Skip to content
Part 16 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Ita kuwa Samha kai tsaye gidansu Zayyad ta nufa ta gaya masu cewa shi ya ajiyeta, yana sauri zai je kaduna. Sharifat ta ji dadin zuwan Samha, haka ma Umma da Abba. Abba ya tambayeta me ya sameta a goshi? Ta dan shafi wurin ta ce bigewa ta yi. Daga nan Dakin Sharifat ta shige ta yi Sallah sannan ta haye gado, kasancewar akwai barci a idanunta. Cikin barci ta ji muryar Sakina tana kuka tana gaya masu Samha ta fasa mata kai, kuma Zayyad ya koreta ya ce kafin ya dawo ta bar masa gida. Abba ya jinjina kai yad ubi Umma.

“Me yaron nan yake so ya zama ne?”

Umma ta dubi Sakina ta ce, “Ita kuma waye ya fasa mata kai?” nan da nan idanun Sakina suka raina fata. Ta fara kame-kame. Umma ta girgiza kai,“Kema ki shiga ki zauna kafin ya dawo.” Ta shige cikin dakin Sharifat tana cewa, 

“Wannan Umman ‘yar renin wayo ce don ta samu na zo gidanta?”

Idanu ta hada da Samha. Ta firgita ta juya da sauri zata fice. Samha ta yunkura ta zauna tana cewa,

“Dawo ki karashe zagin”

Sakina ta dawo tana yi mata mugun kallo,

“An gaya maki tsoronki zan ji?”

Samha ta girgiza kai ta mike ta shiga bandaki. A lokacin idanun Sakina suka kai kan wayar samha da a ke ta kira. Sunan Uncle Zayyad ta gani baro-baro. Nan da nan kishin ya motsa, don haka ta daure fuska tana jin zuciyarta tana tafasa. Shi kuma wanda zata gayawa matsalarta a yau shi yayi mata fyade, ya hada wurin da mahaifiyarta kadai ke da iko da wurin, wurin da har abada babu wanda ya isa ha lasta mata shi. Hawaye suka wanke mata fuska. Mahaifiyarta kuma ba wani shiri suke ba, saboda yadda take da son yi mata nasiha.

Samha ta tsaya shiru a bandakin gabanta yana tsananta faduwa, ko kadan bata ji dadin zuwan Sakina ba, ta tabbata Sakina zata iya bata mata aiki. Ta yi shiru tana tunanin abin yi. Fitowa ta yi, ta dauki hijabinta da wayarta ta fice. Cikin ikon Allah babu kowa a falon, don haka ta yi saurin ficewa daga gidan, tana tafe babu ko waige bare har mai gadi ya yi tunanin wani abu. Kai saye wani babban chemist ta nufa, ta ce a bata maganin barci mai karfi. Suka bata ta karba ta juya. 

Tana shigowa ta ci karo da Abba, da sauri ta durkusa tana gaida shi. Ya kalleta ya ce, 

“Ina kika je?” Ta dan sosa kai sannan ta ce, “na je siyan magani ne.” 

Bai ce komai ba ya wuce. Sai yanzu ta kula da kamar baya cikin walwala. Har ya kai bakin kofa ta ce, “Abba ba ka jin dadi ne?”

Ya yi murmushi ya ji dadin maganarta, “Babu abin da ke damuna Samha. Allah ya yi maki albarka.” 

Duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, sai dai ya zama dole ta cikasa aikin da ta fara, da ba haka ba da tuni ta tafi ta bar Zayyad ya karasa rayuwarsa a hakan. 

Bata samu daman zuba masu maganin ba, kamar yada ta yi ninya, domin ta samu har an gama abinci. Sakina kuwa sai habaice-habaice, da ta dame su, sai suka dauko Alqur’ani ita da Sharifat suka shiga yin tilawa. Tana kwance tana danna waya tana jin su. Kiran wayar mahaifinta ya shigo wayarta, da sauri ta katse kiran. A yanzu babu wanda take jin tsanarsa kamar mahaifinta. 

