Skip to content
Part 4 of 19 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

Ya saka wannan ya kwance wancan. Da haka har asuba tayi. Yayi alwala ya wuce masallaci. Bayan ya dawo suka nufi duba marasa lafiya. Dakin Samha ya fara shiga. Sauran nasis din sai rarraba idanu suke yi suna mamakin wani irin mahimmanci gareta haka? Almajira a dare daya ta sauya masu dokto. Mutunin da ko magana da mata bayayi. Haka zalika ba ma’abocin sakin fuska bane, bare har wata hira ta hadaku. Mutunin da kowa ke yi masa kallon Miskilin namiji.

“Kinyi Sallah?”

Tambayar da yayi mata kenan, bayan ya dora tattausan hannunsa a wuyarta. Wani irin shock ne yajata a lokaci daya jikinta ya kama rawa. Shine namiji na farko a duniya, da ya taba rike hannunta. Mahaifiyarta ta sanar da ita tunda aka haifeta mahaifinta bai taba kallon inda take ba, bare ta saka ran zai dauketa ko sau daya.

“Ya kike jin jikin yanzu?”

“Da sauki.”

Ta bashi amsa cikin sanyinta. Mamaki yake yi, sai kace ba ita bace mara kunyar yarinyar nan, da ko kwarjini bai yi mata ba, a lokacin da take maida masa magana tana murguda baki.

“Me kike son ki ci?”

Ya tambayeta yana cigaba da shafa goshinta.

“Kunu da kosai.”

Ya jinjina kai. Ya mike tare da kallon daya daga cikin nasis din ya ce,

“Ke ki zauna da ita, ki tabba tar ta tsaftace jikinta sai ki mayar mata da karin ruwan. Anjima za a kawo mata kayan da zata canza. Kai kuma kaje ka nemo mata kunu da kosai, kamar yadda ta bukata. Ku zo mu karasa wurin sauran marasa lafiyan.”

Duk ya kasasu, sannan suka fice. Asiya ta kalleta ta zabga mata harara,

“Ke idan ma son dokto kike yi gwara ki dawo hayyacinki. Shi din ba namiji ne da ke son wargi ba. Kuma ke yaushe ma kika kai matsayin da zai so ki? Yanzu zan kira matarsa a waya sai na gaya mata ga wata banzan almajira tana shirin shiga huruminta. Wallahi idan ta ji sai ta kasheki ta kashe banza.”

Asiya ta ciro wayarta tana kokarin danna lambar Sakina. Ita kanta Sakinan ba tasan Asiya aikin night take yi ba, da babu ko shakka ita zata kira.

Ji ta yi anzare wayar daga hannunta, ya kuma kashe kiran da take kokarin yi. Da sauri ta juyo cike da bala’i. Tsananin tsoro yasakata sakin fitsari a tsaye. Kafafunta babu inda baya kyarma. Yadda ta ganshi kamar wani mahaukacin zaki haka ya koma mata. Fuskarsa babu sassauci. Kafafunta suna rawa ta durkusa kasa tana kuka. Sauran nasis din su kansu sun firgita. Har sun kai kofa ya dakatar da su. Sunyi mamakin yadda ya dakatar da su, amma jin muryar Asiya da abinda take cewa ya nuna masu abinda ya tsaya ya ji ne. Su kansu da basu bane, sai da suka yi ta gumi.

“Nasan za ayi haka. Gulma ke hanaku cigaba matan arewa.”

Ya sunkuyo sosai sannan yace,

“Zaki gane wanene ni idan kika yi kuskuren biyewa zuciyarki da shirmen da take saka maki. Zaki jawowa kanki matsalar da fitarki sai dai Allah. Bana duba kankantar kwaro wajen tsinke masa kai, da zarar yayi barazanar cutar da ni. Ga wayarki. Zaki iya kiranta. Wacce ba almajira ba. Ba zaki gane da gaske ni miskilin namiji bane, sunan da kuke kirana, sai kin sake yunkurin shiga gonata.”

Mamaki ya sake lullube sauran nasis din. Ashe yana sane da duk abinda suke cewa akansa. Sau tari Dokto Zayyad yana ayyukansa kamar aljani. Bai sake magana ba, yayi hanyar waje sauran suka mara masa baya. Sister Khadija tana yi mata alamu da yatsa akan ta kiyaye.

Yana cikin duba marasa lafiya kamar ance ya dago, sai ganin Sakina yayi tana huci. Kallo daya yayi mata bai sake kallonta ba, ya cigaba da duba marasa lafiya. Ita kanta irin kallon da yayi mata ya sakata shiga taitayinta. Masifar da take ganin ta kwaso ta kasa sauke masa.

