Baba Yahya ya yi matukar murna, ya yi ta addu'a yana sanya albarka, ya rungumi kudi ya tafi dasu, wai zai je yayi duk wani abin da ya dace a gama komai sai bayan tafiyar tashi ne ma maganar ta watsu a cikin gida.
Mama tayi matukar kidimewa, hankalinta ya tashi ta shiga rusa kuka tana zage-zage, Zubaida kuwa sai faman tsalle take yi tana murna tana fadin yau fa ga inda haihuwar 'ya mace tayi rana.
An mallake ta ita kuma ta mallako wa uwarta mijinta, Gambo kam ba zan iya kwatanta farin cikinta ba, kan ka. . .