Skip to content
Part 45 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Da gudu na nufi dakin ban san yanda aka yi ba ganina kawai nayi a kwance kan Yaya Ibrahim na rufe shi da jikina, gigitaccen ihun da na kurma shi ne ya fahimtar da Ado har dani a dukan da yayi Ado yana haki yana tambayarshi me ya kawo ka gidana?

Nima kazo ne kayi min abinda kuka yiwa ubanku? Hannu biyu na saka na rufe baki na zaro ido jikina sai rawa yake yi saboda tsoratar da nayi da irin zagin da Ado yake yi mishi, amma ko a jikinshi, muna da gaida ku ne uwarku ce ‘yar uwata itama bata takowa in da nake ba balle ku.

Fita ka bar nan dan iska… Na yi maza nace ni dan uwana ne wurina yazo na soma kuka don ban taba ganin duka da wulakanci irin wanda Ado yayi mishi ba.

To nemi inda za ki kai shi ki kai shi amma in kika bar min shi a gidannan kin sanni da kyau lokacin da zan turo N.D.L.A su kama shi ba za ki sani ba, sai dai kawai ki neme shi ki rasa.

Kuka sosai na soma yi na ce mu tafi Yaya Ibrahim tunda dan uwana ba zai iya zuwa wurina ba ai nima bani da wurin zama ya ce eh ba ku dashi kuje.

Ibrahim yaja ya tsaya a’a Anti ba zan zo in same ki a gidan mijinki in kashe miki aure ba, kiyi zaman ki kawai bar ni ni in tafi aini kadai ya kora na çe a’a tare ya kore mu.

Na tasa Yaya Ibrahim a gaba muka fita muka bar gidan, Ado ko Baba Yahya ban dauka ba saboda zuciyata takai matuka wajen zafi da wulakancin da Ado ya yi wa Ibrahim ba shi ya yi wa ba ni ya yi wa tunda dan uwana ne wana ne uban mu daya mu kuma da yä zauna a namu gidan rayiwar yanci yayi babu wani wanda ya wulakanta shi. “

Har mun shiga mota mun zauna muna jiran Direba yazo mu tafi, sai gá Baba Tanimu da saurinshi yana bin motocin da ke lodi yana leka cikin su har yazo kan tamu yana ganina ya ce, fito k fito nan.

Muka fita muka bi bayanshi, ba ki kyauta min ba, ko kadan ba ki kyauta min ba. Ban taba sanin ba ki dauke mu iyaye ba sai yau.

Gaba na ya fadi jin maganar tashi, in kin dauke ni matsayin uba ba za ki yi mun haka ba, na soma yiwa Baba Tanimu kuka saboda jin abin da yake fada.

Yaya za ki fita ki bar dakinki da sunan bacin rai ba ki sanar dani ba’? Wato nayi kadan ko? Har muka isa gida bai bar maganar ba.

Cikin zuciyata nayi nadama da na tuna mai babban allo ya gaya min cewar Hajiya Kubrah bata taba tsallake shi taje ta kai kara gun nata iyayyen ba. Saboda ta yarda shi din ubanta ne.

Muna shiga gida Ado muka fara gani zai fita da Baba Yahya a hannun shi, mutumin banza mutumin wofi, wato ban isa a zo wurina ba sai kayi hukunci da kanka? Wato ni ban isa ba?

Wato in ban da yarinyar nan Hasiya tayi hankali  tazo ta gaya min da sai kawai iyayen yarinyar nan su ganta a gida ni ban san komai ba, to ina amfanin girman nawa kenan?

Kayi hakuri Baba, Ado ya ba shi hakuri ya hada mu yayi mana fada, ya kuma hana Ado korar Yaya Ibrahim ya ce mishi wurina yazo ba wurinshi ba, ya bar shi tunda dan uwana ne, muka dawo muka zauna, amma ni da Ado ta ciki-na-ciki.

Rannan da daddare muka yi mummunan tashin hankali ni da Ado yayi min wulakanci irin wanda bai taba yi ba.

