Skip to content
Part 37 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ado ya katse ta ya ce to tsofaffin mata Goggo ba sun san zafi da mutuncin kansu ba, amma ita fa tana da hankali ne? Goggo ta rufe Ado da fada.

Wanne irin magania ne wannan? Yarinya tayi kokari ba za ka yaba mata ba, bata hutar da kai biyan kudin asibitin nan na zamani mai tsada ba?

To ni dai ban gode mata ba Goggo in tayi ne don in yaba mata to ban yaba ba, ya juya ya bar ta tana tayi mishi fada ina jin shi yana kwalawa Sa’adatu kira, tayi maza ta fita ta tafi wurinshi.

Aka gama min komai aka dawo dani dakin Goggo Ayalle wai a nan zan yi jegon, ina zama Sa’adatu ta sake shigowa rike da kwano, ga dabinon da Gambo ta ce kar ki manta dashi.

Na kalle ta nayi murmushi na ce ai kuwa in ban da kin tuna da na manta na karba ina ci ita kuma sai kallon yarinya take yi tana murmushin jin dadi.

Ran Yaya ya baci, wai kin zauna kin haihu a gida baki ga nima fadan da yayi min ba akan wai ban je na gaya mishi ba. Na ce ai nima kukan yarinyar kawai naji, in kai mishi ita ya ganta?

Na ce ke Sa’a, kin san nan gidan komai muka yi za a iya cewa ba muyi daidai ba, ta ce haka ne. Naci dabinon sosai nasha ruwa kamar yadda Gambon ta ce a gaya min, na gyara nayi kwanciyata.

Kan ka ce meye wannan? Sai na ji ni garau kamar ba ni ce nayi wannan uban wahalar ba.

Jimawa can Ado ya shigo dakin wuri ya nema ya zauna suna gaisawa da Goggo cikin girmamawa irin wannan alheri ya same mu, ka tashi kana fada?

Ado ya ce kiyi hakuri Goggo raina ne ya baci ana jaruntaka da wahala ne Goggo?

Ba za ta fada a san bata da lafiya ba? Ta ce to tunda Ubangiji ya raba su lafiya ai sai muyi mishi godiya, yayi murmushi ya ce haka ne.

Goggo taci gaba da yi mishi bayani ita haihuwa ai duk ta wuce yadda ake maganarta, gida da asibitin duk daya ne. Ubangiji ke yin ikonsa ayi ta lafiya.

Yayi maza ya sake cewa haka ne Goggo, mun gode mishi. Ta tashi ta dauko yarinyar nan wai zata ba shi ita kamar yadda ta saba kawo mishi sauran yaran da aka haifa kafin ita a gidan.

Ya ce “A’a Goggo, ai zan ganta a hankali.” Ta ce ai haba? Ai na dauka ba za ka yi kunya ba, ta maida ita ta ajiye ta fita saboda kiran da Baba ya yi mata.

Yayi maza ya dawo bakin gadon yasa hannu ya dauko ta ya kare mata kallo ya tofe ta da addu’o’I ya maida ita yana kallona cikin murmushi.

Wannan yarinyar ta fito a jikinki Humairah ba ki samu matsala ba ko? Ban kula shi ba, ya dan yi waiwaye don kar yayi maganar da wani zai ji shi ganin ba kowa yasa shi matso da bakinshi kunnena ya fadi abinda yake nufin fadin.

Kallonshi kawai nayi ba tare da na ce mishi komai ba, hidima sosai Ado yayi sai dai yaja ya tsaya kan bai yarda ayi taron suna ba, tunda sauran haihuwar ma duka ragunan suna kawai ya bayar aka yi yanka sai sunan da babu taro mai yawa.

Don haka nima ba zai yarda da gayya daga wani wuri ba, Sa’adatun da tazo ita kadai ta isa.

Ni kam kuka nayi tayi, Goggo ma ta ce akan me kuwa zaka yi haka? Wadannan yan uwa nata ka ce ba za su zo sunan ‘yarsu ba?

Ya ce to ‘yarsu tazo cikin tsululun damina Goggo ba sai suyi hakuri ba, manomi yana hidima mai tsanani ne da damuna? Goggo tayi dariya ta ce, wannan shi ne iya shege.

Ni kam da hankalina ya tashi da hana yan uwana zuwa suna da Ado yayi sai da naji yana yi wa Gambota bayanin cewar shi din ya riga ya shirya zuwana gida da zarar mun yada wanka, don haka kar ayi wahalar zuwan.

