A’a-a’a to mu kam barî mu tafi, su Ruwailah suka soma zare jiki suna shiga suna gaida Mama daga can kuma sai su wuce, ta sake kallona cikin natsuwa ta ce min.
Sai dai kiyi hakuri Anti, ko kuma ki mike kiyi ta dukana amma zan gaya miki cewar wannan kishin naki bai dace da ke ba, don kuwa yafi kama da kishi irin na jahilan mata, ba matan da suka karanta addini suka san shi ba.
Ita kaddara yarda da ita ai sharadi ne na cikar Imani, kaddarar kuma wacce ka ke so ne da wacce ba ka so, kan ayi miki kishiya ai Anti Aliya aka fara yi wa ba kya nan ne lokacin yasa baki ga bikin da muka yi ba, ita irin kishin Innarmu take ji ke kuwa kina yin irin na Mama.
Na kalli Sa’a cikin tsananin fushi na ce, ranki zai baci fa, ta ce kiyi hakuri.
Ado ya shigo, Sa’a tana ganin shi ta soma murmushi, Yaya ashe kana gida? Ya ce, mata eh, yasa hannu ya dauki danta ya rungume a jikin shi, me yaron nan yake ci ne haka?
Ta taya shi murmushin da yake yi ta ce ai shekaran jiya naji Barisster yana cewa wai wannan yaron irin Baba Yahya zai yi. Ado ya kyalkyale da dariya ya ce, ina ruwan Super D.
Ta gaishe shi cikin ladabi tana tambayarshi yaya ashe hidima tazo? Bai amsa ba ya dan kalle ni kun tattauna ne da yayar taki? Ta ce uh uhn ai ni ba wurinta nazo ba, ba ita nazo wa bukin ba.
Ni kika zowa kenan? Tayi maza ta ce mishi eh, ai shi yasa nazo da wuri don in akwai wani abin da za’a shirya mishi sai a shirya. Dadi ya kama Ado ya ce to muje wurina mana ki sauka a can ai akwai daki, kya so ki zauna a nan?
Ya mike ya daukan mata danta ita kuma taja jakarta suka tafi, ina kallonta sai da ta shiga wurin
Mama ta dade kafin ta fito ta shiga wurin nashi, a zuciyata nace lallai Sa’a ba karamar mara mutunci ba ce, amma barta ni da ita ne.
Daga can nesa ne kawai nake hangen Sa’adatu da irin kaiwa-da-komowan da take yi tsakanin wurin Ado, wurin yara, da kuma na Mama da ma kuma ita din aminiyar yara ce.
Amma ni ko kallon wurina bata yi, sai mamakinta nake ji wato ita wannan saboda Ado abokin mijinta ne shi kenan ta koma bangarenshi kenan?
Wajen karfe hudun yamma sai ga Hajiya Aliya da ‘ya’yanta guda biyar maza biyu mata uku da kannen mijinta biyu yan mata ya’yan amaren Hajiya Kubrah.
Tana ganina ta kalle ni ta ce yaya haka Anti? Nayi murmushi na ce babu komai Aliya, me ki ka gani? Ta kalli ‘yanmatan da tazo dasu har da ya’yan nata ta ce wa Umamatu da tazo gaisheta kuje tare ki kuma maida su yan gida tayi murmushi ta ce Inna ai ba baki ba ne ta ce eh amma ki kara, suka tafi.
Sa’adatu ta hauro saboda ganin zuwan Aliyan, na gaya mata abinda Sa’an tayi tun kan Sa’a tayi magana Aliya ta kalle ni ta ce haba Anti, in kika ce haka za ki yi ai mu da uwarmu ki ka tozarta babu irin mutanen da ba mu tarawa yaya Ado a gidan nan ba sanda yayi hidimar Sa’a ya kuma yi mana goma shatara ko ma ashirin da tara ta arziki.
