Sai Zubaida da ke ta faman kai-kawo tsakanin kicin da tabarmar Babanmu.
Kai Antin Sa’adatu kin yi kwalliya kin kuma yi kyau ba an ce min garin naku kauye ne ba? Na kalli Zubaida nayi murmushi na ce, Anti kenan. Karo na farko da bakina ya yarda ya kirata Anti, ba akan an tilasta mishi ba.
Babana yayi tsaki ya ce, ka ji wani zance wurin yarinyar nan, to harkar yau aljihunka ba shi ne birninka ba? Kana zaune a birni ba ka da ko kwabo ai ka zama dan kauye, sai dan kauye ya ci duniya in yana da kudinshi kai baka ci ba.
Tayi maza ta ce, haka ne kam, itama bin atanfar tawa take yi da ido, a zuciyata na ce itama ta koya wurin Mama, zuwa can kuma sai naji ta ce mu ma fa atamfofin da ya aiko mana super ne, ban tanka mata ba
Na kalli Babana wanda shima dadin ganina ya kama shi, ga kwalliya mai kyau mai kuma tsada, na ce mishi Baba bari in je in gaida Mama, ya ce to kar ki dade, don yanzu zamu karya. Me ki ke so ki karya da shi?
Na ce duk abin da Anti Zubaida tayi dashi zan karya. Yana murmushin jin dadin ganin mu’amallata da Amaryar tashi, Sa’adatu ta kawo mishi Umamatu daidai zan shiga dakin Mama.
Sau biyu nayi sallama katin ta amsa, bayan tana ganina ina ganinta, na ce mata sannu Mama, ta ce yauwa sannu kadai, muka sake gaisawa ba tare da ta tambayeni Ado ba, balle ‘yarshi.
Ni kuwa na bararraje na zauna mata a daki sosai, cikin zuciyata ina fadin abinda ka shuka shi ka ke girba, komai na dakin yayi dikin-dikin alamar datti ya kama shi saboda ba ta shi ake ba, ba a da lokacin shi balle a samu zarafin gyara shi.
Wai Mama da Babana suna hade a gida amma babu mai kula wani, kowa harkar gabanshi kawai yake yi, in da wani abin da ban taba zaton zai faru ina raye ba ai shi ne wannan.
Ni ‘yanjakar ubannan sun ma zo sun gaishe ki kuwa? Daga waje Babana ya daga murya yayi min wannan tambayar, nayi kamar ban gane su waye ba, tunda ina jin motsin mutane a dakın Mama, na kuma san su Suwaiba ne sun ki fitowa ne kawai don kar muyi ido hudu da su.
Watakila suna tunanin kwana daya ko biyu zan yi, su waye kenan Baba? Cikin natsuwa da murmushi mai yawa don dai ma Mama ta kara sanin mun shirya da Baban nawa, nayi mishi tambayar.
“Wadannan ‘yanjakar uban mana.” Ya sake yin zagin, mamaki ya kama ni ban san Babana da yawan zagi ba, watakila itama Mama abin ya dame ta, don wani mummunan tsaki naji taja kafin naji ta ce.
“Kai Allah kenan, rayuwa dai bata yi ba tunda an kare da zage-zage. Da sauri na kalli Mama saboda jin maganar tata dan kiris ya rage in kyalkyale da dariya, saboda yadda ta tsuke fuska ga ta kuma dama ta zama ‘yar karama.
Wadannan yan jakar uban mana su Habiba masu gadon mugun abu ai suna nan a ciki.”
Gabana ya yanke ya fadi, cikin tsoro da kunyar masu gadon mugun abin da yake fada nayi maza na ce, a’a Baba, ai ma ba laifinsu ba ne nawa ne, da na yi wa gidan shigowar dare.
Da sauri na mike na nufi can cikin dakin na Mama na barta tana tsaki tare da fadin wannan yaron ai wahala ta same shi, tunda ya gamu da mutane marasa Imani, balle tausayi.” Ko a jikina.
Ashe kuna ciki? Nayi tambayar daidai na daga labulen kofar wanda ya zama tanfar ba na Mama ba don datti. Abinda na ganin yayi matukar kadani, tukunyar alala akan risho a bayan kofar Mama yana tafasa, ga Anti Sha’awa da Habiba suna kwance kan katifar da ke yashe a kasa sun tasa ‘ya’yansu a gaba suna basu nono.
