Tafiya yayi sosai bai ga alamar kowa ba. Har ya gama dube-dubensa bai sami wata alama da zata nuna masa wata halitta tana rayuwa a cikin wurin ba.
Har zai koma, sai kuma yakai dubansa ga wani kango, dan haka ya tura kai babu ko tsoro.
Ya firgita kwarai ganin Mace a kwance, tana fitar da numfarfashi sama-sama.
“Ruwa…ruwa..”
Zayyad ya dubi gefensa akwai ruwa a wani bokiti. Ya dibo da sauri ya daga kanta babu ko kyama ya ba ta. Bayan tasha ne ta saki ajiyar zuciya.
“Me ke damunki?”
Ya tambayeta cike da mamaki da al’ajabi. Tunani kala-kala babu irin wanda bai shigo kansa ba. Ba sai an gaya masa ba, babu shakka akanta Samha ke wannan wahalar. Ya tabba ta mahaifiyarta ce. Kamanninsu ya baci.
“Me kuke yi akango? Ina danginku?”
Cikin numfarfashi ta ce,
“Idan kayi yunkurin taimaka mana kasheka za ayi.”
“Waye zai kasheni? Fada mini waye zai kasheni?”
Ya tambayeta tare da tallabo fuskarta.
“Alha…Alha… Ruwa-ruwa.”
Da sauri ya sake ba ta ruwan.
“Waye zai kasheni?”
Ya sake tambayarta.
“Alhaji Bako..” Wani irin faduwar gaba yaji, irin wanda ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffara ba, bai taba jin irinsa ba. Ya shiga rudu irin wanda bai taba shiga ba. A karo na farko tsoron Alhaji Bako ya kawo ziyara cikin zuciyarsa da ilahirin jikinsa.
Yana shirin yin magana, yaji motsi. Da sauri ya mayar da kanta ya kwantar sannan ya ce,
“Kada ki bari ‘yarki tasan ina nan. Zan taimakeku.”
Bai jira amsawarta ba, ya tafi can bayan windo ya boye yana lekensu.
Samha ta shigo hannunta dauke da abinci a leda.
“Mama na tafi na barki ko? Kiyi hakuri da kyar na samo mana abincin.”
Ta daga kan mahaifiyarta cike da kauna tana ba ta abincin. Da ya leka sosai, abin tausayi kanzon shinkafa ce ta samo.
“Kin ga magungunanki ya kare, zan yi iya bakin kokarina insha Allahu insiya maki magani.”
Yana nan yana kallon ikon Allah. Tsantsar tausayi, da kauna irin wanda ya jima bai gani ba, su ya tsinta a cikin idanun Samha. Yarinya ce karama, wacce ta taso da tausayi da jinkan mahaifiyarta.
Yana kallon yadda ta dagata ta kaita har waje kafin ta dawo ta dauke shimfidar ta sake shimfida wata, ta kwashe wandancan domin ta wanke. Hankicif ta gani, hakan yasa gabanta ya fadi da karfi,
“Mama waye ya shigo nan? Wani ya gano maboyarmu ne? Mama kashe mini ke za ayi idan suka kasheki bansan ina zan saka kaina ba.”
Duk ta gigice ta haukace.
Zayyad ya runtse ido yana jin bakin cikin yadda ya mance hankicif dinsa. Maman dai sai kallonta take yi, daga bisani ta yafitota da hannu. Ta karaso gabanta jikinta yana kyarma.
“Babu abinda zai faru. Ki je ki huta zan gaya maki ko na waye.”
Samha dai ba ta musu da Mahaifiyarta shiyasa tayi shiru. Amma a firgice take.
Zayyad ya zagaya ya fice daga wurin gaba daya zuciyarsa cike da tausayi. Cikin dare bayan barci ya kwashe Samha, aka shigo. Firgigit tayi ta bude idanu. Ganin ana kokarin fita da mahaifiyarta yasa ta haukace tana ihu tana burgima. Artabo sosai akayi a tsakanin Samha da masu daukar mahaifiyarta. Daga baya suka riketa suka toshe mata baki da wani abu, ba ta sake sanin inda kanta yake ba.
Idanunta ta bude su a hankali, tanaso ta tuna abinda ya faru. Da sauri ta tashi zaune tana duba shimfidar Mama. Babu ita babu dalilinta. Ta daddage ta fasa kara, irin wanda ya yi sanadiyyar tafiya da muryarta.
