Skip to content
Part 18 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Ta hadiye kukanta tana sake kallonsa.

“Da yana da ikon yin ajalina da tuni ya yi hakan. Ka taimakeni na yi maka alkawarin babu wanda zai san mun yi irin wannan tattaunawar da kai.”

Ya jinjina kai ya dawo ya zauna yana dubanta.

“Zayyad abokina ne tun yarinta baki yi karya ba, sai dai bani da masaniyar me yake faruwa da rayuwarsa. Na rabu da Zayyad lafiya lau, bayan mun dawo daga ofis ya ce mini zai je ya gaida su Umma. Ni kuma na wuce gida akan zamu hadu washegari da safe. Abin mamaki sai ga kiran waya, wai Zayyad yana cikin wani hali. Na sami zuwa asibiti, amma ban sami wanda ya bani amsar tambayoyin da suke zuciyata ba. Babban tashin hankalin shi ne Zayyad yana farfadowa ya farfado yana tambayar wane ne shi. Hankalinmu ya tashi, ni dama ban iya zuwa ba saboda kuka.”

Ya dan numfasa yana kallon Samha sannan ya ci gaba da cewa,

“Kwatsam Alhaji Bako ya kirani, a tare da shi akwai mahaifin Zayyad. Na yi mamakin furucinsu. Sun tabbatar mini idan na sake kusantar in da Zayyad yake duk abin da ya faru da ni, kada in yi kuka da kowa, in yi kuka da kaina. Sannan suka ce in mance na taba sanin Zayyad kamar yadda ya mance ya taba sanina. Babban tashin hankalin da na shiga shi ne, yadda ina ji ina gani Zayyad ya sake auren matar da ya rabu da ita, wacce a gabana ya yi mata saki har uku! Kuma diya ce a wurin Alhaji Bako.”

Ya yi shiru idanunsa suka kawo hawaye. Samha ta jinjina kai ta ce,

“Meya sa ya yi mata saki uku? Kuma ya akayi ya sake aurenta?”

Shirun ya sake yi kamar mai tunanin abun da zai fada,

“Saki na farko da ya yi mata, akan wulakanta masa iyaye ne, saki na biyu wanda shi ne na ukun, akan ya kamata da mai gadin gidansa ne, tana aikata zina. A tare muka shigo gidan, shi ya shige ciki ni kuma ina falo. Da yake mai gadin matashi ne, ita ta ce a dauke shi aiki, ashe saurayinta ne. A ranar Zayyad kamar zai yi hauka. Bayan ya saketa ta tafi gidansu sai ga mahaifinta Alhaji Bako, ya tabbatarwa Zayyad bai isa ya sakar masa ‘ya ba.”

“Kayi hakuri ban tari numfashinka ba.Ta sake yin wani aurenne? Ko a haka ta dawo gidansa?”

Ya furzar da zazzafan huci.

“Bata sake yin wani auren ba. Domin da na ji labarin ya sake aurenta sai na bibiyi lamarin. Anan na samu sunyi amfani da mantuwar da ya samu ne suka kara bashi ita. Iyayensa sunyi iya bakin kokarinsu akan su jawo hankalinsa a boye ba tare da sanin Alhaji Bako ba, sai dai hakan bai yiwu ba, a sakamakon idanunsa sun rufe Sakina ta hada da asiri, shi kuma ya kwashe abin da iyayensa suka ce ya sanarwa Sakina, ita kuma ta gayawa mahaifinta. Lamarin da ya janyo gaba mai tsanani kenan a sakanin mahaifin Sakina da kuma mahaifin Zayyad. Duk da ana zargin akwai wani gagarumin abu a boye a tsakaninsu.”

Samha ta yi shiru.

“Yanzu babu yadda za ayi ka iya taimakawa Zayyad?”

Ya mike tsaye yana dubanta.

“Ki bani lambarki, zan tura maki adireshin wuraren da muke zuwa, da kuma hotuna da wasu maganganu da zaki dinga yi masa, insha Allahu zai taimaka masa wajen dawowar tunaninsa.”

Ta jinjina kai, ta mika masa wayar ya saka lambar. Still hirar da suka yi duk ta nada a wayarta.

Haka suka yi sallama Samha ta koma ciki, ta kasa tsaye ta kasa zaune.

*** ***

A can bangaren kuwa, sunan Dokto Zayyad ya mamaye ko ina, duk in da ka bi maganarsa ake yi. Gidajen Jaridu duk sun wallafa shi, a matsayin wanda ya cafke wani likita yana kokarin sakawa mai girma shugaban kasa guba.

Wannan lamari ya girgiza al’umma daga ciki har da Alhaji Bako. Ya fusata, a wannan karon bai ki ya rungumi Zayyad da bomb duk su mutu ba.

