Gari ya gama wayewa ne kawai a cikin gida ni da Ado muka ga gaba daya cewar jiya da daddare Ado da Goggo Ayalle sunyi kaca-kaca akan kawai ta gaya wa Humairah gaskiya.
In ban da ma ita Goggó ta nuna halin girma, bata tanka wa maganganun nashi ba watakila da dukan tsiya ya nada mata.
Baba Tanimu da kanshi a wannan lokacin salati yake yi, yana karawa, tare da kanbama al’amarin, sai fadi yake yi “Lalle al’amarin Adamu akan wannan yarinyar ya wuce yadda duk ake zato.”
Sai yada wannan maganar ake yi, Goggo Ayalle tana ji ta ki yarda ta dubi girman shekarunta ta gyara al’amarin, ni na yarda ta fadi gaskiyar abinda ya faru kar ta rufe komai, yafi min sauki kan ace wai Ado ya zage ta a kaina, wai har mą in ban da tayi shira da duka ya nada mata.
Cikin zuciyata ta ce, watakila ma dai dama itama Goggon dan kiris take jira da ni.
Tuni matan gida suka mike tsaye suna ta aikéwa ‘ya’ yan gidän mata da suke aure a wasu gidaje da labarin abin da suka ce wai ya faru.
Ita kuwa Goggo tayi kwanciyarta a daki ko kosan ranar bata fito tayi ba, wai ba za ta iya ba sai Ruwaila ce tazo ta dauki kullin ta soya, wai don kar abar shi ya lalace.
Ni kam ina kwance lamo akan gado, in ban da kuka babu abinda nake yi, ana cikin haka naga Ado ya shigo dakin, ko kallon inda Goggon take bai yi ba, ya ce min tashi Humairah tashi ki koma dakinki”.
Ban motsa daga yanayin kwanciyar tawa ba, ban ma so ya shigo in da nake ba, balle yazo yana yi min wata magana ba tare da ya kula da Goggo Ayalle me dakin ba, tashi mana.
Hannu biyu ya saka ya đauko ni ya saukar dani, alamar zai iya daukana ya fidda ni in ma ban yi hakan ba.
Na kalli in da Goggo ke kwance, na gaisheta idonta a rufe bata amsa ba, wai ita a dole bacci take yi.
Tasa ni a gaba yayi ya kai ni wurinmu, sai ki share hawayenki, kar in sake-ganin zubarsu, in ba so ki ke gaba daya ranmu ya baci ba, ka sani da baka yi mata magana ba. ‘
Shhhhhhh! Ya dora dan yatshinšhi a lebenshi ya fitar da sautin alanar kashedi na kar in sake furta mishi wannan maganar.
Sa kai yayi ya fita ya bar ni bayan yasan nayi wanka ya tasa ni a gaba sai da yaga nayi shafa na gyara jikina na sanya atamfata mai kyau na kuma shiga dakin dahuwarmu wanda na same shi a gyare tas, na kama aikin girka mana abincin da zamu ci.
Amma dai ni kam yi kawai nake yi, amma ni kadai nasan yadda zuciyata take ciki gace da tsoron abin da zai faru, duk da dai Adon yayi tayi min kashedin wai kar in tsorata, yana kallon duk abin da ake yi babu kuma abin da zai same ni.
Kan ka ce meye wannan? Matan gida suka hadu akan sai an kama ni an dana min duka ne zai sa in natsu in shiga hankalina, in daina kwasar maganar mutane ina gayawa mijina, ina bata tsakaninshi da ‘yan uwanshi.
Na shiga tsakaninshi da Hajiya Majadan ta hakura dashi ta bar min shi, to su ba zan shiga tsakaninsu da shi su hakura dashi su bar min shi ba, maganina kawai zasu yi.
A wannan lokacin na kai matuka wajen tsorata, ba wai dukan da zasu yi min din ne yafi tsorata ni ba, a’a! abin da zai faru tsakanin Ado da masu zuwa dukan nawa ne yafi zamo min abin tsoro, gashi kuma ya tattara komai ya dora laifinshi akan Ruwailah, duk da har zuwa yanzunnan babu wanda ya ji bakinta a ciki.