“Na shiga uku na lalace. Sun kashe mini rayuwa, sun dauke min mahaifiyata. Ku taimakeni ku dawo min da ita, shikenan na rasa gatana. Mama ki taimakeni ki dawo.”
Sumba ta kala-kala babu irin wanda ba tayi ba. Ta dauki zanin rufarta ta rufe jikinta da shi tana karkarwa. Hakoranta suna hadewa da juna.
Tun daga nan rayuwa ta juya mata baya. Yau kwananta uku babu ci, babu sha. Ga ciwo da ya kwantar da ita. Kullum cikin kuka sunan Mama take kira kawai. Ta sake lalacewa. Maganarta ta zama ba ta fita. A daren na hudunne gaba daya jinta daganinta ya dauke.
Ba ta sake sanin duniyar da take ba, sai jin iskar fanka da ta ji yana kadawa. Ahankali ta ware manyan idanunta tana kallon yadda fankan ke kadawa. Abubuwa da yawa suka fara dawo mata kwanya.
Ta tashi zaune.
Idanu hudu tayi da Dr. Zayyad. Yana zaune ya zuba mata fararen idanunsa idanunsa kamar mai zaman gadin ta farka. Ta sake saurin kallon inda take. Asibiti ne sai dai babu kowa a dakin sai ita kadai. Ta fashe da kuka tana cewa,
“Na shiga uku. Ina mahaifiyata?”
Yayi magana a natse,
“Mahaifiyarki tana hannun Alhaji Bako.”
Yayi maganar domin yana neman wata amsa daga gareta. Anan kuwa dabararsa ta yi aiki, dan kuwa zazzare idanu ta dinga yi tana cewa,
“Waye Alhaji Bako? Wanene Alhaji Bako? Wallahi idan ya taba min mahaifiya sai na karar da dukka zuri’arsu. Innalillahi Wa inna ilaihiraji un. Me tayi masa? Duk yadda nake boye mahaifiyata sai da aka sami wadanda basu da imani? Mamana ba ta da lafiya.”
Surutai take yi cikin wani irin kuka. Dr. Zayyad ya daga kai ya dubi nas din da ke tsaye da ruwan allura a hannu. Ya lumshe ido tare da daga mata kai. Cikin sauri ta tsayar da karin ruwan ta juye mata ruwan allurar a tsintsiyar hannu. Kafin Samha ta iya furta wata kalma wanda yaso ya ji me zata ce, sai dai maganar ta kakare ayayin da barci ya dauketa. Ya yi ajiyar zuciya tare da zuba mata idanu. Ba fara bace tas! Amma tana da sassanyar kyau irin na mutanen ethopian. Akwai arzikin gashi, duk da ya kudundune saboda azaban rashin gyara.
‘Meyasa Samha ba tasan Alhaji Bako ba? Me yasa? Tayaya mahaifiyarta tasanshi har tana ikirarin zai iya illatata ko ya kasheta, amma ko kadan Samha ba ta taba saninsa ba? Meyasa Samha ta dauke file din da ya ajiye?’
Tambayoyin da baida amsarsu ya dinga watsowa kansa. Ya duba file din sama ko kasa a wurin bai gansa ba. Yana so ya lallaba ta ta dauko masa wannan file din. Dole yana bukatar yarinya mai wayo kamar Samha ta kasance a cikin gidansa, ya tabba ta zai sami duk amsoshin da ya dade yana nema.
Yana nan zaune kusa da ita baida alamun tashi.
“Sir da ka barta zamu cigaba da duba ta.”
Ya dago ya dubeta sau daya, bai ce komai ba, ya mike kawai ya kama hanyar fita. Har ta sakankance ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce,
“Idan kika barta ta gudu ki tabba ta a bakin aikinki.”
Da sauri ta amsa da,
“Insha Allahu zan tsaya akanta sir.”
Bai ce komai ba, ya wuce abinsa.
Misalin karfe sha biyun dare, yana zaune a gaban Samha yana kallonta. Rashin farkawarta ya dame shi matuka. Wayarsa ta yi kara, wanda yayi sanadin farkawar Samha, amma kuma ba ta bude idanu ba. Ya zaro wayar yana kallon fuskar wayar. A natse ya dauka tare da yin shiru.
“Masoyi kwana biyu ina kake kwana ne? Kasan gidan nan yayi min girma da yawa, bana iya barci idan baka kusa. Ko nayi maka wani abu ne da kake kaurace mini?”