Da misalign karfe ukun dare, kowa ya yi nisa a makwancinsa, Zayyad da Samha kuwa barci ya kauracewa idanunsu. Shi yana can yana tunanin halin da take ciki,ita kuma tana nan tana tunanin yadda za ayi ta gano katin asibitin gidan. 

Har asuba ta yi bata samo mafita ba, dole ta yi Sallah ta ci gaba da karatun Qur’aninta. Da safe bayan ta yi wanka aka bukaci duk su fito a karya a teburin cin abinci, wanda wannan ka’ida ce ta gidan. Samha ta so a kyaleta a dakin, amma sai Sharifat ta nuna mat aba zai yiwu ba. Tana fitowa ta durkusa har kasa ta gaida mutanen gidan, sannan ta dan dubi Sakina ta ce, “An tashi lafiya?” Sakina ta hade rai ta kuma ki amsawa. Samha bata damu ba, ta janyo kujerarta. Bata wani ci abincin ba, ta dubi Umma ta ce, 

“Umma ko akwai family card? Ina so in je asibiti ne bana jin dadi.”

Gaba daya aka yi mata Allah ya kara sauki, amma banda Sakina, da ta mayar da hankali wurin cusa dankalinta.

“Sharifat idan kun gama ki dauko mata family card din sai ki rakata, ku je driver ya kaiku.”

“Ok. Ni na gama ma, idan kin gama kawai ki je ki shirya mu je.”

Sharifat ta shiga dakin, sai gata ta fito da kati. Suna Mota babu wanda ke cewa wani komai, sai dai lokaci zuwa lokaci Sharifat tana yi maata sannu. 

“Bari in kira yaya in gaya masa.”

Da sauri Samha ta rike hannunta,

“A’a kada ki tada masa hankali yana aiki.”

Sharifat ta mayar da wayarta, sannan ta kalleta ta ce mata,

“Amma tun jiya baku yi waya ba, ina kula da yadda ake kiranki kina katsewa. Ko dai kun yi fada ne?”

Samha ta yi kamar bata ji me ta ce ba, ta ci gaba da karanta wasikar jaki.

Bayan sun isa ne, aka fitar masu da file, Samha ta shiga. 

“Amma asibitin nan ya dade.”

Ta tambayi dokto din tana kallonsa. Shima ita ya kalla sannan ya ce, 

“Eh ya dade gaskiya. Sai dai an taba rufe shi na tsawon wasu shekaru daga baya aka bude.”

Samha ta dube shi da sauri,

“Meya sa aka rufe?”

Kafin ya yi Magana wata dokto ta shigo, take gaya masa ya zo ana nemansa aikin gaggawa zai shiga. Dan haka ya mika mata Samha shi kuma ya wuce. Samha bata so hakan ba, ta dan jawo file din tana dubawa, a lokacin ita dokto din ta mayar da hankali wurin duba wasu takardu. Babu wata alama da zata nuna wannan file din tsohon file ne, don haka ta ajiye tana jin tabbas akwai tsohon kati wanda babu mamaki an daina amfani da shi ne

Bayan ta yi mata bayanin tana fama da ciwon kai, da rashin barci aka rubuta mata magunguna, ta je ta karbo suka wuce. A hanya take cewa Sharifat,

“Amma dai ba a asibitin nan aka haifeku ba ko?”

“Anan aka haifemu mu dukka.”

“Amma naga katin nan kamar ba wacce ake amfani da ita ba.”

Sharifat ta dan muskuta sannan ta bata amsa,

“Haba ba katin bane. Wannan file din tuni an rufe shi, tun lokacin da aka ce an rufe asibitin tsahon shekaru.”

Samha ta jinjina kai. Bayan sun koma ne, ta sami Sakina tana ta taunar cingam, ita kuma ta kwanta domin ta koma barci. Har yanzu Zayyad kiranta yake, tana so ta cusgunawa Sakina sai ta daga.

“Haba Samha mene ne haka? Ya za ayi in yi ta kiranki kina kallo ki kasa dauka?”

Ta dan yi kasa da murya.

“Ina jinka barci nake ji.”

“Ki yi hakuri ki yafe min na yi kuskure.”