Har ya gama duba marasa lafiyar tana biye da shi. Anan suka sake tabba tar da ko a gidansa babu wargi. Kowa yana zaton ko har Asiya ta kirata ne? Basusan da kyar barci ya iya kwasarta ba. Ba tason ta gayawa mahaifinta, bare har ya ce me take nufi? ko ta fara sonsa ne? Ofis ya wuce yana zare safar hannunsa.

“Nazo ne ka gaya mini wacece najika da ita jiya cikin dare har take kuka? Dokto ko neman mata ka fara yi ne? Me kake nufi da ni ne? Ka fito ka gaya mini ka gaji da zama da ni, insan inda dare yayi min.”

Bai ce mata uffan ba, ya je ya jona kettle na ruwan zafi ya jira har ya tausa sannan ya koma ya zauna a kujerarsa yana kurba a hankali.

“Bazaka yi mini magana ba? Me nayi maka?”

Ta rushe da kuka. Ya tsani kukan mace yanzu sai ya ji hankalinsa ya tashi. Muryarsa a tsaye ya ce,

“Babu abinda kika yi mini. Ki daina kuka.”

Shi ko irin lallashin nan bai iya ba. Komai zai yi cikin gadara yake yinsa. Ko wurin kwanciya bai cika lallashin nan ba, sannan ba ta isa ta ja ajinta ba, yanzu zai tsinke duk su rasa. Shi bai biya bukatarsa ba, bai kuma biya mata ba. Tana fara jan aji zuciyarsa zata sanar masa kawai ya takura mata ne. Dan haka sai ya kyaleta, duk yadda zuciyarsa takai da son yayi wani abun haka zai hakura.

Shiyasa take cewa ita ba ta taba ganin kamar mijinta ba.

“To ka gaya mini babu komai a tsakaninka da yarinyar da naji sautin kukanta? Hakanne kadai zai kwantar mini da hankali, dan nasan baka taba yi mini karya ba.”

Wannan karon sai da ya dago ya dubeta. Bayason ya dagula mata lissafi idan ba haka ba, da kai tsaye zai gaya mata amaryar da zai aura ne. Hakannan sai ya tsinci kansa da tausayinta. Bai ce mata komai ba, ya cigaba da kurbar shayinsa. Har ya kammala tana zaune tana kallonsa. Duk yadda taso ko yayane ta nemo muninsa abin ya faskara. Namiji ne mai cikar zati. Kyawunsa ya wuce a tsaya misaltawa.

Yana kammala shan tea din ya mike yana tattara wasu files ya mika mata, tana biye a bayansa suka fito.

“Zanje gida indawo ku kula da duk wani abu da yake aikinku ne.”

Duk suka amsa da “Yes sir!”

Ya cigaba da magana yana tafiya, su kuma suna biye da shi a baya.

“Idan Dokto Munnir yazo ku sanar masa ya kirani. Dokto Amina tana da tiyata sha daya, a kirata a sake tuna mata. Zan dawo by 2pm insha Allah.”

Duk suka dinga amsawa. Karaf idanunsa ya sarke da na Asiya. Tayi saurin yin qasa da kai. Sakina ta ce,

“Asiya ashe night kike?”

Ta hadiye wani yamu da kyar, sannan ta ce,

“Eh yanzu zan mikawa abokiyar aikina in wuce gida.”

Sakina ta danyi shiru, sannan ta ce,

“Ok. Zan kiraki idan kin koma mu gaisa.”

Dokto Zayyad bai ce masu komai ba, bai kuma kalli Asiyar ba. A haka har ya karasa motarsa Sakina ta shiga ya figeta. Kai tsaye gidansu ya nufa.

Sakina ba taso ya nufi gidansu da ita ba, dan ta tsani iyayensa.

Ga mamakinsa ganinsu yayi afalon, kamar masu tattauna wani mahimmin abu. Harda yayan mahaifinsa da kuma kaninsa. Ga mahaifiyarsa ga kuma aunties dinsa. Ya ware idanu yana kallon yadda dukkansu suka razana da ganinsa.

Da kyar ya iya boye mamakinsa ya karaso ya durkusa a kasa. Sai da yayi shiru kamar mai tunani sannan ya gaida su. Murya babu karsashi suka amsa.

Mikewa yayi sannan ya ce,

“Na dawo daga wurin aiki ne nace bari in gaidaku.”