Ya dan shafi sajensa sannan ya ce,
“Aiki ya rikeni. Abokin aikina da yake karbana baya qasar. Kiyi addu’a ki kwanta.”
Zata sake magana ya kashe wayar. Ta sake kiransa. Wannan karon a fusace ya daga,
“Dan Allah ka tausaya min ko zo ka bani hakkina. Wallahi idan baka dawo ba komai yana iya faruwa da ni.”
Ya girgiza kai yana kara jin tsanarta,
“Kina iya yin duk abinda kika gadama rayuwarki ce.”
Yana kokarin kashe wayar yaji muryar Samha tana kuka,
“Wayyo Mamana. Ni dai ka kaini wurin Mamana. Ka taimakeni ka kaini wurinta dan Allah dokto.”
Ya yi kasa da murya, cikin lallashi ya ce,
“Sai kin daina wannan kukan.”
Sakina da ta ji wani masifaffen kishi ya rufeta. Jikinta har rawa yake yi a lokacin da ta dubi fuskar wayar ta tabba tar da ya katse kiran. Ta tashi ta dinga safa da marwa, tana jin zuciyarta tana tafarfasa.
“Zina Dokto ya fara yi? Neman mata? Akan wata dama ya juya mini baya? Inaaahh… Wallahi Wallahi baka isa ba dokto. Kayi kadan ina numfashi kana numfashi ka hadani da wata. Yadda nake ni kadai a gidanmu, haka a gidan mijina ni kadai zan zauna.”
Shi kuwa Dokto, bayan ya tabba tar da ya lallashi Samha, sannan ya danna wayarsa ya kira wata nas. Ya ce ba Samha ruwan zafi tayi wanka sannan a hada mata tea mai kauri da Bread.
Ya tashi ya fice. Kai tsaye ofishinsa ya wuce. Maimakon yayi Sallah ko zai ragewa kansa radadi, sai kawai ya zauna yayi tagumi da hannunsa bibbiyu. Yana kallon irin kiran da Sakina take antayo masa kamar wata mara aikinyi. Can ya ji alamun sako ya shigo. Ya bude tare da karantawa a zuciyarsa,
‘Wallahi Dokto bazaka kawo mini kishiya cikin gidan nan ba.’
Ya jinjina kai, yana jin zancenta tamkar famin wani gyambo ne a zuciyarsa.
“Dokto ta yi wankan, amma ta qi shan tea din.”
Ya jinjina kai,
“Ok zaki iya tafiya.”
Da kansa ya taka cikin takunsa irin na basarake ya isa har dakin. Ya zuba mata idanu kawai yana dubanta. Bayason yawan magana, amma yarinyar nan tana so ta saka shi,
“Kisha tea din muyi maganar da ya shafi mahaifiyarki.”
Da sauri ta dauki cup din ta fara sha da sauri da sauri. Ya rike hannunta, yana watsa mata lumsassun idanunsa,
“Kisha a hankali.”
Ta dubeshi sannan ta sunkuyar kai. Hannunsa akwai taushi kamar auduga. Jinjina kai kawai tayi, dan haka ta cigaba da sha a hankali. Can ta tuna da mahaifiyarta ko a wani hali take? Sai kuka. Bai hanata ba, tana sha tana kuka har ta gama. Ta sakko da kafafunta kasa, ta yadda suke iya gogar nasa kafafun.
“Ka taimakeni ka nemo mini mahaifiyata.”
Ya kalleta sosai yana nazarin ta yadda zata karbi zancensa,
“Zan dawo maki da mahaifiyarki cikin koshin lafiya, duk da aikin karbota da zanyi akwai hatsari sosai. Amma nayi maki alkawarin zan karbota idan nima zaki yi mini abinda nake so.”
Ta yi saurin dubansa, sannan ta rike hannayensa jikinta babu inda baya bari,
“Na yarda. Indai aiki ne a gidanka zanyi.”
Ya girgiza kai,
“Ba aiki bane kawai. Ina so in aureki na tsawon shekaru biyu kacal! Da zarar shekaru biyun sun cika zan sakeki, ki je ki cigaba da rayuwar da kike so, da mahaifiyarki.”
