Jikina ya rinka rawa nayi matukar kidima na gigice na rinka jin tanfar wani abu yana yi min yawo a jiki, ya rasa hanyar fita, waiyo! Wayyo!! Wayyo!!! Abin da kawai nake fadi kenan zuwa can nayi sa’a wani tunani yazo min na bar waiyo na koma ‘lahaulah’.
Ban san tsawon lokacin da na dauka ina cikin wannan kidimar ba, sai kawai na ji ni jike sharkaf da gumi, na mike naje nayi wanka na yiwo alwala nayi nafila raka’a hudu nayi addu’o’i na shafa na zauna gaban madubi ina shafa mai ina kallon kaina a madubin.
Ko da bani da nonuwa a tsaitsaye ni din kuma ba zai yiwu ace Ado zai yi wuju-wuju dani ba, a cikin ganiyar kuruciyata nake na kuma riga na zama mace mai daraja wato dai mata irin na zamani da kana ganinsu ba sai an tsaya yi maka bayani ba.
Don haka na tsayarwa raina da cewar da in wani ya ce bai sonka to lokacin ne wani kuma zai ce shi da kwana yake kaunarka, don haka ba zan lamunci irin wannan matsanancin bakin cikin ba daga gare shi, don zai iya nukurkusani ya karya min zuciyata.
Kwalliya sosai na tsaya nayi ba don komai ba, ba kuma don kowa ba sai don in tabbatar wa kaina cewar kuruciyar da nake kirawa kan nawa tana nan.
Daga ido nayi na kalli agogo da nufin in ga lokaci don fitar da nake son yi in bar gidan ya gama abin da yake a dakin ya fito bai same ni ba, sai kawai naji gabana ya fadi
Sha daya da rabi ne lokacin dora abincin ranar gidan yayi, gashi mai girkin bata zo ba, na ce tayi hutun kwana biyu don ta huta wahalar hidimar da aka yi kenan, in har ban tsaya ni nayi girkin ba yara za su dawo gida basu samu abin da suka ci ba.
Kan haka na fito na shiga kicin na soma aikina abincin gidana bakina da zuciyata basu daina ambaton lahaula’ ba.
Duk da ban shiga kicin din don kowa ba sai don yaran da nake gudun kar su dawo gida basu samu abincin da zasu ci ba, ban kuma iya yin girkin yaran kawai na fita na bar sauran mutanen gida ba.
Don ban saba ba, ba kuma zan iya barin iyalin gidana da yunwa ba, don haka sai kawai na shiga aikin girkin sosai, gefe daya ina yin dafaduka mai hade-haden kayan lambu gami da naman rago a ciki.
Daya gefen tuwon shinkafa ne miyar agushi, wanda nima shi nake sa ran zan ci don in rage matsananciyar ramar da nayi a kwanakin maganar aurennan zan ci abincin girki na kwana biyu.
Na sake yin farfesun kayan ciki da na yi wa hadi sosai na kuma yi na kaji saboda Balkisu, a dalilin nanata min da zuciyata take yi cewar ita yarinyar bata yi min komai ba, bata da wani laifi a wurina, ba ita ta kawo kanta ba, ba ita taga mijina ta ce tana so ba.
Sannan kwata-kwatanta bata wuce Umamatu ba, ashe kuwa ko don Umamatu ta samu wadanda zasu yi mata adalci a rayuwa zan yi wa Bilkisu.
Na hangi fitowar Ado daga dakin ban san sanda bakina ya ce mishi dan iska ba, sai da na tuna mijina ne nayi maza nayi tayin istigfari.
Yara suka shigo da gudu suna murnar ganina a kicin din su, na shiga zuba musu ina mika musu da kananan na fara kafin na isa kan manyan.
Ado ya shigo ya same ni ina magana da su Umamatu dukansu saboda na lura in ba yi nayi da gaske ba shiga za su yi cikin lamarin da ba nasu ba ne, suyi kane-kane.