Yana zaune a gaban shugaban kasa, yana latsa wayarsa. Kiran waya ya shigo masa, ya daga yana murmushi.

“Kai Zayyad! Ka yi kadan Wallahi ka lalata mini aikina.”

“Dakata Alhaji Bako! Kai waye? Me ka isa kayi? In har ina raye baka isa ka cutar da shugaban kasa ba. Me ya yi maku? Saboda zalunci? Tun lokacin da ka ci nasarar saka camera a ofis dina, zuciyata ta daina yarda da Dokto Salim. Saboda nasan ka riga ka kwashi lambarsa da email dinsa. Hakan yasa ko ruwa ban yarda Dokto Salim ya sakawa shugaban kasa ba. Da gangar na dan fice domin in ga shin tunanina gaskiya ne ko kawai zargin faruwar hakan nake yi. Sai gashi komai ya bayyana. Ina baka shawara tunda wannan bakin zaluncin bai yiwu ba, ka gaggauta sauya sana’a. Don wannan bata karbeka ba.”

Ya datse kiran yana sake mamaki. Ganin Alhaji Mamman ya yi, yana kallonsa. Da sauri ya karaso ya rike hannunsa yana yi masa sannu.

“Dama Alhaji Mamman ne ya aiko a kasheni?”

Zayyad bai da amsar da ya wuce eh domin ya riga ya ji komai.

“Amma rankashidade me kayi masu ne haka da suke neman rayuwarka?”

Shugaban kasa ya dan muskuta sannan ya ce,

“Ba zan iya cewa ga dalili mai karfi ba. Amma abin da na sani dai, da ni da Alhaji Salisu, da Alhaji  Bako, aminai ne da muka taso tun muna yara. Masoyan junane. ‘Yan uku ma ake kiranmu. Har muka girma bamu taba rabuwa da juna ba.”

Zayyad ya dakatar da shi ganin yana haki.

“Ka bari ka sake samun sauki rankashidade ka ga yanayin jikin naka sai a hankali.”

Bai yi musu ba, ya mayar da kansa yana ajiyar numfashi.

Dole Zayyad yana da bukatar zuwa gida ya ga iyalansa, don haka ya bar jinyar Shugaban kasa a hannun wani amintaccensa, ya kuma kara karfin matakan tsaro, sannan ya dawo gida.

Gidan babu kowa kamar yadda ya yi tsammani. Kai tsaye gidansu ya nufa. Ya sami Sakina a gidan, bata aikin fari bare na baki, sai dai ta wanke goma ta tsoma biyar. Umman ce ta dinga yi masa fada, akan sabuwar rayuwar da yake so ya daukarwa kansa. Sannan ta ce ya dauki matarsa su wuce gida. Ya yi mamakin da Umman ta gaya masa kwanakin Samha a gidan. Bai ce komai ba, don baya so a gane akwai matsala a tsakaninsu. Bayan ya dauki Sakinan ya kaita gida ba tare da sun cewa juna uffan ba.

Ya ci gaba da kiran wayar Samha, daga karshe aka ce masa a kashe. Ko kadan bai yi tunanin zuwa gidan Rahama ba, sai ya gyara kwanciyarsa kawai.

Sakina ta zo ta zauna kusa da shi tana yi masa tausa.

“Don Allah kayi hakuri ka yafe mini. Na yi kuskure insha Allahu bazan sake ba, kuma ba dadin baki nake yi maka ba, da gaske na gyara rayuwata.”

Ta dinga yi masa abubuwa. Samha kuwa shirinta ta gama yi tsaf! Anti Rahama bata nan, don haka ta bayar da sallahu akan ita zata koma gida.

Haka kawai jikinta bai bata ba. Tana isowa gidan ta karasa ciki. A hanyar shiga dakin Sakina ta ganshi, babu ko riga a jikinsa. Nan da nan jikinta ya kama bari, musamman yadda ta ga idanunsa sun rine zuwa ja. Tuntuben karya ta yi, ta zube anan tare da dan dauke numfashinta bayan ta yi ihu.

Da sauri ya saki Sakina ya karaso wurinta yana jijjigata. Sakina tana tsaye idan ranta ya yi dubu to ya baci.

Ta karaso ta na ci gaba da shafa shi.

“Ka zo mu je my Dokto zuwa anjima zaka ga ta wartsake kada ka bari wata ta bata mana jin dadinmu.”

 Wani irin tureta ya yi sai gata a kasa, sannan ya ja tsaki ya dauke Samha ya shiga da ita bangarenta. Sakina ta dube su, saboda bakin ciki kawai ta fasa kuka.

