Skip to content
Part 40 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Tafiyace ta fara mikawa sosai kewar mijina taci gaba da karuwa a gare ni ina kara nesa dashi kewa da kaunarshi suna karuwa cikin zuciyata.

Ban san yadda aka yi ba sai kawai naji zuciyar tawa ta kama yin nazari da tunani cikin al’amarin aurena da Ado wanda aka faro shi watanni ashirin da daya da suka wuce watanni ukun farko muka yi su a gidan Babana, kusa da yan uwana da iyayena da dangina watanni goma sha takwas din bayan nan kuma tare da na shi dangin.

Tunani na sosai nayi har kafin zuciyar tawa ta kawo ga tunanin hali da kuma irin sallamar da nayi da kowane bangare, na rabu da Ado ne bayan ya tabbatar min da cewar fatan shi da burinshi bai wuce nuna min halaccinshi ba, ta hanyar tabbatar min da cewar shi din da namiji ne.

Yayin da ita kuma Ruwaila da nata mukarraban suma suke yi min fata da barin muna nan tare daşu shi Adon ya nuna min cewar shi din da namijin ne.

To wai wane ne da namiji? Ko kuma me kalar da namiji ke nufi? Wannan ita ce tambayar da ta zo min cikin zuciyata.

Namiji ni a sanina shi ne suna mafi daraja da Ado ke yi wa kanshi lakabi ko kuma in ce kirari dashi.

Sannan duk da ban taba yi mishi tambaya yayi min bayanin abinda yake nufi da kiran kanshi da wannan sunan ba, ni a fahimtata kalmar Namiji a wurin Ado yana nufin suna na cikakken mutum jarumi mai iya fuskantar kowane irin al’amari da zurfin zuciyarshi.

Mai tsayawa kan abinda ya sanya a gabanshi, mai iya tsayawa ya fuskanci kowane irin wahala da jaruntakar shi don ya zamo kariya ga na kasa dashi, mai sanin ya kamata wanda yake iya saka alheri da alheri.

To amma a wurin mutane kamar su Ruwailah da masu fahimta irin nata, ina ganin shi ‘namiji’ ba kowa ba ne a tasu fahimtar face jarumin da ke iya danne na ƙasa dashi.

Jarumin da bai kamata mace ta bashí amana ba saboda bai da alkibla guda daya, yana iya canzawa a kowane lokaci, ya manta da farko ya saka aheri da mummuna tunda shi din kanshi kadai ya sani.

Bai kuma damu da rayuwar kowa ba sai tashi, tunda a bakunansu dai kusan kullum sai ka ji su suna fadin in dai ‘Namiji’ ne ai gashi nan ga ta nan yanzu-yanzun nan ne kuma zaka ji su suna cewa wa shi ‘namijin ba dan goyo ba ne.

Da dai na tsunduma sosai cikin wannan tunanin musamman da na tuna tun kafin in ji irin wannan kalmar a bakin su Ruwaila, na taba jin ta a bakin  Babana, shima ya taba ce min in dai Ado namiji ne to gani nan gashi nan.

A bakin Mama kuwa ta gaya min yafi sau shurin masaki, sai na kasa ganewa na kasa gane wanne zai dauka cikin biyun?

Namiji zan dauka a fahimtar da na yi wa Ado ko namiji zan dauka a fahitar su Ruwailah? Mama har da Babana?

Da na kara nazari cikin tunanin hankali sai naga to ai ba zai yiwu in karyata fahintar su Ruwailah ba tunda har da Babana a cikinta. Haka nan ba zan Karyata mijina kai tsaye ba, saboda girma da darajar shi a wurina.

Don haka sai naga to me zai hana in bar komai na bar wa zamani lokaci mu kara tafiya cikin al’amarin rayuwa a sannu don in kara yin ilimi da fahitar da zan gane wane ne cikin biyun’?

Zan gamsu da nasu ra’ayin? Tunda ai kwata kwata ma yanzu ne nake cika shekaru ashirin da daya a duniya, don haka bai kamata in fara yankewa al ‘amura hukunci ba kallo kawai ya kamata in yi tayi ina kara ilimi da fahinta, musamman ma da yake masu ra’ayoyin nan duka biyu ba sa’o’ina ba ne.

