, Gambo bana ba ayi zafin ba ne sosai a Bauchi? Ta sake wani murmushin kafin ta ce min.
“Hala ba ki san mijinki ya aikowa Umar mai shagon dinkishi kudi ba? Wai azo a sanyawa mai sunanshi (A.C), ai mu tun nan muka daina jin zafi.
Na ce bai gaya min ba Gambo, cikin zuciyata kuwa tunawa nayi da ranar da naji hirar Ado da Sa’adatu yana tambayarta mai sunanshi, tana bashi labarin ai tunda zafin nan yazo baya baccin dare kwana yake yana kuka wai shi nan ma baya son zafi.
Ado yana jin anyi ruwan saman farko a Bauchi ya fitar da hatsinshi da ya noma gaba daya ya kai kasuwa ya sayar, sai dan kadan ya bari. Dama tunda aka yi girbi ya fidda Zakka tun a gona na baiwa makwabta da ‘yan uwa nasu hakkin.
Ya tattara saura ya adana da niyyar sai damuna ta gabato zai kai hatsinshi kasuwa, don yayi amfani da kudin wajen yin noman wannan damunar.
Ado yana ta shirye-shiryen noma bana na wannan damunar da muke addu’ar zuwanta lafiya nima ina nawa shirye-shiryen na rubuta jarrabawata ta gama Secondary a lokacin nan kuwa ina da ciki wata hudu.
Sai dai babu wanda ya sani don babu alamar shi ga ni kuma lafiyata kalau yan matsalolin da nake dasu ba wasu masu yawa ba ne.
A wannan lokacin babu abin da nake so irin Ado ya yarda ya barni in je gida in ga iyayena da yan uwana. Amma sai in yi tayi mishi maganar yana jina baya ma amsawa sai in ya ji na matsa mishi da zancen sai ya ce min io wai me za ki jie ki yiwo ne?
Da Aliya ta dawo daga aikin Hajji sun zo gidan nan ita da Atika da Sa’a har da Baba karami suka kawo miki tsarabarki suka yi miki bakunta ta kwana uku. A wannan dan tsukakken dakin naki balle ko in ce tsarabarki kike son karbowa.
Gambo kuwa kina jin maganarta a waya mai babban allo in yana son ganinki shi da matanshi sun san in da kike tunda yazo Hajiya ‘yar dubu ma tazo to wa yai saura? Kullum yayi min irin wannan maganar bata rai nake yi in daure fuskata in ce mishi su kadai ne yan uwana da dangina?
Babana fa? Sai in hado da Mama don in yi mishi kara tunda na gane har yanzu yana sonta yana kuma girmamata, sauran ‘yan uwana fa? Sai ya ce to ba yanzu ba sai ya duba yaga lokacin da ya dace.
Rannan muna tare da Ado a dakinmu bayani yake yi min kan kudin hatsinshi da ya noma bara wanda sai à wannan lokacin ya sayar da kuma na lambunshi da ya sayar shima ya adana yana harin damunar bana da gonakin da yake shirin nomawa.
Bana duk gonakina na gado zan noma Humairah ki taya ni da addu’a, nayi murmushi nayi mishi addu’o’in tun a gabanshi wanda kuma dama ka’ida ne sai dai in ban yi sallah ba.
Haka kawai ma na kan shi da irin kokarin shi da wahalarshi in roki Ubangiji ya sanya mishi albarka mai yawa a ciki.
Muna cikin hirar ya daga ido ya kalle ni, amma anya Humairah ba zan kure hakùrinki, in sa ki gundura da halayena da dabi’una ba kuwa? Nayi kamar ban ji shi ba, saboda tunda muka yi fadan da nace halayenshi da dabiu’unshi ne suka gunduren ya maida maganar ta żama ka idar neman magana a wurinshi.
Ban taba ganin mutum nmai son kai irina ba Humairah alherin da na samu a noman banan kawai ya ishe ni in yi miki ginin da za ki zauna a ciki ki yalwata.
Amma ban yi ba, wai so nake in juya kudin in sake maida su gona wai da a irin nawa son kan so nake duk abin da ya fito daga gona in maida shi gonar a aikin da nake yi in yi tattalin da zan rinka yi mana hidimominmu.
Ban kula zancen nashi ba, wucewa kawai nayi na kwanta a bayanshi.
A wannan noman da Ado ya yi na wannan damunar ne na gane talaka dai ba karamar wahala yake sha ba a kasar nan duk abin da zai yi karfin shi kadai yake yi mishi bai da wani mataimaki ba dai na Ubangijinshi ba.
An riga an sani sarai babu yadda za’ayi a hada noman wanda yayi amfani da karfi yayi da na wanda yayi amfani da hanyoyin noma irin na zamani wanda bai yiwuwa sai ana da wani abu a hannu.
Amma an ki a yi wa manomanmu na asali taimakon da ya dace da su wanda za su sau so bunkasa aikin nomansu sai kullum ayi ta bayani a baki a gidajen Radiyo da Jaridu, amma wasu yan tsirarun mutane suke tsare komai su amfana da shi a birane ba tare da ya kai ga manoman na asali ba.