Samha ta dan bude idanunta bayan ya shimfideta ya hade bakinsu wuri daya wai yana zuko mata iska. Ta bude idanun ta kafeshi da su. Kyawunsa ya zarce yadda ake tunani. Ya dago idanu ya kalleta. Duk suka tsaya kallon juna. Cikin wani irin kasala ta shafi fuskarsa ta kai yatsunta biyu cikin bakinsa. Ya cafkesu yana tsotso kamar ya sami sweet.

Dukkansu sun shiga wata duniya, jikinta ya dinga amsar sakonninsa ko ta ina. Ta lumshe idanunta, a lokacin da ta ji ya saki yatsunta, ya saka hannu cikin wuyan rigarta, ya ci nasarar taba in da ya rikirkitata. Jikinta ya fara rawa. Batasan yadda akayi ba, ta mika masa bakinta yana tsotso. Da sauri ta fizge kanta tana ja da baya, tare da goge bakinta tana zare idanu.

Ta tuna Sakina tana dauke da h.i.v gashi a yadda ta same su ya tabbatar mata akwai abin da ya faru a tsakaninsu. Yana kokarin sake jawota ta ja da baya tana cewa,

“Kada ka taba ni. Kila ma ka riga ka kwashi cutar h.i.v wa ya sani? Innalillahi Wa inna ilaihiraji un.”

Ta fashe da kuka sosai. Shi kuwa da mamaki yake kallonta da rinannun idanunsa. Ransa ya soma baci saboda a yanayin da yake ciki yana tsananin bukatar mace.

“Ke kinsan wahalar da ni za ki yi shiyasa kika hanani zuwa wurin Sakina? Idan ba zaki iya faranta mini ba, bari in koma in da zan sami farin ciki. mtsww..”

Ya mike a fusace. Yana kokarin murda handle din kofa, ya ji muryarta mai sanyi tana cewa,

“Idan baka sadu da ita ba, kada ka fara yin kuskuren saduwa da ita, idan kuma ka riga ka sadu da ita, ina baka shawarar ka gwada kanka domin tabbas kana da cutar kankamau!”

Da sauri ya waigo yana dubanta. Duba mai cike da mamaki.

“Meya sa zaki dangantata da cutar kanjamau? Wani irin zaman kishi ne haka kuke yi da juna?”

Zai fice ya saki jin ta ce,

“Sai kayi danasanin rashin saurarona Wallahi.”

Bai ce mata komai ba ya fice, kansa yana jujjuyawa. Kai tsaye falo ya nufa ya sha ruwa mai sanyi sannan ya zauna yana jin kansa yana jujjuyawa.

Sakina ta karaso wurinsa tana shafa kirjinsa. Yana jin yadda take shafa shi, sai dai kalaman Samha sun yi rugu-rugu da zuciyarsa, ta yadda baya jin ko digon sha’awa. Da ya ji zata dame shi, ya cire hannunta ya ce,

“Samha bana jin dadi don Allah ki rabu da ni.”

Ta mike cike da masifa,

“Au! Da sunan Samha kake kirana? Ni yau dole ka biya mini bukatata, saboda ina fama da sha’awa kwana biyu. Kasan hakkina ne idan ka hanani kuma Allah ba zai barka ba.”

Ya mike yana watsa mata mugun kallo, sannan ya koma dakin Samha. Ta yi rigingine hawaye ya yi mata kaca-kaca.

A hankali ya zauna a gefen gadon, ya jawota jikinsa. Ta kwanta luf… Ya saka hannunsa yana shafa bayanta.

“Samha ki gaya mini me ke faruwa ne?”

Daga kanta ta yi, sannan ta dube shi sosai,

“Ka yarda da ni? Ka yarda ba zan taba cutar da kai ba? Ka yarda ba zan yi maka karya ba?”

Ya shafi sumar kansa, sannan ya daga kai,

“Na yarda Samha.”

Ta jinjina kai,

“Daga yau kada ka sake kusantar Sakina. Akwai matsala.”

“Samha na yarda akwai matsala. Amma na fi son ki yi mini bayani sosai ta yadda zan fahimceki.”

Ta dauko wayarta ta kunna masa tare da mika masa. Tun kafin ya gama kallo ya mike tsaye jikinsa yana rawa,

“What! Innalillahi Wa inna ilaihiraji un.”

Ya juya a fusace, da sauri Samha ta rike shi sosai ta ce,

“Don girmar Allah ka dawo.”

Ta rungume shi tana bubbuga bayansa. Sai da ya dan sami natsuwa, amma jikinsa bai daina rawa ba.

“Ka yi hakuri don Allah. Akwai ranar da zaka nuna irin fushin nan, amma ba yanzu ba. Idan ka aiwatar da wani abu za a gane shirinmu. Kasan ashe ka taba auren Sakina a baya kuma ka saketa saki uku? Daga baya mahaifinta ya sake aura maka ita.

