Skip to content
Part 7 of 19 in the Series Miskilin Namiji by Fatima Dan Borno

“Ni babu inda zanje. Ka tafi wurin amaryarka banason ganinka Dokto ka cuceni ka cutar da rayuwata. Sakamakon kaunar da na samu daga gareka bamai dadi bane. Kowa ya juya mini baya saboda kai, amma baka tausayina. Gwara kawai ka bani takarda…”

Bai bari ta dire maganar ba, ya dauketa cak! Kamar wata takarda. Dama gata babu auki ga kuma gajarta. Luf tayi a jikinsa, babu wata alama da ta nuna wai zata tirje masa.

Akan gadonsa ya shimfideta, sannan ya  cire kayan jikinsa, ya taimaka mata itama ta cire kayan jikinta. Sannan suka shiga wanka a tare. Lamarin da ya sanyaya mata zuciya kenan, tana ji a jikinta Dokto ba kaunar Samha yake yi ba, da yana kaunarta babu yadda za ayi tana amarya amma ya kasa kusantarta a wannan dare da duk angwaye suke zumudinsa.

Rabon da ta sami farin ciki irin na wannan dare ita kanta ta dade. Bayan sun fito ya shimfideta akan gado, ya fara aika mata da sakonni masu rikita jiki. Babu inda bai saka harshensa ya lasa a jikinta ba. Sai da ya tabba tar ta gama fita hayyacinta, sannan ya fara karbar hakkinsa, wanda shi kansa yayi kewarta, yayi kewar mace a kusa da shi. Sanin halinta yasa yau din ya shammaceta.

A kalla sun share awa biyu yana sauke duk wata gajiyarsa akanta. Kafin barci ya yi awon gaba da shi. Ita kanta ta kasa daga ko da hannunta, har barcin yayi gaba da ita.

Sai asuba ya farka a gajiye, sannan ya je yayi wanka da ruwan zafi ya gasa jikinsa. Ya fito yana goge tawul akansa, ya tasheta taje ta yi wanka tayi sallah, amma ko kadan ta kasa bude idanunta. Tashin duniyar nan yayi mata sai sake narkewa take yi. Sai da ya daka mata tsawa, sannan ta bude idanun.

“Sallar da zaki yi ne kike ganin sai lokacin da kika gadama ko me?”

Da sauri ta tashi ta nufi bandaki. Har sai da ya gama shiryawa sannan ta fito daga wankan.

“Muje dakinki zan rufe wannan dakin.”

Tayi turus tana kallonsa. Har yanzu lamarinsa mamaki yake ba ta.

‘Ko dai ya gane ina yi masa bincike ne?’

Ta tambayi kanta. Jiki babu kwari ta bi bayansa. Ya daukota ya kawota, a yanzu da burinsa ya cika sai ya barta tana takawa da kanta. Duk da haka ta sami farin ciki fiye da zatonta. A zuciyarta tana cewa,

‘Kwanan nan zan maidaki tamkar ‘yar aikinmu, kafin ki zo ki bar mini gidana.’

Bai duba Samha ba, kasancewar yayi latti, dan haka a gurguje ya fice hayaso ya rasa jam’i. Sakina tayi shewa har da juyi tana dariya. Duk da idan ta tuna kyawun Samha gabanta yana faduwa, amma kuma idan ta tuna yadda mijinta ya nunawa Samhar ita ba komai ba ce sai kawai ta kama dariya tana jin nishadi.

Kiran mahaifinta tayi a waya,

“Hello Abba. Kasan ko kallon amaryar bai yi ba? Yayi ta ji da nayi kamar nice amaryar.”

Alhaji bako yaja wani irin tsaki ya kashe wayar.

Takaicin Sakina ya sake turnuke shi. Ya tabba ta dai yarinyar nan ba zata yi masa abinda yake so ba.

Da misalin karfe goma sha daya ne, aka fara hasko Alhaji Bako a gidajen tv da radio. Ana live da shi.