Watakila kowane bangare a cikinsu yana da madogarar da ya dogara da ita, wacce shi din ganau ne a kanta ba jiyau ba.

*****

Mun isa gidanmu lafiya, idan tsaya cewa an karbe ni? To na tsaya bata bakina ne, sai dai abinda yafi komai bani mamaki shi ne wanda yafi kowa karban nawa da nuna farin cikin ganina wai Babana ne.

Duk da cikin dare muka isa, daren ma har ya fara nisa dakin Mama na fara shiga saboda umarnin da Adon ya bani kenan amma wai a wannan tsohon daren ina gaida Mama, idonta yana kan zanina tana kokarin tantancewa super ta asali ce ko ta kwaikwayo?

Ni kuwa na gyara mata sosai don taga abin da take son, cikin zuciyata kuwa cewa nake yi uh uhun, ba a dai bar hali ba.

Na fito daga dakin Mama jikina a sanyaye kwarai saboda tsananin ramar da na gani a tare da ita, gashi tayi duhu ga wasu wunduna guda biyu a tsakanin hakoran gabanta guda biyu.

Nayi tunanin abinda ya baddasa mata hakan, sai da kyar na iya tunawa da cewar jajayen hakoran da ta sanya ne sanda ta tafi aikin Hajji suka tafi suka bar mata bakin nata, a zuciyata nayi dariya na ce kai  wadannan hakora sunyi tsiya.

Maimakon su tafi su bar mata natan sai suka hada har dasu? Na ce to ko da yake dai ai tayi ado dasu, na sake tunawa da irin adon da Mama tayi da hakoranta na ce to sun mori juna.

Na shiga dakin Gambota wacce ko lekowa mu hada ido bata yi ba tun zuwana gidan, jikina a sanyaye kar dai duk mutanen gidan haka suka zama tunda Baban nawa ma ya zube ba kamar da ba, amma kam nashi wasa ne akan na Mama

Gambo tana nan kalau dinta, sai ma kara murjewa da tayi, ta yi shar gwanin sha’awa da ita, kuruciyarta sai karuwa take yi, tayi kwalliyarta daidai da ita, gashi komai da kuma ko’ina dinta sai kamshi yake yi a cikin kuma tsabtar da ta dace da shi.

Zama a gaban kujerar da take zaune nayi a kasa na kwantar da kaina a jikinta ina shakar kamshinta, waiyyo Gambo! Na fadi hakan cikin murya mai Rauni kwarai.

Ashe kuna tafe? Ai bai fadi kuna hanya ba, sai dazu dazun nan da ya tabbatar kun kusa shigowa gari wai don kar in yi ta damuwa.

Na kara makalewa na kara kwantar da kaina a cinyar Gambo sosai, cikin shagwaba na soma ce mata naji mararinki Gambo, naji marmarinki na ji mararinki har na rasa yanda zan yi ke kuma ki ka ki zuwa.”

Ta ce, to ba muna gaisawa a waya ba? Ai abubuwan rayuwa ma sunyi sauki, ko baka ga mutum ba zaka ji muryarshi ku debewa juna kewa, mu da iyayen mu suka bada mu ai gamu gasu amma basu ganmu ba basu kuma ji muryoyin namu ba sai da aka dauki lokaci mai tsawo.

Sa’adatu tazo ta wuce tana goye da Umamatu a bayanta, Babana ne yake kwala nata kira, a zuciyata na ce kai lalle wani sabon abu yana faruwa a gidanmu, ko ma in ce ya faru. Babana yana mu’amallah da kowa daidai da cewar mu’amallar a gaban Mama tana kallo lalle an samu yancin rayuwa.

Sa’a ta sake dawowa tana kallona cikin murmushi, “Kai Anti, wane irin tsarata kika yi haka?

Na kalle ta cikin natsuwa na ce mata, ban ma ganta ba Sa’a, sayayyar yayanki ne.