Suwaiba ce a gaban tukunyar tana rantsuwar ita da kanta zata raba don ba za ta yarda ta bar musu ba su kwashe su baiwa ‘ya’yansu, su bar mutane da yunwa.
Na kalli ‘ya’yan sun kai biyar ban da masu shan nonon, sun takura waje daya gaba dayansu ya’yan Anti Sha’awa ne. na ce, kai su Buhari ne haka? Suka zubo min ido alamar a cikin doka suke.
Muka gaisa da Sha’awa da Habiba har na karasa shiga na yi wa ‘ya’yan da suke shayarwa wasa, Suwaiba ta sunkuyar da kai kasa tayi kamar bata ganni ba, nima na wuce na fito ban tanka mata ba.
Na kama hanya zan fita saboda jin muryar Salisusu da nayi, na kalli Mama nayi murmushi na ce Kawu fa ya ce a gaishe kir da kyau-da-kyau, ta ce madallah.
A tsakar gida Salisusu yana tsugune suna gaisawa da Babana, ga katuwar kula a gefenshi alamar shi yazo da ita, sannu da zuwa Yaya, ya dago ya kalle ni cikin murmushi, Anti ashe kun iso? Na ce eh.
Ina Baban ba ka zo min da shi ba? Yayi murmushi, suna nan zuwa. Muka gaisa sosai, cikin yanayin surukai kafin ya mike ya shiga wurin Gambo.
Babana ya kalle ni ya ce min, ga abin karyawa nan daga wajen Atika.
Nayi murmushi na ce, an gaishe su, amma sai naci na gida na Anti kafin in ci na wani, dadi ya sake kama Babana.
Muna cikin haka sai ga su Buhari a guje Suwaiba ta biyo su tana duka, wai ta ce kar suyi warwaso sun yi, Baba ya daka musu tsawa kai ku min shiru ku koma dakinku ku zauna kar kuzo nan ku cika min kunne da ihu, ‘yan jakar uba kawai marasa da’a masu abin tsiya. To an koya musu.
Cikin zuciyata na ce, oh oh, Baba kuma sarar da ya samu kenan? Ko da yake dai ba laifin shi ba ne, Maman ce ta koya ishi komai yaro yayi, ta ce mishi wai uwarshi ta koya mishi.
To gashi abin yazo kanta, a wancan lokacin da take sha’aninta kuwa bata taba tsammanin abin zai koma mata ba.
Salisusu ya yi wa Babana sallama ya tafi, sai kuma ga dan aika daga gidan Hajiya Aliya, da manyan kuloli itama abin karyawan ta aiko dashi, ga kuma na Zubaida shima ya kammala.
Na kalli Babana a hankali cikin natsuwa na ce mishi, bari in kira su Habiba mu karya tare Baba. Ya yi maza ya yautsa fuska, kar ki kira in wadannan yan jakar uban yaran.
Na sake bashi hakuri kafin na dauko wata katuwar tabarmar na shifida na leka falon Mama na ce “Habibah ku fito nan mu karya. Buhari ku ma kuzo dukkanku.
Na koma sabuwar tabarmar don mu zauna dasu, tunda sun kasa zuwa kusa da Baba, na ce ‘rai dai’ wai in ji kuda, Mowowin Baba wadanda suke komai suka yi daidai ne, sune yau suka zama babu wata mu’amalla a tsakani sai na zare ido da muzurai.
Na kira Zubaida na nuna mata abin da Atika da Aliya suka aiko dashi, na ce mata samo wuri ki diban wa Baba nashi da na Mama da Gambo da naki ta ce to, nayi zaton Mama zata ce ba ta so sai naga tasa hannu ta karba.
Mu ma na zuzzuba mana har yaran nasa musu nasu n ace kuci a natse in baku koshi ba sai a kara muku, suka ce to ita ma Suwaiba na aike mata na kira Sa’a na ce mata ta kawo mana kunun gyadan da Gambo tayi.
Gabadaya mun suke muna hira har Habiba tana tambayata mace fa kema ki ka haifa ko? Nayi murmushi ban yi magana ba, sai kawai naji Babana yana cewa uh’uh hun abinda suka iya kenan, su sami abin dadi su rufan mishi su rinka ci suna zare ido suna gwalo.
Amma su su zauna ana su dakunan auren sun kasa mugun halin da aka koya musu ya hana su, gabadaya zaman aure ya gagaresu, sun dawo min gida sun zo sun zama min da wasu munanan ya’yansu masu kama da “ya’yan tanda. Duk ku watse a nan ku bani wuri, yan jakar uba.