Ai ke ba ki san kowa ba sai kanki, shi yasa ba ki san girma da darajar kowa ba in ba naki ba ne, ba a bakin ki naji labarin irin lalacewar da Mama ta yi ba? Har kina gaya min wai wadaman mazaunan na Mama da take juijuyawa tana tafiyar takama duk sun zagwanye sun zama kamar fata ko tsunma?

Sannan ina zaune ni Adamu ina zaune a inda kika amsa wayar da Atika tayi miki tana baki labarin Mama ta fadi har ta samu stroke tana asibiti, ba ki ji kunyata bare tsorona ki ka bude baki ki ka cewa Atika ke duk abinda zai samu Mama ba zai dame ki ba.

In da abin zai tsaya ne a kanta ita kadai ba zai shafi ‘ya’yanta ba. Yaya Habiba ta koma dakinta aka ce miki eh, ki ka ce to madallah.

Kina nufin don naki rabuwa da ke kamar yadda Mama tayi min umarni shi kenan hakan yana nufin bana sonta ko bana ganin girma da darajarta?

Idanuwanshi suka baiyanar da bacin rai mai tsanani wanda yayi dalilin da náyi magana naja bakina nayi shiru saboda a yanzu tsoroni abinda zai taba lafiyar jikina nake yi.

Na kuma san na saki baki na fadi maganganu iri-iri akan Maman a gabanshi ban taba sanin basa yi mishi dadi ba sai yau.

Rainà ni ki ka yi yasa kike iya fadin mugun abu a kanta a gabana ko kuwa ke din kin manta ne cewa ita din madadın uwa take a wurina? Shiru nayi baniya ce mishi komai ba.

Ibrahim ba zai zauna min a gida ba na gaya miki, don ba za su nakasa min yar uwa suyi sanadin shigarta cikin musibar rayuwa ba, sannan su zo min gida su zauna don sùna gadarar ga ki a gidan, in da ba su lalace ba in da ba su maida kansu haka da ba su zama abin da suka zama ba Babanku zai rinka yi mata abinda yake yi mata a yanzu?

Wai har yana gayawa mutane ita din macuciya ce shi da ita wa ya cuci wani? A ina aka ce wa namiji ya bari mace ta…Da sauri na kátse Ado.

Na ce, a’a ya ya haka? Me Babana ya yi maka? In anyi wa Mama…Kan in karasa ya wanke ni da mari, ai ba za ki sake zaginta a gabana ina kallonki ba, ai kun riga kun kure ni.

Yau ma Baba Tanimu ne ya raba ni da Ado. Kwanaki kadan bayan nan ma aka sake masifar Ado ta ishe ni naje na kai karar shi wurin Baba Tanimu ya hada mu ni dashi duk gaba daya bayanin akan Ibrahim ne.

Baba Tanimu ya ce to ke ki bar shi mana kawai ya kore shi ba yarshi ce ta haife shi ba? Na ce a’a Baba ba wurin shi yazo ba, wana ne sune ya’yan Babana manya ba asan in da dayan yake ba, shi yazo wurina a kore shi, in shima ya tafi bai sake dawowa ba fa?

Na yarda tunda gidán shi ne yasa mishi ka’idar zama’ in bai bi ba shi kenan, amma ba kora ba, in an bar shi ma in yaga zai tafi sai ya tafi don kan shi.

Baba Tanimu ya ce, gaskiya’ ne, kasa musu ka’ida ita dashi in basu bi ba ni ne zan kore shi ba kai ba.

Ado ya ce za a rinka salloli biyar dashi a Masallaci, Baba ya ce ko ba ka nan zan sa maka ido kan wannan, ban yarda kuma asha ko da sigari ne ba a cikin gidana, balle wani abinda yafi sigari.

Kina ji? Baba Tanimu ya tambaye ni na ce mishi eh Baba. Sai me kuma ya sake juyawa wajen Ado, Adon ya gyara zama ya ce, zama kawai zai rinka yi a gida ban da fita in kuma ya ki ya fita to kar ya dawo.

A haka maganar ta dan lafa ni kuma na tasa Yaya Ibrahim a gaba kullum ina kaf-kaf-kaf dashi ina tsoron kar yayi abinda za a ce yayi laifin kora tunda maganar tana gaban Baba, ba zan iya jayayya da shi ba.

