Na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi ni fa ji nake ma kamar abun nan yazo min da sauri, ya tsuke fuska yana fadin wasa kenan, ki ce min duk wannan kwalliyar da kyale-kyalen a haka nan za su tashi?
Rannan sa ar da muka yi ni da Ado shi ne na samu ya saiwa Umamatu dan gadon jarirai a ciki tun farko ya sanyata ban da haka kuma dakin namu can gefe yake babu mai jin abin da muke ciki. Ya ce Gambo ce ta kara gyara min ke, shiru nayi ban tanka mishi ba. Gambo tana sona Humairah, ya gama maganganun shi, ban yarda na ce mishi komai ba.
Washegari da wuri na fita na gaida kowa na kaiwa Goggo Ayalle Umamatu na kai mata ita tare da danbun nama da man shanu har da yaji, na kuma ce mata boye Goggo don ku kadai na baiwa daga ke sai baba, ya kamata to wannan tsaraba dama ai ba na kowa da kowa ba ne.
Tun daga ranar ban sake ganin wani yaro ya shigo wurina na kore shi don takamar na gyara wurina ba, wai kar su lalata min.
Sai dai ma in dau abu na mika mishi don ya kara mike kafa yayi zamanshi.
Sannu a hankali ‘sai wurin nawa ya zama wurin wasansu, kasancewata ba mai jurar magana ba ce in dai ba da mijina zan yi tayin maganar ba.
Sai na soma ce musu ku kawo littattafanku muyi karatu, kan kace meye wannan? Kowa ya dawo makaranta da matsalar shi zai zo wurina Maman Umamatu.
Rannan na ce musu kai kar wanda ya sake kirana da wannan sunan.
Ado yana jin mu da su ya ce da wane suna ki ke so su kira ki? Na ce oho, ya ce to ku rinka kiranta da sunan tsofafi Goggo na ce oho ya yi min, tun daga ranar gaba daya yara Goggo suke ce min in amsa.
Cikin hikima na baiwa Ado shawarar mu tashi mu koma wani wurin, da sauri ya tambaye ni muje ina?
In bar dangina in je ina? Naja bakina nayi shiru cikin zuciyata dai na san ina da aiki tunda ba zai yarda ya tashi ba, don haka na dauki mataki na gyara mu’amalla tsákanina da manya kamar yanda na samu da yara.
Kullum Juma’a in zan je gaida Goggo zan kai mata goro murza-murza ko kuma abin sayen goron, bini-bini kuma zan lallube abin dadi cikin hijabina in kai mata.
Itama Ruwailah haka, danma kuma ina jin ta gaji da zaman namu a haka, don haka tunda taga na dan yi sassauci sai tayi maza ta saki. Bini-bini zata leko wurina.
Goggon yara nace ko da abù kaza ne a wurinki? In ce mata eh, ko in ce a’a aje a sayo mana in mika mata kudin tayi godiyá ta tafi.
Gari yana wayewa kumă žata turo a daukan mata Umamatu ta hada da Nusaiba tayi musu wanka ta bar su a wurinta.
Rannan ba karamin tashin hankali Ado yayi min ba, akan ya gane na koma yin mu’amallah da Ruwaila nayi tayi mishi kuka, ita ta riga kowa karbanmu a gidan nan abin da ya faru bayan häkan in aka bar shi zai wuce ka bar ni in yi mu’amalla da kowa don kaima ka sanmu natsuwa.
In yaso taji dadin koya miki iya shege ba? Na ce to in ta koya min nan dauka mana ai jiki magayi, da nayi maka ka kyale ni ne? wacce irin azaba ce ba ka gana min ba? Ado ya kalle ni yayi murmushi ya ce ni kar ki kulla min sharri.
A haka na lallaba Ado ya bar ni na soma shiga harkar cikin gida, ina zuwa wurinsu muna hira, iyaka dai ina kula da bakina bana kuma yarda da zaman dakin wata.
A haka sai na soma shiga ayyukansu zan yi musu tankade na tuwo ko na abin kadi zan zuba garin tuwo suyi tuki zan zuba abin kadi suyi kadin zan yi sharar wurin girki.