Yadda Ado ya bada ragon suna guda daya a duk haihuwar gidan da aka yi haka nan a wannan sunan ma rago guda daya ya bayar da safe ranar suna Baba Tanimu ya fadi sunan da ya sanyawa yarinyar Umamatu.

Gabadaya kowa a gidan mamakin sunan yake yi, wasu ma tambaya suke yi ina Baba ya samo wannan sunan kuma? Sai da Baban ya shigo Goggo tayi mishi tambayar naji yana yi mata bayani.

Sunan jikar Manzon Rahama ne, Goggo tayi maza ta ce, (S.A.W), rannan da naje wajen wa’azi naji ana tarihinta na ce to in aka yi wa Adamu haihuwar ya mace sunan da zan sanya kenan.

Goggo tana dariyar farin ciki ta ce ai kuwa dai Mallam tunda suna ne mai daraja, ya ce haba don ma ba ki ji tarihin nata ba.”

Duk da nanata haihuwar tsululun damuna da Ado yayi tayi, hidima sosai yayi min. Mutane da yawa kuma sun zo, mafi yawanci matan abokanshi ne da kuma yan uwanshi, nawa yan uwanne kawai ba su zo ba, shi ne abin da ya dan rage min jin dadi.

Amma duk da haka na yiwa sunan kwalliya ta burgewa da ban sha’awa. Lesuna masu tsada guda biyu da atamfofi super suma guda biyu gami da shaddojin gezna na asali suma guda biyu, dukkansu a dinke.

Dinki kuma mai ban sha’awa ya kawo min gami da takalma da jakakkunansu designers, ki zabi wadanda za ki yi amfani da su.

Na daga ido na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi ya ya zaka kwashi kudi masu yawa haka ka saya min irin wadannan kayan? Bai kula ni ba sai kawai yasa hannu a aljihunshi ya ciro wata sarka da yan kunne mai kyau English Gold.

Ya miko min ki shirya in ga kwalliyar taki kafin in fita don Kaduna nake son tafiya kan maganar nan da nayi miki. Kar dai ki fasa yin addu’a ko kina zaune na gayawa Gambo ma ta kara yi min addu’a na ce mishi to.

Sa’adatu ta shigo itama tayi kwalliya mai kyau atamfar super ce a jikinta itama Adon ne ya bata don tayi fitar suna.

Nayi kwalliya sosai na kuma yi matukar yin kyau, shaddar na fara sakawa saboda dinkinta yayi matukar daukan hankalina.

Nayi dauri mai kyau na sanya sarka da yankunne, ga agogo da zobe tunda nazo Dabai ban taba kwalliya irin na ranar ba, mutanen da ban basu taba sanina cikin kwalliyar da ta dace da ni, tunda shima Ado kananan zannuwa yake saya min sai ko yau da in a suna.

Ina cikin gyaran daurina Goggo Ayalle sai kallona take yi tana fadin iko sai Ubangiji sai ga Sa’ adatu ta shigo Anti wai kizo ki nuna mishi in da links din shi suke na kwatanta mata ta tafi ta dawo.

To kije mana kawai ki bashi tunda ya ce sauri yake yi zai tafi, nabi maganar ta Goggo na nufi dakin nawa da na kwana bakwai ban shige shi ba, komai a kammale sai kanshi yake yi a tsakar dakin.

Na samu Ado a tsaye shima yayi kwalliya rigar da ke jikin nashi sabuwa ce sai kamshi take yi.

Yana ganina ya rage fara’ arshi kai ke kam ko wayo baki dashi can zan biyo ki dakin Goggo in ga kwalliyar sunan naki?

Ya sake kallona cikin wani yanayi na sakin fuska da murmushi alamar ya gamsu da abin da ya gani, ya ce wannan ita ce asalin Humairar da Gambo ta bani ba wacce na kawo na ajiye a wannan dan tsukakken dakin ba.

Nayi murmushi don in rama mishi wayan nashi ya ji dadi, sai na ce mishi ba fa Gambo ce ta baka Humaira ba, Baba da Mama ne suka baka ita.

Ya sake fadada murmushin shi tare da jawo ni jikinshi har dankwalin nawa ya fadi a kasa, kankame ni sosai yayi a jikinshi kafin ya ce mini Gambo ce ta ba ni ke Aisha, ita ce tayi dalilin da ki ka sallama min kanki.

Ita ce ta biyo mu Dabai da umarnin da take bayarwa ne na samu nayi sa’ar samun zaman lafiya a gidana don haka ni a wurina ita ce ta ba ni ke.

