Skip to content
Part 20 of 24 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Bayan aurena da Farida na bar Katsina na koma Kano. Cikin hukuncin Allah kasuwancina ya bunkasa. Duk da haka ban daina karatu ba, haka zalika ina taba siyasa. Na karbi shugabanci tun daga makarantar firamare har izuwa matakin degree dina. Farida ma ban kyaleta ba, na mayar da ita makaranta.

Ganin ci gaba tana ta samuna, yasa na sake komawa wurin su Bako, ganin yadda suke zaune babu abin yi, sannan babu wata ci gaba. Da suka ganni da dukiya, sai suka nuna mini sun hakura, sun yafe mani. Ashe abin ba haka yake ba. Na sami sun yi aure, don haka na ce duk su kwaso iyalansu mu dawo Kano.

Hakan akayi. Suka dawo muka ci gaba da zumunci kamar babu komai.

Na dora su akan dukiyata, amma sai da suka san yadda suka yi, suka kwashe fiye da rabin dukiyata suna gina kansu a boye.

Da na zo na gane hakan sai ban ce masu komai ba, duk kokarina mu hada kanmu.

A lokacin na sami aikin gwamnati a Kaduna. Don haka na saki kasuwancin na koma Kaduna. Dukkansu matansu sun sami haihuwa.

A duk lokacin da Bako ya zo gidana bai da aiki sai na kallon Farida, abin yana damuna, don haka na tattarata muka koma Kaduna. Da ga nan dukiyata gaba daya ta dulmiya suka tabbatar mini da sun zuba kudin a wani kasuwanci kudaden sun dulmiya. Mafarin rasa arzikina kenan. Su kuma sai suka yi kudi.

“Ana haka Farida ta sami ciki. Ban gayawa kowa ba, har ciki ya isa haihuwa. Na tanadi komai na suna. Allah ya nufeta da samun yaro na miji. Don haka na sanarwa su Bako. Anan ma sai da muka yi kamar zamu yi rigima wai ban gaya masu tana da ciki ba. Haka akayi suna yaro ya ci sunan Babana Mahmud muna kiransa da Muhseen.

“Tunda aka haifi Muhseen hanyoyin arzikina suka bude. Na dinga samun ci gaba. Na dinga fito takarkaru kuma ina samun nasara. Muhseen yana da shekaru uku a duniya bazan mance ba. Sun tafi suna a gidan Alhaji Salisu, ba zan iya tuna wani yaro ne a cikin yaransa aka haifa ba. Na tura Farida da driver ni kuma na tafi wani kauye yawon kamfen.”

Shiru ya yi ba tare da ya ce uffan ba. Sai jinjina kai kawai yake yi. Zayyad ya qagu ya ji me ya faru. Don haka ya sunkuyar da kansa, domin ba zai iya tambayarsa ba.

“Kasan me ya faru?”

Ya girgiza kai yana kallon yadda hawaye ke bin fuskarsa.

“Tun daga wannan ranar ban sake ganin Farida da danta ba. A yadda labarin ya zo mani, wai Muhseen ya yi ta amai aka kwantar da shi. Itama mahaifiyar sai ta kwanta jinyar amai da gudawa. A lokacin wai aka kashe su a cikin asibitin. An yi ta nemana ba a sameni ba, Bako da Salisu suka kwace gawansu a hannun ‘yan sanda suka ce ba za a bar musulmai ba, suka jagoranci burne su. Bayan na fito daga kauyen na sami service kai tsaye Farida na fara kira. Sai na ji muryar Hajiya Hannatu matar Salisu, tana kuka tana gaya min abin da ya faru. Ni dai bansan yadda aka yi ba, na tsinci kaina a Kano. Nasan dai na yi ta gudu a mota wanda Allah ne kawai ya tsareni.

“Ina isowa su Bako suka fashe da kuka, suka sanar mani da komai. Ban yarda ba, ban ji na amince ba. Dole na saka aka rufe asibitin, na haukace masu sosai, na kuma ce sai an je makabarta an tone mani su. Da kyar aka shawo kaina.

“Mafarin da na ji muguwar tsanar Bako da Salisu kenan, tun daga nan ban sake waiwayarsu ba, na tsane su, ina ji a jikina sune silar rasa iyalina. Daga nan mummunar gaba ta shiga tsakanina da su. Su din ma basu sake nemana ba, ko da kuwa a waya ne.”

Zayyad ya yi shiru yana wani nazari.

“Daddy ni yaron Alhaji Salisu ne.”

