Skip to content
Part 1 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Shimfada

Sanye yake cikin kananun kaya da suka yi matukar dacewa da fatar jikinsa. Fari ne tas! Dogo mai dauke da faffadan kirji. Gashin kansa da yasha gyara ya kara taimakawa kyawunsa wurin fitowa. Yana dauke da kwantaccen saje, wanda yayi bala’in kawata fuskarsa.

Sannu ahankali yakai hannu ya dauki lapcoat dinsa ya dora akan kananan kayansa. Sannan ya dauki abin gwaji ya dora a wuyansa.

Sassanyar kamshinsa ya cika ofishin, haka ya fito yana tafiya tamkar mai jin tausayin kasa.

Nasis sun kai uku da suke biye da shi, hannayensu dauke da files. Tunda ya fito ma’aikatan suke durkusawa suna gaida shi, sai dai babu wanda ya kalla, bare su saka ran zai iya amsawa.

Wannan dabi’a tasa ta riga ta zame masu jiki, duk da da yawan mutanen wurin basu jin dadin yadda yake sharesu.

Gado na farko ya fara isowa, ya jawo kujera ya zauna, ya kama hannun tsohuwar da ciwo ya gama cinye jikinta, sannan aka kawo masu.

Zuciyarsa tana tafarfasa kamar zata fito waje. Zai so yayi masu fada, sai dai kuma waye zai yiwa fadan a cikinsu? Tsohuwar ko kuwa yarinyar da shekarunta ba za su gaza sha bakwai ba.

Yana rike da hannunta yana matsawa, sannan ya dago tare da sauke ajiyar zuciya.

“Ina masu jinyar tsohuwar nan?”

Ya yi maganar cikin izza! Da kuma isa. Cike da takaici Samha ta murguda baki ta ce,

“Ni ce nan.”

Yadda ta yi maganar ya saka shi zare gilashin idonsa, yana dubanta. Wata zuciyar tana cewa da shi, kada ya duba tsohuwar ya kyaleta kawai ya tafi. Da kyar ya tausasa zuciyarsa, sannan ya sake duba files dinsu.

“Ina nufin ina babba wanda zan iya magana da shi?” Samha ta dan yi shiru. Daga bisani ta ce,

“Nima bansan kowa nata ba. Ni da ita muka tsinci junanmu. Dan haka ni dai da ka gani anan nice nan mai jinyarta, ko Inna?”

Innar ta gyada kai alamun hakane. Dr. Zayyad Yayi nisa, kamar bazai sake furta komai ba, sai kuma ya dubi nasis din ya ajiye files din, sannan ya tashi zuwa gado na gaba.

Da zarar ya dago sai idanunsa sun sarke da na kazamar yarinyar nan, da take yi masa magana kai tsaye babu rusunawa. Ba zai iya tuna ranar da wata mace ta iya kallon tsabar idanunsa ta furta masa irin kalmomin da Samha tayi amfani da su wurin bashi amsa ba. Huci mai zafi ya furzar sannan ya cigaba da duba marasa lafiyan.

Yau ba dadewa zai yi a asibitin ba. Yana gaggawa ya gama, sai kuma tiyata dake zaman jiransa har na mutane biyu, da zarar ya gama zai fice zuwa wurin meeting.  Ko kadan Dr. Zayyad baya wasa da lokaci, dan haka duk abubuwan da yake yi, yana yi yana duba agogo.

Har ya fice Samha ba ta daina kallonsa ba. Yana ficewa tayi saurin karasowa wurin Inna ta dagota da kyar sannan ta dauko goran kunun da ta samo mata tana ba ta tana sha.

“Inna likitan nan mai kyau da shi. Sai dai kwata-kwata baida mutunci.”

Inna ta zaro idanu, sannan tayi magana da kyar,

“‘Yar Baba ki daina babu kyau. Kada ki jawo a sake korarmu a asibitin nan dan Allah. Sannan ki daina cewa bamu san juna ba dan Allah.”

Samha ta yi dariyar da sai da gefen kumatunta suka lotsa, sannan ta ce,

“A’a Inna! Kada mu yi haka da ke. Ni ban iya karya dan asoni ba. Ko na gaya masa ina da alaka da ke ba tausaya mana zai yi ba. Kuma kin dai san yadda nake da farar kafa ko? Ki bari kawai mu dinga gaya masu gaskiya.”

Inna dai ta yi shiru tana sauraren bayanin Samha ba ta ko hadiye yamu.