Sai kuma yanzu hidima tazo kan shi zai yi kice za ki tsuke fuska ko ayi tashin hankali da ke? To Gaskiya ba ma ciki, shi kishin fa ba yadda kika ga na gidanmu yake ba, ki kama mijinki kawai ki rike gam a hannunki, ba wai ki rike shi a jiki ki hana shi zuwa wajen wata matar ba.
Ki hanata hakkinta a’a ki bar mishi jikinshi yayi ta yawo yaje wurinta ya ji dadi yayi abinda yake so ya more, Ubangiji ne ya halatta mishi ita, amma ke kina rike da zuciyarshi in da duk yaje yana tunawa da ke in zai yi magana sunanki zai ambata, in zai fadi alheri naki ya sani.
Sannan ko mu yanzu a gidan namu ba ki ga yadda Gambo ta maida gidan ba, Zubaida da ‘ya’yanta ai basa gabanta, tuni ta sake hada girkin gidan tunda Mama ta fita ta bar musu gidansu ke baki ga yadda Baba ya yi gwanin kyau ba?
Sa’a ta ce a to, shi Yaya Ado ma ba zai takuru ba tunda ba ki ga abinda ke cikin wurin nashi ba wal kawai in kin ganshi sai kin yi mamaki, gashi kuma naji yana maganar kayan daki ina jin shi ne mai yi.
Na ce to ba gashi ba tun ba a yi auren ba zai fara zalunci. Aliya tayi maza ta ce zalunci anti?
Yanzu ke akwai wani abinda Yaya Ado zai yi wa wata mata ki ce ya zalunce ki?
Sunkuyawa fa yayi ya yi noma yana yarfe gumi ya tara kudin ya biyawa ummar mu kujera taje ta sauke faralinta, bayan nan ki ka biya mata da kudin aikinki, yazo ya mallaka miki gonar da a yanzu duk shekara ki ke kaita Ummura da watan Azumi kin kai Baba kin kai mai babban allo.
Ba daga gidanmu ki ka zo da gonar ba sannan in kin manta in tuna miki ba ki zo gidan shi da kayan daki ba, kuma in ba ki sani ba in gaya miki ba fa tsoronki yake ji ba.
Yana jin kunyar ki ne saboda kin yi sa a yana sonki yana kuma ganin darajar iyayenmu, to taimake mu ki bar shi a haka kar ki kure hakurinshi don ko su Ahmad da suke ‘yan uwanmu ne in suka balle hancin tsiya ba dadinsu ake ji ba. Sa’a tayi mazá ta ce, na dai gode.
Ado ya shigo daga waje da sauri da alamar yaga zuwan nata, Hajiya Aliya ashe kema kina tafe tun yau? Ta ce eh, Gambo ce ta roke shi ya bar ni in zo da wuri don in kawo maka wannan sakon.
Sako? Yayi tambayar cikin tunani, ta ce eh, tayi maza ta jawo katon akwatin da ta zo dashi wanda nayi zaton kayanta ne da na ya’yanta a ciki, tana bude shi ta soma zaro atamfofi tsala-tsala duka super guda shida, manyan lesuna hudu da kuma shaddoji masu tsada guda biyu.
Tana gama zaro su ta ce wai in ji ta a kawo maka ka zuba akan na lefe.
Wani irin matsanancin dadi ne ya kama Ado, a hankali ya nemi wuri ya zauna a bakin kujcra cikin natsuwa ya ce, Aliya, tayi maza ta amsa na’am Yayya,
ya ce mahaifiyarku tana da girnma a wurina, saboda ita din wata irin mata ce da samun irinta yake da wahala.
Ina matukar girmamata saboda halayenta na girma da mutunci ga ta da adalci ga na kasa da ita, amma Humairat bata gane abin da nake nufi ba. Naje na same ta ita da mai babban allo nayi musu maganar zan yi aure amma ina so suyi wa Humaira magana don bana son matsala a cikin iyalina.
To kan akai ga hakan ga Mallam babu shi, ni kuma a yanzu ba zan je in kai kararta wurin Gambo ba, zan bar Gambo kawai tunda nasan ita bata manta mahaifinta ya rasu ba, kamar yadda ita Humaira ta manta.