A haka rannan sai na karbi girkina daga hannun Furerah ban kuma yarda mun bata ba, don haka sai muka samu saukin zaman mu’amalla kuma ta gyaru duk da dai nasan gyaruwar mu’amallar bata kawar da su daga dokin ganin Ado yayi aure ba.
Sai dai kuma an daina yin maganar a kan idona, nima kuma nayi sassauci mai yawa a kan hakan, saboda na riga na yarda da cewar a yau don Ado yayi auren shi bai zalunce ni ba.
Shi yakai min Gambo Makkah, ta sauke farali ko wannan kadai yayi min ni ya biya ni, balle kullum a cikin hidimarta yake ita da kaņnena.
A wannan lokacin ne Ado ya soma gini a cikin gida ciki da falo ne guda biyu manya, daya da kicin da bayan gida a cikin shi, daya kuma babu ga kuma wani daki guda daya suma biyu a jere. Yana soma ginin gidan gaba daya ya dauka aure zai yi ya gano wata kenan, ai kin ga namiji ba?
Tuntuni tana zaune a tsukakken daki bai yi mata gini ba sai yanzu da ya gano wata kuma ki duba ki gani tun ba aje ko ina ba yana yiwa amaryar gini irin na zamani mai hade da kicin da bayan gida a ciki.
Ita kuma nata babu bayan gidan bare kicin din, ban ce komai ba ban kuma taba daga hankalina har wani ya gane ba, na bar wa zuciyata komai.
Rannan dai muna tare da Adon a daki, laptop din shi yake dubawa a dalilin ba wani kula juna sosai muke yi ba, saboda wai na bata mishi rai nima naja nayi shiru ban bada, hakuri ba don fushin ya dan yi tsawo saboda wasu dalilai nawa.
Ina jin dai aure ka ke shirin yi ko? Shi yasa ka ke yi min abubuwan da ka ke yi, barin abinda yake yin yayi ya dago ya kalle ni me na yi miki? Na daure fuska na ce, gashi nan wułakanci iri-iri, wanne da wanne? Nayi shiru, ya ce ai kin lissäfo su tunda ki ka ambaci wulakanci saï kin gaya min.
Shim nayi ban tanka mishi ba, ya gaji ya ce in kuma kece ki ke yi min wulakancin saböda kin ga na kasa yin auren”to zan yi wa kaina maganin abin saboda na lura raini ya shiga tsakanina da ke ba kya ganin mutuncina.
Kullum kawu ya soma yi minirin wadannan kalaman kuka nake yi doń ba sa yi min dadi na kuma kasa sabawa da su.
In yi mata biyu mana nima in ji dadi in wannan bata tattake ni ba a yau to gobe wata zata yi.
A lokacin da Ado ya gama gininshi wanda ya yi matukar yin kyau ya kuma kawata wannan ciki da falon mai kicin da bayan gida da kayataccen tails da rufin silin irin na zamani.
Sauran kuma ya yi musu suminti jiranshi kawai nake yi ya ce min ga ranar aurenshi ga kuma ni dakin da ya bani.
Ana cikin haka, rannan sai gashi rannan yazo da kujeru ana zubawa a falon nan ya sanya darduma ya kawata wurin sosai. Mamaki ya kama ni na ce.
To wannan sai ya gama sanya musu komai ne za su bashi ‘yar ko yaya? Ni dai ban ce komai ba, tunda dai na tseguntawa Gambo maganar, ta ce in zuba mishi ido na ce mata to na zuba.
Da daddare ranar muna hira ya ce min ni fa gado bai damen ba, nafi jin dadin kwanciyar katifa shi yasa bai sayi gadon ba, amma in kina so a sai miki.
Na ce a’a a sai min gado kawu ai mutuncin daki ne ya ce to shi kenan.
Kwana biyu daga nan na tare a sabon dakina ciki daya guda daya ya mayar min da shi aji don karatunmu da yara har bencina da black boad yayi mana daya dakin kuwa ya gyara shi don baki ya bar daya ciki da falon.
