*****
Rayuwa ta juyawa Sakina baya, ta rame ta lalace alamomin cutar kanjamau sun bayyana karara a jikinta. Ita kuwa mahaifiyarta ba ta dauke da wata cuta, domin ta dade rabon da Alhaji Bako ya kusanceta. Tun lokacin da ta gano mazinaci ne, ta kaucewa kwanciya da shi, shi kuma ko a jikinsa kasancewar yasan yana da dubunnenta.
Duk halin da Sakina take ciki ba ta taba zuwa ta dubata ba. Musamman da ta ji Sakina tana baiwa wata kawarta labarin mahaifinta ne ya saia mata cutar, sai ta kara jin tsanar Sakina, ta yi mamakin yadda Alhaji zai iya kwanciya da ‘yarsa. Ta kasa hakuri har sai da ta shigo dakin da wuka tana zare idanu.
“Kika ce mahaifinki ne ya kwanta da ke? Yanzu iskancin naki har ya kai ki kwanta da mahaifinki?”
Sakina tana kuka ta gaya mata duk yadda akayi. Hajiya ta saki wukar tana salati. Ba ta iya sake cewa komai ba, ta fice tana jinjina kai.
Haka Sakina ta dinga wani irin wari tana fitar da tsutsotsi ta gabanta. Wani irin mugun infection take yi, wanda hatta asibiti da ta je sai da abin ya basu tsoro.
A cikin keke napep din da ta tare zai kaita gida ta mutu. Bayan ya iso in da ta kwatanta masa ya ce,
“Hajiya mun kawo.”
Shiru babu magana. Ya Juya ya ga kamar tana barci, nan da nan ransa ya baci ya fito yana cewa,
“Baiwar Allah ki tashi na kawoki ki bani kudina in wuce. Ni na taba ganin fasinja yana barci haka?”
Ya leka fuskarta a gigice ya dinga ihu yana kiran jama’a su taimaka masa. Haka mutane suka taru. Nan da nan halittarta ta sauya ta yi wani irin mugun ba’ki halittarta ta jirkice.
Wani ta yi salati ya ce,
“Ai wannan Sakina ce.”
Ya ruga da gudu ya kira mahaifiyarta. Yadda ta ga Sakina sai da ta yi hawaye.
Haka dai aka samu aka lallaba aka kaita gidanta na gaskiya.
Zayyad ya shigo yana ba Samha labari. Gaba daya sai jikinta ya yi sanyi. Tsoron Allah ya kara kamata. Ya jawota jikinsa ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna.
“Kinsan bana son ganin damuwa a bisa kyakkyawar fuskar nan ko?”
Ta lumshe idanu hawayen suka sakko, ya saka harshe yana side hawayen. Ba ta hana shi ba, tana jin yadda yake aika mata da sumba ta wuya ta fuska ta kunne. Ya saka hannu yana mulmula na shanunta, ya riga yasan weak point dinta don haka ta yi lakwas. Cak ya dauketa suka yi daki, ya rabata da dukkan kayan jikinta.
Tana jinsa, ta kasa jurewa tanaso yau a karo na farko ta mayar masa da martani, don haka ta dinga yi masa wasanni wadanda suka birkita masa lissafi, tun yana iya jurewa har ya kasa jurewa. Dukkaninsu sun fita hayyacinsu, baka jin komai sai sautin tsantsar soyayya.
Wannan karon da ga shi har ita sun sami gamsuwa irin wanda suke da bukata. Suna cikin bargo suna lullube dukkaninsu babu kaya a jikinsu. Ya manna mata sumba a labba.
“Baby mai taushin baki.”
Ta sake cusa kanta a kirjinsa tana shinshinarsa.
“Ina sonka Uncle.”
Ta karashe da cusa kanta a kirjinsa tana jin wani matsanancin kunya. Ya dago fuskarta yana dubanta cike da farin ciki,
“Na dade ina jiran in ji wannan kalmar daga bakinki amma hakan ya gagara. Sai yau kika amince ki bani wannan kyautar? Ki shirya sai mun zagaya kasashe biyar, daga karshe mu je mu yi umrah kafin mu jira lokacin yin Hajji ya yi, mu samu mu sauke farali.