Kwanaki kadan da ya yi yana tsare a gida sai da jikinshi ya canza ya soma yin kyau.

Rannan ne nemi Yaya Ibrahim na rasa, ban ganshi ba baya cikin gida ba kuma lokacin Sallah ba ne balle in ce yana masallaci.

Na kasa buda bakina in tambayi wani shi, don kar ya yada maganar cewar ba a gan shi ba har Ado ko. Baba suji, don haka naja bakina nayi shiru nayi ta leke-leke ko zan hango shi har dai na hakura.

Ina zaune tsakar gida sai gashi ya shigo layi yake yi nayi salati mai karfi ya waiwayo ya kalle ni “Anti Humairahhh ki shouumn kawai kin gane? Ki rabu da wannan mugun mutumin muuu dah yah zan… Nayi maza na tura shi dakinshi na tura mishi  bincin shi wanda sakwara ne da miyar taushen da aka yi da kayan ciki da busasshen kifi naja kofar na rufe shi a ciki ina ta addu’ar kar Ado ya dawo ya ce ina yake?

Washegari da Asuba Ado yana fita Masallaci da yake yana fita da wuri tun kafin kiran Assalatu nayi maza na tashi naje na shiga dakin Yaya Ibrahim.

A kwance shame-shame na same shi, yayi filo da sakwarar da na mika mishi, ko loma daya bai yi ba, a tsorace na tashe shi ya wastsake na nuna mishi binda yayi, shima ya tsorata.

Na sa shi yayi wanka kafin ya fita Masallaci aka yi sallar Asuba dashi ya shigo gida ya gyara dakin nashi.

A haka ina zaune da Yaya Ibrahim kullum ina kab-kab-kab ina kuma addu’a har nayi sa a zaman nasa ya mike ya soma wattsakewa daga abubuwa masu yawa.

Natsuwa ta soma zuwa mishi, har dai daga baya ya yarda ya koma makarantar addini da ta boko. Ado ya yarda da zamanshi a gida, ya saki jiki dashi ya soma jan shi zuwa gona da ma wuraren harkokinshi, har ma daga baya yake iya tura shi ya wakilce shi kan al’amura masu yawa.

Shekaru goma cif sun cika daga wannan ranar ta daidaituwar al’amuran Yaya Ibrahim.

Shekaru goma sha biyar kuma kenan na aurena da Ado, auren da kaddara da rabo na abubuwa masu yawa suka tilastawa Mama yin sanadin shi.

A yau ni din mahaifiyar ‘ya’ya biyar ne cif na Kawu Ado, cikinsu akwai namiji guda daya Baba Yahya, sai kyawawan ‘yan mata guda hudu, Umamatu ita ce ta farko, sai Baba Yahya bayanta ne kuma muka samu Zainab da Khadija da Fadima.

Wadanda mahaifinsu ya zaban musu sunayen nasu saboda kaunar da yake yi wa yayarsu Umamatu, don haka ya ce to tunda a tarihin da ya karanta na Umamatu Zainab yar Annabin Rahama ce mahaifiyarta ita kurma Zainab kowa yasan ‘yar Nana Khadija ce.

Sannan ita Nana Fadima sonta da take yi wa Umamatu ne ya sanya ta bar wa mijinta wasiyyar auren Umamatu bayanta, to bari ya jera mana sunayen.

Haka don neman albarkar masu sunan na ce mishi to Kawu don haka Ado bai taba yiwa kowa takwara ba tun bayan wanda yayi wa Baba Yahya.

Duk kuma da wadannan ‘ya’ya biyar din da ke gare ni shekaru kusan biyar ne kuma yau rabona da haihuwa a dalilin son miji da neman gindin zama a wurinshi ya sanya ni shiga harka ta bin tsarin iyali.

Mahaifar tawa a daure take, watakila in ban dá haka da yanzu an wuce biyar an kai shida ko bakwai ko ma takwas ko da yake dai ina da sani da kuma imani na cewar babu wani wanda ya isa ya hana wani zuwa duniya a lokacin da kaddarar zuwanshi tazo.