Da sauri ya kalle shi, ya sake kallonsa. Daga bisani ya girgiza kai,

“A’a Alhaji Salisu bashi da yaro kamarka.”

Zayyad ya dube shi sosai,

“Da gaske ni yaronsa ne. Sannan ni surukin Alhaji Bako ne, ina auran diyarsa.”

Zayyad ya zaro hotuna ya nuna masa. Alhaji Mamman ya yi shiru yana nazarin hotunan. Bai mance lokacin da suka dauki hoton ba.

“Meya sa Alhaji Bako yake so ya kashe ka?”

Zayyad ya jeho masa tambayar da ya saka shi barin kallon hoton ya mayar da dubansa akansa.

“Ban san me na yi masa ba kuma. Akan Farida ce kuma sun rabani da ita. Duk da haka bai daina tsanata ba.”

Zayyad ya mike yana cewa,

“Ka koma ka kwanta Daddy kana bukatar hutu. Insha Allahu matsalarka ta zo karshe. Na dade ina zargin wani abu, amma yanzu na gane komai.”

Ya gyara masa kwanciyar sannan ya mike ya koma ta baya ya saka waya a kunne.

“Hello Samha. Ya gidan?”

“Lafiya lau Alhamdulillah.”

“Samha ki natsu ki gaya mani komai da kika samo daga rayuwata.”

Ta sake warware masa komai, sannan ta kara da cewa,

“Wallahi ba Abba bane ya haifeka. Dukkan bayanan da na samu sun tabbatar mani Abba ya daukoka ne kawai.”

Ya jinjina kai sannan ya ce,

“Alhaji Mamman shi ne mahaifina. Amma ba zan bari ya sani ba, abin da zan yi yanzu shi ne neman mahaifiyata. Idan har ina raye suka gayawa mahaifina na rasu, ina da tabbacin mahaifiyata itama tana raye kenan.”

Motsin da ya ji ya saka shi saurin sauke wayar tare da juyowa. Alhaji Mamman ne tsaye yana kallonsa. Da hannu ya yi masa alama da ya taho. Bai musa ba, ya taka ya karaso kusa da shi, ya rungume shi tsam yana kuka.

“Tun ranar da na fara ganinka nake jin wani abu akanka. Ko ka boye mani matsayinka na Muhseen jini ba karya bane.”

Zayyad ya sake shiga rudu, yana kokarin yin magana, Daddy ya hana shi. Shi kam har yanzu yana mamaki yana kuma tantama. Da sauri ya fice daga dakin, ya kira wani likita ya din ce a dibar masa jinin Shugabansa.

Fitowar sakamako ya yi daidai da daina harbawar jininsa na wani dan dakika.

Tunda Allah ya halicce shi bai taba jin abin da ya ruguza jinsa da ganinsa ba, sai yau dinnan. Zubewa ya yi a kasa yana jin numfashinsa yana tsinkewa.

Ya kasa tuna komai, kansa ya yi wani irin dumm… Da ga bisani zufa ya dinga keto masa. Tambayar farko da zuciyarsa ta harbo masa, bayan dawowarta da ga dogon tunanin da ba zai iya cewa ga irin tunanin ba, ita ce

‘Ina mahaifiyata? Meya sa suka zabi wannan hanyar a matsayin hanyar daukar fansa? Meya sa suke ta cutar da mahaifinsa bai taba ramawa ba, bai taba yunkurin daukar mataki ba, bayan yana da karfi da izzar da zai iya daure su dukkansu?’

Ya numfasa yana jin zuciyarsa tana wani irin tafasa. Ruwan sanyi kawai yake daddaka ko zai sami saukin radadin da yake ji a kirjinsa.

Tausayin mahaifinsa ya darsu a zuciyarsa.

Da sauri ya mike, sai dai wani irin jiri da ya debe shi ya saka shi komawa ya zauna yana mayar da numfashi.

Yana kallon kiran wayar Samha sai dai ko yatsunsa sun kasa motsi, bare har ya iya dauka. Har kiran ya katse ya sake shigowa bai yi yunkurin dauka ba.

Kokari yake yi dole sai ya gano duk wani abu da ya shige masa duhu, amma hakan ya gagara. Da kyar ya iya tashi ya fada bandaki. Ruwa ya sakarwa kansa kawai yana jin zuciyarsa kamar za ta fito waje. Babban burinsa a yanzu ya hadu da Alhaji Bala. Hakan ba zai yiwu ba, dole sai ya nemo natsuwa ya dorawa kansa, kasancewar titi zai hau.