Gabadayan su da ya’yan nasu suka watse da gudu, yuu suka shige dakin Maama.
Ni kam duk da na sani da wuya kwarai in ga Mama cikin wani hali da zai bani tausayi cikin sauri, halin da ya’yanta ke ciki na kasa zaman ‘aure da yadda suka lalace suka zama tanfar ba su ne wadannan yan gatan ba-da suka sha’aninsu irin yadda suka ga dama. Su daura zani irin wanda suke so komai suka yi shi ne daidai, ra’ayinsu kuwa shi ne abin dauka, a bar nà kowa ya bani tausayi bana kuma jin dadin irin tsana da tsangwàmar da Babanmu ke nuna musu a zahiri nafi sha’awar da sai ya bar abin tsakaninshi da uwarsu, tunda ita ce tayi sanadin komai.
Wanda duk yasan Mama, ya santa yasan halinta, yagar hain da ita da ‘ya’yanta suke ciki a yau, kalma guda daya da zai iya furtawa cikir sauri ita ce, laifin uwarsu ne.
Watsewar da aka yi aka bar mu da gani sai Baba atsakar gida, yasa shi kallona cikin nutuswarshi ya ce min ba za ki sa a kwashe kayan da ki ka zo da su kaia wa Gamborku ta raba ba?
Nayi murmushi na ce ai sai ta rabewa danginta Baba, namu dangin basu samu bą. Babana yayi dariyar jin dądi a dalilin jin da yayi na tsame kaina daga cikin dangin Gambota.
Na ce, ai kai ne za ka raba sai kowa ya samu tunda kowa naka ne. Wani dadin ya sake kama shi, na ce amma kar ka manta da mutanen giyade, yayi dariya mai karfi.
To in yi rabo kuma in manta da mutanen giyade Humaira? Rabo na gaskiya Babana ya yi yanayi ina tuna mishi wadanda ya manta da śu.
Makwabta yan uwa, abokan tare ta kowane bangare ya bayar, don ko ta bangaren Zubaida ya bata turmi biyu ya ce na mahaifiyarta da kanwarta, sabulai da omo na mutanen gidansu.
Mama kuwa kaya masu yawa ita da duk wanda tasa zata ba har ma nata kason yafi na Gambota yawa, yana kallona ya ce bamu yi wa Gambo kwauron nata ba ko? Nayi murmushi na ce, in bai ishe ta ba sai ta sayà da kudinta ta kara, ya ce to haka.
Mun kammala komai ne muka shiga falon Babana ni da shi muka sake gaisawae na isar da gaisuwar Ado a gare shi. Wai shi har yanzu yana fushi dani ne ko?
Nayi maza na ce mishi a’a Baba, ya zubo min ido yana kallona, nan take kuma ya zubo min hannayenshi alamar dakwa.
“Kul ki ka kawo min iya shege, in ba fushi yake yi dani ba don me tunda ya tafi bai sake waiwayowa ba, ko a waya bai taða nemana ba’?”
Cikin natsuwa da nuna ladabi na ce, ba zai yi fushi da kai ba Baba, to shi a wa ma da zai ce zai yi fushi da kai? Shi din kullum a cikin fadar alherinka yake.
Yana kuma gaya nin cewar ya karu da ilimi iri-iri a wurinka na darasin rayuwa, yasha gaya min cewar kai ne mafi alherin mutanen da yasa ni wanda bai taba kyashin na kasa dashi ya samu alheri a tare dashi ba.
“Bai yi fushi da kai ba Baba, sai dai kuma zai ji nauyin kiranka a waya, watakila so yake ya samu damar da zai zo gabanka ya roke ka gafara kan kuskuren da ya aikata maka.”
To wane kuskure ya aikata min Humaira? Da ya rike min ke? Shi mijinki tun kafin ya aure ki ai ni da na dauke shi to balle kuma da yake aurenki yake kuma rike min da ke cikin rufin asiri a yanzu.”
Dadi ya kämä ni na ce to zan gaya mishi ya daina tsoron kiranka Baba zai kuma kira ka, to to to gaya mishi.
Bayan wannan hirar nabi sai na isar da sakon Ado gare shi na ce, amma ya ce kar in gaya mata sai in kai din ka yarda ka amince, don haka sai in ka yarda ne zata ji Baba.
