“Ke da masu koya miki iya shege ba zan yi maganin ku, zan sa kafar wando daya daku.” Abinda ya ci gaba da gaya min kenan.
Bayan ya mika wa Mama kudin ita kuwa ta karbe su ta juya tayi tafiyarta, bata sake aiken nawa ba wai kar in je in sake kifar mata, can cikin zuciyata kuwa nasan ba sake saye zata yi ba.
A kullum irin kalaman da Babana kan furta kenan an koya min halin tsiya an yi min hudubar banza, an cusa min dabi’ar da ba za ta amfane ni ba, zai yi maganin mu alhalin shi din bai taba kama wani ko jin wani yana yi min daya daga cikin wadannan abubuwan da yake fada ba.
Illa iyaka dai abinda ita Mama take gaya mishi kenan. Kan hakan ne ma ni ko magana baya yi in dai wadda ta shafi muhimmin abu ne a gabana, sai ta nuna mishi ni ta hanyar yin zunde ta ce mishi dama dai kayi shiru tunda ga ‘yan baka nan a kusa.
Amma ta yarda yayi a gaban su Habiba, wadanda a wajenta wasa zaka ji suna fadin Babanmu ya ce, kaza ya ce kaza da maganar zata fito kuma ya zamo ba wacce ake son ji ba ne sai Maman ta ce mishi ai ta hana shi sakin bakin shi a gabana ya ki ne yasa ta zuba mishi ido.
Gidanmu gida ne da ake da karancin ‘ya’ya maza, ko a dakin Mama mai gadaran uwargidanci da ‘ya’ya maza guda uku ne mazan, mata kuma biyar.
To balle ita Innata da ko daya namijin bata dashi, sai mata guda hudu. To amma su mazan wadanda guda biyu sun ci ace sunyi nisa, Baba da kuma Ibrahim don sune a gaban su Anti Suwaiba da Anti Kaltume wadanda a lokacin aurensu Babana yayi komai don ya burge Mama, ya basu mazan da suke so su da uwarsu, alhalin shi ba sune zabin shi ba, ya kuma kashe makudan kudi wajen hidimar auren nasu a kayan daki da walima gami da ciyar da mutane.
Don shi dai ma mijin Anti Suwaiba ko kwakkwarar sana’a bai da ita, amma Mama taja ta tsaya sai shi tunda shi ne saurayi ai shima Baban namu lokacin da ya aure ta ba komai ke gare shi ba, in ban da ‘yan jamfofinshi guda biyu.
To amma duk da haka da taro ya watse sai Mama ta budi baki ta ce, wai wannan hidimar da Baba yayi bata yi rabin wacce yayi ba a hidimar auren Innata da yayi, har rayuka suka kai ga baci kan hakan.
Sannan a hakan a irin soyayyar da Mama ke yi wa ‘ya’yanta na ace su wasu ne a gan su ace sun burge a kalle su ace babu wasu sai su, Baba da Yaya Ibrahim sun ki karatu tana kallon su babu boko babu Arabi, sai gata a gabanta Ado yazo daga kauye yayi karatu har yau din kuma ba barin karatun ya yi ba.
Yana karatun yana kuma kasuwa ya tsunduma kan shi cikin al’amuran Babana tsundum, mutanen da suka san yanda lamurran gidan namu yake tafiya, fadi suke yi, “Ko da kokarin Mama wajen samun shigar kanin nata cikin lamurran Babana, to jaruntakarshi kuma ita ce kan gaba wajen saman mishi fada mai yawa.”
Duk wata aika da Babana zai yi to Ado ne, shi ne yake wanke mishi kayanshi, ya goge mishi su, daga zuwan Ado gidanmu ne Babana ya daina kaiwa masu wanki da guga kayanshi.
Shi ke wanke mishi mota, ya share kofar gida ya sare bishiyoyi in ganyensu ya yi yawa, wadannan ayyuka kuma ya kan yi su ya gama kafin fitowar rana, ba kuma sa shi ake yi ba, shi yake sa kanshi, gashi ya iya girmama Babana, dama duk wani mutumin da ya yi nufin girmamawa.