“Idan har zan iya mance mahaifiyata babu ko shakka zan iya mance  kaina. Nayi mamakin ni ba dan siyasa ba, ni ba mai neman takarar gwamna ko dan majalisa ba, me zai sa aje ana ba ta min suna? Mahaifiya fa ta wuce wasa.

“Bazan mance ba, na rabu da ita akan tana fama da ciwon idanu zan kaita egypt a duba idanunta. Kwatsam sai ga mummunan labari.”

“To yallabai meyasa ka barta a wannan gidan da take?

Ya dago babu alamar razana a fuskarsa, domin sai da ya shirya sosai sannan ya fito.

“Babu yadda banyi da ita ba, ta dawo gidana cikin iyalina, amma ta qi. A lokacin da aka saceta ina wani meeting ina sauri ingama inje gareta, sai ga mummunan labari daga wanda na saka ya dinga kulawa da gidan. Nayi kuka nayi bakin ciki. Kuma a yanzu, ina so insanarwa duniya, indai wadanda suka dauki mahaifiyata suna jina, dan Allah su dawo mini da ita, nayi alkawarin zan basu ninkin abinda suke nema. Domin har yanzu sun qi yarda suyi magana da ni. Su gaya mini inda suke so akai masu kudinsu, su dawo mini da rayuwata.”

Ya goce da kuka yana goge hawayen da hankacif.

Sakina tasha mamakin jin maganganun mahaifinta. Amma da yake tasan halinsa dan wasan kwaikwayo ne, sai ba ta damu ba.

Shi kuwa Dr. Zayyad a lokacin ya shiga tiyata. A gajiye ya fito yana nufar teburinsa. Kamar ance ya daga kai ya kalli tv. Hirar ta ja hankalinsa sosai. Ya zauna yana kurbar bakin tea yana murmushi. Yana da tabbacin idan mahaifiyarsa ta fito zai iya sakawa a kasheta domin ya samu saukin barazanar da yake ciki. Tunda Dr. Zayyad yake jin labarin mara imani bai taba jin labari irin na surukinsa ba.

“Samha!”

Zuciyarsa ya tuna masa da ita. Gabansa yayi wani irin faduwa. Ya mance da yarinyar. Ya mance yana da wata mata. A gurguje ya kintsa ya fito. Da gudu nas ta biyo bayansa tana cewa,

“Dokto kana da bakuwa.”

Bai kalleta ba ya cigaba da tafiya yana cewa,

“Ko wacece aba ta hakuri ina da uzuri a gida.”

Dole ta koma, dan tasan ba zai taba tsayawa ba.

Sakina ta kasa hakuri dan haka ta haura sama. Tunda Samha ta tashi take jin yunwa, dan haka ta ci ragowar kazarta, sannan tasha lemu. Ko kitchen din ba ta leka ba. Tana sanye da wani riga da wando masu bin jiki. Wanda Anti Rahama ta yi mata akwati guda na kananan kaya. Dama kuma ita din ma’abociyar son kayan shan iska ne. Gashin kanta yasha gyara yana ta walwali.

“Amarya kinsha kamshi.”

Samha da ke zaune a falo tana kallo ta ji muryar Sakina a tsakiyar kanta.

“Ke kuwa wani irin aure ne haka kamar dole? Mijin nan bai damu da ke ba, Ko jiya baki ga a wurina yazo ya kwanta muka sha soyayya ba? Tun anan idan nice ke sai intattara ingudu abina. Kina bani tausayi Wallahi. Amarya da ake dokinta sai aka buge da dokin uwargida.”

Samha ta dubeta fuska a sake tace,

“Daga yau kuma bazaki sake ganinsa kusa da ke ba, har sai na kammala kwanaki bakwaina. Dama jiya tausayi kika bani yadda na ganki kamar sabuwar kamu a hauka, shiyasa nace masa ya je ya ji da ke. Amma tunda kika ce haka, ni zan nuna maki cikakkiyar mace ce ni.”

Nan da nan fuskar Sakina ta canza.

“Karya kike yi ‘yar matsiyata. Ni zanyi maganinki. Kin yi kadan ki ce wai zaki dauke shi. Ke awa? Bari ingaya maki wani abun da baki sani ba. Wallahi mace ba ta isa ta juya Doktona ba. Idan kin shigo da tsafi ne ki ajiye dan baya tasiri a zuciyar mijina.”