Tayi murmushi, to wai in ji Baba a ina za a sa miki kayan gasu nan ana shigowa da su, na kalli Gambo naga sha’aninta take yi.

Na maida kallona wajen Sa’adatu na ce mata kin ga ni Sa’a akwatin kayana kawai za ki dauko, tsarabar asa a dakin Baba ko falonshi, ta ce haka ne ta juya ta fita.

Rannan ni da Gambo muna kan gadonta yayin da Umamatu take wurin Sa’a a dakinsu, na kalli Gambo bayan mun gama magana da Ado a wayar Gambo nayi murmushi na ce, Gambo ina ta tunanin yanda zan gan ki gabana yana ta faduwa sai kuma na gan ki fess da ke.

Komai din ki kalau, sai ma abinda ya faru ga su Baba Karami da…ban san yanda aka yi ba kasa fadin sunan Adam nayi kamar yadda na saba, ban taba sanin sunan yana yi min nauyi haka ba sai yau.

Don haka na bar fadin sunan na ce duk sun girma Gambo, komai na ki a cikin rufin asiri yake.

Gambo ta saki wani irin lallausan mnurmushi ta ce, ai haka al’amarin Ubangiji yake, wani lokaci sai ya yi maka wani abu, kayi ta bakin ciki saboda wauta da ajizanci na rashin sanin abinda yake boye.

Sai daga baya a hankali sai ka gane ai wanan abin da ya baka shi ne alherin da kullum da kullum ka ke rokon shi ya ban, ba tare na fahimci in da zancen Gambon ya dosa ba na ce mata haka ne Gambo, sai naga ta zuba min ido cikin tsananin natsuwa ta ce min ni kadai nasan irin bakin cikin da nayi akan aurenki.

Ni kadai nasan irin kukan da nayi a bayan idon kowa, ni kadai nasan tunda aka furta auren ban sake rufe ido cikin dare nayi bacci ba, gayawa Ubangiji ina rokonshi ya kawo wani dalili da auren zai fasu ba tare da wata fitina ta auku ba, in kuma kaddara ce sai an yi, to ya hana su cutar min da ke ya kuma tsare min ke daga duk wata fitina, ya kuma nuna mana alheri mai yawa bayan hakan.

To gashi nan a yau ba a je ko’ina ba auren naki ya zama shine aure mafi ‘yanci da duk yaran gidannan suke yi, gabana ya fadi jin abinda Gambon ta fada, na kuma san da iyakacin gaskiyarta take yi.

Don haka nayi shiru kawai ina sauraronta, ta ci gaba da cewa, auren naki shi ne aure mafi zaman lafiya da kwanciyar hankali, cikin raina na sake cewa uhun, Gambo kenan, ko dai don ban tona miki abinda nake ciki bą? Shi ne kuma auren da yafi kowanne zamo min sanadi na rufin asiri mai yawa, shagon nan da yaron nan ya bar min ai ba karamin alheri ya bar min ba.

Ga wannan yaron da aka sanyawa suna kina ta kuka ina baki hakuri don bai kamata komai in biye miki muyi tayin abu ba, ashe shima alherin ne, na samu A.C saboda shi. Na samu albashin wata sabo da shi, nayi maza na kalli Gambo na ce, albashi? Ta ce, eh, bai gaya miki ba ne? Nayi maza na ce, a’a Gambo.

Ta ce, ai tunda mijinki ya soma aiki bai taba fashin aiko mishi da kudin madararshi ba, a zuciyata na ce uh uhun, Gambo tana ta famann murna kan wadannan abubuwan don ma bata san wani alherin da Adon ya sake aiko mata ba.

Sai na ji ta ce min, shi yasa dukanku a yanzu nake gaya muku dama duk wani wanda zan gayawa ya ji, kullum ka tsaya akan yin addu’a, kar kuma ka cuci kowa, a kan saninka.

Abinda duk ya same ka kuma ka dogara ga Ubangiji kar ka yarda zuciyarka ta raya maka cewar wani ne yayi maka ko da kuwa a zahiri shi ne sanadin abin.