Muka yi sallama ya kama hanya ya tafi nima na dawo dakin Goggon in da ake sha’anin suna,

Goggo sai bina da kallo take yi tana kokarin ganin idona, ko me take son gani oho?

Suna da kwana biyu Ado ya dawo yana dawowan yaje ya sayo wani katon rago ya kawo gida aka yanka yasa aka soya ya zuba shi a cikin kwalla wacce itama sayota yayi ya hada da katon din minti na malta sweet.

Da katon din cingam Bazooka 200 da goro dan takarda biyu da dabino mudu biyar da shadda yadi goma-goma, guda hudu da atamfofin super guda uku ya tashi Bala ya ce mishi yayi wa Sa’adatu rakiya zuwa gida gabadaya kayan ya ce a kaiwa Baba a gaya mishi shaddojin guda hudu, shi daya Baba Yahya daya, Mallam Liman daya, Mallam Harisu ma daya, atamfofi kuwa Mama daya Gambota daya, Zubaida ma daya, sauran kuwa akai mishi a gaya mishi na haifi Umamatu ga kayan suna nan a rabawa Jama’a.

Sannan itama Sa’adatu yayi mata tata tsarabar.

Kwanan Bala uku a can maimakon daya ko biyun da Adon ya ce mishi ya yi ya kuma dawo da shatara ta arziki.

Jego mai kyan nayi mai kuma dadin gaske na murje nayi gwanin sha’awa in ban da ina lissafin kwana kin tafiya ta gida ma ina jin da nafi haka morewa jegon nawa.

Rannan Ado ya dawo gida daga Danja a lokacin nan kuwa kwanana arba’in ne har da uku.

Yana shigowa dakin ya nemi wuri a bakin gadon da nake zaune ya kama kallon yarinyar da ke ta faman bacci.

Ni wannan yarinyar da wa tayi kama ne? Na yi murmushi na ce wa yasan mata, wasu suce da ni, yayi maza ya galla min uban harara wadanda basu san ka ma iso ba ko?

Nayi shiru naci gaba da abin da nake yi, to wai ni ba kin yi arba’ in bane me kuma kike yi a naan dakin? Nayi murmushi na ce to ai ban gama wankan ba Goggo ta ce sai na kara.

Wai wata biyu ba kwana daya zan yi zamu bar wankan yau ne gobe mu tafi gida. Ya tsuke fuska ya ce a’a ban yi miki wannan alkawarin ba, na dai ce in kin yi wata biyu za ku tafi amma ai ba daga nan dakin za ki tashi kiyi tafiyar ba.

Nayi maza na ce ban gane ba, ya ce to kar ki gane, kina nufin haka zan yi ta zama? An gama hakurin tsohon ciki an yi na zaman jego sai kuma in yi ta zama ina jiranki sai kin dawo daga tafiya?

Ki gayawa Goggo za ki koma dakinki yau sai muyi ko kwana bakwai ne tare in yaso rana ita yau ma kiyi tafiyarki, na sunkuyar da kaina kasa na ce ba zan iya ba.

Ya ce to shi kenan ni zan koma duk ranar da ki ka gama wanka ki ka koma dakin naki sai in zo muyi kwana bakwai tare kafin ki tafi, in kuma naga raina ya baci da yawa ma sai in fasa tafiyar taka gaba daya.

Da sauri na kalle shi “Me nayi maka?” Hawaye suka soma ganagarowa daga idanuna, saboda fargaba. Na matsa na matsu in je gida in ga Gambota da Babana dama sauran dangi baki daya.

To tun yaushe muke zaune ni da ke a haka Humaira? Sai kuma ace ba za ki tausaya min ba ai babu son kai a tsakanina da ke.

Goggo ta shigo ta same ni ina kuka ta soma salati ina dalilin wadannan hawaye da suke zuba, kai Ado me kayi mata? Ban yi mata komai ba Goggo wai babu hali ne kawai ta ce ga yadda za’ ayi in ce a’a.

Ai kuwa dai ba zai yiwu ba. Goggo ta soma yi min fada bakin cikin Ado ya kama ni don haka ma ban sake daga ido na kalle shi ba balle in san maganar da yake yi min. Kwana uku bayan nan ya sake baro Danja ya dawo gida ina ganinshi na tsuke fuskata, amma bai hana shi yin magana ba. Wurinki nazo saboda naje na yi wani sabon tunani…

<< Mijin Ta Ce 36Mijin Ta Ce 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×