A razane ya juyo yana kallonta. Ta gyada masa kai.

“Ina so ka kwantar da hankalinka, insha Allahu komai ya kusan zuwa karshe. Ni dai babban addu’ata ita ce ko a fuska kada ka nuna damuwar nan.”

Zayyad ya jinjina kai tare da komawa ya hau kan gadonta ya kwanta. Cikin ‘yan mintuna barci ya yi awon gaba da shi. Samha ta fito domin ta je ta dora masa girki.

Tana shiga kitchen Sakina ta yi saurin murda kofarta tana so ta shiga sai dai ta ji shi gam! Samha ta fito tana dariya.

“Wai har sai yaushe tunaninki da kwakwalwar kifin da ke dankare akanki za su daina gaya maki ni ba shashasha ba ce kamar ke! Ko kin ga na yi kama da wacce ta taba haduwa da hauka irinki ne? Tayaya zan bar kofa a bude bayan nasan akwai bera a gidan nan, berar ma jaba!”

“Ke! Samha, ki kama kanki, kisan irin maganar da zaki dinga gaya mini. Ni kike kira jaba? Wallahi duk mugun asirinki sai na bankado duk wani sirrinki.”

Samha ta yi dariya sosai tana kallonta,

“Asiri? Sirrina ai ba wani mummunan abu bane da zan ji tsoron duniya ta sani, ke kuwa naki sirrin ko kare ba zai shinshina ba, saboda tsabar doyinsa. Ke har ana maganar bankado sirri kina saka baki? Fankon banza! fankon wofi, wacce take kasa sarrafa kanta ayayin da shedan ya buga mata ganga. Kuma kin ga key nan a hannuna, idan kina da karfi sai ki zo ki kwace.

Ta koma kitchen tana ci gaba da girkinta. Sakina kuwa suman tsaye ta yi, gaba daya yarinyar da ta gama rainawa, tana neman ta zame mata kadangaren bakin tulu.

Jikinta a sanyaye ta koma ta zauna tana kada kafafu. Har Samha ta gama girkinta ta kasa tuna irin tunanin da ya kamata ta yi, tana kallonta ta shige da kuloli ta sakawa kofar key.

Sakina ta rushe da kuka tana jin zuciyarta kamar zata fito kirji. Ta gama cin burin sakawa Zayyad ciwon kanjamau sai gashi Samha ta shiga tsakaninsu a daidai lokacin da komai yake gab da faruwa.

Barci ya yi mai cike da mugayen mafarkai! Haka ya tashi duk yadda dakin ke dauke da na’uwarar sanyaya daki, hakan bai hana shi jikewa ba.

Samha ta kalle shi da tausayawa, sannan ta ce,

“Ka yi hakuri ga ruwa can a bandaki na tara maka. Ka je ka watsa ka fito.

Bai yi musu ba, ya shiga ya dinga kwarawa kansa ruwa. Ji yake kamar kwakwalwarsa za ta tarwatse.

Ya fito daure da tawul a kugunsa. Da sauri ta dukar da kanta saboda yadda gabanta ke faduwa. Shi kuma gaba daya ji yake tamkar an zare masa duk wani karsashi.

Fitowa ta yi, ta nufi dakinsa ta bude ta dauko masa jallabiya, sannan ta dawo ta mika masa ya saka. Ta sunkuya a hankali, ta shafa masa mai a kafafu. Duk yana zaune yana kallonta.

Gaba daya kansa ya kulle, ya rasa irin tunanin da zai yi.

Ta zauna kusa da shi, ta zuba abincin. Duk da baya jin cin komai, amma kamshin abincin ya saka shi buda baki, a lokacin ca ta tunkaro shi da cokali.

Ya ci abincin sosai, sannan ya sha zobon da ta hada masa mai dauke da cinnamon.

Ta kama hannunsa suka mike. Falo suka dawo ta kunna masa labarai.

Ta dan kwanta a jikinsa shiru.

Ya saka hannu yana shafa sassan jikinta. Har hannunsa ya kai kan dukiyar fulaninta.

Allah ya dora masa son kirjin Samha, yana saurin gigita shi. Tun tana iya daurewa, har ta sakar masa jikinta yana luguiguitata yadda yake so. Bata san ya aka yi ba, ta tsinci kanta da mayar masa da martani. Anan suka lalace. Tun suna kwance a doguwar kujera har suka dire kasan kafet.

Mahaukacin bugun kofar da ake yi ne ya dawo da su cikin hayyacinsu. Bai taba rikicewa irin na yau ba, haka zalika bai taba tunanin akwai abin da zai iya saka shi jin sha’awa ba, kasancewar labarin Sakina da mahaifinta ya tsaya masa daram! A zuciya.

<< Miskilin Namiji 17Miskilin Namiji 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×