Skip to content
Part 7 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Ni kam bana iya kin taya ta don ina tsoron Mama ina kuma tsoron azabar da take gana min.

Tunda Mama ta shawo kan Baba suka daidaita sai kuma al’amura da yawa suka yi ta bullowa, a yanzu in tayi girki to dan kankani take sawa Innata, mu ma ta dan mindira mana su kuwa su Suwaiba ta tura su dakinta ta zuba musu yanda suka ga dama in mun zo mun ce ba mu koshi ba sai ta ce kuje ku sha ruwa.

Da yake an ce muku akwai wata baiwar uwarku a gidan nan da zata rinka yi muku girki kuna wage bakunanku kuna durawa, duk zaku ci uwa ku daga ku har uwar taku ba dai ta ce itama ita ce ba?

Ni da ku ne a gidannan ni kam tunda naje neman kari  ta rattaba min wannan bayanin ban sake komawa ba, da na gane kuma Inna kan ba mu nata ne ita ta hakura sai na daina ce mata ban koshi ba, suma su Aliya na hana su tunda dukanmu muna da wayon mu.

Rannann na farka cikin dare a firgice saboda dada min dukan da naji anyi, “Ke tashi ki koma can dakin.” Nayi maza na bude ido jin maganar Hajiya Kubra, me kuma ya sake faruwa? Tambayar da ta zo cikin zuciyata kenan.

Sai kawai na ganta rike da jariri sabon haihuwa, nan da nan na wastsake saboda sanin Innata ta haihu. Nan da nan na shiga murna ina farin ciki, Hajiya Kubra sai murmushi take yi alamar itama tana farin ciki.

Babana ya leko “Sannunku da kokari Hajiya.” Tayi maza ta ce, ‘yauwa sannu Alhaji.” Ya ce, “Babu matsala dai ko?” ta ce, a’a babu lafiyarta kalau haka nan danta, ya yi maza ya ce na’am ta ce eh ai da namiji muka samu gashi nan kamanshi daya da Humaira, ya yi murmushi ya yi addu’a ya juya ya fita.

Mama ta turo kai cikin falon daidai Inna tana fitowa daga wanka ta ce, “ai ke kadai ki ka haihu a daki baki kira kowa ba? Lalle yarinyar nan kina jin wani abu.

Hajiya Kubra tayi murmushi ta ce, “Ba ita kadai ba ce ina ciki.” Mama ta dan kadu alamar bata san Hajiya Kubra tana ciki ba, ai kina ciki ne Hajiya? Ta ce eh, ai nazo suka shiga gaisawa.

Inna tana zaune tana shan kamun gyadan da Hajiya Kubra ta dama mata, Babana ya sake lekowa babu wani abinda ake bukata ko Hajiya?

Tayi murmushi ta ce, a’a babu, tanfar dai ace gaskiyar Mama da ta ce Babana mai dabi’ar son haihuwar da namiji ne, kusan ace mancewa yayi da Mama tana gidan ya shiga zirga-zirga da kai-kawo na sintirin ganin jariri da tambayar lafiyar maijego.

Gari na wayewa dangin Inna suka kama zirga-zirgar kaiwa da komowa, da suka saba kan kace meye wannan sun cika gidan sai hidimarsu suke yi cikin farin ciki da annashuwa don ma dai suna tsoron Mallam mai babban allo don ya ce in suka sake zuwa gidan aka yi fada da su to zai hana su zuwa in ban da haka da ba karamin iya shege suka yi wa Mama ba.

Da Azahar rannan Babana yana dakin Mama nima ina ciki ina gyara mata farcenta sai kawai na ji ta ce mishi a ka’ida fa wannan dan ba naka ba ne, don kuwa shege ne tunda satan kwana aka yi aka je gun uwarsa.

Nan da nan Babana yayi fici-fici ya bata rai ya shiga yin tsaki yana fadin wannan wane irin zancen banza ne? Bai ma dauki wani lokaci ba ya tashi ya fita ya bar mata dakin.