Ta zaro idanu. Sai kuma tayi lakwas! Tana so tayi rashin kunya, ta nuna masa bazata yi ba, amma kuma rayuwar mahaifiyarta ta fiye mata komai. Hawaye suka wanke mata fuska. Ta jinjina kai,
“Na amince. Amma dan Allah kada ka cutar dani, kuma muyi komai a rubuce.”
Mamakin kaifin wayo irin na yarinyar ya wuce hankalinsa. Hannu ya zura a aljihu ya fitar da wata takarda ya mika mata. Ga mamakinsa tsaf ta karance shi. Babu komai a ciki sai dokokin da yakeso ta bi, da kuma sharadin ranar da ya saka na kwanan wata yana cika zai sallameta ta tafi. Dokokin kuwa, sune baya bukatar ta gayawa kowa wannan sirrin, baya son ta shigewa uwargidansa. Yanaso ta gano masa dukka abubuwan da take kullawa. Yanaso ta zama mai saka idanu akan duk wani motsin kowa da ke cikin gidan. Kuma dole duk ranar girkinta ta shigo dakinsa ta kwana. Duk a ciki wannan ne yayi mata tsauri.
“Gaskiya ka cire na karshen nan bazan iya ba.”
Ya karbi takardar don ya mance menene na karshen. Murmushi ya sakar mata,
“Babu abinda zanyi maki. Idan kin amince ki saka hannu babu abinda zan cire a ciki. Rayuwar mahaifiyarki ta fiye maki duk wani dokokin da ke cikin takardar nan.”
Da sauri ta karbi biron hannunsa, ta saka hannu.
Ya dade yana duban yanayin saka hannun. Yarinyar tana bashi tsoro. Abubuwan da take aikatawa ko alama ba ta yi masa kama da mai ilimi ba. Ya dauki dayan takardar ya mika mata, ta sake saka hannu, sannan ya ce,
“Wannan naki ne. Ki ajiye da kyau. Kada ki bari wani ya gani. Daga lokacin da wani ya gani, kin jefamu dukka a matsala. Domin iyayena baza su dauki wannan abun ba.”
Ta jinjina kai kawai tana jin zuciyarta tana suya akan rashin mahaifiyarta da basu taba raba wurin kwana ba.
“Yaushe zaka karbo mini Mamana?”
Ya cira kai ya dubeta sannan ya ce,
“Bani nayi alkawari ba? Ki zuba ido. Inaso zan kaiki a yi maki gyaran jiki. Banaso ko sau daya ki nunawa dangina da matata ke ba wayayya bace. Daga lokacin da ta gane kina da karancin wayewa, daga lokacin zaki fara fuskantar barazana daga gareta.”
Ta sake jinjina kai.
“Koma ki kwanta.”
Ta girgiza kai,
“Zanyi Sallah.”
Ya shafi sumarsa ya ce,
“Zaki iya tashi ko insaka a taimaka maki?”
Ta hadiye wani abu, gabanta yana faduwa da danyen hukuncin da take kokarin yankewa.
“Zan iya. Cire mini karin ruwan.”
Ya kama tsintsiyar hannunta ya cire mata. Yana nan zaune har ta shiga bandaki. Shi kansa tunanin irin hukuncin da ya yanke yake yi. Ya tabba ta muddin Ummansa ta ji wannan aika-aikan babu ko tantama zata iya yin mugun fushi da shi. Bama ita ba, kowaye ya ji kai tsaye za ace yana wasa da aure. Ya lumshe idanu yana jin kirjinsa na bugawa.
Har ta fito bai sani ba, ya lula wata duniyar. Qira’arta ya dawo da shi duniyar tunani. Har yanzu yarinyar tana bashi mamaki. Gashi duk irin binciken da yayi akanta bai gano komai daga tarihinsu ba, da ya wuce almajira ce.
Sai da ya tabba tar da ta idar yana nan zaune sannan ya mayar mata da karin ruwan ya tashi ya rufo mata kofar.
A wannan daren Samha ta kasa barci. Tunani ne na irin rayuwar da zata yi da Dokto Zayyad a matsayin matarsa ta bogi. Tasan ba a taba yin irin hakan ba, sai akanta.
Shi kuwa Dokto yana komawa ofis, ya rufe kansa ya kwanta akan ‘yar madaidaiciyar katifarsa. Idan ka shigo ofishin ba zaka taba sanin akwai wani daki a ciki ba. Saboda kofar shigar ta lafe da bangon, babu yadda za ayi ka gane akwai kofa a wurin.