Daga haka ne Ado ya samu shiga wajen Babana, da ma Dattawan unguwarmu duka. Sannu a hankali-sannu a hankali sai ga Ado a shagunan Babana sai kuma Baban ya gwammace zaman adon a kan nasu Yaya Ibrahim da ma sauran yaran shagon.
Saboda jaruntakar shi ta wajen aiki da tsayuwa akan gaskiya, daga baya ne da ya lura ya gane ya riga ya samu shiga mai yawa, ya shiga kwashe mishi dukiya suna kashe-mu-raba shi da Mama.
Amma su su Yaya Ibrahim ta kyale su suna yawo kan Baburan da ta saya musu da kudinta da Babana ya yi magana kan hakan da tayi sai ta ce “Kai Alhaji kenan, kai baka saiwa yara ba bayan ga sa’o’insu nan da ma wadanda ba su kai su ba na abokanka wa su har motoci iyayensu suke sai musu.”
Ya ce, “Da suka tsaya suna yiwa kansu abin arziki ba? Suna bin umarnin da iyayensu suke ba su in da suma sun tsaya kan karatunsu kamar yanda wadancan din suka tsaya me zai hana in saya musu?
Ai taimakon kai ne da kullum ka baiwa yaro kudin motar zuwa Makaranta da na kasuwa, ai gara ka dunkule ka samar mishi abin hawa, to su wadannan basu tasa komai a gabansu ba sai la…”
Tayi maza ta katse shi ta hana shi karasawa, ta hanyar fadin “A’a, kar kayi musu baki gara kai, yauwa shi karatun boko ai ba shine kadai hanyar samun arzikin duniya ba, da shi kadai ne kai ma da baka samu ko kwabo ba.”
Ta juyar da fuskarta can gefe ta daina kallon inda yake.
Tun Babana yana yi wa su Yaya Ibrahim da Baba fada kan abubuwan da suke yi na kin karatu da yawan abokai har ya gaji ya watsar, watakila ganewa yayi hakanne zai fi komai saman mishi zaman lafiya.
Jarumtaka guda daya da yayi dai ita ce, ta hana su zuwa kasuwa su zauna mishi a shaguna, ita kuwa ko a jikinta sai su wanke goma su tsoma biyar, ka’ida ne kuma wanda ya kai musu abincin ya koma ya kwaso kwanukan in sun gama ci a kuma yi musu shara.
Abokansu kuwa sun fi kowa mutunci a wurin Mama, don a bayyane yake bata shiri da mafi yawancin abokan Baba na tun ba Baba Yahaya ba ta ce, babban munafuki kenan.
Ana cikin haka suka tasa Mama a gaba wai su a bar su su koma daya gidan na Babana wanda Ado ke ciki, tunda Baba baya so abokansu suna shigowa gida.
Da farko Babana bai yarda ba, amma Mama ta dage to menene ba gashi manne jikin wannan ba ga kuma Ado a ciki? A dole ya hakura suka koma, nima na dan ji dadi duk da dai ana tura ni kai musu abinci, debo kwanuka da yi musu shara.
A fili yake gabadaya ‘ya’yan Mama daga matan har mazan da ma ita Maman kanta basa sona ba kuma sa iya boyewa, babu halin in dan zauna a cikinsu sai ka ji suna cewa.
“Haka kawai muna zaman zamanmu Babanmu yaje ya auro mana wannan matar tazo ta haifan mana wannan shegiyar.”
Da zan dago ido in kalle su don sanin ni da uwata suke zagi, sai ka ji sun daka min tsawa, “Daina kallona in ba haka ba in buga miki rankwashi.”
Wata ranar ko nayi maza na kawar da kan nawa na daina kallon nasu sai sun bi ni da rankwashin.
Ko kadan ba ni da farin jini a gidanmu, nafi kowa bakin jini a ‘ya’yan dakin Innata, na fi su kuma wahala don ni kam kullum a cikin fitina nake, a cikin azabar duka ba wurin Mama da ‘ya’yanta kawai ba, har wurin Baban nawa.