Samha ta mike tana kallonta,

“Kin taba gwada tsafin kenan, har kika gane baya tasiri a wurinsa? Kinsan tsafin iri-iri ne, ki bari in jaraba nawa mana, sai muga ko da gaske ne baya tasiri a zuciyarsa? Wai dan Allah meyasa ban damu da lamarinki ba, kike damuwa da nawa? Meyasa? Kije ki ji da abinda ke damunki. Kuma zan nuna maki karfi da tasirin tsafina.”

Kalaman Samha masu zafi ne. Tabbas Samha zata iya yin kisa da wadannan kalaman nata. Sakina tayi danasanin hayowa saman nan. Haka ta yi ta masifa, amma Samha ko kallonta ba ta yi ba. Ta fice tana cewa,

“Bari ya dawo zanji ko shi ya daure maki kugu ki dinga yi mini rashin kunya.”

Ta sauka tana huci. Ba ta dade da  zama ba, ta ji sallamarsa. Da sauri ta dukar da kai tana kuka.

“Me kuma ya faru? Kinsanni sarai kinsan bana son fitina.”

Ya furta yana jin mugun haushinta.

“Dokto dan Allah ka maidani gidanmu. Ba zai yiwu ace amaryarka tana gasa min maganganun da ta gadama ba.”

Dr Zayyad ya zaro idanu cike da mamaki,

“A ina kuka hadu?”

Ya tambayeta yana kara mamaki. Nan da nan ta rikice sai kuma ta ce,

“Ina zaune anan ta biyoni ta dinga gasa min magana dan kawai nace mata ka fita. Wai don me zan rikeka ita matsafiya ce sai ta tsaface ka.”

Murmushi ya saki, sannan y haura saman.

Samha ya samu cikin shigarta na pink. Tayi masa kyau kamar ya dauketa yayi ta juyi da ita.

“Kin sauka kasa ne?”

Ya tambayeta ba tare da ya amsa gaida shin da take yi ba.”

Ta zaro idanunta tana dubansa,

“A’a.”

Ta bashi amsa a takaice. Idanun Zayyad ya sauka akan agogo ya tsuguna ya dauka yana kallo,

“Agogon waye?”

Ya tambaya yana tsareta da idanu.

“Na matar gidan nan ce.”

Bai ce komai ba ya dubeta.

“Kiyi hakuri aikin gaggawa ya fitar da ni.”

Har yanzu mamakin saukin kai irin na Dr. Zayyad take yi.

Daga nesa idan bakasan shi ba, kai tsaye zaka cigaba da kiransa da sunaye kala-kala. miskili, mai wulakanci, mara tausayi.

“Kin ci abinci?”

Ta dan girgiza kai. Ya taku uku, ana hudu ya kara sai gashi agabanta suna fuskantar juna. Ya kamo kafadunta yana cewa,

“Ko innemo maki mai aiki ne?”

Anan ma girgiza kai ta yi.

Har zai juya ya ji ta yi magana,

“Ina so idan akwai dakuna a qasa a mayar da ni kasan.”

Sosai yake dubanta.

“Babu matsala. Zan saka a gyara maki sai a siya maki wasu sabbin kayan, tunda babu yadda za ayi a kwashe wadannan.”

Ta gyada kai alamun ta gamsu. Har yanzu mamakin yadda yake yiwa yarinyar sanyi yake yi. Da sauri ya sauka qasa. Sakina tana zaune tana aikin murmushi. Sai ji ta yi ya cillo mata agogonta.

“Ga agogon da kika je neman bala’i nan garin masifa har kin mance shi a dakin.”

Nan da nan Sakina ta hau kame-kame. Da hannu ya dakatar da ita,

“Dakata dan Allah. Kinsanni sarai na tsani makaryaci banason karya. ki yi kokari ki kama girmanki tun kafin yarinyar nan ta rainaki.”