In ka nemi abu ba ka samu ba kuma ko wanda ba ka zato yazo maka to ka roki Ubangiji ya zama shi ne mafi alheri a gare ka, tunda duk al’amarin nashi ne.

Cikin natsuwa na ce mata haka ne Gambo.

Rannan haka muka kwana muna hira ni da Gambo akan gadonta muna kwance yayin da itama Sa’a ta kwana hidima da Umamatu, wacce ta ki yin bacci tana ‘yan koke-kokenta a nasu dakin.

Ko kawota kuma bata yi sai in Gambo ta ce to tunda ba ki da nonon da za ki baiwa yar taki ai gara ki kawo ta a bata ko ta kara jin dadin rikicin nata, a duk lokacin da na karbi Umamatu ina bata nono Gambo ta rinka kallonta kenan tana bin gabobinta tana dubawa.

A duk sanda ta gama dubawan kuma sai ta ce to yaushe wa ya taba sanin wannan shi ne abin da zai faru?

Ni kam ban mike na gyara kwanciya da nufin yin bacci ba, sai da aka yi kiran sallar farko, Gambo tayi maza ta kallen ta ce, wannan ai shi ne karya, ki kwana kina magana Asuba tayi ki ce za ki yi bacci Ai mikewa za ki yi kibi alwala kibi nafila kafin lokacin sallar tayi.

Ina idar da sallah su Atika da sauran yan uwa suka soma kiran wayar Gambo suna yi min sannu da zuwa tare da fadin ga sunan zuwa, don haka na mike naje nayi wanka da ruwa mai dumi na wattsake nazo na zauna ina shafa. Sa’adatu ma tana sanyawa Umamatu kayanta, suma wankan suka yi.

Kai Anti, kin iya sayen rigunan yara, na ce bani ba ce Sa’a kai ji wannan ma, wanne zan sa mata? Ji wata ma, kai ga wata. Gambo ta ce, da dai kin hakura kin sa mata guda daya yau da gobe sai ki ga kin sanya mata sauran ma, kin gansu a jikinta.

Kwalliya sosai nayi, wata super na sake daukowa gara ta jiya da nazo da ita ma na taba daurata, wannan sabuwa ce dal, Sa’a ta kalle ni tayi dariya ta ce “Anti ai ke har kin fi ma matan masu kudin daura zannuwa.

Nayi murmushi na ce, “Wannan shi ne iya shege, matar me kudi bata daura zani ta daura gwal ta hau mota me numfashi ba me tayi?

Gambo tayi murmushi ta kalli Sa’adatu ta ce mata, kawo yarinyar ki kawo mata ajiyarta, ta kawo mata ita ta wuce cikin dakin Inna, wata ‘yar leda ta kawo min wacce da gani na sani daga Saudi take, ga kuma alamarta, ga yan akwatina a ciki har guda uku.

Daga ina wannan Gambo? Ina bude su ina tambaya, sarkokinki ne da ki ka tafi ki ka bari na baiwa Mama sanda za su tafi aikin hajji da Aliya, na ce ayi ciko a canzo miki sarkoki ne guda biyu babba da karama, ga kuma warawarai guda hudu da zobuna biyu, wanda ni su suka fi daukan hankalina ma.

Don nan take na zuba su a hannayena na kuma sa zobunan, in ban da Gambo ta ce in sanya karamar sarkar ma ni ka da hakan ma ya ishe ni. Godiya mai yawa nayi mata.

Na tashi na fito tsakar gida saboda jin da nayi Babana yana tambayar wai ni Aisha bata tashi ba ne? Nayi maza na ce ai ban ma kwanta ba Baba, wanka nayi.

Akan katuwar shifidaddiyar tabarma na same shi a tsakar gida yana zaune wanda wannan ba wani abin mamaki ba ne, dabi’ar gidan ne yin hakan, abin mamaakin dai shi ne, yau shi kadai na ganshi zaune akai, ban ga Mama ba, ban ma ji motsin fitowarta wajen ba tunda gari ya waye ban ma ji wo muryarta ba ko da daga cikin dakin ne, shiru.

<< Mijin Ta Ce 39Mijin Ta Ce 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×