“Idan na tashi zamu yi Magana.”

Ta katse kiran, sai kuma ta mayar a kunne,

“Nima nasan kana sona, ka kula da kanka.”

Sakina ta zabura. Samha ta tashi zaune ta nunata da yatsa, 

“Idan kika yi kuskuren taba ni, na yi alkawarin baki mamaki Wallahi. Kada ki ga muna gidan surukai, tsaf! Zan koya maki hankali.”

“ke har kin isa ki koya mini hankali? Ji min ‘yar tatsitsiyar yarinyar nan haihuwar jiya-jiya. Ke din banza! Wallahi kika yi min sai dai in barki kwance. Ko don kin ga na fasa maki kai, kin ram ana kyaleki? Sai dai idan ba gida daya zamu koma ba, sai na hallakaki Wallahi! Shi kansa Zayyad din bai isheni kallo ba, bare ke banza a banza, gayyar tsiya haihuwar titi.”

Da sauri Umma ta karaso ciki, dama kuma yadda take daga murya, Samha tasan za’ayi haka shiyasa ta yi banza da ita, tana ci gaba da latsa waya.

“Innalillahi wa inna ilaihiraji un. Sakina! Dama tunda kika zo kina fadin karya da gaskiya nace ban yarda da ke ba. Sai gashi da yake bata da alhakinki ai gashi nan kin zayyane komai. Yanzu kisa kike Shirin yi? Samhar zaki kashe? To bari shi Zayyad din ya dawo baza a taba yin wannan kuskuren da ni ba.”

Sakina ta murguda baki, ta kauda kai tana kananan maganganu. Umma ta fice tana girgiza kai. Samha ta dubeta tana murmushi sannan ta yi Magana a hankali,

“Girmar banza girmar wofi. Kina zaune yarinya karama zan zautaki Wallahi. Sannan kinyi kadan ki ga bayana. Ke uban da ya haifeki ma ya yi kadan ya ga bayana duk iya tuggunsa kuwa bare ke. Duk ranar da kika ga kin barni kwance kuwa, ki rubuta ki ajiye daga ranar na yarda in zama baiwarki, zan yi ta maki bauta har karshen rayuwata.”

Sakina ta tashi a zabure, ta yi kan Samha. Sai dai mugun kallon da ta aika mata ya ja burki. A lokacin kuma Sharifat ta shigo tana kallonta da mamaki.

‘Ke kuwa Anti Sakina me yake damunki? Tun dazu kike takalar Anti Samha bata baki amsa ba, bata kula ki ba, Umma ta yi maki Magana, yanzu kuma kin mike zaki yi dambe da ita. Tunda bakya jin maganar kowa sai a gayawa Yayan.”

Sakina ta juyo kamar zata cinye Sharifat.

“Munafuka ai nasan bakinku daya. Bakya jin ita me take gaya mini ne? Ko don kun tsaneni?”

Sharifat ta girgiza kai ta ce, 

“Anti Samha ki yi hakuri.”

Samha ta koma ta kwanta tana gyada kai. 

Umma da kanta ta saka aka canzawa Samha daki, tunda ta ji furucin Sakina ta tsorata da ita. Hakan kuwa ba karamin dadi ya yi wa Samha ba, domin zata samu damar yin abin da ta gadama.

Yau din ma maganin barcin bai samu shiga ba, domin tana ji a jikinta a wannan dakin karatun kadai zata iya samun abin da take nema.

“Sharifat ko zaki taimaka ki samo mini key din dakin karatun Abba? Wani tsohon littafi nake nema kuma ranar da na shiga naga kamar yana da shi.”

Sharifat ta dan yi shiru daga bisani ta ce.

“Sai dai mu yi irin na rannan. Kinsan halinsa.”

Samha ta gyada kai. Sharifat ta je ta dauko ta bata. Ita kuma ta ajiye tana cewa, 

“Bari in bari sai can anjima.”

Duk hirar da suke yi Sakina tana cikin bandaki, don haka bata ji me suke cewa ba.