Duk suka kalleshi, sannan suka kalli Sakina. Sun san ba zai taba tambayar dalilin da ake zaman meeting babu shi ba, amma tabbas dole abin zai dame shi, dole zai gano akwai gagarumin sirrin da basu son ya sani.

“Zayyad! Dawo.”

Ya dago yana duban Abbansa. Dan dai bai taba musu da shi bane, da babu dalilin da zai sa ya dawo. Sakina tayi saurin dawowa itama. Dan tanaso ta ji ko menene ya sakasu irin wannan zaman, ta sami abin gayawa mahaifinta.

“Mun kasa kiranka ayi zaman nan da kai ne saboda munsan kana wurin aiki. Sannan bama son saka maka damuwa. Sharifat kanwarka ce, ta dauko mana magana. Soyayya take yi da yaron nan dan gidan Gwamna, munyi munyi mu rabasu sun qi rabuwa.”

Yayi mamakin yadda mahaifinsa ya zauna yana shimfida masa tsararren magana kamar bashi ne wanda ya horar da shi akan gaskiya ba. Ba zai taba yarda wannan ne dalilin da za akira meeting da sassafe babu shi ba. Dan haka yayi shiru bai ce komai ba.

“Allah ya daidaita. Zan koma. Na barku lafiya.”

Daga nan ya mike. Ya kasa kallon mahaifiyarsa da ke binsa da kallo, mai kama da kallon tausayi. A cikin mota Sakina ta ce,

“Gaskiya wannan wulakanci ne, sai kace an cireka daga cikin family? Haba! Babu wanda babu a wurin nan sai kai kadai. Allah yasa dai ba wani abun suke kulla…”

Da sauri ta hadiye maganarta tana sake tsuke baki. Ta mance agaban wa take. Ko da yake ta daburce ne, saboda ganin irin wannan meeting din kai da gani kasan akwai magana.

Bai ce mata um bare um-um ba. Da kanta ta nemowa kanta natsuwar da ta rasa a farko. Duk yadda zuciyar Dr Zayyad yake tafarfasa hakan bai isa ya saka ka gane ba, kasancewar fuskarsa da miskilancinsa sun qi barinsa ya bayyana tashin hankalinsa.

Ba kowa ne ya fara kawo masa wannan rudanin ba, da ya wuce Alhaji Bako. Ya dafe goshinsa da hannu daya, yana tuna ranar da ya fara haduwa da Sakina, wanda yake kiran wannan rana a yanzu da bakar rana, domin wannan ranar ita ta zama mahadin tashin hankalin da yake a yanzu. Ji yake kamar ya tsaya ya ce ta fice masa a mota.

Har suka iso gida babu mai cewa dan uwansa ci kanka.

“Bari inyi sauri inhada maka abin karyawa.”

Tana maganar ne fuskarta tana nuna tsantsar tausayi. Wanda yafi kowa sanin karya take yi.

“Na koshi. Zan kwanta banason hayaniya.”

Ya wuce ya barta anan tsaye tana zazzare idanu.

Ko da ya shiga dakin tunanin Samha ya hana shi sukuni. Sai juye-juye yake yi. Yasan dai ba son yarinyar yake yi ba, ko zai so mace ba zai iya son almajira kamar Samha ba. Sai dai ya kasa gane me yake ji a zuciyarsa? A tsakanin tausayi da tsananin son zama kusa da ita? Iyayensa suka sake fado masa a rai. Yana son ya cire tunanin komai aransa amma hakan ya gagara. Sakon message ya shigo wayarsa. Jiki asanyaye ya jawo wayar.

“Idan kana son zaman lafiyarka ka zo ka sameni a gidan gona yanzu. Idan ba haka ba rayuwarka zata cigaba da zama a cikin barazana.”

Zayyad ya lalubo ‘yar bindigarsa yana dubanta,

“Idan na kasheka tamkar na kashe abinda ke kawo mini barazana a cikin rayuwata ne. Kafin ka kasheni ni ya kamata in kasheka.”

Ya furta tare da komawa kan gadon yana lumshe idanu. Barci mai nauyi ya kwashe shi. wanda shi kansa yayi mamakin irin barcin da yayi. Sakina takai ta dawo yafi a kirga, tana jiran fitowarsa. Gashi ya hanata zuwa dakinsa bare ta kwankwasa, dan tasan tabbas ya rufe da key.

