Skip to content
Part 10 of 19 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Ta koma samanta bayan ta gama gyara wurin da ta ba ta, ta shiga ta watsa ruwa. Doguwar riga ce a jikinta ‘yar egypt. A lokacin karfe tara ya buga. Zayyad ya shigo da sallama. Ta amsa sannan ta dan dube shi,

“Ka tashi lafiya?”

Ya jinjina kai ba tare da ya amsa ba. Kallonta yake yi kamar wacce bai taba gani ba. Kyawunta ya wuce yadda za a tsaya misaltawa.

“Ina so infara yin wanka. Asibiti na wuce na sami kiran gaggawa.”

Ta gyada kai suka shiga ciki. Mamakinsa ya karu, ya shaki kamshin turaren ya lumshe idanunsa. Ya shiga ko ina ya sami an gyara wuraren tsaf! Hatta tarkacen da yake cikin dakin an tattare su.

“Na gode Samha da kika mayar mini da dakina tamkar na sabon ango.”

Ta dan yi murmushi kawai.

Bandakin ma ya burgeshi fiye da tsammani. Yayi wanka ya fito. Kanta a qasa, bazata iya kallonsa ba. Da kansa ya kimtsa sannan ya ce,

“Muje insamu in karya.”

Suna fitowa suka nufi dining. Samha ta kalli Sakina sosai. Zuciyarta ta sanar da ita akwai abinda Sakina ta aikata. Sakina ta gaida shi, da kyar ya amsa, sannan Samha ta gaidata. Ko kallonta ba ta yi ba, bare ta saka ran zata amsa.

Dukkansu suka hau kan tebur. Sakina tana murmushi kawai. Zayyad yana kokarin bude kular Samha tayi masa wani abu da idanu, nan da nan ya gano abinda take nufi, sai dai kuma bai cire hannun daga saman kular ba, ya kafeta da idanunsa.

“Au! Bari indauko maka naka. Da na gama na zaci a daki zaka ci sai na ajiye naka daban. Wannan na anti Sakina ce.

Sakina ta dubeta da sauri cike da tashin hankali. Shinkafar bera ta zuba masu a cikin abincin. So take dukkansu su mutu ko zuciyarta zata huta da radadin da namiji. Domin ko Samhar ce ta mutu hankalinta ba zai kwanta ba, dan tasan dole ne ya koma rigar fulani a sake bashi irin Samhar.

Ta tashi ta haura sama ta kwaso masa kayan abincin. Ta zuba masa komai yayi godiya ya fara ci. Ga mamakin Sakina sai gashi ya cinye komai tare da korawa da ruwan tea.

“Na gode Allah yayi maki albarka.”

Ta amsa da “Ameen.”

Ya dubi Sakina tana latse-latsen waya kamar zata hadiyi zuciya ta mutu.

“Ke ba zaki karya bane?”

Ta dago tana yaqe.

“Kafin ku fito na fara cin nawa.”

Ya juyo zai tambayi Samha tayi saurin cewa,

“Nima na ci nawa.”

Anan suka tashi suka bar kwanonin.

“Zan koma wurin aiki sai na dawo.”

“Allah ya dawo da kai lafiya Uncle.”

Ya amsa tare da wucewa. Sakina ko dago kai ba tayi ta dubeta ba.

“Uncle manya. Wannan yarinya akwaiki da kinibibi da iyayi.

Ba ta ce komai ba, ta shiga tattara kayan abincin.

“Matsiyaciya. Tunda kika zabi rayuwa da mijina sai na shayar da ke ruwan mamaki.”

Samha ta dan dubeta ta ce, “Banda mamakin da kika saba baiwa mijinki?”

Ware idanunta tayi cike da zargin Zayyad yana gulmarta kenan.

Shiru tayi ba ta ce komai ba. Samha ta tattare kwanonin da sauran abincin da ba aci ba. Kai tsaye ta nufi kitchen. Har zata zubar wani tunani ya zo mata. Ta dauki kwano daya ta nufi wurin karen da ke daure a can baya. Ta zuba masa abincin. Tana nan tsaye taga baiyi wani abu ba, sai ta koma ta zubar da sauran ta wanke kwanukan ta tsaftace kitchen din.

Tana hawa sama ta sami Sakina tana kokarin bude dakinta amma ya qi buduwa. A firgice ta juyo tana kallonta. Samha ta daga mata key tana karkadawa.

“Ga makullan a hannuna. Kinyi ajiya ne a dakina?”

Sakina ta hade rai kawai ta juya. Lamarin Sakina yana daurewa Samha kai. Haka ta shige tana waswasi. Barci yayi awon gaba da ita. Sai wajen karfe goma sha biyu ta tashi.