Sai suka koma cewa sai ya gama gyara wannan din tukuna zai yi auren gashi ya killace min wurin da yar katanga amma duk da haka ban daina shiga can cikin gida nayi abubuwan da muka saba ba.
Kaka tana zuwa ciki da falon Ado ya bayyanawa mutanen gida cewar don buhunan hatsinshi ya tanade shi tun da rumbunan da yake amfani da su basa isan shi.
A wannan lokacin ne kuma ya sanya ni na fara karatuna na (N.C.E) a makaranta nan a Zariya kullum nake zuwa ina dawowa.
A wannan lokacin harka sosai yake yi don tun a shekara ta biyu da soma aikin shi ya zama mataimakin (Princepal) a makarantar yanmata ta kafur a yanzu kuwa shi ne (Princepal) na makarantar Gozaki.
Ban shekara cur ina zuwa Zaria ba ya sai min motar hawa ya kuma koya min duk da shi din har yanzu babur din shi yake burgawa yaje duk in da za shi, ko kuma ya hau motar haya in kuma ina gida ya ce min in kai shi.
Umamatu, Nusaiba da Hindu tare da Usman makaranta daya ya sanya su, don haka kullum in zan fita da safe nike kai su in wuce Zaria in lokacin tashinsu ya yi kuma ‘sai. Bala yaje ya dauko su a motar haya.
Rannan na dawo daga Zaria da yamma a gajiye nake sosai saboda muna cikin karatu mai zafi, ina zaune ina dama furar da zan sha don ragewa kaina yunwar da nake ji sai ga Ruwailah ta shigo min da dan waken da ta ce wai don ni tayi na karba cikin farin ciki ina mata godiya.
Na soma ci, lomar farko da ta biyu da nayi abin gwanin dadi, sai kawai naji ta ce min ni fa wata magana naji na ce to ba za ka ji za a cuci naka ko ana cutar shi ba kayi shiru.
Dole ka gaya mishi ko da kuwa ba jin dadin maganar zai yi ba, sai da naji cikina ya ba da sautin kulululu don tsoron abin da take shirin gaya min din.
Sai kawai naji ta ce min wai ashe Baban yaran nan cikina ya sake ba da wani sautin na kulululu, tunda nasan sunan da take kiran Ado kenan, wai ashe matar nan da ake cewa ya ajiye yana karyatawa wai har ta haihu.
Karfin hali nayi na iya karasa tauna dan waken da ke bakina, na hadiye ban tofo shi waje ba, cikin natsuwa na daga ido na kalle ta. Na ce mata shi Baban yaran nan wani irin mutum ne Yaya Ruwaila da ban isa in tuhume shi kan abinda yake yi ba?
Kin san kowane mutum da yadda yake, da irin lagon da matarshi take samu akan shi, to shi wannan wanda nake da shi a kan shi bana in tuhume shi ba ne in akan wannan ne ban isa ba.
Don haka ko kawo min dan ya yi ya ce in rike ba zan tambaye shi inda ya samo shi ba, musamman ma da yake nasan ba kan shi farau ba, don haka ko kin ji irin wadannan maganganun daina gaya min su kawai.
Wai dama kai da naka ne kar kaji ana cutarshi kayi shiru, na ce eh ai dama, to bani da iko akan shi ai kin ga gaya min din bai yi min amfani ba kenan.
Sai dai ma kawai ya yi dalilin tashin hankalina ke kuma nasan ba za ki so ganina cikin tashin hankali ba tayi maza ta ce yo to ina fa?
Da haka sai na kashe bakin Ruwailah akan dauko min wani labari ta kawo min.
Na kara haihuwa da namiji muka samu na roki Ado ya sanya min sunan Babana ya ce min to sai kawai ranar suna naji yana fadin sunan yaro Yahya, ban ce mishi komai ba tunda shi ma uban nawa ne Baba Yahya kuma yayi matukar jin dadin takwaran da Ado ya yi mishi don tasowa ya yi yazo har Dabai wai yazo ganin takwaran nashi.
