Skip to content
Part 9 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Inna ta mike ta tsaya tana kallonta ta ce aiya Zubaida wannan kaya da kika taka na riga na wanke su, sai kawai naji ta ce an taka din menene? Ko shure su nayi na watsa  su me zaki yi? Tana fadin hakan kuma sai kawai naga ta shure tarin kayan sun watse sunyi dai-dai a kasa mai datti.

Ban san yanda aka yi ba, sai kawai na samu kaina da tambayar  ta ha’a wannan wane irin abu ne haka? Ta wanke kayanta kin taka tayi magana kin watsar mata da karfinki? Ta ce an watsar ko kina da abin yi ne mai uwa?

Ta miko hannu ta murde min baki ta saki don kawar da kan da na yi bakin nawa  ya subuce daga yatsunta ta sake miko hannu zata sake. Na kaiwa hannun nata duka da iyakacin karfina.

Lah, ni kika buga? Da karfi tayi tambayar Inna tana fadin ki bari ki kyale ta kawai kije daki, amma ina? Idona ya riga ya ru fe don haka Zubaida na sake kawo min duka ban tsaya ba rarumarta kawai nayi da wani irin karfi da ban taba sanin ina da shi ba na jefar da ita cikin kwanukan wanke-wankennan.

Ga zaton Mama duka zata yi min in aka yi danben, don haka tana ganin mun fara ta bar falonta, ta shige can cikin daki. Inna tana kiranta tazo ta raba don ita kadai ba za ta iya ba, ta ki kulawa.

Sai data ji Zubaidan da kanta tana ihu saboda mummunan shakan da nayi mata sannan ta fito a guje, ta daga ni akanta. Ta kuma yiwa Babana waya ta ce mishi maza-maza ya bar abinda yake yi yazo gida gani nan ni da uwata mun taru zamu kashe mishi amarya.

Inna tayi murmushi kawai ba ta ce komai ba ni kuwa can cikin zuciyata na riga na gamsu don haka ban damu da hukuncin da za a zo ayi min ba.

Babana ya zuba min ido cikin matsanancin bacin rai bayan ya gama sauraron jawabin Mama na cewar ni da Inna ne muka taran mata. Ya ce “Ke Binta.” Gabana yayi mummunan faduwa ga zatona cewa zai yi ta bar mishi gida ko ga takardar saki ya bata.

Sai na ji ya ce zan sa kafar wando daya dake a gidannan ba dai kina bakin ciki da abinda nake so ba, to ai kuwa kin rinka bacin rai kenan za kuma mu hadu a daidai. Tashi min daga nan ki koma dakinki don bana son ganinki a yanzu.”

Inna ta mike ta fita ta bar ni a tsugune a zuciyata ina farin cikin ganin abinda nake tsoron akan Inna bai faru ba, don haka duk wani abin da zai faru to ni kam in dai a kaina ne zan yi hakuri da shi.

Ke kuma Humaira bar min gidannan tunda ba kya jin maganata tafi duk inda ki ka ga dama na bar musu ke.”

Na fito gida sanye da jikakken hijabina ina kuka saboda ban taba tsammanin irin hukuncin da Babana zai yi min kenan ba, na kora daga gida, na dauka dukana kawai zai yi ya bar ni in yi zamana tare da Innata.

Gidan Baba Yahaya na tafi baya nan a gida don haka nayi zamana kamar yanda Baba Hairan ta umarce ni. Bayan na gama rattaba mata bayanin komai. Ai kadan ya fara gani in dai bai yi himma ya gyara lamarin cikin gidan shi ba. Ci abinci kije kiyi wanka in kin gama kije ki duba cikin kayan ‘yan uwanki ki zabi wanda zai yi miki daidai.”

Na ce “To” ban san yanda aka yi ba ina zaune ina shafa mai ta juyo ta kalle ni, Salati mai tsanani naji ta saka wannan wane irin tabo ne haka a jikinki? Na dan yi murmushi na sake zubawa tabon ido ina karasa bare wadanda basu baru da kyau ba wake yi miki irin wannan duka Humaira?”