Kullum irin korafi da maganganun da nake yi wa Ado kenan a duk lokacin da ya zauna yayi min bayanin mai dadin ji kan aikin da ake yi mishi a gonakin nashi in ganshi kuma garau babu wata alama ta wahalar da zata tayar da hankali a tare da shi.
Hannu babu bororo balle kanta, balle aje ga jallin yin fason kafa ga ciwon baya da na kugu,gashi kuma ya tabbatar min da cewar noman nashi na bana zai nika na bara sau goma ko a fiye da haka.
Sannan a hakan duk dan wani dama da ya samu na zama zaka gan shi yana tashe da laptop din shi bincike yake kara yi kan hanyoyin noma irin na zamani a kasashe daban-dabarn da suka ci gaba, wai ya kara koyo da sanin sabbin dabarun noma don ya kara samun sauki.
A wannan damunar ta bana sau biyu ina kaiwa gonakin Ado ziyara sabanin na bara da na ki zuwa saboda aikin ya wahalar min da mijina da yawa ya fitar min dashi daga hayyacinshi, don ma shi din namiji ne.
A duk lokacin da na kaiwa gonakin nan ziyara kuwa tsayawa nake yi in yi ta kallon yabanya, yanda ta mike fetal ta tafi tayi nisa cikin jeji ban iya hango karshenta. Gashi ta yi kore shar.
Wani irin dadi ne yake kama ni wani irin sanyi ya sauka cikin zuciyata, in ji ba ni da wani sauran nauyi ko kunci da ya addabi zuciyata in ji babu abin da yafi dacewa da ni irin in kara tsarkake Ubangijina.
In kara kadaita shi da bauta, in kara jin tsoronshi saboda ko daga Kallon ayyukanshi na zahiri a kawai wadanda su ba sai mai hankali da ura ne kawai zai gansu ba.
Misali halittar sama da kasa canzawar yanayi daga rani zuwa damuna, yadda dan Adam ke shuka kwaya guda daya ya fitar da daruruwa kasa guda daya ruwa iri daya ya fitar da nau’o’in tsirrai daban-daban ya ishe mu zamowa abin lura.
Bin bayan Ado nayi can cikin gonar saboda hangenshi da nake yi yana ciccire kananan ciyayinda ke son fitowa da tsirran da bai son gani don in gaya mishi tunanin da ke damun zuciyata.
A duk lokacin da na kalli yanayin sama ko yanayin shuka a lokacin da tayi shar a jeji in ji ko shima tashi zuciyar tana raya mishi irin wadannan al’ amuran, Ban san yadda aka yi ba, ban san ina na tsunduma wajen aikin ciccire mishi kananan ciyayin ba sai da na ji shi yana cewa “Ke Humaira ba fa abin da na kawo ki gonar nan kiyi kenan ba.
Kawo ki kawai nayi ki ganta kiji dadi ki taya ni yi mata addu’a na rokon Ubangiji ya sanya mata albarka mai yawa.” Na ce mishi amin Kawu.
Taso ni yayi a gaba muka fito daga cikin gonar muka dawo in da ya ajiye babur dinshi da muka zo akai, cikin natsuwa ya kalle ni bayan ya burga mashin din.
“Hau mu tafi mana.” Na kalle shi na ce, “uh’uh yi gaba zan tako da kafa ba zan sake hawanshi kayi ta tsalle da ni a kan kunya ba.”
Cikin natsuwa da nuna kulawa ya ce “Ba kunyaa ba ce Humairah, hanyar ce babu kyan, na ce eh to jeka. Ya sauka daga kan mashin din ya shiga tura shi, ni kuma ina takawa da kafa muna tafiyar mu muna hirarmu mai dadi.
Mafi yawancin hirar kuma kan abin da ya shafe mu ne, haihuwata da ta matso, gonarshi da kuma aikinshi, kullum hirarmu bata wuce wadannan abubuwan guda uku.
Ranar Juma’a sha tara ga watan tara cikin damuna sosai a lokacin da manoma suke matukar taka tsan-tsan da dan abinda yai saura a hannunsu saboda tuni karfinsu ya koma gona. Ita kuma gonar bata fara bayar da komai ba, na haifi diyata ta mace lafiyayya, kana ganinta kasan ubanta manomi ne, taci ta koshi.
Ado ya shigo gida cikin sauri a dalilin ya kwana a dakin zauren gidanne saboda zuwan da Sa’adatu tayi. Ina jin shi yana dariya yana tambayar Goggo Ayalle.
Goggo wai yau ma an yi haihuwa a gidan nan ko? Tana taya shi dariyar tana fadin “An kara wata haihuwar. In ce ko dukansu ne suke shirin haihuwar ne Goggo.”
Goggo tayi dariya ta ce, to wa yasan musu ne? Wacece kuma ta haihu yau? Goggo ta ce a’a ashe baka ji mai haihuwar ba, ai Aisha ce.”
Dib naji Ado yayi, yayi shiru na lokaci mai tsawo yana sauraron bayanin da take yi, jarumar yarinya ita kadai ta haihu sai zuwa Kanwarta tayi ta tashe ni, hatta tsofaffin matannan da suka haihu basu haihu su kadai ba, sai da suka taso mu muka zo muka kwana muna zaune da su amma ita.