Kankame shi ta yi, cike da farin ciki. Ko babu komai itama za ta je yawon bude idanu, da wanda take so kamar ta hadiye shi.
A bangaren Hajiya Farida kuwa, shugaban kasa ya dauketa daga Najeriya suka wuce London. Don haka Shima Zayyad da London din suka fara.
Umma ta kara kyau da haske. Kyawunta da haskenta duk sun bayyana. Zayyad ya ji dadin yadda ya ga iyayensa cikin kwanciyar hankali.
“Umma yaushe zamu je wurin danginki?”
Ya tambayeta a lokacin da ya sauke sassanyar madarar da yake kurba. Ta dan yi shiru, sannan ta dubi shugaban kasa.
“Muna dawowa Najeriya zamu tattara mu je can. Amma muna Kaduna da yawansu sun kawo mata ziyara, tare da jajen abin da ya faru.”
Zayyad ya dan dukar da kansa, sannan ya ce,
“Wato Daddy da ba dan Samha ba, da ban gano komai ba, haka zalika da babu ita, da tuni Sakina ta kasheni. Hakika Samha yarinya ce karama mai tsananin jarumta. Haka zalika da muka rasa ta yadda zamu fitar da Umma daga gidan da Alhaji Bako ya ajiyeta, Wallahi Samha ce ta yi shahada ta tafi zuwa garesu.”
Duk suka dubi Samha da ta dukar da kai.
“Allah ya yi maki albarka. Ganin farko da na yi mata na ji kaunarta, na hango tsantsar tausayina a idanunta. Ganinta a kusa da ni, sai zuciyata take gaya mini wani haske zai bayyana a gareni. Allah ya yi maki albarka ya saka maki da alkhairi.”
Duk suka amsa da “Ameen.”
Daddy ya ce,
“Zayyad ya kamata ka mayar da yarinyar nan Makaranta. Sannan ka tambayeta irin kasuwancin da take so ta yi, insha Allahu zan bude mata katafaren wuri a duk garin da take da bukatar hakan.”
Duk suka jinjina kai. Samha kuwa farin ciki ya sanyata kuka. Daddy ya fara tashi ya shiga ciki, sannan Umma ta bi bayansa.
Da sauri ya karaso gabanta.
“Mene ne abin kuka kuma? Kinsan bana son kuka ko?”
Yadda ya sha mur yasa ta sake fashewa da kuka, ta kwanta a kirjinsa tana shessheka.
“Dole in yi kuka Uncle. Kaine sanadin canza tarihin rayuwata. Kaine ka yi sanadin mayar da bakin fenti izuwa fari. Mahaifiyata ba ta ciwon komai, tana samun abinci mai kyau, ta kwanta a wuri mai kyau, duk a dalilinka. Gani nake yi kamar duk biyayyar da nake yi maka ban gamsar da kai ba.”
A kunne ya rada mata,
“Zo mu je namu dakin ki gamsar da ni kin ji babyn baby.”
Hannunta ya jawo suka shige dakinsu. A yau din ma salon soyayyarsu ta sake canzawa. Yadda Samha ta kama bakinsa tana tsotso kamar wacce ta sami mintin yara ta sake gigita tunaninsa. Ya kara gazgata Samharsa daban ce da sauran mata.
Kullum sai ya ji ta canza masa, ga shi wurin kullum a matse.
Da sassafe ta tashi ta nufi kitchen domin ta hadawa Umma da Daddy abin karyawa. Duk da ma’aikaciyarsu baturiya tana kitchen din.
Samha ta ce mata ta je ta huta yau ita za ta yi komai.
Zayyad ya laluba bai ganta ba, hakan yasa ya ware idanunsa. Cikin kayan barcin ya taka ta nufi kitchen domin yasan halinta.