Gabadaya cewa suke yi wai ni muguwa ce kuma munafuka halina iri daya ne da na Innata, in yi ta kallon Inn ata ina tunanin yanda halin nata yake, tunda ni ban taba sanin muguntarta ba balle kuma munafurcin.
Sai dai kuma abin mamaki, duk da wannan matsi da tsana da nake fuskanta a gidan mu wurin dangin Innata, farin jini ne da ni. Tun ma ba wurin Alhaji Mai kudi da Hajiya Kubra ba.
Tun kuma ba wurin Mallam Mai babban allo da uwar gidanshi Hajiya ‘Yardubu ba, ita kam Hajiya Turai yanda ba kula Innata take yi ba haka nima ba wani shiga harkata take yi ba.
A mafi yawanci ma nakan shiga gidan mai babban allo ban leka dakinta ba in gama in tafi, sai da shi mai babban allon ya koya min bin ta dakin ta in gaishe ta.
Su dangin Inna kullum sukan danganta tsanar da ake nuna min a gidan namu da yawan son Innata da kuma tausayinta da aka san ina yi.
Donni kam kullum cikin tausayin Innata nake, ban sani ba ko shi ne dalilin da su kuma suka maida ni ‘yar lelensu, ba komai ba ne a wurinsu suyi min sayaiya ni kadai su bar su Atika da Aliya da Sa’adatu.
Kwata-kwata shekaru goma sha uku ne da auren Innata cikin wadannan shekaru kuwa ‘ya’ya shida cif ta haifa, gaba dayanmu kuma mata ne mu hudu muna nan a raye, biyu kuwa babu su.
Ni da Atika da Aliya dama a jere muke, sai Zainab da Kubra su babu su, sannan Sa’adatu.
Yawan haihuwar Inna ba karamin damun Mama yake yi ba, duk da cewar da take yi wai mai haihuwar ‘ya’ya mata zalla bai san dadin haihuwa ba tunda shi wai mai son haihuwar da namiji ne, to amma kuma duk da matan da take haifan ba ta iya zuba ido ba sai da ta dauki matakin shiga tsakanin Inna da mijin nasu.
A wannan lokacin ne Mama ta kawo wata ka’ida ta wai in kana goyo to ba za ka yi girkin gida ba, ba kuma zaka je gun miji ba, ko shi din yazo wurin ka.
Kowa yasan don Mama taga haihuwa ta tsaya mata ne yasa ta fito da wannan ka’idar, to amma tunda wanda aka yi domin shi ya yarda itama Innata bata tanka ba, don haka hakan ake yi.
Innata bata da miji sai dai ba girki ne bata yi ba, kamar yanda aka ce na wai mai goyo taji da hidimar goyonta, don kar taje tana girki tana kazanta.
To amma kuma kusan kullum sai Mama tayi cefane ta ajiye ta fita unguwa ta bar ma Innata girkin da ba nata ba ne tayi.
A farkon tasowata dauka nayi kwata-kwata Babana bai son Innata saboda ganin abubuwan da ke gudana a gidan baya iya magana da Inna ko kallon inda take baya yi.
Baya sauraron ta komai nashi ko hidimar shi Mama ce, itama kuma Innan bata daga ido ta kalli abinda ake yi, sai daga baya da na soma wayo na soma fahimtar al’amura sosai, sai na soma yarda da maganganun da mutane da kuma makwabtanmu masu sa ido kan lamurran gidan namu ke yi.
Cewar ai babu yanda za’ayi Babana ya ajiye kyakkyawar mace mai kyan diri da kyan halitta irin Innata, bugu da kari ga tsabta da yawan ado sannan ya ce bai sonta, sai dai kawai ya kasa mu’amalla da ita a zahiri, saboda an sha gaban shi.
To ilai kuwa, ina soma wayo sai na soma yarda da cewar ba son Inna ne Babana ba ya yi ba, akwai shakku ne mai yawa tsakaninshi da Mama, na kuma kara yarda da hakanne a dalilin ganewar da nayi cewar Mama tana sanya kafarta waje tabar gida da sunan tafiya unguwanninta da kusan kullum sai taje je su.