Kamar kiftawar ido, Dr. Zayyad yaga wani abu da gudu ya wuce ta gabansa. A lokacin da yake kokarin shiga mota domin barin harabar asibitin.

Haka kawai yaji yana so yaga wani yaro ne yake irin mugun gudun nan. Kurawa gate idanu yayi, yana kallon yadda take kokawar bude hanyar da mota kadai ke bi.

Rungume hannayensa yayi a kirji, babu ko shakka ya gane yarinyar. Yana kallon yadda ake dambe da ita wajen hanata bin hanyar da take so. Duk da suna da ‘yar tazara, hakan bai hana kunnuwansa zuko masa manya-manyan ashariyar da take auna masu ba.

Wani tunani ya shiga yi, kafin ya ankare har ta bace daga wurin. Ya girgiza kai yana ayyana wasu abubuwa a zuciyarsa.

Tamfatsetsen kamfanin ya nufa, wurine na manya wadanda suka ci suka tada kai.

Bayan ya rufe motar yana kokarin shiga ya ji muryar wata almajira tana cewa,

“Ka taimakeni Alhaji ko zan sami abinda zanci. Tun safe nake bara ban sami komai ba.”

Muryarta tayi masa kama da muryar da ya sani, kasancewar yana sauri ya hana shi tsayawa. Sai dai fa almajirar nan ba ta daina binsa ba. Ya juyo a fusace. Sai dai me zai gani? Samha ce sanye da katuwar gilashi baki, ta daga kanta sama kamar wata makauniyar gaske. Hannunta rike da doguwar sanda tana lalube.

Sai da ya rufe ido ya bude, domin ya gane anya ba gizo take yi masa ba? Tabbas ita ce.

“Ke! Bake ce na gani a asibiti kina jinyar wata tsohuwa ba?”

Da sauri ta cire gilashin, suka yi ido hudu.

Taja masa tsakin da ya zama sanadin tarwatsewar duk wani farin cikinsa.

“Kai dai kawai kana yi mana bakin cikin mu sami abinda zamu ci. Idan ba haka ba menene na tona min asiri a tsakiyar kasuwa?”

Ta furta tana murguda baki.

‘Ya ilahi.’

Ya furta a cikin zuciyarsa.

A fili kuwa wani abu ya hadiye da kyar, sannan ya juya ya cigaba da takunsa. Baki bude take kallonsa. Yana burgeta musamman yadda kamanninsa yake juye mata kamar na ‘yan indiya.

Tana kallo har ya shige sannan ta mayar da gilashin ta bar wurin.

Dr. Zayyad dai har aka kammala tattaunawar bai san me ake cewa ba. Zuciyarsa tafarfasa kawai take yi masa.

Bayan sun fito ne Dr. Najib ya tsayae da shi yana masa surutun da shi kansa ya gaza gane me yake cewa? Haka zalika ko amsa daya bai bashi ba. Shi kuma da yake yasan halin miskilancinsa bai damu ba.

“A taimakeni dan Allah Alhaji, muna neman abinda zamu ci. Ga kuma yayata hannunta ya karye muna so mu je asibiti ne.”

Dr. Zayyad dai bai kalli yaron ba, hasalima hankalinsa ya tafi wani wurin. Kamar ance masa ya juyo, ya sake ganin Samha hannunta anannade da bandeji.

“Kada ka basu komai Najib. Wannan yarinyar da alama annoba ce.”

Ya furta yana sake watsa mata manyan idanunsa, masu firgita ‘yan mata.

Da sauri ta dago tana dubansa. Bakin ciki, da tsanar Dr. Zayyad suka darsu a zuciyarta. Mahaifiyarta ta tuna. Yau komai ba ta ci ba. Kokon da ta samu ne, ta je ta kaiwa Inna, kasancewar likitar mace ta gaya mata dole a dinga ba ta abinci akan lokaci saboda cutar gyambon ciki.

Hawaye suka wanke mata fuska. Ba zata iya tuna ranar da idanun nan nata suka zubar da hawaye ba. Ga sabbin kudi a hannun Najib, wadanda za su iya isarta tasiyawa Mahaifiyarta abinci har da magani. Sai dai dan hana ruwa gudu ya hana faruwar hakan.

“Sai na zamar maka annobar da ka ambaceni da shi. Ka cutar da ni bansan me nayi maka ba.”

Dukkansu idanu kawai suka saka mata. Shi kuwa almajirin nan durkusawa yayi yana cewa,

“Ku yi  hakuri kada ku kamani ba laifina bane, ita ce ta matsa mini akan mu je za ta bani naira talatin. Dan Allah kada ku kamani.”