Yarda? Yarda kai Humaira in da ina da hali kamar da da bara ban biya mata ba? To bani da hali, komai da ki ka sani babu shi, babu shi Baba? Nayi mishi tambayar a firgice, ya ce ai babu ba ki gani ba?
Ina ki ka ga ina zuwa? Nayi salati na ce yaya aka yi Baba? Na shiga hankalina sosai don jin äbin da ya same shi.
Sai kawai naji ya ce min Baba da Ibrahim, hannu biyu na saka na dafe kaina, cikin tsananin kaduwa.
Bayan tafiyar mijinki sai wannan ja’irar matar muguwa ta tasa ni a gaba akan in maida su makwafin mijinki a kasuwa.
Ta tasa ni a gaba da fitintinu iri-iri sai da na kái su kasuwar, ba aje ko ina ba sai na gane kasuwar tawa ba za ta juri ta’adin da ako yi mata ba don haka sai na rufe ido nayi ta maza na kore su na kuma haramta musu zuwa kasuwa.
Ni da uwarsu muka shiga wani hali na babu dadi, ga can kasuwar ma babu dadi, tunda na riga na samu matsala, abokaina duk sun yi gaba sun bar ni, don haka sai na ce to wadannan gidaje da mijinki ya dawo min dasu tunda dama ban san da su ba, bari in sanya su a kasuwa in karbi kudinsu in kara jari don in koma harkar sosai.
An kawo min kudin gidajennan da kwana biyu don mutum daya ne ya saye su, barayi suka zo min gidan nan da daddare suka shigo min nan.
Kin ga kin gani ya nuna min wani shafcecen tabo a keyarshi wanda na tabbatar ban san shi dashi ba ya ce su suka buga in karfen da suka zo dashi suka bincike min daki suka dauki kudi suka bar ni nan a kwance a sume.
Sai daga baya sai da asiri ya tonu aka samu aka kama guda daya, sai ya ce wai su Ibrahim da Baba ne suka turo su zo suyi min satar.
Ni kam kuka sosai na kama yi saboda bakin ciki da tausayin Babana, tabbas Mama ta cuci Baba na, don kuwa ita tayi mishi sanadin lalacewar ‘ya’ yanshi. ‘Yayan da kowa yasan babu abinda bai yi akan su ba don su zama mutanen kirki.
Bata aike shi ba, bata kuma bar shi yayi shi kadai ba, kullum gini yake yi tana rusawa share hawayenki kiyi shiru, Humairah ai ya wuce.
Ya wuce, kana zaune baka komai Baba? Yayi murmushi ya ce to ba gani a raye ba? Da sun yi nasarar kashe ni ko nakasa ni a wani wuri fa? Na sake fashewa da wani sabon kukan.
Baba Yahya ne ya iso saboda kiran da Babana yayi mishi, matar Sarkin Noma ne ta iso, nayi murmushi na soma gaishe shi ai tunda naga tsaraba na ce to ta Dabai ta iso kenan?
Babana ya kyalkyale dadariya, ya ce ai sunan da ka sanya mata kenan? Baba Yahya ai ni sunanta kenan a wurina tunda dai ta ki zama cikin mu ta koma cikin danginta, to ba zan kirata da wani suna ba, sai wannan ina ta ke?
Babana ya daga murya ya kira Zubaida da ke goye da ita ta kawowa Baba Yahya ita ya karbe ta cikin farin ciki yana fadin ka gani ba, wannan da ganinta ai kasan gidan noma ta fito, taci hatsi ta koshi.
Baba ashe abinda ya faru kenan mu ba mu sani ba? Na tanbayi Baba Yahya cikin natsuwa don in yi mishi jaje, sai ya ce min kece ba ki sani ba ai shi ka mya sani, dan ko sanda muka je wurinku, ni da Mallam ai mijinki ya yi mana jajen al’amarin ya ce min Gamborku ce ta gaya mishi.
Mamakin Ado yayi matukar kama ni, me yake nufi da wannan abin da yayi bai gaya min ba, bai kuma yi wa Babana jaje ko a waya ba? Maganar tafiyar Gambo da ya soma yi wa Baba ya katse tunanin nawa, ni kam in ban da alheri Ado ya yi wa Gambota ai da na karbe kudin na mayar mishi dasu, ban ji dadin yanda yayi ko in kula da abin da ya samu Babana ba.