Baba Tanimu ne ya hana yunkurin dukan nawa da aka yi bisa dalilin da ya basu na cewar shi a matsayinshi na babba, yana gida bai kamata ya bari ayi abu na rashin hankali irin wannan ba.
Ado dai dan shi ne da dan uwanshi ya Haifa ya bar mishi, don haka ba zai yarda a raba shi da shi ba, tunda kuwa abin yazo kan iyalinshi, to ai gab yake da isowa kan shi, ko ma ya ce ya iso.
Don haka abar mishi lamarin kawai a hannunshi a ga abin da zai yi, gaba daya suka amsa haka ne Baba, haka ne.
Adamu ka ai bai taba sabawa da kowa ba, gabadaya dangi da ‘yan uwa kowa nashi ne, sai a wannan lokacin a sanadin matarshi yanzu tsakaninshi da Jafaru basa wata mu’amallah.
Shi da matar Jafaru kuwa Ruwaila basa ko ga maciji, da ya ba, ‘ya’yan Jafaru wani abu su anfana dashi gara ya baiwa na waje da bai hada komai da su ba, ai kuwa da magana suka ce kwarai Baba.
Duk wannan karin bayanin da na ji na Baban yana yi musu ne, a zuciyata na ce uh’uh hun! Baba ashe kaima “MIJIN-TA CE’ ne, wannan lokacin ne na kara yarda da maganar Ado.
Tun kafin yamma tayi kuwa sai naji Babà yana yi wa Ado magana, kan yaje ya duba wasu yanmata da suke wasu gidaje da ya gaya mishi su.
Ina jin Adon yana ce mishi ni da ba ni da daki Baba in naje naga yarinya aka ce an bani ita ina zan sa ta? A dai yi min hakuri kadan in samu in gina ‘yan dakuna ko da biyu ne.
Da daddare muna tare da shi nayi wanka nayi kwalliya da sabbin rigunan baccin da na tarar ya tara a dakin don in sa shi ya ji dadi, duk da nasan cikin bacin rai na wuni, amma nasan bai kai nashi ba, tunda sau biyu ina jin shi yana tarmbayata.
Anya da namiji yana da ranar da yake fita daga maraicin uwa kuwa Humaira? Na kalle shi cikin natsuwa aa ce mishi, “Yana fita mana.” Ya sake kallona ya ce anya?
Sanin yana cikin wani hali da kuwa jin maganar Baba Tanimu da na yi ya kara sa ni fahimtar Goggo Ayalle ta niyyar taimakon surukarta a kaina ne, yasa ta cusawa mijinta wasu maganganu.
Musamnan da yake rashin shirin Ado da Ruwailah ya haifar da koma bayan mu’mamallah tsakaninshi da Yaya Jafaru, tunda shi ma watakila tana gaya mishi wani abu yana dauka.
Gyara yarinyar nayi tsaf, hayan nayi mata wanka na gasa mata jiki don taji dumi tayi bacci mai nauyi tun akan ‘ya’yan da Gambota take haifa na koyi wannan.
Na kaita can gefen katifa ta karshe na kwantar da ita, na lullube ta na dawo na samu Ado a inda yake zaune, ya mike kafarshi guda daya ya kuma tsayar da guda daya ya tsaida gwiwan hannunshi akai don ya ji dadin dafe goshinshi da tafin hannun nashi.
Na matsa jikinshi na jingina kaina da kirjinshi nasa hannu ina cire mishi botin din da ke jikin T-shirt din shi. Ya zubo idanuwanshi akan fuskata cikin murya mai sanyi ya ce min a bacin ran abin da ‘yan uwana suka yi mi a gidan nan yau Humaira har za ki iya kulawa dani ki bani lokacinki?
Na kalle shi cikin natsuwa, sannu a hankali na sakar mishi lallausan murmushi, don in samu damar isar da sakon da nake son isarwa zuciyarshi, don kuwa na riga na yi niyyar rike mijina a hannuna.