Jego mai dadi Inna ke yi saboda Hajiya Kubra tana tare da ita, nan take wuni nan take kwana tana kula da ita da komai nata, Sa’adatu tana wurin Inna Balki tun ranar da aka yi haihuwar ta tafi da ita gidanta, gashi komai a wadace Babana yake bayarwa babu kuma halin Mama ta tauye shi.

Rannan ma ta shigo dakin saboda ganin jariri da uwarshi, ko sun tashi lafiya saboda sanin Hajiya Kubra na nan suna hira da ita, tana rike da shi a hannunta sai kawai ta ce wa Hajiya Kubra mazan nan da kike ganinsu fa munafukai ne, ba su da gaskiya ko ta anini.

Tayi murmushi ta ce mata, ba duka ba ne, Mama ta ci gaba da yi mata bayani don ta gamsu da maganarta, har tana kawo mata misali da abinda ya auku na gidanmu, ta kare maganar tata da cewar to ko ke Hajiya ai ina ganin sai kin yi hakuri da wadannan amaren naki yara.”

Hajiya Kubra ta sake wani murmushin kafin ta ce mata, to kin san shi hakurin iri-iri ne, kamarni kin ga amaryata ta farko sa’ar Binta ce, tunda an yi auren Binta da wata uku ne kawai ya yi nashi auren.

Shekara daya da rabi bayan nan kuma ya karato bana shiga harkarsu da mijinsu in dai bana sa zasu yi wani rashin hankali in tsawatar musu ba. To shima ya sani ya san na kame girmana, don haka yana bani girmana suma suna bani girmana saboda sun san mijinsu ba zai yarda su kawo min raini ba, tunda ban raina kaina a gabansu ba.

Mama ta ce haka ne, haka ne abin yake, tayi sallama ta fita.

A wadannan kwanakin yake kawai Mama take yi amma kana kallon idonta kusan sai da ta gama kuka a daki sannan ta fito.

Kwana uku da haihuwar, Baba Yahaya ya rako Alhaji Mai kudi suka zo gidanmu ganin jariri, rannan a falon Babana suka sauka ni Hajiya Kubra ta baiwa yaron naje na kai musu sai fara’a yake yi yana karawa shi kuwa Babana yana gefe shima da alamun farin ciki a tare dashi.

Ya kalle ni yana murmushi, kin yi kani Aisha, sai dai shima baki ne irinki, Alhaji Yahaya yayi dariya ya ce, to ai gaskiyarsu suma wadanda suka yi farin ai karanbani ne ya kai su.

Shi kam Alhaji Mai kudi wasa da ‘ya’yan Inna yake yi tanfar  jikokinshi don ya ce Inna ‘yarki ce, Inna ta shigo ta durkusa ta gaishe su, ya tambaye ta ina ‘yar uwar taki take?

Babana ya ce mata, biya ki gaya mata ga Alhaji yazo. Mama tazo itama suka gaisa da ta juya zata tafi sai ya ciro kudi masu yawa ya bani ya ce in kai mata a sai mana alewa, na ce to. Naje na kai mata su. Na dawo na karbi jaririn na kai dakinmu.

Ko da Babana bai yi wa Inna zannuwan goyo ba, Mama ta hana ta ce duk sanda Inna ta haihu yayi mata zanin goyo, to hatta kayan jariran da yayi sai yayi mata itama don har da gangan Inna ke irin haihuwar da take yi saboda tasan in ta haihun zai kwashe kudin abincin mutane yayi ta kashe mata.

To duk da hakan yayi hidima, goro murza-murza a wadace gami da butter mint da dabino mai yawa, ga ragunan suna tima-tima masu kama da ‘yan Maruka. Ga abincin suna iri-iri kuma mai dadi, ‘yan uwan Innan ne suka dauke cefanen da aka kawon suka yi don sun saba zuwa sunan Inna su kai yamma Mama bata ba su abincin suna ba a dalilin wai ba a gama ba, don haka wannan karon ba su ma saurare ta ba.