Aliya tayi maza ta ce, itama bata manta ba Yaya, ya ce ta manta tunda ta bude baki ta zage ni ta ce in tuna mata da adalcin da na taba yi mata don ita bata san shi ba.
Aliya tayi salati ta ce, in ita ta mantra su mu ba mu mance ba, ba kuma zamu mance ba. Amma maganar zagi kar ka rinka fada yaya, ya ce kar in ce ta zagen Aliya! Ta zagi Mama a gabana ta kuma durawa ya’ yana ashar a gabana?
In haka ake karatu zan barta tayi ta zaryar makarantar addini? Aliya ta ce ai matsalarmu kenan yin aiki da abin da muka sanin gashi kuma kullum ana gaya mana cewar mu mata babu abin da yake saurin kai mu wuta irin kafurcewa ni’ ima.
Amma kayi hakuri ya ce to yaya zan yi? Alamar dai ranshi ya baci sosai da abinda nayi mishin.
Gaba daya ‘yan uwana har Atika da ta iso bata goyi bayan yadda naso mu yiwa bikin ba, itama cewa tayi mutuncinmu zamu zubar, don haka rungumar hidimar suka yi da hannu bibiyu suka kankane komai, wanda ba haka Mama taso ayi ba.
lta taso ne a ware ga ‘yan uwan Ado da nawa sai ita ta jagoranci hidimar Ado sai taga ba haka ba ne.
Dangin Innarmu da na Babana da suka zo min bukin ba za su lissafu ba, su Habiba da Anti Kaltume ma muna hade dasu, Sha’awa da Suwaiba ne suka koma wai su suná dangin miji.
Ga kawaye na zamani, kawayen da aka yi bayan daula ta samu, don haka hidima sosai aka yi.
Kane-kanen da Sa’a tayi kan hidimar Ado ba karamin taimako ko amfani yayi min ba, ba don ina ganin ko za a zarce ni da wani abu ma to ba wani mai yawa ba ne sai dai duk da haka zafin yana nan a can ciki zuciyata tafasa take yi.
Wani lokaci ni da kaina ma mamakin kaina nake ji, saboda a farkon rasuwar mai babban allo na dauka babu wani abin’da zai sake samuna in ji zafinshi, sai gashi maganar auren Ado yayi min wani irin dukan da ya kidimar dani.
Ya mantar dani wasu abubuwa masu yawan gaske, kai kishi al’amarin shi yana da girma, sai dai kawai hakuri. Tsananin bacin rai ne yayi min yawa, bakin ciki ya addabi zuciyata yayi dalilin da ya sa na kame bakina na kulle shi nayi shiru na daina fadin komai in ban da ‘la’haula wala kuwata.”
Hidima irin wacce Ado yayi tana da yawa, wane ta bukin Sa’adatu, da nake ta bada labari, iyaka dai kawai na sani ko da nake wurina a kammale ‘yan uwana su Habibah su Aliya, Atika, Anti Kaltume, Sa’a sune suke tsare da komai.
Anyi daurin aure an kuma ce min har sü Babana da su Baba Yahya da su Alhaji Maikudi duk sun zo wa Ado daurin auren.
Da daddare kúwa ana idar da Sallar Magariba amarya ta iso, duk wacce taga amaryar sai naji tazo tana fadin kai mazan nan sai fa a bar su kawai, ban dai san me suka gani ba.
Sannan koda nasan gidan Mallam Haruna da iyalinshi na kasa gane ita wannan yarinyar da aka ce wai sunanta Balkisu, saboda ni nafi sanin uwargidan gidan Hannatu da ‘ya’yan dakinta.
Wannan kuwa an ce yar amaryar gidan ce Mama wacce ko gaisuwa da ita ban cika yi ba, don ba kasafai ka ke ganinta a waje ba.
Taro ya tashi, Jama’a sai tafiya suke tayi saura wadanda suka rage saura kadan Hajiya Kubra ta shigo wurina tana murmushi, yau uwarki har da goggoro ta daura.