To shi kuma zai dawo cikin gidan ya baro kasuwarshi kenan sai ya tabbatar ta kusa dawowa sannan zai fice ya bar gidan ya koma shago.
Yana shigowa gidan kuma zai nufi wurin Inna, wurin da bai rabuwa da tsabta da kamshi saboda ita din mai tsabta ce, iyayenta kuma masu yi mata hidima ne bata neman komai ta rasa har turaren daki da na jiki da namu na yara kawo mata ake yi.
Baba yana shigowa gida in dai Mama bata nan to zaka ji yana magana cikin natsuwa “Ina Fatima take?” ko kuma ya ce, “Ke Humaira ina Mamanku? In gaya mishi sai ya nufi inda take din. Sai dai Inna bata sauraron shi.
Innata mai kyau ce, gata da kwalliya ga tsabta duk da nasan ta ne a shekarun da tayi fama da matsalolin aurenta saboda fin karfin da kishiya ta yi wa mijinta, hakan bai hana ni sanin kwalliyarta ba.
Haka nan mutanen da suka san farkon zuwanta gidan basa gajiya da fadin kai ai farkon zuwan yarinyar nan gidan nan anyi wani abu a wurin, ga kyau ga ado ga yauki ga murmushi ga ta kuma da girmama mutane.
Rannan ma Mama bata nan tun safe ta bar gidan ita da su Suwaiba. Babanmu ne ma ya dauke su a motarshi ya tafi dasu wai anyi mata haihuwa, ni da Inna ne kawai a gida sai ko Sa’adatu.
Suma su Atika sun tafi Makarantar allo, ni na taimaki Innar ta gama`aikin abincin ranar da Mama ta tafi ta bar mata. Sai da muka kammala komai ta shiga dakknta don yin wanka, ni kuma na tsaya ina gyaaa kicin din da muka yi aikin a ciki.
Yayin da sa’adatu ke bayana tana ta tsala uban kuka, muna cikin haka sai ga Babana ya shigo.
“Ke Humaira ina Innarku take?” nayi maza na ce mishi sannu da zuwa Baba, wanka take yi. Ado ya shigo ya ajiye kayan cefanen da yazo dashi, Babana ya kalle shi ya ce mishi, koma shagon sai an yi sallah sai ka zo ka dauke ni.
Cikin ladabi ya ce mishi, to ya juya ya tafi, shima Babana ya shiga wurin Innata, bai dade da shiga ba naji Innan tana cewa, ina kike? Kawo min ita, na ce to, naje zan kai mata ita.
Tana zaune kan kujerarta ta kwalliya a gaban mudubi yayin da Babana ke tsaye a bayanta yana magana a hankali tare da kallon abinda take yi na gyaran gashinta.
Ke fa halina dake kenan, ke fa halina da kenan babu halin in dawo gidan nan saboda ke sai kin bata min rai, to ka daina dawowa mana, tayi maganar a wani yanayi da ya sanya ni hanzarin cewa, gata don su san na shigo dakin.
Har ta mika hannu zata karbe ta sai kuma ta ce min shiga ban dakin can kiyi mata wanka sai ki kawo min ita don kar ta bata min jiki.
Na ce to, na je yin abinda tace din duk da kukan Sa’adatun.
Ina cikin yi mata wankan naji Babana yana cewa, wai me kike nufi ne da wadannan abubuwan? Ta ce abinda nake nufi kenan mu zauna kamar yanda aka ce mu zauna.
Ya fara magana kamar zai yi fada ban san dalili ba sai kuma naji ya canza yana cewa ke baki da wayo, tayi maza tace eh, ai nima na sani.
Zo ki ji abinda zan gaya miki, bata kai ga bashi amsa ba na fito da Sa’adatu zan bata ita har lokacin bata gama shafe jikinta da mayukan dake kan madubin nata ba, wadanda ni na kawo mata su daga gidan Alhaji Maikudi.