Ita kanta ba ta taba yin aikin da yake wahalar da ita kamar wannan aikin ba. Ji take yi kamar akan Zayyad asirinsu zai tonu ita da mahaifinta. Kiran wayarta ya ankarar da ita a inda take tsaye. A firgice ta dauka tana cewa,

“Daddy sai mun bi komai a hankali. Yana da wayo ya daina sakin jiki da ni, dole sai mun yi hakuri mun daga kafa kadan.”

Daga can Alhaji Bako ya hadiye miyau da kyar yana sake jin haushin mahaifin Zayyad.

“Nima na kula da hakan. Na ajiye masa file, wanda nayi zaton ganin file din zai saka shi ya fita hankalinsa har ya bada kai bori ya hau, da alama bai ga file din ba. Da gangar na bar cctv dinsa na ajiye dan nasan zai ganni a lokacin da nake ajiyewa. Har yanzu shiru babu wata magana.”

Sakina ta yi nisa sannan ta ce,

“Kasan shi da iya hadiye damuwa. Ko ya gani zai iya yin shiru kamar bai gani ba.”

Alhaji Bako yayi wani murmushi sannan ya ce,

“Duk iya hadiye damuwarsa ba zai taba ganin file dinnan bai haukace ba. Ke yarinya ce Sakina bakisan me duniyar take ciki ba. Ina tabba tar maki da ya ga file dinnan da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba. Da har damar kawar da shi daga duniyar sai mun samu.”

“Daddy menene a cikin file din? Kuma baka da wasu copies?”

Ya girgiza kai, yana jin daci a zuciyarsa,

“Banyi dogon tunani ba, na kwashesu dukka na kai ofis dinsa. Ban taba tunanin ba zai gani ba. Da kyar na samu na hada files din. Na kai shekaru da dama ina hadawa har Allah yasa na kammala. A ce rana daya aikin yana neman lalacewa? Zan saka a sake duba min inda na ajiye a ofis din.”

Ta jinjina kai,

“Allah ya baka nasara.”

Yayi murmushin mugunta yace

“Ameen my baby.”

Bayan ya sauke wayar ne yayi magana a zahiri yana dariya,

“Kema kin kusa barin duniya Sakina my daughter. Kina kammala yi min aiki kema zan aika ki. Sirrina ni kadai ne bani da abokin da nake tarayya akan sirrina. Gudun baciwar rana.”

Sanye yake cikin kananun kaya, da suka yi matukar dacewa da fatar jikinsa. Yayi kyau har ya gaji, sai kamshi yake zubawa. Ya sakko falon yana kallon yadda Sakina take barci a kujera. Abin ya bashi mamaki, ya dubeta kamar zai tasheta, sai kuma ya fasa ya wuce abinsa.

Ko tashin motar ba ta ji ba, kasancewar ba ta da kara. Mota ce da ta amsa sunanta mota.

Kai tsaye asibitin ya nufa. Har ya shigo kusa da dakin da nasis din suke zama amma babu wanda ya ankare da kamshin turarensa da ya cike wurin.

“Kinsan Allah? Ki kiyayi Dokto Zayyad ina jiye maki wulakancinsa.”

Asiya ta ce

“Ni ai na tsorata da lamarinsa. Ko da yake dole yayi duk abinda yake so. Ga kudi ga kyau.”

Safiyya ta cire taguminta ta ce,

“Wallahi kullum kamar kara mini sonsa ake a zuciya. Ya hada komai. Izzarsa da girman kansa ke damuna da shi. Yanzu dan Allah wannan ‘yar kauyen da ya dauko me zai yi da ita? Wannan yarinyar ba zata wuce shekaru goma sha bakwai ba. Wallahi dazu kiris in wanka mata mari.”

Asiya ta ja tsaki,

“Wallahi na tsaneta. Yarinyar ga rashin kunya. Kowacce magana kika gaya mata da irin amsar da zata baki.”

Dahiru ya ce,

“Ni ku kuke bani haushi Wallahi. Bansan dalilinku na nace masa ba. Oganku ne ku je ku nemi daidai da ku. Amma idan kuka ganshi daga mai zuwa ta shafa fauda, sai mai shafa turaren asiri. Shima ana gaida shi yana ji da kansa, fuska babu fara’a kullum cikin hada rai kamar wani sarki.”

Duk suka kwashe da dariya. Safiyya ta ce,

“Wallahi ina gab da sallamar yarinyar nan idan yaso yazo yayi fadarsa ya tafi ba shikenan ba? Naje zan ba yarinya magani ta qi karba ta kuma bini da bakaken maganganu. Ajiyewa nayi nace kada kisha, jikinki ba nawa ba.”

<< Miskilin Namiji 3Miskilin Namiji 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×