Na sake wani murmushin kafin na ce mata, Mama da Babanmu, ta ce tirkashi, taja bakinta tayi shiru. Baba Yahaya kuwa yana dawowa ta kai ni gabanshi ta mayar mishi da bayanin komai yayi min fada sosai akan danben da aka ce mishi nayi da Zubaida kafin yayi tsaki ya ce, kai Alhaji Surajo lamarinshi sai shi.

Gida ba doka ba oda? To ya ya za’ayi a zauna lafiya? Baba Hairan ta ce, ai duk Mama ce ta dama gidan nan, kalli jikin yarinyar nan ka gani ta matso tana kokarin kwaye rigar dake jikina, wai yaga tabban, ni kuwa ina ki saboda kirjina cike yake da nonuwa na riga na shekara goma sha shida.

“Barta kawai Hairan, ai na riga na san komai babu wani laifin Majadan da nake gani, nashi yafi yawa don shi ya bnar damar shi ta cewar shi ne Maigida mai wuka da nama a hannunshi ya bar ta take yi mishi kwabar da taga dama.

Yanzu wannan abu da me yayi kama, ace ‘yarka tayi danbe da matarka ina alherin haka? Wa kuma gari ya waya? Sannan wai ya zartar da hukuncin korarta, to taje ina? In ban da tayi hikimar zuwa nan din da wani wuri ta nufa da wa gari ya waya?

Kwanana hudu a gidan Baba Yahaya kafin ya dawo dani gida a dalilin wai Baban nawa yana nemana.

“Ka gyara zaman gidanka Alhaji, ka fita cikin wannan rudani da ka sanya kanka kai da iyalinka, musamman ma ‘ya’yanka abin zai dame ka fa don in ba sa’a kayi ba zumunci zai yi wuya a tsakaninsu. Baba ya ce “To su wa zasu sha wahala? Ai sune kanana, ba shi ke nan ba tunda dama uwarsu da danginta ne basa so ayi zumuncin don su sake koya musu mugun abu suna kokarin ganin sai sun watsa min hadin kan gidana.

Baba Yahaya ya ce, ai gidanka bai taba zama cikin hadin kai ba Alhaji, yau in da da fitina aka fara wannan zaman da wannan rikicin da sai ka ce to gara itama duk juyi iyayenta a tsaye suke akan zaman nata in ban da haka ai da tuni zaman naku ya zama labari kamar yanda na sauran matan ya zama.”

Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min shiga gida Humaira kar in sake jin wani abu ya sake faruwa tsakaninki da wata mata musamman ma ita Zubaida, dukkansu iyayenki ne dukkansu ki rinka girmama su saboda matan ubanki ne kin ji ko ba ki ji ba?”

Na ce mishi na ji, to in ki ka sake ni da kaina ne zan yi miki hukunci don ba zamu yarda ace ‘ya’yanmu ‘yanmata suna mana danbe da matanmu ba, wannan lalacewar ai ta kai in da dai.

Babana yayi kwafa alamar dai har lokacin yana cikin tsananin bacin rai game da lamarin.

A wannan lokaci mun shiga hali mai tsanani a gidanmu ban da maganar fadan da nayi da Zubaida wacce yaja ya tsaya kan shedar da Mama ta bayar ce gaskiya cewar Innan ce ta kwashewa Zubaida kafa yasa na kada ita.

Ita Innan da shi kuma suna cikin wani rikicin na zaman hirar da Babana yake yi a dakin Mama sai sha daya ko sha biyun dare kafin ya shiga dakin mai girki.

Gari na wayewa kuma can wurinta zai sake komawa a dalilin wai ita tayi kyautar kwananta. Inna taja ta tsaya kan tunda ba ita aka yi wa kyautar kwanan ba, to kuma babu abin da zai tauye mata kwanakin girkinta.

Sai abin ya tsaya can a tsakaninsu ita da wacce ta yi wa kyauta kan haka dai nasan ta kulle mishi kofa yafi sau goma shi kuma yayi mata duka har sau biyu.