Na sani babu abin da zai farantawa Mama rai irin ta ganni a gida babu auren Ado a kaina, ace mata yan uwanshi ma’ana dangin ubanshi ne suka yi nasarar raba ni da shi.
Yan uwanmu ne dukanmu kawu, ba ‘yan uwanka ba ne kai kadai, don sunyi mana wani abinda bai yi daidai ba ba zai hana ka samun lokacina ba, kai mijina ne.
Kai ne kuma mafi darajar mutane yanzua wurina, ina kuma sonka. Ban taba furtawa Ado irin wadannan kalaman ba, ban taba kallon idonshi na furta mishi wata kala ta nuna kauna ko mihimmancin a wurina haka ba.
Don haka maganar ta shige shi da kyau, abin da kuma dama nake son gani kenan.
Humaira! Ya fadi sunan cikin wani yanayi, yaja bakinshi yayi shiru, watakila saboda ya rasa Kalmar da zai gaya min, ina sonka kawu, na sake furta mishi kalmar.
Jikin Ado ya dauki rawa, tanfar dai wani irin tsimi aka bashi, nayi amfani da damar da na samu wajen yi mishi abinda ya dace in yi saboda in kara mallake abinda yake dama nawa ne.
Lokaci mai tsawo muka dauka ni dashi cikin wani irin yanayin da ba zai yiwu in kwatanta shi ba, sannu a hankali ya yi gyaran murya bayan ya samu natsuwar da ta dace da shi, a hankali ya soma yi min magana.
Zan sallame ki gobe in muna raye kije gida kiyi bakuntarki, duk da ba a haka naso kiyi tafiyar ba, ba kuma a goben na shirya ki tafin ba.
To amma kuma ba zan iya barinki a gidan a yanzu ba don ina bukatar kwanciyar hankali da zan yi wasu abubuwa kan abubuwan da suke faruwa.
Wani irin sanyi ya sauka cikin raina, ina fata za ki je ki dawo ba tare da kin gayawa Gambo wannan damuwar ba? Nayi maza na ce mishi ko, kadan, to gaya min in ji ke da kanki don in ji irin adalcin da za ki yi min, kwana nawa zaki yi?
Cikin zuciyata naji tanfar in ce mmshi to in yi wata biyu? Sai naji tsoro kar ya ce ya tasa, na ce mishi da dai kai da kanka ne ka gaya nin da yai.
Yana makale dani a jikinshi yayin da kuma nake bai wa yarinya nono, ya ce a’a ai ni nace ki fada sai dai a duk wani hukunci da za ki zartar a tsakanina da ke, na roke ki kar ki so kanki a kaina, komai za ki yi kiyi adalci a tsakaninmu.
Ki sani ba a yau ki ka fara ji na ina furta kaimar ina sonki ba, nayi hakan yafi a kirga. A yau kuwa ina so in kara jaddada miki ina sonki fiye da duk yadda kike tunani, gabadaya fatana da burina kuma bai wuce in samu wata dama da zan nuna miki halaccina ba, in dai nuna miki cewar ni din namiji ne.
Na ce to in yi ban san yadda aka yi ba, sai naji bakina ya ce mishi, kwana goma? Yayi murmushi alamar ya ji dadin hakan da na fada, za ki iya yin har sati biyu babu damuwa. Na ce mishi to na gode.
Gari na wayewa na soma shirye-shiryen yin tafiyar da Adon ya ce zan yi a ranar yayin da shi kuma ya ce min zai je wani wuri ya dawo, na ce mishi to.
Yana fita kuma ya toro min Bala, wai yazo in ba shi ayyukan da zai taimake ni da su, na kuma san har da tsaro yasa ya turo shi.
Yana taya ni aikin yana ta murna, Mallam ya ce zai yi min rakiya zuwa gidanmu, kai Innarku da kirki take Anti Humaira, na ce ko? Yayi ta rantsuwa, na ce ai na yarda Bala huta da rantsuwar taka haka.