Rannan ina tare da yara a aji karatu muke yi saboda wunin na ranar Lahadi ne tun safe kuma Ado yana gida sai da yayi azahar ya fita, don haka nima da muka yi azahar din sai na ce mu shiga ajin zuwa lokacin La’asar sai mu fito muyi sallah su taya ni aikin abinci.
Muna cikin karatun sai ga wani yaro dan makwabta da nake kira Baba saboda sunanshi Surajo, ya shigo da sauri sai da ya gaishe ni sannan ya ce min Goggo wai kinyi bako wai a gaya miki wai yayanki ne daga Bauchi.
Yana yi min maganar cikin wani yana kamar tsoro ko kunya Jin da nayi ya kira Bauchi ya sani nuna mishi kofar baya na ce mishi jeka ka shigo min da shi ta wancan kofar, ya ce min to.
Ya tafi ya dawo ya zuba min ido, kafin ya ce “Goggo kila ma fa karya ne, nayi murmushi na ce je ka dai ka shigo min da shi.”
Na ci gaba da tsayuwa a wurin don ganin wanda zai kawo min din, ai kawai gashi ya shigo min da Yaya Ibrahim. Yana ganina ya zube a kasa wai ni yake gaisarwa, gaisuwar girmamawa, sannu Yaya sannu dai, ina wuni yaya aka ji damu?
Zuba mishi ido nayi ina kallon shi, gabadaya yayi baki, baki ya gama rubewa ko’ina a jikinshi tabo ga wani katon yanka ya raba goshinshi biyu.
Yau kuma ni ka ke kira yaya? Nayi mishi tambayar don in hutar dashi girman da yake ta kokarin bani sai kawai naji yayi maza ya ce, au baba..baba ki yi hakuri ai mancewa nayi nake kiranki Yaya.
Sallamar yara na yi na bar Hasiya na ce ta kula min da girkina naje na budewa Yaya Ibrahim dakin baki na sauke shi a ciki na kai mishi abinci da na sha na kuma zauna don mu gaisa dashi gaisuwa irinta yan uwantaka.
Yana kai lomar abincin bakinshi ya sake canza min suna Anti ai baki san abinda ya faru da ni ba, ai hatsari nayi na rantse miki, Anti ai in ban da rabon za a sake shan ruwa a gaba ba ai da yanzu babu ni.
Ai mota da ta fadi damu ai ni kadai na tsira shi ne naji wadannan raunukan gama wani ko warkewa bai yi ba, ya kwace min wani shafcecen ciwo a kwaurinshi babu ko kyan gani tausayinshi yayi matukar kamani sannu Yaya lbrahim na soma gaishe shi.
Kan ka ce meye wannan ya lamushe abincin da na kawo mishin na fita don in karo mishi sai kawai nazo na samu wai har ya fara bacci, don haka na koma naci gaba da aikin abincina cikin zuciyata dai tausayin Yaya Ibrahim yafi komai damuna.
Ko ina Baba yake ko suna tare bari ya tashi daga bacci sai in tambaye shi.
Wajen karfe biyar da rabi Ado ya dawo gida da sauri naje na same shi na gaya mishi albishirinka, ya ce goro na ce mishi su Yaya Ibrahim da tunda suka tafi ake cewa ba a taba jin ga wanda ya ce ya gansu ba.
Ya ce, eh na ce to gashi nan yau yazo, yana ina? Na ce gashi can yana bacci a dakin baki, ba ka ga ciwanwukan da ke jikinshi ba, hatsarin mota suka yi.
Ya ce, ayya! Ya wuce ya shiga can cikin daki, nima amsawar tashi ta ban haushi, na juya na nufi kicin din tsakar gida wanda nake aiki a ciki.
Ban yi aune ba, ban san yanda aka yi ba sai kawai na jiwo ihu mai tsananin firgitarwa, na zare ido tare da kasa kunne don kokarin tantance daga ina ihun yake fitowa, ban gane ba.
Daga ina ne Hasiya? Cikin natsuwa naji ta ce min watakila Baba ne yake dukan bakon nan don naga ya shiga dakin da dorina a hannunshi.