Kai tsaye kitchen dinta na sama ta nufa, tayi girkinta ta zubawa maigidan, duk da ba ta da tabbacin zai dawo da wuri.

Daga nan ta sake bin lafiyar gado.

Ji tayi ana bubbuga kafafunta, ta ware idanu bakinta dauke da addu’a.

“Zo ki sameni a kasa. Ki fito min da abinci da yunwa na dawo.”

Ta tashi tana murza idanu. Shi kuma ya fice zuwa qasa.

Bayan ta hada masa komai ta nufi kitchen ta kwaso masa abincin. Anan falon suka zauna yana cin abincin. Har ya fita ya dawo bai daina kokarin tuno abubuwan da suka faru a baya ba. Sai dai ko alama bai tuna komai ba. Zuciyarsa kamar zata buga saboda zafi. Alhaji Bako shi yayi sanadin shigarsa matsalar nan, duk da haka bai daina neman rayuwarsa ba.

A hankali yake cin abincin kamar ba zai ci ba. Sakina tana zaune tana taunar cingam.

Ya ciro waya sabuwa kar a kwali. Kirar iphone 13 promax ya mikawa Samha.

“Gashi naki ne. Akwai layi da katin waya a ciki. Na saka maki numbers din su Anti Rahama.”

Ta karba tana jujjuya kwalin.

“Na gode Allah ya kara arziki.”

Anti Rahama ta koyar da ita yiwa miji godiya. Ya jinjina kai kawai. Dadin girkinta ya debe shi har ya cinye abincin.

Kirr wayarsa ta yi kara. Ringing din da ya sakawa ma’aikatan gidansa ne.

“Yaya akayi?”

“Ranka shi dade Kare ne ya mutu.”

Da sauri ya tashi tsaye.

“What! Ya mutu? Ina zuwa.”

Duk suka kalleshi.

“Me aka ba karen nan ya mutu?”

Samha ta fi kowa shiga tashin hankali. Duk suka biyo bayansa. Ya juyo yana kallon Samha. Bai yi mata magana ba, da ido ya nuna mata shigar jikinta. Ta dan dubi kanta babu aibu a shigarta, amma sai ta juya da sauri ta saka hijabi. Sakina ba ta fahimci komai ba, sai da ta ganta da hijabi. Mamaki ya isheta. Wato yafi kishinta akanta kenan.

Cirko-cirko suka yi a gaban gawar karen, wanda bakinsa yake dilalan miyau.

“Me aka bashi?”

Samha ta yi shiru. Kowa ya ce bai sani ba. Ya girgiza kai kawai ya  ce a dauke shi a fitar da shi.

Haka duk suka dawo gida jiki babu kwari. Samha kuwa kanta ya dauki zafi. Tsoron Sakina a karo na farko ya shigeta. Tayaya mace kamar Sakina zata iya aikata wannan bakin zaluncin? Lallai aji tsoron Allah aji tsoron Sakina. Da yanzu Uncle Zayyad ne zai mutu kenan? Sai kawai ta saka kuka. Hawaye yayi mata kaca-kaca a fuska. Duk suka kalleta cike da mamaki. Kuka take yi na gaske. Zayyad ya kasa jurewa, dole ya jawota gaba daya ta koma jikinsa.

“Kinsan bana son kuka ko? Dan kare ya mutu menene abin kuka?”

Ita dai ba ta ce komai ba, sai kuka. Sakina ta ja tsaki ta juya zata wuce.

“Ke! Wa kike yiwa tsaki?”

Yadda taga tsananin fushi da bacin rai a fuskarsa ya sanyata dawowa hayyacinta. Sai kawai ta girgiza kai,

“Ba da kai nake ba.”

Da gudu ta shige bangarenta.

“Ya isa haka.”

Ta hadiye yamu tana jin jikinta yana rawa.

‘Waye ni? Me ya faru da ni? Me kunnuwana suka ji ana tattaunawa a farko?’

Ya dafe goshinsa da hannu daya,

‘Ohhh Ya Allah. Idan ba alkhairi naji ba, idan abinda zai tarwatsa rayuwata ce, ya Allah ka hanani tuna komai.’

Duk w zuciyarsa yake magana. Dakinsa suka koma. Ko ina tsaf-tsaf. Tana son gaya masa wacce tayi wannan aikin, tana tsoron abinda zai je ya dawo. Amma yanzu tunda ga waya komai ya faru gwara ta nad’a a ciki.

Yadda yaga dakinsa ya saka shi sumba tar goshinta, wanda shi kansa bai san yadda akayi ya aikata hakan ba.