Rannan dai aka wayi gari Inna bata nan a gida babu kuma wanda yasan lokacin da ta fita. Mama da Zubaida sai maganganunsu suke yi a tsakar gida na nuna murnarsu kan abinda ya faru.

Ni kuwa ina dakinmu ina yiwa kannena hidimar da ta dace in yi musu don hatta Baba karami bata tafi da shi ba, na gama basu kunun da na dama musu kenan Mama ta kira ni ta bani abin karyawar gida tana kuma zagina kan munafurci na da kuma ware kannena da wai nake yi ina nuna su kadai ne nawa.

Har dai na koma daki ban ji Zubaida ta tanka mata ba sabanin da da itama kanta zagin nawa take yi a yanzu kuwa ni da ita mun shiga taitai juna bana shiga harkarta ko daga ido in kalle ta bana yi, itama bata shiga tawa ta kuma rage yiwa Inna irin hawan kawarar da da take yi mata.

Ina zaune a dakinmu ni da kannena su suna kallon katun din (ABATAR) da na sanya musu yayin da ni kuma nake ta faman share-share da goge-goge kamar yanda kullum muka saba yi da Inna.

Can cikin zuciyata kuwa tunaninta nake yi itama ta tafi gidansu kawai taje tahuta da wannan wahalar da take ciki tabar mu kawai tunda mu gidanmu ne a cikin ta aka haife mu mu zauna muyi ta shanta amma kuma da na tuna yin hakan yana nufin ba zamu sake zama wuri daya da ita ba sai kawai na ji hawaye suna gudu a idona.

Babana ya shigo dakin ya same ni ina kuka ya yi kamar bai ga kukan da nake yi ba ya ce min, “Yauwa ki kula da su kin ji ko?” na ce mishi “To.” Yasa hannu a aljihu ya ciro kudi ya bani ya ce, ki boye wannan in kuma bukatar wani abu ki sai muku na ce mishi to.

Har yayi kamar zai fita sai ya sake juyowa cikin murya kasa-kasa ya ce min, ina Innarku ta ce miki zata tafi? Na ce bata gaya min ba, na ji kukan Baba karami ne kawai na fito na gan shi shi kadai a kwance.

Kwana biyu a jere babu Inna babu dalilinta, an neme ta gaba daya bata nan. Bata gidan mai babban allo bata gidan Alhaji Mai kudi yayinta maza da mata duka an je bata nan gaba daya hankula suka tashi ko ba a gaya min ba kuwa nasan Babana yana cikin wadanda suka fi kowa damuwa.

Don na ji yana cewa Mama abin nan kamar wasa fa an nemi Binta ba a ganta ba, ta yamutsa fuska ta bata rai ta ce ai sai kuyi ta nema abinda dama take so kenan da yake ku kuma kun iya daurewa karya gindi in ba haka ba yarinya ce karama balle ace ta bata?

Tayi  maza ta rike baki ta ce, au, haka fa in ba a yi neman da kai ba, Alhaji Mai kudi ga kuma munafukin abokinka, taja bakinta tayi shiru, zuwa can ta sake cewa ai ace ma kana da tsayaiye da dadi sai kayi ta dama tsiyarka yanda kaso dole a kyale ka ayi ta bi in ba haka ba ai ina? Ta sake yin shiru, shima ya tashi ya fita ya bar mata gidan.

Kwana biyar da barin Inna gida na fito da safe ina goye da Baba karami don ko Ali  ya da Atika baya yarda su taba shi sai ni, a kofar gida naga Babana yana tsaye naje zan wuce shi tunda dama naje na gaishe shi.

“Zo nan Humaira.” Da sauri naje na same shi na ce mishi, gani Baba. Ya yi kamar zai fasa gaya min maganar da zai gaya min din sai kuma ya ce min yanzu in na shirya zanje wajen maganar Innarku.”

 Da sauri na ce mishi Baba an ganta ne? Ya ce eh, dama ashe tana can ne sabon gidan Alhaji Abba dake can bayan (C.B.N Kuarters) can ya kaita ya boye ta kin san dama ba wani mutunci ne dashi ba tunda ya wayi gari ya gan shi da kudi a hannu na lura yana yiwa mutane kallon banza na fitar harkarshi.