Wunin rannar Inna da ‘yan uwanta da na Babana da abokan arziki suna hidimar suna, ita kuwa Mama bata da aiki sai baiwa mutane labarin yanda aka yi aka haifi yaron tana fadin wai shege ne.

Tunda satan girki aka yi aka same shi, tun tana bada labarin  ga masu sauraronta har taje tana baiwa masu yi mata dariya, uwargidan Baba Yahaya Hajiya Hairan wacce ta yi wa sunan hidima mai yawa a dalilin wai mijinsu aka yi wa takwara.

Kallon Mama tayi a sakarce ta ce mata, dama dai kin bar bada labarin nan don kuwa kanki ki ke tona wa asiri, ina ruwan wannan jariri da abinda aka yi da zai zama shege?

Ko dama a waje aka yi cikin nashi balle a aure? Sannan gashi nan tubarkalla tanfar amanshi Alhaji Surajo yayi. Nan da nan ta soma sake mata mata maganganu don dama ita da Mama ta ciki na ciki ne kawai.

Kullum Maman takan ba da labarin Hajiya Haran a matsayin maciyar amana, wai duk da irin amincin da ke tsakaninsu ita ce ta jagoranci komai da aka yi na neman auren Innata.

Ita kuwa Haran ta ce aminci ba zai hana ta bin umarnin mijinta ba ta kuma yi duk abinda zata yi don ta nunawa Mama tana tare da ita don su ci gaba ita Maman ce ta ki.

Hajiya Haran ta kalle ta tayi murmushi, ta ce “Mama kenan, to ai ba ni na kar wannan zomon ba ko ratayen shi kuma ba a bani ba balle ya zama sanadin fada a tsakaninmu, tunda ke kin saba.

Ba’a hidima a gidanki a rabu da ke lafiya saboda zubar da girma, ta ci gaba kuma da sabgoginta tana kuma zaune a falon na Mama bata fita ba sai in wani abu ya kama taje tayi ta dawo.

Can a dakin Inna kuwa wata gwanar ajiyar ce tazo da kaset din da Muhammadu Shatan dangi yayi wa Babana da Inna waka, lokacin aurensu. Don haka tuni matasa-matasan cikinsu suka mike sai faman taka rawa suke yi.

Da yamma rannan kowa ya zo yayi wa Inna salamma zai tafi ‘yan uwanta za su kawo kyauta su bashi na kunshin goro da minti da dabino gami da cincin, babu ruwansu da cewar kai wanene?

Da daddare rannan a dakinmu bayan watsewar Jama’a babu masaka tsinke saboda tarin kaya na sutura da na amfani, atamfa-atamfa turmi ashirin Inna ta samu mafi yawancinsu masu kyau.

Don ko daga gidan Baba Yahaya wanda sunanshi aka sanyawa yaron manyan super biyu aka kawo mata da rigunan yaro guda bakwai gami da sauran tarkace, ga kuma wasu lesuna da shadda da material guda goma can gefe wadanda Alhaji Mai kudi ya yi mata.

Rannan yanda Hajiya Kubra ta wuni cikin hidimar kai-kawon ganin abin da ake yi haka har cikin daren bata huta ba, kokari take yi wai taga ta samar wa komai muhallin da ya dace dashi.

Ni kam sai murna nake yi bini-bini sai in matsa jikin Innata in dauki yaro ko in zuba mishi ido ina kallon shi, ji nake tanfar kar Hajiya Kubra ta tafi, musamman da yake tunda ta zo babu wanda ya zungure ni balle ya doke ni. Ko wannan fitinanniyar aikar ma an rage yi min ita.

Washegarin suna da sassafe su Anti Ramla da Anti Sajida matan Baba da Abba surukayen Hajiya Kubra suka sake dawowa, kamar yanda tayi musu umarni suka zo suka karasa gyara komai suka kuma soye ragunan suna ta kasabta komai ta baiwa kowa nashi gaba daya makwabta da dangi har kauyen su Babanmu Giyade sai da ta bayar ta ce a kaiwa Mahaifiyarshi tare da goro da minti da kuma turamen atamfofi biyu.