“Na gode Samha.”

Ita dai har yanzu jikinta rawa yake yi.

Sakina tana komawa dakinta tayi ta kaiwa tana komowa. Mamaki ya isheta. Tabbas Samha ce ta kaiwa kare abincin nan. Tsoro ya bayyana a fuskarta. Idan ta gayawa Zayyad ta tabba ta yau ko mintuna goma ba zata sake yi a gidan ba. Sannu a hankali ta tuna da yadda ya saketa saki uku.

Rayuwarsu na aure a baya babu kyawun gani. Bayan saki uku da yayi mata ya kuma bita da dukan da har gobe tana dauke da tabonsa.

Ta tuna haduwarsa da lalurar mantuwa ita ce silar sake dawowa rayuwarsa a karo na biyu.

“Duk ranar da ya dawo cikin hayyacinsa ya gane komai shikenan na tashi a tutar babu kenan? Noo bazan bari har ya dawo hayyacinsa ban raba gangar jikinsa da numfashinsa ba.”

Ta cigaba da zuzzurfan tunaninta. Daga karshe ta daga waya ta kira Alhaji Bako,

“Abba akwai matsala. Amaryar nan tashi da ya auro yadda kasan wata c.i.d dinsa. Dazu na saka masu abincin bera su dukka, sai yarinyar nan ta shiga daki ta dauko wani abinci, wai dama nasa yana daki. In takaita maka maganar nan tana daukar abincin da na zuba guba takaiwa karenmu yanzu karen ya mutu.”

Alhaji Bako ya mike tsaye.

“What! Bai dai gane komai ba ko?”

Ta numfasa,

“Hmmmn… Bai gane ba. Na dai ga sun shiga daki bansani ba ko zata gaya masa. Abba idan ya gaya masa na shiga uku, kada a sake maimaita abinda ya faru a baya.”

Ya girgiza kai,

“Ina da hanyoyin maganinsa. Kada ki damu.”

Har Samha ta gama kwanakinta bakwai babu abinda take yi sai hidimarsa. Yanzu tausayinsa take ji, tayi alkawarin bashi kariya har na tsawon shekaru biyunta.

Sakina kuma tunda ta ga Samha ba ta gaya masa ba, ta saki jikinta.

Su Safina sai rawar kafafu akeyi yau ta karbi girki. Ita kuma Samha ma’aikata suna ta kwashe abubuwan bukatunta suna mayar da shi sashenta na qasa. Ba karamin kyau sashen yayi ba.

Sai farin ciki take, tana daukar ko ina na gidan a wayarta.

A haka Zayyad ya shigo ya sameta. Murmushi kawai yayi, yana son ganin yarinyar tana cikin farin ciki.

Da hannu ya yafitota. Har ta fara sabawa da shigewa jikinsa ya manna mata sumba a goshi.

“Yayi maki kyau?”

Ta gyada kai,

“Yayi kyau Uncle.”

Ya shafi kanta dankwalin ya subuce ya fadi. Kwantaccen sumarta ya bayyana. Hannunsa yakai yana shafa gashin.

“Gashinki yana da kyau.”

Tayi shiru ba ta ce komai ba. Wani iri take ji a jikinta.

“Ahh lallai wuri yayi kyau.”

Da sauri ya saketa yana ja baya. Sakina ce ta shigo ranta a jagule da yadda ta gansu. Dama kuma abinda tazo ta gani kenan.

“Wuri yayi kyau masha Allah.”

Duk basu ce mata komai ba, sai idanu da suka rakata da shi.

“Allah ya sanya alkhairi.”

Da kyar Samha ta ce,

“Ameen.”

Ta durkusa tana daukar dankwalinta. Sakina ta kafe gashin Samha da kallo. Duk a zatonta karin gashi take yi.

Zayyad ya karasa shigewa ciki yana duddubawa. Shi kansa wurin yafi masa kyau sosai fiye da saman.

Yana wucewa Sakina ta watsa mata mugun kallo, sannan ta fice tana jin zuciyarta kamar zata faso kirji.

“Kin dafa abinci?”

Ya tambayeta a lokacin da ta biyo bayansa.

“Eh. Amma yau ba anan zaka ci abinci ba.”

Tayi maganar tana yi masa kallon Allah ya tsareka.

Ya girgiza kai,

“Kullum ki dinga dafa mini abinci, anan zan dinga ci.”

Ta gyada kanta.

Ya fice ya leka dakin Sakina da ke zaune tayi tagumi.

“Zo mu je ki tara mini ruwan wanka.”