Bayan ya fito wankan ya tsane kansa, sannan ya shirya a gurguje.

Waya kawai ya yi da mai kula da mahaifinsa, sannan ya saita kan motarsa bisa titi tare da jero addu’o’i.

Shi dai yasan ikon Allah ne kadai ya kawo shi gidansa. Yana shiga ya sami Sakina a falo da kanta nannade da bandeji. Sai yanzu ya tuna kiran da Samha ta dinga yi masa babu kakkautawa. Gabansa ya fadi. Cikin zare idanu ya ce,

“Ina Samha? Me…Me… Ya sameta?”

Sakina ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki. Sai kuma ta rushe da kuka. Hankalinsa idan ya yi dubu to ya tashi, duk a zatonsa wasu ne suka shigo suka dauke masa Samharsa.

Da sauri ya dafe kujera da hannu daya yana jin jiri yana dibarsa.

“Innalillahi Wa inna ilaihiraji un… Samha… Meya sameki? Sakina ina tambayarki ina Samha?”

Sakina da zuciyarta ke tafasa ta ce masa,

“Samha ta mutu. Ga gawarta can a dakinta.”

Sosai jirin ya ci nasarar kayar da ingarman namiji kamar Zayyad. Wanda duk tsananin tashin hankali ko a fuskarsa baka isa ka gane ba, sai ga shi yau gaba daya ya rasa wannan jarumtar.

Yana nan zube a wurin yana kallon Sakina tana rarrabe masa bibbiyu. Duk yadda yake kokarin yin magana duhu ya ci nasarar rufe masa idanunsa. Bai sake sanin komai da ke faruwa ba.

Samha kuwa barci sosai take yi, kasancewar ta gaji, jikinta ya yi mata tsami. Domin ba karamin bugu Sakina tasha a hannunta ba. Kamar an ce ta fito falo. Tana fitowa ta ci karo da Zayyad a yashe a wurin baya numfashi, Sakina kuma tana zaune tana waya tana kwasar dariya. Addu’arta Allah yasa dai Zayyad mutuwa ya yi. Ta kuma kira mahaifinta ta tabbatar masa da ga Zayyad nan a kwance yadda zai iya sakawa a dauko shi. Wannan albishir ya yi masa dadi kwarai da gaske. Da kansa ya biyo yaransa domin su zo su dauki Zayyad.

Samha ta kwala kara ta yi wurinsa da gudu tana kuka. Sai dai ko motsi bai yi ba, kasancewarsa ya fi karfinta. Kuka sosai take yi tana jijjiga shi. Sakina kuwa sai kwasar dariya take yi. Bakin ciki da zuciya suka kwasheta, ta mike da gudu ta nufi kitchen ta dauko katon muciya. Sakina ba ta ankara ba, ta dinga jin saukar muciyar nan a jikinta. Ihu kawai take yi tana rokar Samha. Amma ko kadan ba ta kyaleta ba, sai da ta tabbatar da ta yi mata targade hannu da kafafu. Sannan ta jefar da muciyar tana zare jajayen idanunta.

“Sai na yi ajalinki a cikin gidan nan na yi maki wannan alkawarin.”

Da gudu ta nufi frij ta dauko ruwa. Ta dinga watsa masa. Cikin ikon Allah ya saki ajiyar zuciya.

“Samha… Meya sami Samha? Sakina  ban yarda Samha ta mutu ba, ki gaya mini gaskiya ina Samhata?”

Sai yanzu Samha ta gane me ya faru, da sauri ta kama hannunsa ta kai fuskarta da ke jike da hawaye tana ce masa,

“Uncle bude idanunka gani nan don Allah ka tashi. Ka da ka yi mini haka bani da kowa sai kai.”

Da sauri ya bude idanunsa. Ya dan jima yana kallon fuskarta sannan ya ji wani irin karfi ya zo masa. Da sauri ya jawota ya rungumeta tsam a jikinsa da ke rawa.

“Samha… Meya sameki? Kina lafiya?”

Ta lumshe idanunta hawaye suka zubo,

“Wallahi Uncle lafiyata kalau. Babu wani abu da yake damuna. Karya take yi maka babu abin da ya sameni.”

Ya jinjina kai, yana sauke ajiyar zuciya. Sakina da ke kwance tana kallonsu, zuciyarta kamar za ta fashe.