Babu wani zumudin bukin da suka yi sai ma da Sa’adatu tayi musu kaca-kaca ne suka je suka yi kwalliya. Nusaiba ai kun san Babanku yayi aure ko? Hindu ta ce eh Goggo, amma ai mun girmeta ma, na rage fara’ata na ce uwarku ce, ko kun girme ta zaku girmamata don matar Babanku ce, balle ma ba ku girme ta ba, za dai kuyi sa’anni ne kawai.
Ina maganar ina zuzzuba musu farfesun a kwanuka daban-daban ina ajiyewa, ga kuma abincin shima duk na zuba musu shi na sake bude oven na dauko wata katuwar kaza da na yi wa gashi na musamman na hada na sake jawo flask na cika da ruwan tea mai citta na ce ku diba kuje ku same ta bakuwa ce ku sata taci abinci ta kuma sha tea suka ce to, suka diba suka tafi.
Ado ya matso kusa dani, nawa abincin fa? Ban iya yi mishi magana ba, na dauki na Mama na tafi wurinta sai da nayi sallama sau biyu bata amsa ba, nasa kai na shiga tunda nasan tana ji na.
Sannu Mama, ta ce yauwa sannu kadai, ta bude ido sosai tana kallon irin kwalliyar da nayi, na zauna ina bata abinci, Ado ya biyo ni yana tambayata ina abincin shi? Kan in yi magana Mama ta ce mishi har ka fito daga dakin amaryar ne?
Shima bai amsa ba balle ni, to kaima kenan ana jin haushinka ba a baka abinci ba to balle kuma ita wannan aure ai fata dai kawai Ubangiji yasa ba asarar dukiya aka yi ba, tunda ban ga alamar yayi wani tasiri ba.
Na fito daga dakin Mama na dawo nawa nayi maza na dauki gyalena zan fita, sai ga Ado ya shigo ina za ki Humaira? Maimakon in tsaya gaya mishi inda zanin sai kawai na soma yi mishi kuka.
Kuka kuwa mai tsananin gaske, saboda bakin cikin shi ya ishe ni, kiyi hakuri, hakuri yake ta bani sai da ya ga na dan natsu sai ya ce min ban fa yi miki wani aibu ba Humairah, ban kuma zalunce ki ba, ba kuma zan zalunce ki ba.
Saboda ban yi aure don na gundura da ke ko kin ishe ni ba, nayi ne don ina son karawa yin hakan kuma ba laifi ba ne, gode ni’imar da aka yi min nayi, na roki alfarmar ki bi ni mu zauna lafiya kar kiyi min abin da kika san da can ba kya yi min.
Kar ki fita ba da izinina ba, zan hakura da komai amma ban da wannan, in ki ka dan yi hakuri da ni kadan nayi miki alkawarin zan yi mai yawa da ke.
In ki ka dan kawar min da kai ki ka yi min kawaici na miki alkawarin zan ji kunyarki, in kuma yi ta girmamaki, saboda ke din dama kina da girma a wurina. Yanzu muje ki bani abinci yunwa nake ji, nace ai ya kare, ya sake kallona cikin natsuwa kafin ya ce min Humairah kenan.
Kina ganin idan ki ka azabtar dani da yunwa da akwai wata riba da hakan zai kawo miki? Ai yanda kika shirya abin da ya dace ki ka tura wa Balkisu tare da yara sa’o’inta don su debe mata kewar zaman gidan su saboda kin yarda bata yi miki laifin komai ba, ba ita ta kawo kanta bani naje na kawo ta.
Haka ya kamata ki yarda nima da na kawo ta ba laifi nayi ba, Humairah. Sannan ko da nake ni na ajiye ku dukanku kin fi kowa sanin ina gudun bacin ranki, ina tsoron ganin fushin ki.
Ina yin komai ko barin komai don neman zaman lafiya dake, to na roke ki kar kiyi amfani da damar da ki ke da ita a kaina don ki kuntata min ki hana ni morar halal din da aka halalta min.