Ta mike jiki babu kwari ta bi bayansa. Suna shiga ta fashe da kuka,

“Idan ka gaji da ni ne gwara ka sakeni kawai inyi tafiyata. Wulakancin da kake yi mini yayi yawa. Haba me nayi maka? Agaban yarinyar nan babu irin tozarcin da baka yi mini.”

Bai ce mata komai ba, ya shige bandaki yayi wankansa. Har ya fara kewar Samha. Ya tabba ta zai yi kwanan bakin ciki yau. Haka ya fito ya sameta zaune a bakin gadon. Bai ce mata komai ba, ya kimtsa ya fice masallaci.

Yana dawowa ya sake shiga dakin Samha lokacin ta hada masa abincin. Ta je ta saka key a kofar falon gudun kada Sakina ta sake afko masu.

Sosai yaci abincin ya dora da jus din da ta hada masa.

“Na gode. Allah yayi maki albarka.”

Da fara’arta ta amsa da,

“Ameen.”

Ya kama yatsunta yana cewa,

“Idan kunshin nan ya gama fita zan saka Rahama ta sake kaiki ayi maki. Yayi kyau sosai.”

Ta ce ,

“To.”

Bayan ya fito ne ya leka dakin Sakina ya ce na dawo.

Ta biyo shi falon, sannan ta jere masa abinci.

Yana dubanta ya ce,

“Bazan ci abinci ba na koshi. Amma gobe insha Allahu zan yi wata ‘yar tafiya. So ki tashi da wuri ki shirya mini abincin Break da kuma na launch. Zan tafi da abincin dan bana iya cin abincin wani wuri idan ba ya kama dole ba.”

Sauran kalamansa su suka wanke na farkon. Dan haka ta dan saki fuska.

Har karfe goman dare yana nan a falon yana danna laptop. Daga baya ya fara hamma.

“Ki tashi muje mu kwanta.”

Ta mike da sauri tana kallonsa. Ta gane dakin Samha yake so ya fara shiga, shiyasa ta kafe ta tsare. Ko kallon inda take bai yi ba ya kama hanyar dakin Samha. Ta fara taku zata biyo shi, yayi mata mugun kallo.

“Wai me yake damunki ne? Idan na shigo yi maki sallama meyasa ba ta biyoni sai ke dan jarabar kishi. Ko angaya maki idan na shiga cinyeta zanyi?”

Ta dawo kawai ta zauna tare da daure fuska. Duk da haka yana shiga sai da ta je kofar dakin tayi masu labe.

“Meyasa kike barci a falo?”

Ta dan bude idanunta, a lokacin da ya daga kanta ya saka akan kafafunsa, yana shafar dan sajenta na gefen kai.

“Barcinne ya kwasheni.”

Wani abu ya dinga jansa har sai da ya hade bakinsu wuri guda. Ba ta hanashi ba, jikinta yayi lakwas. Hakan yasa ya kara kaimi wurin tsotsar lallausar bakinta. Dan kansa ya zare bakinsa. Sannan ya ce,

“Mu kwana lafiya.”

Ba ta amsa ba, amma kuma ta kafe shi da idanu har ya bude kofar. Sakina ta dage sai cusa kunnuwa take yi. Da ta ji shiru zuciyarta ta dinga gaya mata kawai yana aikata wani abu ne da ita. Tayaya zai satar mata girki?

Yana fitowa suka kusa cin karo. A firgice ta ce,

“Naga ka dade ne nazo inkiraka.”

Bai ce komai ba ya wuce yana jin jikinsa babu kwari. Dole ya sake watsa ruwa sannan ya haye gadon. Ta kasa jurewa yadda ya kyaleta, dan haka ta dinga shafa jikinsa tana masa wasu abubuwa. Bai san lokacin da ya biye mata ba. Yadda taga yana rawar jiki akanta ya faranta mata. Hakan yasa ta gane ashe tana da mahimmancin da zai kalleta.

A ranar Sakina ta kwashi gara, wanda yayi amfani da ita a matsayin Samha. Gaba daya gizo ta dinga yi masa tana juyewa sak! Samha.

“Na gode Samha. Allah yayi maki albarka.”

Bude idanunta tayi ta fasa kuka,

“Yanzu ni ce kuma Samha? Wani irin wulakanci ne wannan akan shimfidarmu muna sunna kana tunanin da wata kake yi.”

A kunne ya rada mata,

“Kubutar baki ne, amma kema kinsan ke ta musammance.”

Nan da nan ta yarda da abinda yace, suka mori daren kamar basu taba samun wata matsala ba.

<< Miskilin Namiji 9Miskilin Namiji 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×