Nayi maza na tambaye ta wacce a cikin iyayen nawa? Ta ce wacce uwa ke gare ki da ta wuce Mama? Na tsuke fuska na ce Mama kuma Hajiya? Tayi maza ta ce eh, ita uwarki ce kar kuma ki yarda ki biye mata akan komai.
Kiyi hidimarki kawai, wannan yarinyar kuma kar ki yarda kuruciyarta tasa ki zalunceta, shi kuma mijinki ki kara mutunta shi don ki karawa kanki girma da daraja albarkar ‘ya’yanku ma ta karu, na ce to Hajiya na gode.
Dare yayi babu kowa a gidan, ina kibance kan gadona tun bayan fitar Ado daga dakin da yazo yayi min sai da safe, ban iya motsawa na tashi naje na kulle kofar tawa ba, sai kallon agogo kawai nake yi ina lissafin cikin zuciyata a sanin halin Ado da nayi yanzu ya gama kaza ne yana yin kaza.
Ina cikin haka ne kawai naga yarinya ta fado min daki da gudu a firgice kwarai take, tayi matukar tsorata da abinda ta gani, tsallake ni tayi ta wuce can bayana ta makure wuri daya.
Na waiwaya na kalle ta, bari take yi kar-kar-kar daga ita sai yar wata lalatacciyar shimi ne a jikinta, ga nonuwanta nan ba suma karasa fitowa sosai ba, Yarinya ce ‘yar karama da ba ta wuce shekara sha hudu zuwa biyar ba.
Kamar dai ace sa’ar Umamatu, kyakkyawar yarinya don kuwa zafin kishinta bai iya rufe min ido ya hanani ganin kyan nata ba. Na tuna sanda nima nawa nonuwan suke kamar nata..
Cikin zuciyata na ce, kai lalle Ado! Ado namiji ne, yau ne na gane me yake nufi da yawan ambaton kanshi namiji da yake yi, sai gashi ya shigo yana daure da rigar baccin da ke jikinshi da belt. Muna hada ido dashi ya sakar min wani lallausan murmush, a zuciyata na ce shi ma yasan ya cuce ni, ya gama da ni.
To zo mana Humaira, ya juya ya fita ban yi jayayya da shi ba na bi bayanshi zuwa tsakar gida dan fito min da yarinyar nan sai ki turo kofarki ki kulle, ai dare yayi me ki ke yi har yanzu idonki biyu?
Na harare shi na çe, kai me kake ? Yayi murmushi ya ce to naji fito min da ita don kin ga na riga nayi niyya zan shiga dakinta. Na ce to ai bani na kawo ta ba, ka shiga ka dauke ta mana.
Cikin natsuwa ya ce ina jin kunyarki ba zan iya ba, shi yasa nake so kiyi in adalci ki bani ita. Na wuce shi naje nayi kwanciyata gabana sai faduwă yake yi, kar dai Adó ya shigo min dakin nan ya ce zai fitar da yarinyar nan don ban san abinda zai faru ba.
Sai aka yi sa’a har gari ya waye bai shigo ba, sai dai kuma ina ta jin zirga-zirgar, shi nayi zaton ko lemon tsami yake nema da jar kanwa bai samu ba.
Washegari da safe na kammala abin da zan yi na sallah da jan carbina na mike zan fita don shiryawa yara abin karyawa da tafiyarsu makaranta.
Sai na kalli Bilkisu na ce mata ke je ki đakinki kin ji, yanzu ba zai zo miki ba balle ya taba ki tunda gari ya waye ta ce min to.
Tuni su Nusaiba suna kicin suna kokarin kammala komai, don sallamar kannensu kafin suma su sallami kansu, saboda sun riga sun saba ko ban fito ba ba za su yi komai don haka ina shiga na kammala suka gama suka tafi.
Suna fita suka bar gidannan sai kawai na hango wucewar Ado zuwa dakin yarinyar nan kan kace meye wamnan sai kawai na jiwo ihunta a kidime.