Kin san kudi a hannun yaro in ba mai natsuwa ba ne sai ya shiga aikin rashin hankali da wulakanta na gaba dashi, don ko gidan nan da yake zuwa wurin Innarku ba gaishe ni yake yi ba sai in ta kure mun yi kacibis dashi.

Shi yasa ma nake ganin tunda shi ne mai daure mata gindi take yi min iya shegen da take yi min to ina ganin zan hakura da ita ne kawai don in samu ma gidana ya zauna lafiya musamman ma da yake Mama tayi min alkawarin zata kula min da ku.

Na kalli Babana na ce mishi, to Baba Allah ya zaba mana mafi alheri, na wuce shi na tafi.

Da daddare har na turo kofa na rufe na kuma kullewa Inna kofarta da take kwana bayan na kintsa shi na kuma tattara duk wani abu mai daraja na shigar mata ciki, gaba daya sun yi barci nima abin da ya hana ni kwanciya ina damawa Baba karami kunun da zan ba shi ne in ya tashi cikin dare.

Sai kawai naji ana taba kofa nayi maza naje na bude, Innata na gani. Tsalle nayi ina ihu na kankame ta. Mama ta leko da sauri ta ga abinda ke faruwa, ta ce au kece ki ka dawo?

Ta ce, eh mana ina wuni? Bata tanka mata ba ta juya gun Babana wanda nima sai lokacin na gan shi a tsaye a tsakar gidan ga alama dai tare suke, ta ce mishi uhun ai dama tunda naga ba ka dawo ba na ce kana can wurinsu.

Gaba daya suka rurrufe mishi kofa ya dawo dakin Innata wanda ban so hakan ba, naso ace ya yi zamanshi a can don nima in samu in shaki kanshin jikinta da na dade ban ji ba.

‘Yan kwanaki kadan din da Inna  tayi bata gida har ta dan canza, ta yi girkinta na kwana biyu ta fita cikin kwanakin kuwa Babana baya hirar dare a dakin Mama iyaka dai ya shiga da safe su gaisa kamar yanda yake yiwa kowacce sai kuma da rana in ya dawo, nan ma nanne wurin zamanshi.

Amma da daddare yana shigowa daga Masallaci in anyi sallar Isha’i wurin Inna yake shigowa, Mama kuwa sai yada maganganu take yi shi kuma in ban da harara da tsaki babu abin da take yi mishi.

Kwana biyu da dawowar Inna Hajiya ‘Yar dubu tazo gidanmu ina dakin Mama ta shiga suka gaisa ta fita ta nufi wurin Innata tana barin dakin Mama ta kalli Zubaida ta ce mata wani maganin uban ya sake bayar wa a kawo mata duk zanci abu kazansu ba dai da ni suke yi ba.

Na tashi nima na fito dakinmu nazo don in kara gaida ‘yar dubu sai na same ta tana cewa, Inna wannan hankoro da ake yi na kashe miki aure fa ba gata ba ne.

Da ma kin yi hakuri kin zauna a dakinki kin daina kai kara da fadin maganganu da ya fiye miki daraja yanzu irin maganganun da wannan yaron yayi ta gayawa mijinki da ya zuciya ya ce ya hakura da wa gari ya waya?

Duk wani gatan da za’ayi miki yanzu ya wuce ayi miki tattalin yanda za’ayi ki zauna a dakinki tare da ‘ya’yanki? Ke mai ‘ya’ya mata? Hudu ne fa dake a jere ga su nan reras, don ma sauran babu kuma don zafin rai irin naku na ‘ya’yan yau da ba a gaya muku gaskiya danki mai wata bakwai da za ki tafi ai sai ki goyo abinki ki tafi dashi.

A’a ke ga mai zafin rai kin ajiye shi kin tafi to dube su shi da wacce ki ka bar wa din yanda suka zama, su ‘ya’ya in gaya miki in suka kintsu suka zama mutanen kirki ne suke zama na kowa da kowa, amma in suka lalace to na mai su ne shi kadai.

<< Mijin Ta Ce 8Mijin Ta Ce 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×