Kalaman nashi suka dan sani natsuwa, naje na dauko daya kazar da na bari a cikin oben din na kai mishi falonshi tare da ruwan matsattsen lemo, to zauna mana na ce mishi ina zuwa na dawo wurina ina shiga wayata na dauka saboda rurin da take yi.
Gabana ya fadi kar dai wani laifin aka je aka cewa Gambo nayi take nemana? Jikina a sanyaye na soma amsa wayar tata, sai naji ta ce min, taro ya tashi lafiya? Na ce lafiya Gambo.
Ta ce, to Ubangiji yayi miki albarka, ke da zuriyarki, ya saka miki da alheri, ya kuma baki hakuri da juriyar rike girmanki, na ce to amin Gambo.
Muka dan fara hira da ita har na dan saki jiki na gaya mata wulakanci da cin mutuncin da Ado yayi min, na shiga dakin matarshi da rana tsaka, sai da tayi ajiyar zuciya kafin ta ce min.
Kar ki rinka kokarin shiga tsakaninshi da ita, babu ruwanki kamar da ido kawai kan al’amarin nasu kamar yanzu ne kawai sai ki ka zafin shi yana ta raguwa a zuciyarki.
Yafi Yafi ace za ki rinka damuwar da su ku rinka samun matsala ke dashi har ita yarinyar tayi wayon da zata gane kina da damuwa a kanta, sai ta raina ki. Kin ga abu ya baci kenan, aa ce haka ne Gambo.
Muka dan yi shiru kadan sai naji ta nişa ta ce ai kishiya zafi ne da ita, sai kayi hakuri in ba haka ba sai ki ga ka gudu ka bar ladanka.
Na ce ai aima dazu ji nayi kamar in gudun, tayi maza ta ce kar ki fara ai gidanki ne kiyi mata adalci, kawai Ubangiji zai hore miki zama da ita na ce to. Dama Gambo ta bani sosai na na saki jiki in yi magana da ita.
Magana kuma ba irin ta uwa da ‘ya ba kawai, a’a har da zancen kawa da kawa aminan juna tana yi min magana in muka soma gaisuwa zata sako min maganar kishi’.
Watakila don tasan shi ne babbar matsalata ta lokacin ni kuma da yake na riga na kidime bana iya boye mata zafin da nake ji, in yi tá gaya mata abinda nake ji da yaddda zuciyata take tafarfasa in fadi maganganu masu zafi a kanshi.
Rannan ma dai da’yake na riga na tunzura da yawa saboda abin da nake ganin yanayi da tayi min wayar ce mata nayi, kai ni kam Gambo to me zan sake yi da Kawu ne kuma? Me zai sake yi min in ga ya burge ni kuma a rayuwar nan Gambo?
Ai ni kwata-kwata gaba daya ya riga ya fita kaina babu abinda na tsana irin in ga wulgawarsu ko in ji maganarshi balle in gan shi ya shigo in da nake, sai in ji kamar in mike kawai in rufe shi da duka in yi ta duka.
Dariyar da tayi ne yasa na katse zancen nawa, nayi shiru, me yayi miki da zafi ne haka Baban Umahman? Na dan yi murmushi saboda jin sunan da ta kira shin na ce bare-barenshi ne yayi yawa Gambo.
Ba ki ga irin rawar jikin da yake yi akan yarinyar nan ba, shi yasa ma na ce ni kam ko ya sake dawowa wurina ba zan sake sauraronshi ba, tunda dai abin nashi haka ne na hakura dashi na bar mata shi na yafe, suje can su karata kawai
To in ki ka yi haka ai ba kiyi mana adalci ba, nayi maza na ce kamar ya ya Gambo har da ke a ciki? Tayi murmushi ta ce, dani kai tsundum a ciki, ke din ai tanfar uwa ki ke a gare ni a yau, zaman lafiyarki da kwanciyar hankalinki a gidan aurenki yana nufin al’amura masu yawa a gare ni, don nasan shi ne kwanciyar hankalin ‘ya’yanki.
Ni nasan babu wani bare-baren da rawar jikin da zai yi akanta da har zai tsole miki ido, in ba kin bar abin da yake gabanki kin maida hankalinki a gare su ba. Me zai mata ya kai wanda ya yi miki?
Ai babu shi, maganganu masu dadi tayi ta yi min har dai na hakura na yarda da cewar wai duk abin da yake yin bai kai wanda ya yi min ba, amma ni kam in ban da Gambon ce ta gaya min haka da ban yarda ba.
Don gani nake tanfar babu ma in da aka taba yin irin abin da shi yake yi din. A haka sai gashi ya dawo dakin nawa, kashedin da ‘Gambo tayi min na cewar matukar ba-shi ne ya kawar da kai daga gare ni ba, to kar in bijire mishi dashi nake shirin yin aiki.
Don haka nake ta fatan shi din da kanshi ya fita hanyata tunda ni kam a yanzu nafi so ya bar ni kawai.
Zo nan kiji Maman Umamatu cikin zuciyata na ce wani wayon zai yi min don kuma ya kan kira ni Maman Umamatu ne a irin lokutan da yake-ganin tanfar al’amura suna shirin cabe mishi a tsakaninmu.
Ai babu wata amaryar da zata yi irin amarcin da kika yi a hannuna, Humairah ke ce fa, ya. Soma lissafo min alarmura masu dadi da suka gudana tsakanina da shi a lokacin amarcin da muka yi sannan ya kalle ni ya ce to a yanzu wanne nake iyawa a ciki?
140
Sannan ke ce Humairah da na kamu da sonki sai na iya tsayawa na nunawa kowa har da wadanda bai kamata in yi musu wannan tsaurin idon ba, cewar ke din ke kadai nake so, ke kadai nake bukata.
Zan kuma iya barin kowa saboda ke a yanzu wa zai sani in yi irin hakan? Ado ya soma lissafo min al’amura da tun ina jin shi ne kawai har ya soma sani murmushi har ya sani na hakura na fidda komai çikin raina nasa hannu biyu na karbi al’amarin aurena.
Shi da kanshi Ado ya fahinta tare da sanin cewar Gambo tayi tasiri mai yawa a cikin harkar zamantakewar rayuwar aurena dashi da kuma amaryar da yayi, don haka kullum a cikin girmamata yake, kullum kara ganin mutuncinta yake yi.
A kullum kuma in ya bude baki zai fadi wani abu game da ita, to alherinta da karamcinta da adalcinta ga suruki shi ne abinda yake bayar da labarinta akai.
Rannan na wuni cikin farin ciki da zumudi saboda Ado ya gaya min zai tafi Abuja gobe, a dalilin hutun da ya dauko ya kare, dadi ya kama ni a zuciyata na ce zan dan huta da ganin mu’amallarshi da ‘yar yarinyar nan da ko kunyar tubewa a gabanta ba yayi, duk da karancin shekarunta.
Tsananin farin cikin nawa ne yasa na yi wa Gambo waya nake bata labarin da zai yi, sai ta ce min ba da ita zai tafi ba kenan? Nayi maza na ce, a’a shi kadai zai tafi, ta ce to me zata yi miki a gidan ba shi ita kawai ya tafi da ita, ai kawaici yayi miki kin ga kuma ki sata ta bishi da kanki yafi ace shi ne ki ka kure hakurinshi ya ce zai tafi da itan.
Ko ba zai iya yin hakan ba ne? na ce zai iya wanda yafi wannan ma, ta ce to kin gani.
Duk da bana son tafiyar tasu tare na daure nayi abinda Gambon ta ce in yi.
Dadi yayi matukar kama shi sai dai ya daure ya hadiye ya biyo ni dakina yana muzurai, to tunda kin ce dole sai an tafi da wannan yarínyar ai sai kije ki ga shirin nata wannan wani shiri zata iya? Na ce mishi to.
Duk da ni na ce ayi tafiyar tare da ita bayan tafiyarsu kuka nayi tayi, to ina ga in da shi ne kawai ya zartar da hakan? Bayan tafiyar tasu ne Gambon tayi min waya don jin lafiyata, na ce mata sun tafi Gambo amma nayi kuka.