Tunda Ado ya bar gida wajen shidan safe bai dawo ba, sai wajen sha biyun rana. Kan nan kuwa babu abinda ban yi ba har miyar da na saba yi mishi wacce yake tafiya da ita Danja tun bayan rikicin da muka yi kan zamanshi a can na soma yi ishi.
Kin gama dai ko? Na ce mishi eh, ya ce ina Umamatu? Na ce tana wurin Goggo Ayalle. Ya zuba min ido, nayi mishi bayani na gyarata naje na kai mata ita.
Ba zai yiwu ace zan dauki mataki akanta ba, suma mutanen gidan duk naje na gaishe su, amma ban yi musu maganar tafiyar ba, tunda baka gaya min ba.
To kin kyauta, bari in je in gaya musu, na ce to.
Ya fita bai dade ba ya dawo, kai Bala jeka kayi shiri kazo ka fitar da kayan nan ga motar da zaku yi tafiyar da ita can a waje, yayi maza ya fita sai washe baki yake yi.
Na zubo abinci naje na kai mishi na zauna yana ci shi kuma yana yi min bayani, na dan yi miki sayayyar tsaraba, sai dai bata da yawa tana bayan mota nayi godiya tare da yi mishi addu’a bayan na tabbatar mishi da cewar ta ishen.
Ya turo min wani dan kunshi wanda ya nade cikin leda, ya kuma yi rafin din soletep ya nadu sosai, nasa hannu na dauki kunshin ina dan jinjina shi a hannuna, bai kalle ni ba ya ce min kudi ne a ciki, ki kaiwa Baba ki ce mishi na roke shi ya biyawa Gambo kujera taje ta sauke faralinta.
Ban san san’da nayi jifa da sunkin kudin nan ba na kankame Ado don farin ciki, in kin je gida ki ce ina gaishe su na ce mishi to.
Sallama nayi da kowa a gidan cikin wani yanayi da bazan iya kwatanta farin cikina ba, ina fitowa daga wurin Ruwailah ina jin ta tana cewa yar hirarta ai muna nan da ita sai ya nuna mata cewar shi din da namiji ne.
Na shiga wurin Goggo Ayalle nayi mata sallama nasa hannu na dauki Umamatu na rungume a kafada maimakon in bari a biyo ni da ita saboda gaskiyar magana ita ce girma da kunyarta da nake ji sun yi matukar raguwa don ta riga ta bar ni na gane in da ta dosa.
A cikin motar ni da Ado ne a baya saboda wai zai sauka ne a mararrabar Danja ya tafi Danjan mu kuma sai mu nufi Kudan zuwa Makarfi, daga nan mu isa Kano mu dauki hanayr Bauchi, shi kuma Bala da direba suna gaba.
Kwalliya sosai Ado yayi yana rungume da yarinyar a cinyarshi, na kalle shi naji dadi mijina ai cikar halitta ne mai kuma tsabta ga kwarjini ga zati kalaman Baba Tanimu suka fado cikin raina na yaje ya duba wasu ‘yanmata.
A hankali cikin natsuwa na tambaye shi, amma ai ba za ka fara zuwa tadi a bayana ba ko? Bai juyo ya kaile ni ba murmushi yayi ba tare da ya daga shi daga kallon ‘yan yatsun hannun Umama ba a hankali ya ce min kina tsoro ne?
Na dan matsa kusa dashi na kwantar da kaina a gefen kafadarshi nayi mishi magana a hankali ba tsoro nake ji ba ina dai son mijina ne kawai, shiru yayi bai ce min komai ba.
A mararrabar Danja ya miko min yarinya na karbe ta ina shirin sallama dashi yasa hannu a kwibin shi wandonshi ya ciro kudin da ban san adadinşu ba, ya jawo jakata ya sanya a ciki ya zuge zib din ya fita, bayan yasa bannu ya dauki food flaks din miyarshi.
Suka yi sallama da direba da kuma Bala ya tsallaka in da zai hau mota mu ma muka mika muka kama tafiya.