Karfe hudun asuba ta tashi kowa, yana barci ta sadado ta nufi dakin karatun. Ta kunna wuta tana sanda. Wasu hotunan ta kwaso, amma basu take da bukata ba, don haka ta dage wurin binciken komai. Wani katon file ta gani, tana kokarin dauka ta ji motsi. A hankalinta ya yi matukar tashi, jikinta babu in da baya rawa. Ta dauke numfashinta kafafunta suna rawa. Motsi ta ji alamun za’a shigo, ta rude kwarai. Gumi ta dinga tsattsafo mata. Ji ta yi an bude kofar an shigo. A lokacin kiris ta suma. Kasha fitilar akayi, sannan aka rufe kofar.

“Anti Samha.” Ta ji an kira sunanta a hankali. Sai yanzu ta gane muryar Sharifat ce,

“Ki zo mu fita ga Abba sakkowa.”

Duk suka dauke numfashi, a lokacin da ya sakko yana dube-dube.

“Waye anan?”

Suka sake dauke wuta. Bayan ya gama dubawa ya wuce. Suna sanda suka sake jin motsinsa. Ita kuwa Samha kiris fitsari ya zubo mata tsabar tsoro. Tana da tabbacin muddin ya ganta sai jikinsa ya bashi wani abu. Bayan sun ji shiru ne, Samha ta mika hannunta ta dauko katon file dinnan ta cusa a jikinta. Sauri-sauri suka fito Sharifat tana rufe kofar ta ji ana Magana a bayanta,

“Me kuke yi a cikin dakin nan?”

Duk suka juyo cikin tsananin firgici. 

“Umma don Allah kiyi hakuri wani littafi Anti Samha take nema, shi ne muka zo mu duba.”

Umma ta girgiza kai,

“Ku yi sauri ku bar wurin nan, kun dai san yadda Abbanku ya hana a shigar masa dakin karatu ko?”

Duk suka gyada kai suka bar wurin da sauri. Lokacin ya fice masallaci, kasancewar wataran tun hudu da rabi yake fita, har gari ya dan yi haske. 

Samha tana shiga dakin ta saki ajiyar zuciya.  Ita kuma Sharifat ta wuce dakinta. Da sauri ta je ta sakawa kofar key, sannan ta dawo ta zauna ta bude file din. Tarin tarkace ne a ciki. Sai wani kundi, sai kuma katin da take nema. Bata bude kudin ba, katinne a gabanta, don haka ta zaro shi tana murmushi, sai kuma katin haihuwar yayan Zayyad mai suna Mukhtar wanda aka haife shi a 10-10-1980 da sauri ta duba sunan wacce ta karbi haihuwarsa, sunanta Dr. Rose Abraham. Hakan yasa ta zakulo dukka katin yaran gidan. Dukka mace guda ce, ta karbi haihuwarsu, da alama ita ce likitansu a wancan lokacin. Amma na Sharifat ba ita ce ta karba ba. Ta dade tana kallon katin haihuwar Zayyad tana wani Nazari. Jikinta ya fara yin sanyi game da tunanin da take yi na cewa ba su suka haifi Zayyad ba. Wani tunan ta yi, sannan ta mayar da sauran tarkacen cikin akwatinta ta rufe.  

Washegari da safe, bayan an gama karyawa ta bukaci Umma ta sanya a mayar da ita gidanta ta ji sauki. Kuma Dokto kila ya dawo yau tana so ta yi masa abinci. Umma ta jinjina kai. Mamakin danta take yi da har yanzu bai kirasu ba, alamu sun nuna yana jin zafinsu sosai.

Sharifat ta rakata suka yi dukkan ayyukansu tare. Sakina ta ji bakin cikin komawar Samha. Da a ce ba zai yi mata komai ba, idan ya dawo ya ganta da babu abin da zai hanata komawa, sai dai irin kalaman da ya yi mata sun tsorata ta.

Sharifat tana komawa, Samha ta saka riga da wando, ta dora bakar baya ta yane kanta da gyale. Taxi ta dauka har zuwa asibitin.

<< Miskilin Namiji 15Miskilin Namiji 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×