Kafin su yi magana ya ruga da gudun gaske. Shi kuwa Dr. Zayyad ji ya yi kamar ya shake Samha har sai ta daina numfashi.

Masu katatu ku gyara zama domin zaku sha labari irin wanda kuka jima baku ji irinsa ba. Labarin ya sha bamban da sauran labaraina. Ni kaina sai da littafin ya rikitani ayayin rubuta shi. Ku dai ku gyara zama.

Yana kallonta har ta bacewa ganinsa. Bakinta bai daina motsi ba. Najib ya jinjina kai ya ce,

“Yanzu wadannan yaran har sun san irin wannan cutar? Gaskiya kasarmu tana cikin wani hali. Da ka sani ka bari na basu, bakasan halin da suke ciki ba.”

Dr. Zayyad ya mika masa hannu, hakan ya tabba tarwa Najib bazai yi magana ba. Bai damu ba, idan da sabo ya ci ace duk wanda yake mu’amala da Dr. Zayyad ya saba da miskilancinsa.

Tafiya yake a mota yana murza sitiyarin kamar mai tsoronsa. Jefi-jefi yana jin gabansa yana faduwa. Yaso ya koma asibitin, domin acanne yake iya samun sassaucin halin da yake ciki. Amma hakan ba zai yiwu ba, kasancewar akwai tarin takardun da suke jiransa ya shigar ta cikin Computer.

Ya kai a kalla mintuna biyar yana matsa horn amma ba a bude ba. Duk da yadda zuciyarsa ke tafarfasa hakan bai saka shi sakkowa ba, sai ma kwantar da kansa da yayi yana kallon wata yarinya karama a bolar unguwar tana tsince-tsince. Ta cikin madubin motar yake kallonta ta dage tana bude ledar biredi, wanda babu ko tantama ragowar biredin nan ta lalace. Ya karyar da kansa yana sake saita kansa a daidai madubin. Da gaske ya ji tausayi da imani ya karyo masa. Shikam babu abinda ya nema ya rasa a duniya, amma kullum yana cikin kunci da damuwa.

Tana matsowa yana kallonta, har ta matso daf! Da shi.

Kwankwasa motar tayi, kasancewar akwai duhu sosai ba ta iya ganin waye ke ciki. A zuciyarta kuma tana kissima wannan irin motar azzalumin likitan nan ne.

Sai a lokacin ya gane ashe Samha ce. Bai bude ba, bai daina kallonta ba. Kayan da ta saka a yanzu su suka hana shi ganeta tun tana nesa da shi. Ya sake lumshe ido yana jin ciwon kai kamar kansa zai rabe biyu.

A hankali ya zuge gilashin yana kare mata kallo.

Tsabar gigicewa yasa ta nemi ta gudu, ya saka hannunsa ya kamota ta cikin windon.

Sun jima suna duban juna, kowannensu da abinda yake sakawa. Gabansa ya kara faduwa da karfi. Ya yi saurin cire idanunsa akanta ya ce,

“Sai kin gaya min waye ya turoki?”

Ta girgiza kai,

“Babu kowa.”

Ya sake girgiza kansa,

“Alhaji Bako ya aiko ki shiga rayuwata ko? Gaya mini gaskiya ko in hadaki da ‘yan sanda.”

Samha tana jin zancen ‘yan sanda ta fara rantse-rantse tana kuka. Yadda yaga jikinta yana bari, yasa ya gamsu ba mahaifin matarsa ba ce. A lokacin aka wangale gate din gidan, ya sakar mata hannu ya cusa kan motarsa ciki.

Samha ta ruga da gudun gaske ta bar unguwar tana tunanin me zata kaiwa mahaifiyarta da Inna?

A falonsa yayiwa kansa masauki yana lumshe idanu. Bai nemi ganin matarsa ba, gashi yana jin yunwa, sai dai yasan bazai taba samun komai daga wurin Sakina ba.

Yana nan zaune ya saka wannan ya kwance waccen.

“Ka dawo?”

Ya ji muryarta ta daketa. Ya dago ya dubeta. Matar da ada yake yiwa soyayya mai zafi, matar da soyayyarta ta hanashi ganin kowane aibinta, a yau ita ce ta rikide ta koma masa kamar dodo.

“Eh.”