Ya harde hannayensa yana kallonta. Allah ya yi mata kira mai jan hankali. Kugunta ya bude sosai, yayin da take da shafaffen ciki. Kirjinta kuwa cike suke taf! da na fulani. Gashin kanta mai tsantsi ta tubke a tsakiya ta saka wani hula da bai rufe gashin ba. A hankali ya karaso ya kama kugunta da suka fi jan hankalinsa.
A tsorace ta yi kokarin waiwayowa, sai dai ta gaza hakan. Ta dan saki ajiyar zuciya tare da langwabe masa.
“Mijina ne Wallahi.”
Ya yi murmushi tare da juyo da ita. Maballin rigarta ya dan bude, hakan yasa yake hango saman na fulaninta. A hankali ya saka hannu ya sake cire maballi daya zuwa biyu. Gaba daya suka bayyana. Tsam-tsam da su tamkar ba a taba tabawa ba. Ya saka bakinsa yana tsotso. Ko kadan baya jin ya gaji da shan kirjinta, gani yake yi tamkar wannan ne tushen jin dadinsa. Gaba daya ya gama yamutsata, da kyar ta yi magana cikin shagwaba,
“Abin karyawa zan yi fa.”
Ya zame kansa ya ce,
“Ki taimakeni ki zo mu je just 30 minutes kawai zaki dawo.”
Ta dan yi shiru kamar mai tunani.
“Sai dai idan ka yarda za ka tayani aikin.”
Da sauri ya gyada kai,
“Wallahi na yarda.”
Suka nufi daki suna makale da juna. Sai da ya biya bukatunsa har na tsawon awa daya, kafin suka fito a gurguje don ganin lokaci ya ja. Ya so a kira mai aikin ta taimaka masu, amma fir Samha ta ki yarda, wai ita tana kishin ta zo ta kalle mata miji.
A cikin abin da bai gaza awa daya ba suka kammala komai. Shi yake yi mata yanke-yanke. Ita kuma tana hadawa. Suka je suka jere komai, sannan suka dan gyara kitchen din.
Jin motsin Umma yasa suka boye a wani lungu. Samha tana fuskantarsa suna jin numfashin juna. Ta yi masa rada,
“Yau mun shiga uku idan aka ganmu.”
Shima ya rada mata,
“To mene ne? Itama baki ga tana tare da mijinta ba?”
Ta dan bugi kirjinsa. A hankali suka sulale suka bar falon. A tare suka shiga wankan.
Kafin su fito, har Umma da Daddy sun kammala karyawa sun koma ciki.
Suka fito suna zuba uban kamshi kamar wadanda za su je gasar kyawawa.
‘Yar takarda suka gani akan table din, gaba daya suka hada kai wurin karanta abin da aka rubuta.
“Girki ya yi dadi sosai. Sai dai Zayyad ka mance agogonka, ke kuma Samha kin mance hularki. Yau kitchen ya tabbatar da wanzuwar manya a cikinsa.”
Gaba daya suka kalli juna suna murmushi.
“Kai meya sa ka mance agogon?”
Ya harareta,
“To kema meya sa kika mance hularki? Ai gwara ni agogo ne.”
Haka suka karya suna ta dariya. Sai wajen La’asar suka hadu da iyayensu.
Da za su tafi kamar Umma za ta yi kuka, domin a ‘yar zaman da ta yi da Samha, ta shaku da ita fiye da tunanin mai tunani.
Sun baro Umma da Daddy suka nausa Egypt suka je Spain daga can suka wuce Qatar! Daga Qatar suka nufi Madina, sai da suka yi sati daya a Madina kafin suka wuce Makka. Anan ma Sati dayan suka yi.
Samha ta dawo da tsarabar Makka. Farin cikin Zayyad kuwa ba a magana. A gidan Alhaji Salisu suka sauka. Sai da suka yi kwanaki biyu kafin suka wuce gidansu.
Dukkan gyare-gyaren Sharifat da shi suka yi, ya hana Samha ko da motsawa.