Don haka na yarda nayi hakan tunda abin da maigidan yake so in yi kenan ni kuma kullum a kan bin ra’ayinshi nake matukar dai bai zamo sabo ba tunda nasan ni din ni kadai ke gare shi a gida ko a waje ba mai leke-leke ba ne.

Yadda na zamo mahaifiyar ya’ya biyar a cikin gida, to a waje shima mai gidan al’amura masu yawa ya sanya a gaba farko dai a yau shi din shi ne ‘Dr. Ado Sulaiman’, don kuwa digiri uku ne da shi.

A yanzu yana aiki ne tare da hukumar inganta ilimin makarantun primary ta kasa. Shi ne kuma mamallakin shahararriyar gonar nan ta “HUMAIRAH FARM’.

Wacce ita ce kadai gonar da a nan kurkusa tayi fice wajen bayar da kayayyakin amfani irin na lambu, rani da damina, irin su (Brocooli, Beetroot,Asparagus, Aborigine, Cabbage, Kore ja, ko na Chinese, carrot, ganyen celery, cucumber, lettuce, da abubuwa masu yawa da suka danganci lambu, ga kuma ‘ya’yan bishiya irin su gwanda, abarba, lemo, gwaiba, da makamantansu, wadanda duka ana’ tafiyar dasu ne bisa tsarin nomna irin na zamani.

Haka nan wannan babbar gona ko kusa harkarta da dawainiyarta bai fitar da Ado daga cikin harka ta noma damina ba, wanda da shi dama ya fara.

A yanzu shi din manya-manyan gonaki ya mallaka na noman masara, dawa, wake, ga kuma fadamun noman shinkafa da rake wadanda mutane da yawa suke taimakon shi tafiyarwa.

Amintattun yaran da ya rike irinsu Bala wanda bayan kammala hada haddar Alkur’aninshi, Ado ya tura shi ya dan karanci Boko har ya zamo ya mallakii ilimin digiri akan aikin gona da kuma wasu yaran da ambatonsu zai y yawa…

Ina zaune cikin katafaren gidan da sanda na yi wa Ado rakiya zuwa kasar Singapore ne na dauko sanfurinshi bana komai na aikin hukuma bayan kammaluwar karatuna na N.C.E. nayi aikin karantarwa a makarantar primary ta Dabai na tsawon shekaru bakwai.

Ado ya bani umarnin’ ajiye aikin don in zauna a gida in yi aikin da yafi kowanne dacewa da ni, wanda yafi kowanne zamo min dole don shi ne in ban bayar dashi ba za a tambaye ni.

Shi ne aikin tarbiya, tarbiyar ‘ya’yan da ke gare mu wadanda ba biyar din da na ambatan wa kaina ne kawai tarbiyarsu ta hau kan nawa ba, manyan yanmata kadai guda hudu ne da ni ga Umamatu ga Hindatu ga Nusaiba ga ‘yar gidan Furerah da ta Haifa bayan haihuwarsu da shekara daya har tayi min takwara da ita.

Da zan taso duk na hada su muka dawo a maza kuma ga Usman sai Baba Yahya sai kuma wasu yaran da Adon ne ya kawo su gidan to ga kuma su Nana.

Bisa wannan dalilin ne maigidan ya zaunar dani yayi min gamsasshen bayanin da ya sanya ni gamsuwa da barin aikin nawa na zauna a gida nake sa mana ido kan al’amarin tarbiyar ya’yanmu.

Ganin da yayi na hakura da albashin nawa da nake samu wanda yasan amfaninshi wurina yana da yawa, tunda yasan ina da iyaye da ‘yan uwa da dangi wadanda nake tafiyar da al’amuran da ke tsakanina da su na zumunci ba tare da shi yasan yadda aka yi ba.

Sai yaga na hakura na bari na kuma ja bakina nayi shiru, ban taba tambayar shi yaya za ayi ba? Ya sanya shi yi min tukuici da gonar HUMAIRAH FARM.

<< Mijin Ta Ce 44Mijin Ta Ce 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×