Ya ba ta amsa a kirne. Ta ajiye abincin da ta fito da shi daga dakinta,

“Ga abinci. Na fito da ninyan kai maka kan dinning, sai kuma na ganka a falon.”

Bai ce um bare um-um ba. Shi dai da ido yake rakata. Shinkafa ce ta ji kifi. Kamshin ya daki hancinsa. Zai iya rantsuwa a tsawon shekaru shida da yayi da Sakina bai taba ganinta ta girka abinci mai dadi ba, bare har akai ga abincin yayi irin wannan kamshin.

Bayan ta zuba masa, ya dauki cokali zai kai baki, wata zuciya ta ce,

‘Idan kuma ta hada baki ne da mahaifinta domin su kasheka fa?’

Dam! Kirjinsa ya buga da karfi. Tabbas Alhaji Bako zai iya yin komai domin ganin ya kawar da shi daga doron kasa.

A hankali tunani ya sake shigar masa kai,

‘Daga daki abincin nan ya fito, ba wai daga kitchen ba, Sakina ba zata taba iya yin girkin nan ba.’

Cokalin ya mayar bakinta,

“Gashi ki ci.”

A ninyarsa idan ta ci, zai iya ci shima. Sai dai shu’umin murmushi ta sakar masa,

“Na koshi.”

Shima murmushin ya mayar mata, wanda iyakarsa fuska.

“Ok. Nima na koshi.”

Ya ture abincin. Yana kallon yadda ta ba ta rai kamar zata yi kuka.

“Wai meyasa ka canza minne haka? Ko na yi maka wani laifi ne? Idan laifi na yi maka ka gaya mini zan baka hakuri. Ka canza da yawa Masoyi.”

Ya jinjina kai yana binta da narkakkun idanunsa,

“Sakina ina bukatar in yi wanka in huta.”

Daga nan ya mike. Sakina ta ware idanu tana mamakin yadda ya kira sunanta gatsal! Bayan masoyiya yake kiranta ko a gaban waye. Da sauri ta bi bayansa tana mitan kiran sunanta da yayi. Ko tari bai yi ba. Hakan yasa yana shiga dakinsa yana kokarin cire kaya, tayi sauri ta nufi bandaki ta hada masa ruwan wanka. Ya dubeta ya ce,

“Na gode.”

Wannan dabi’arsa ce, kowane irin aiki ta yi masa yakan gode mata, ko kuma ya yi mata sannu da aiki.

Yana shiga bandakin ya rufe da key. Haka kawai zuciyarsa ke gaya masa an zuba masa wani abu a cikin ruwan wankan. Dan haka ya kwarar da ruwan, sannan ya wanke bokitin ya sake tara wani.

Ya jima yana sake-sake. Yana da tabbacin alhakin iyayensa ke taba shi.

Bayan ya fito ya shirya tsaf! Ya fasa yin aikin, zai je gidansu domin sake neman afuwan iyayensa. Komai ya gani ba daidai ba, yakan alakanta hakan da alhakin iyayensa.

‘Yar mutan Bornonku ce.

“Ina kuma zaka je?”

Ta tambaya cikin razana. Yana tafiya ya ce,

“Gidan Hajiyarmu.”

Ranta ya sake baci. Ta daure ta ce,

“Jirani in rakaka.”

Bai dubeta ba, ya saka kansa ya fice. Duk da ta basa da irin wannan miskilancin, amma kuma ba haka yake mata ba. Idan bazai yi mata magana ba, yakan sumbaceta a matsayin lallashi.

Ta koma ta zauna dabas! Hakika wankin bargo yana neman yakaita dare.

Tana nan zaune ta yi tagumi. Sai ga kiran mahaifinta.

“Hello Abba.”

“Kin kammala aikin?”

Ta dan yi shiru sannan ta ce

“An sami akasi. Ka sake bani lokaci.”

Alhaji Bako ya bugi teburi da karfi,

“Kamar yaya in sake baki lokaci? Rayuwar Zayyad barazana ce ga rayuwarmu. Zayyad masifa ne a cikin rayuwarmu daga ni har ke har zuri’ata. Zayyad guba ne da zai iya kassara rayukan al’umma.”

Sakina da ta ji wani karfi ya zo mata ta ce,

“Hakane Abba. A kara bani kwanaki biyu.”

Ya girgiza kai kamar tana ganinsa,

“Kwanaki biyu sun yi yawa. Na baki kwana daya.”

Ta jinjina kai tare da sauke wayar a lokacin da ta fahimci ya kashe wayar.

Miskilin Namiji 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.