Mama ma aka bata nata tare da turmin super guda daya amma wai sai ta dawo da zanin ta ce a bar wa maijego kawai ta daura.

Da yamma rannan Hajiya Kubra ta koma gida bayan tafiyar surukayen ta kafin ta tafi kuwa sai da na ji ta tana jaddawa Inna cewar lalle ne ta kula da kanta da kuma ‘ya’yanta ta ce, to.

Washegari da sassafe tun Innan bata sauko daga kan gadonta ba Mama ta aiko wai ta fito ta baiwa jama’a abin karyawa. Inna ta leko tsakar gida ta ce mata ina kwana?

Da kyar ta bude baki ta amsa sai da tayi ta sake, ta kalle ta cikin natsuwa ta ce “Mama ko za a ba su na yanzu ni in yi na anjima tunda ai na gama daga abincin dare ne muke canjin girkin.

Ta ce, yau an baki daga na safe in kuma ba za ki yi ba ne sai ki fada.” Ta ce, to, ta koma dakinta ta bani umarnin kintsa mata shi da baiwa kannena ruwan wanka ita kuma ta sanya suwaita da hijabi ta fita.

Inna tana kicin tana aikin abin karyawa ni ina daki ina jin Mama tana cewa tunda ki ka san zuwan gun miji a kowane lokaci ai ya kamata ki san hidimar gidan shi ma a haka nan kuma gidana ne yanda naga dama haka zan dama a kuma sha dole gidana ne ni da mijina da ‘ya’ya ki ka zo ki ka same mu ni da mijnin da ‘ya’yana.

Kin ga zai yiwu ki ce za ki kawo min wani fi’ili? Ai sai dai kawai in kin ga ba za ki iya ba kiyi gaba kamar yanda saura suka yi.

Inna ta dawo dakinta tana murmushi ta bani kudi ta ce in sayo biredi da madara. Nayi maza naje na kawo mata, nan da nan ta gama abinda zata yi ta rabawa jama’a, ta bani na Mama na kai mata.

Na dawo kenan Habiba ta biyo bayan ta zo ta tsaya kerere akan Inna da ke yiwa danta wanka, ta ce mata in ji Mama wai wannan abin karyawar da ki ka basu kunu da kosai za ki rinka yi, ta ce mata “to”.

Rainin da Habiba ta yi wa Inna yana ci min tuwo a kwarya, sai dai babu yanda zan yi, tsoronta nake ji saboda kusan kullum sai tayi mini duka.

Rannan ban san laifin da nayi ba sai kawai na ji Mama ta kwala min kira, da sauri na amsa naje in ji kiran sai kawai ta ce min in shiga can cikin dakinta.

Naja na tsaya ina fadin “Mama me nayi? Mama kiyi hakuri.” Ta ce, “Ba zan yi ba ta waiwaya ta kalli Ado dake gefenta ta ce mishi shi kenan je ka sai ka dawo. Ya tashi ya tafi ba tare da ya ce mata uffan ba.

Ta tasa ta biyo ni cikin dakin tana fadin, ai dama tara ki nake yi ina kallon iya shegen da kike yi sarai kin dauka zasu dauwama min a cikin gidanne?

Mama ta soma kama hannayena tana nadewa ta kwantar dani a kasa ta hada da kafafuwana ta danne ta hau kaina ta zauna da iyakacin karfinta, ta shiga mintsinin cinyoyina ina ihu ina fadin waiyo Mama, waiyo numfashina don tasan ta toshe min kafar hanci guda daya.

Numfashin da nake samu baya isa ta nishi yafi damuna ba tsananin nauyinta da azabar mintsinin da take yi min ba, ya tsaya nunfashin ki mutu don uwarki sai me ba na rage mugin irin da ake tara min a gida ba?

Azaba ta ishe ni na kuma gane da gaske Mama bata damu ba don numfashin nawa ya tsaya ba ban san yanda aka yi ba sai kawai jina nayi na kama mazaunanta dake daidai bakina da hakorana da iyakacin karfina.

<< Mijin Ta Ce 6Mijin Ta Ce 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×