Samha ta zura bakinta a kunnensa tana yi masa kalaman da ita da shi kadai suke iya fahimta. Ya dinga jin kwarin guiwa yana shigarsa. Ya nemi duk wata kasala ya rasa. Yana rungume da ita yana shafa bayanta.

Ji suka yi an bude kofar da karfi. Hakan yasa duk suka mike tsaye cike da mamaki. Zayyad ya sauke idanunsa akan Alhaji Bako. Ga yaransa dauke da makamai.

Zuciya ta dinga cin Zayyad, bai san lokacin da ya karaso gaban Alhaji Bako ba, yana huci kamar wani zaki.

“Ina mahaifiyata?”

Dam! Duk karfin hali irin na Alhaji Bako, yau sai da ya sami wanda ya jijjige karfin halin ya ajiye gefe guda.

“Ina ka boye mini mahaifiyata?”

Bakinsa yana rawa ya ce,

“Ka da ka kawo mani zancen banza mana. Me zan yi da mahaifiyarka? Kai ku zo mu tafi.”

Har sun kai bakin kofa ya ji dirarriyar muryar Zayyad yana magana,

“Idan baka dawo mani da mahaifiyata ba, ina yi maka albishir da ka fara kirga ragowar ranakun shigarka matsalar da fitarka zai zama abu mai wahala. Mahaifina kake kokarin kashewa? Meya yi maka? Ni dansa kake so ka bani guba in kashe mahaifina da kaina? Shi ne ribar da kake nema shekara da shekaru? Shiyasa kuka reneni domin in girma in kashe mahaifina? Kun yi kuskuren renon da kuka yi mini, da kun sani tun lokacin da kasheni kuka yi. Wallahi! Ko a zuciyarka ka ji za ka iya cutar da mahaifina, muddin tunaninka ya fito fili har zuciyata ta saurara ina me tabbatar maka sai na shafe tarihinka daga doron kasa. Zan baka dama ka koma ka sake shiri, domin yakin ya tashi daga kan mahaifina ya koma kaina. Duk in da mahaifiyata take, in dai tana raye, a kwanaki biyu rak! Zan bincikota. Da ga nan wasan namu zai fara.”

Alhaji Bala kai tsaye ya nufi gidan Alhaji Salisu. Bai jira an yi masa iso ba, ya afka falon yana kwala masa kira. A lokacin yana zaune da iyalansa, sai dai kallo daya za ka yi masa ka gane baya cikin hayyacinsa. Jin irin kiran da Alhaji Bala yake yi masa, ya saka shi mikewa tsaye, domin ya tabbatar ba lafiya ba.

“Kana nan ka zauna lusarin banza! Lusarin wofi! Ga shi asirinmu ya tonu. Dakikancinka ya saka har wasu banzaye suka bankado sirrinmu. Da ka amince mu kashe Zayyad da bai girma yana neman daukar fansa ba.”

  Kafin ya gama dire maganarsa yadda ya kamata, ya ji saukar mari a bisa kuncinsa. Da sauri ya waiwayo domin ya ga mai karfin halin nan. Idanu ya zubawa Nura a firgice. Shi kuwa Nura sai huci ya ke yi, da ga bisani ya nuna shi da yatsa, idanunsa sun kada sun yi ja..

“Idan ka sake zuwa gidanmu, ka ci mutuncin mahaifinmu da Yayana sai na illata maka rayuwa. Ko an gaya maka tsoronka ake ji? Cin kashin da kake yiwa mahaifina ya isa haka! Idan ka sake yunkurin zaginsa, zan tabbatar da na dora kalmar danasani a harshenka Wallahi!”

Sharifat ta mike itama tana jin zuciyarsa tana tukuki,

“Malam ka kyale mahaifinmu ya sarara haka. Wallahi idan ka sake zuwar mana gida, sai mun yi maka wulakancin da ko kare ba zai shinshina ba. Ko kunya baka da ita kake furtawa mahaifi wai ya kashe dansa, sai ka ce muna garin dabbobi.”

Alhaji Bala da ya gama tabbatar da karyarsa ta kare, ya saba babbar riga idanunsa sun kankance saboda bala’i.

“Ni kuka wulakanta ko? Ni kuma nasan akan wanda zan rama. Sannan ina so ku sani, ba mahaifinku ya haifi Zayyad ba, Shugaban kasa shi ne mahaifinsa. Sai ya jira abin da zai biyo baya, domin ba ni kadai zan je kurkuku ba, har da shi zamu je.”

<< Miskilin Namiji 19Miskilin Namiji 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×