Da kyar Daddy ya samu ya hada kan iyalansa a vila domin kuwa yana dawowa kasar kai tsaye can ya wuce da Umma. Ya umarci Zayyad da ya dauko matarsa. Da Zayyad ya tashi zuwa sai ya dauko har da Alhaji Salisu da iyalansa.
An sami fahimtar juna, Walid da Mufida suka nemi afuwan Yayansu. Har ma Mufida ta makale akan lallai sai ta biyo Yaya Zayyad gidansa.
Rayuwar family din ta zama abar sha’awa. Alhaji Salisu da Alhaji Mamman sun sake tuna baya, wajen hada kawunansu wuri daya.
Rana daya aka hada bikin Walid da Mufida, wanda Walid ya zabi Sharifat a matsayin abokin rayuwarta. Ita kuma Mufida ta zabo yaron minista.
Nura ma ya nemo tasa matar.
Don haka akayi biki irin wanda ba a taba yi ba, a villa.
Umma ita ce uwar amare da angwaye, domin kuwa Hajiya Samira ta sakar mata komai.
Shi kuwa Alhaji Bako tuni gwamna ya saka hannu aka rataye shi. Har ya bar duniya bai bar zage-zage da kumfar baki ba, bai taba tunanin mutanensa za su kasa fitar da shi ba.
Rayuwa ta mika, Samha ta haifi diyarta mace, aka saka mata Aisha, sunan mahaifiyar Samha.
Sai da Hajiya Aisha ta yi kuka saboda farin cikin karar da akayi mata.
Zayyad ya kammala asibitinsa don haka ya kwashi dukkanin mutanensa suka koma Kaduna. Hatta Alhaji Salisu sai da aka siya masa babban gida da ya fi wanda yake ciki na Kano. Hankalinsa ya fara kwanciya, musamman ma da Samha ta fara zuwa Makaranta.
Alhaji Mamman ya cika alkawarin da ya daukarwa Samha, ya bude mata katafaren wurin siyar da kayan kitchen na alfarma. Sama da kasa duk shake suke da kaya.
Samha ta sake gogewa ta yi kyau ta kara cika.
Duk irin hidindimun da take yi hakan bai sanya ta kyale mijinta ba, hasalima ba ta hada lokacinsa da na kowa. Tsantsar soyayya ko a gaban waye nunawa juna suke yi.
Yau sun tashi da baki cike da gidan, domin kuwa Sani amininsa da iyayensa suka kawo masu ziyara. Don haka Samha da Zayyad sun zage wajen ganin sun karrama su. Sai goshin magriba suka tafi.
Suna dawowa rakiyansu ya matseta a bakin kofa yana shinshinarta. Ya saka hannu yana shafar mararta.
“Akwai ajiyana anan ko?”
Ta dube shi kamar za ta yi kuka.
“Eh kuma ni gaskiya.”
Kafin ta karasa ya hade bakinsu wuri guda. Tun tana daurewa har tsayuwar ta fara gagararsu. Ya zame bakinsa bayan ya tabbatar da ya gama kashe mata jiki,
“Baby ki haifa mini ‘ya’ya masu yawa, yin hakan shi zai kara mini sonki fiye da kullum. Ina son yara kada ki kuskura ko da wasa watarana ki ce mini kin gaji.”
A sanyaye ta kwanta a kirjinsa ta ce,
“Insha Allahu zan bi dukkanin umarninka.”
Ya ji dadin furucinta, don haka ya sunkuceta ya shige da ita daki. Ita kuwa Humaira tana wurin mai renonta.
Suka sake afkawa wata duniyar, wanda alkalamina ya gagareni rubutawa ba.
Alhamdulillah… Taku har kullum ‘yar mutan Borno take cewa sai mun hadu a sabon littafina mai suna “Ni da kawata.”
Anan muka kawo karshen labarin Miskilin namiji. Kura-kuranmu Allah Ya yafe mana.
Kada ku mance, ku dauki abubuwan alkhairin da ke ciki ku watsar da wadanda ba lallai su amfane ku ba.
Na sadaukar da wannan labarin agun mijina. Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana…