Skip to content
Part 6 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Washegari kuwa da safe sai kawai ga katon cikin Inna ya baiyana tanfar dai dama wani abu take saka wa tana daure shi manyan riguna da hijaban da take sanyawa ma yau taki zani da riga ta saka da tayi wanka bayan ta gama kwalliyarta ta fesa turare ta kuma shiga zirga-zirga da kaiwa da kawowan da ta saba ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba kuma na ji Mama tana wani irin firgitaccen salati a tsakar gida.

Wannan menene ki ke son nuna min shi Fatima? Ciki ku ka yi ban sani ba? Lalle yau za’ayi abinda za’ayi a gidan nan, dama cin amanata kuke yi kuna satar kwanana?”

Inna kam bata tanka mata ba, aikinta kawai take yi. Mama kuwa sai faman zuba ashar take yi tana fadin “Su Habiba su fita su kira mata Babanmu, duk inda yake.”

Inna ta bar tsakar gidan ta dawo dakinta tayi zamanta, na kuwa san in ban da tasan ba zata taba Inna ta kwana lafiya ba, da ta gwada yin hakan.

Rannan cikin dare ba mu san abin da ya faru ba, iyaka dai da sassafe naga Babana ya shigo dakin Innata, na ji shi yana ce mata “To bukatarki ta biya Binta kin nunawa Mama cikinki kin tayar mata da hankali, kin yi sanadin da tayi yaji ta bar miki gidan, shi kenan ko?

Inna ta ce, “Tana da gata ne tana da wurin zuwa ni da ba ni da wurin zuwan ba gashi…” yayi maza ya katse ta “Muje can dakina sai muyi magana.” Inna tayi maza ta ce wa? Tafdijan.

Rannan Baba ko tsakar gidanmu bai leko ba, yana dakin Inna suna ciki su biyu gabadaya hidimar gidan ni aka bar wa har abincin rana sai bayan Azahar na ganshi ya fito ya shigo wurin shi yayi wanka ya tafi Masallaci.

Da ya dawo ya ci abinci ne na ji shi yana cewa, “Bari in je kasuwar in ga abinda suke ciki.” Ta ce mishi “To, a dawo lafiya.”

Har washegari Mama bata dawo ba, a dalilin Babana bai je biko ba duk da aiken da aka yi na ana neman shi, gidanmu ya zama gwanin dadi sai murmushi yake yi yana hirarshi maimakon da da kowane lokaci fuskarshi a daure.

Kwanan Mama biyu sai ga Baba Yahaya ya dawo da ita. Da alama shine yaje bikon ta kuma biyo shi duk da cewar da take yi shi din munafuki ne.

Mama ta dawo gida cikin wani karin zafin ita kanta dai kana kallonta kasan tana cikin bacin rai mai tsanani, ban da haka kuma kallo daya zaka yi wa fuskarta ka gane ashe ba karamin gumurzu suka yi da Baban namu ba kafin ta tafi.

A tsakar gida Babana ya zauna shi da Baba Yahaya da Maman suna maida magana, don Maman ce ta nemi ayi hakan duk da shi da ya kawo ta cewa ya yi to ni na tafi Allah ya kiyaye na gaba.”

Ta ce, “A’a ai gara ka tsaya ka ji abin da abokin naka yake yi.”

Mama ta maida bayanin komai dalla-dalla na yanda aka yi taga Inna da ciki alhalin ita din bata da kwanan miji. Baba Yahaya  ya kalle ta ya ce, bata da kwanan miji kamar yaya? Ta sake rattabo mishi wani bayanin har dai ya fahimci komai.

Sai dai maimakon yayi magana kan cin amana da zaluncin da ta ce anyi mata, na satan mata kwana a kai wa wata sai reshe ya juye da Mujiya.

Baba Yahaya ya soma yiwa Babana magana cikin bacin rai mai tsanani, ba laifin Hajiya Majadan ba ne duk abinda yake faruwa a gidan nan Alhaji laifinka ne.

Da ka kasa tsayuwa da kafafunka ka zama kaine mai zartar da hukunci a cikin gidanka. Yanzu ace an zartar da hukuncin hana ka baiwa binta hakkinta na kwana har sai ka saci jiki ka shiga wurinta don kawai bata girki?

Girkin me nene? Ita mace dole ne sai tayi girki kafin ayi aure da ita? Yarinyar nan guda nawa take da kake yi mata irin wannan zaluncin? Har yau din nan fa bata cika shekaru talatin ba tana da shekara goma sha shida ne aka baka ita.

Yaya za’a rinka gana mata azaba ana wulakantata kana kallo?

Maimakon ayi maganar da zata zamo mai dadi ga Mama sai kawai aka shiga yin wadda hakurinta ya kasa jura, ta shiga gaggayawa Baba Yahaya maganganu.

Ya kalle ta ya ce, ba laifinki ba ne shi ya bar ki ki ka zame mishi haka, da har ki ke ganin matarshi da ciki kina tuhumar shi yanda aka yi.” Yayi ficewar shi ya bar su nan a zaune.

Mama ta shiga bori da zage-zage, tana fadin wasu irin maganganu tamfar dai ba daga bakin babba mai shekarunta suke fita ba, Babana yana jin ta bai ce komai har lokacin mai tsawo.

Ban san yanda aka yi ba sai kawai na ji ya daka mata tsawa mai karfi ya ce, “Ya isa haka. Ya kuma ishe ki haka kin gane?” abin mamaki sai kawai na ji Mama tayi dib, tayi shiru. Cikin zuciyata na ce, “A’a ashe dai itama tana dan tsoronshi ina ma dai ace kullum irin wannan tsawar yake yi mata da wasu abubuwan da yawa, ashe da bata yi su ba.

Babana ya shirya ya fita ya bar gidan, ni ma naci gaba da abin da nake yi ban san abin da nayi ba sai kawai na ji Mama ta zo ta fincike ni tana jana zuwa dakinta.

Tuni na saki kwanon dake hannuna ya fadi na shiga kuka ina magiya ina bata hakuri, don kuwa nasan karonmu da ita a kullum nakan gwammace ta hada ni da Babanmu ya buge ni duk da tsananin dukan nashi don shi duka kawai yake yi min baya shake ni.

Mama kuwa bayan shaka ma sai ta ce sai ta hau kaina ta zauna.

Duk da magiyar da nake yi mata bata fasa ba, can cikin dakinta ta kai ni ta shiga gana min azaba tana yi kuma tana cewa wai ke ga shegiya ko? Na bar muku gida kuna murna ke da uwarki, to na dawo zan kuma yi maganinku.”

Gajiya Mama tayi ta kyale ni don kanta, babu wanda ya zo ya kwace ni, tunda ba ma kowa a cikin gidan in ban da Inna da sauran yaran gida, ita kuwa Inna ko meye za a yi min bata yin magana.

Da kyar na fito na dawo dakin Innata na kwanta ban iya fitowa ba sai wajen yamma. Ina fitowa su Habiba suka kalle ni suka kwashe da dariya suna fadin ta ji jiki ban kula su ba.

Tunda Mama ta dawo Babana ya sake kama fuskarshi ya tsuke tanfar ba shi ne ya wuni yana murmushi ba, jiya da shekaranjiya, yana dawowa ya shiga dakin Mama suka yi maganganunsu, kuma ya fito yazo ya shiga dakin Innata ranshi a daure.

“To ai sai ki fito kizo ki dora abincin dare ko, ko shima ba za kiyi ba ne za ki bar mutane da yunwa kamar yanda ki ka bar su da rana?”

Inna ta kalle shi ta ce, “A’ah ni ce kuma mai girkin ba gata ta dawo ba? Ya yi maza ya ce, “A’a ba za ta yi ba karbi girkinki kawai tunda dai taimakonki da aka yi aka hana ki yin girkin ya zama laifi a kanshi ake kiran mutane azzalumai.”

Inna ta kalle shi kawai ta juyar da fuskarta gefe, bayan taja mishi wani irin mummunan tsaki, sai dai kafin takai ga gama tsakin nata yayi maza ya wafce bakin nata da duka.

A kidime nayi tsalle nayi waje ina kurma ihu, saboda razana. Inna da ta wuni cikin wani yanayi da na kasa fahimtarta za kuma a buge ta, ban san yanda aka yi ba na gan shi ya fito yana cewa, in ba za ki fito kiyi girkin ba sai a zauna haka, waye mai kananan ‘ya’ya a gidan in ba ke ba?

Rikici yayi yawa a gidanmu, gaba daya an daina yin girki, Mama ta ki yi itama Innan ta ki. Gabadaya gidan babu dadi, gabadaya an shiga wani hali na wani yanayi.

Ni da kaina na kara shiga wani yanayi na tsoro saboda irin kallon da Mama ke yi min, Babana sai jin haushin Inna yake yi, yana fadin wai dama abin da take son ganin ya same shi kenan, shi yasa tayi abin da tayin gashi kuma ya ce ta karbi girki ta ki ta ce ba zatayi ba, tunda dama can ba a bata girkin ba sai yanzu?

Rannan da sassafe ya shigo dakinmu bai ma tsaya amsa gaisuwar da take yi mishi ba, ya ce mata, shirya kije gidan ku.” Ta ce, kai madallah, ya juya ya fita ni kuma na soma kuka yayin da ita kuma ta shiga shirya dakinta tana kwashe kayayyakinta masu daraja tana kai su dakin kwananta tana kuma gaya min abinda take so in rinka yi wa kannena, ni kam ko amsawa ba na yi saboda kukan da nake yi.

Ta gama kintsa komai ta kulle wurin ta jefa dan makullin a jakarta sannan tayi shirinta tamfar wacce zata unguwa, ta dauki jakarta ban sani ba ko kukan da taga ina tayi ne ya sa ta ce min dauko min jakar muje ki raka ni sai kiyi sauri ki dawo ke Atika kar ku fita ko ina, suka ce to.”

Muka fito sai da muka yi wa Mama sallama bata wani amsa ba muka wuce muka fito kofar gida muka shiga Tadi zuwa gidan Alhaji Mai kudi, sai dai sabanin yanda ni da Inna muka zata cewar Babana ya ce taje gida ne da wata manufa ta barin gidan.

Ashe kararta ya kai wajen Alhaji Mai kudin. Fada mai tsananin Alhaji Mai kudi yayi mata, tayi ta kuka bai kuma fasa yin fadan ba, haka nan bai bata wata dama ta cewa ga abinda aka yi mata ba.

Sai bayan fitarshi ne ta samu ta yi wa Hajiya Kubra bayanin komai, ta yi dariya ta ce ai in baka iya tsiya ba to ba ka yi wa kanka ba, ashe kema kin iya iya shege? To amma ai da ya baki umarnin karbar girki sai ki bi ba kema ki bijire ba.

Wato shi babu wacce zai tankwasa ta tankwasu kenan? Ba ki kyauta ba ai kin rama abinda tayi miki yaushe rabon Mama da yin yaji in ban da wannan karon?

Ki koma dakinki in kun je kuma ki ka samu bata dora girkin ba ke kuyi rashin girki a gida ai wulakanci ne ta ce to, muka kamo hanya muka dawo gida.

Muna shiga dakinmu Inna ta ce min in je in gyara mata kicin, ban kuma san abinda ta tuna ba ta ce min ke dawo, taje ta kama aikinta da kanta, ta gama girkin aka kaiwa Mama abinci ta ce ta koshi, suma su Habiba haka.

Ta gama komai ta kintsa ta dawo dakinta tayi sallar Magriba ta zauna taja carbi sai da tayi Isha’i sannan ta shiga tayi wanka ta fito ta shafa mai tasa su Atika suka je suka kwanta, mu ma muka hau gado zamu kwanta sai ga Babana ya shigo.

Fuskarshi a dan sake, yana dan dube-dube kina fa jin dadinki Binta, sai kawai ki kalelece jikinki da dakinki ki tasa ‘ya’yanki a gaba kuyi kwanciyarku cikin kamshi babu abinda ya dame ki da miji ba kya nemanshi saboda ba ki damu da shi ba.

In dai ‘ya’yanki suna kusa da ke to shi kenan zance ya kare, musamman ace ga Humaira, ta ce eh to su na mallaka sune nasan da wuya ace an yi nasarar raba ni da su a zihiri da badini, amma miji fa?

In na kwallafa rai a kanshi ai sai in yi ta wahala tunda ba zan same shi a lokacin da nake so ba. Yayi murmushi ya ce, karya kike yi ki ce in kin neme ni ba za ki same ni ba, ba ki neme nin ba ma ina kawo miki kaina duk da bata min ran da kike yi, ban taba bari kin rasa ni ba, wurina girki kawai aka hana ki amma ba a hana ki mijinki ba, kuma da aka hana ki girki da kwanan ai ba kiyi magana kin ce ba ki yarda ba, shiru ki ka yi nima na taya ki yin shirun.

Inna ta ce, kai dai ai sha’ani, ya ce to shi kenan ai sha’anin zance dai kuma ai ya kare, tunda gashi yau kin karbi girki ga ni kuma a dakin naki.

Ban san yanda aka yi ba watakila sai lokacin Babana ya ganni a bayan Inna don tsawa na ji ya daka min ya kuma shiga yiwa Inna fada, ina dalilin da take barina ina shigowa nan dakin ina kwanciya bayan ga sauran ‘yan uwana a can. Sum-sum na tashi na fita.

Tuni aka koma wani irin zama tsakanin Mama da Babana sai su suka san irin shi duk kuwa da cewar shi din baya iya shiga dakin Innata akan idonta, ko da kuwa girkin nata ne, ko da daddaren ne ma yakan shigo ne bayan ya dan faki idonta.

Amma duk da haka bata gamsu ba tunda dai tasan yana shigan, a wannan lokacin bata da wani zance da ya wuce na kowa ya ci tuwo-tuwo da ita miya ya sha.

Ai wannan cin mutunci da aka yi mata in bata rama shi ba to ba iyayen da suka haife ta ne iyayenta ba.

Inna kuwa bata kulawa ko dama can kuwa ba dabi’arta ba ne tunka maganganun Mama sai in ya zame mata dole, haka nan kowane lokaci Babana ya shigo dakinta. Ba ta ce mishi don me?

Ko kuma sai yanzu? Sai dai kawai tayi amfani da wannan damar wajen ganin ta kyautata mishi kamar yanda Hajiya Kubra tayi mata umarni.

Inna tayi girkinta na kwana biyu ta fita girkin Ado ya kawo cefane babu alamar Mama zata karbi girkin tayi na fito daga daki zan je aikan da Innan tayi min sai na ji Adon yana ce mata.

“Haba Mama, gidan nan fa ko an ki ko an so gidanki ne, yaya za ki rinka yin abubuwan da kowa zai gane akwai matsala tsakaninki da Baba, kin ce za ki yi maganinta na ce eh, yana da kyau kiyi hakan to kuma sai kiyi ta kin yin girki?

Bayan kin san babu abinda Baba ya ki irin hakan? Yanzu wannan abin da ya farun ba murna suke yi ba? Kuma don kin ganta da ciki bata da kwana sai me? Sai ki daga hankali?

Shi Baba fa ina ganin kamar in aka cika mishi ciki zai iya daukar matakin da babu dadi, ki wattsake kawai ki koma hidimarki, ki sake kama mijinki, ki tattare abinki ki rike kar kiyi sakacin da zata samu wata dama a kan shi, don haka kar ki bari yau mu dawo daga kasuwa ba kiyi girki ba, abin ba zai yi kyau ba in da hali ma sakwara za ki kirba don na ji ya ce min yana marmarinta.

Ki san yanda ki ka yi ku ka daidaita in yaso sannu a hankali sai kiyi maganin nata cikin ruwan sanyi daga ita har wannan mara kunyar ‘yar tata.

Nayi maza na kauce na bar wurin don kar su hango ni, Mama ta ce a kamo mata ni, cikin zuciyata na kara kin Ado na ce, ina ma dai Tanko aka sanya mishi ba Adam ba, tunda halin shi yafi kama da halin mata baya gyara sai zuga  gashi da taya kishi maimakon ya zamo mai ba da hakuri.

Kan in dawo daga aika sai kawai na samu Mama kace-kace a kicin tana aikin girki, naje na fadi aikan da aka yi min din na zo na shiga kicin na soma taya Mama aikin girkin abincin daren da zata yi tunda in ba hakan nayi ba sai in shiga wani hali alhalin su Habiba ko suna kallonta  ta nayi  ba taya ta suke yi ba.

<< Mijin Ta Ce 5Mijin Ta Ce 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×