Ya wuce kawai abinsa. A ranar ya saka aka fara gyaran part din da zata zauna. Ita dai Sakina sai idanu take rabawa. Zuciyarta kawai ta dinga gaya mata aure zai kara. Dan haka wannan karon mahaifinsa ta kira kai tsaye.

“Hello Abba ka tashi lfy?”

Daga can bangaren yana  mamakin yau Sakina shi take jin kira?

“Lafiya lau Sakina.”

Sai kuma ta rushe da kuka tana cewa,

“Abba kasan Dokto wai aure zai sake karawa.”

Abba yana kishingide ne, bai san lokacin da ya tashi zaune ba,

“Auren lafiya? Anya kuwa kin bincika daidai?”

“Wallahi aure zai kara. Gashi can yana gyara bangaren kusa da ni.”

Abba ya yi shiru cike da sake-sake. Yasan dai idan da gaske ne, su ya kamata su fara sani. Zayyad bai taba yin komai ba tare da izininsu ba.

“Ki bari zan bincika.”

Suka yi sallama ya ajiyewa wayar yana kallon Hajiya.

“Wai kin ji danki aure zai kara ko?”

Ta dan yi shiru, daga bisani ta girgiza kai,

“Gaskiya ban yarda ba. Amma kirawo shi.”

Ya daga waya ya kira Dr. Zayyad. A lokacin kansa ya dau zafi, saboda marasa lafiya da ake ta tururuwan kawowa annoban cizon sauro yana ta kai mutane kasa.

“Assalamu alaikum. Ina wuni Abba.”

Ya fada da dakakkiyar muryarsa.

“Yauwa Zayyad. Dazu matarka ta kirawoni wai zaka kara aure.”

Cike da mamaki yake jujjuya maganar.

“Aure kuma Abba? Duka-duka yaushe na yi aure da zan kara? Kuma idan zan kara aure dole sai kun amince sannan hakan zata yiwu.”

Abban ya dubi Umma sannan ya ce,

“To yanzu ta kirani tana kuka. Wai kana gyaran bangaren kusa da ita.”

Sai yanzu ya saki ajiyar zuciya. Sannan ya gayawa Abban Samha ce tafi son qasa. Suka dan tattauna sannan suka ajiye wayar.

Takaici ya ishi Dr. Zayyad. Ya zama dole ya takawa Sakina birki akan yadda duk kankantar abu sai ta kira iyayensa. Bayan haka kawai ba kiransu take yi dan ta gaidasu ba.

Bai bar ofis ba, sai yamma likis. Da ita ya ci karo, domin kuwa Allah ya hore mata ilmin danna waya. Da wahala ya shigo gidan bai sameta a falon nan ba. Yanzu ma ya kula wani sabon gadinsa take yi.

“Sannu da zuwa.”

Ta ce da shi tana tashi zaune.

Bai amsa ba, ya nemi wuri ya zauna.

“Sakina. Zanyi maki gargadi na karshe. Idan kika sake kiran gidanmu kika kai masu qarata, zaki koma can da zama.”

Jikinta ya kama rawa. Tarasa dalilin da ko magana Dr. Zayyad yake yi mata sai ta ji duk ta firgita. Bare kuma zancen komawa can da zama.

Ya mike da nufin haurawa sama.

“Ina zaka je kuma?”

Ko kallon inda take bai yi ba.

A tsakiyar falon ya sameta ta yi kyau sosai cikin doguwar rigarta. Cornflakes take sha kamar bazata sha ba. Ita tunda aka raba ta da mahaifiyarta gaba daya aka zare mata laka. Tunani take yi ko ta mutu ne suke boye mata?

“Sannu da zuwa uncle Zayyad.”

Sunan yayi masa dadi. Amma yayi mamaki dan ba ta taba kiran sunansa ba.

“Yauwa sannu da gida.”

Ya nemi wuri ya zauna.

“Sati mai zuwa zaki koma qasa. Zaki iya zuwa dakina?”

Ya tambayeta yana dubanta. Saboda bangarensa na sama akwai kura sosai.

Maganganun Sakina suka cigaba da dawo mata cikin kai. Dan haka ta daga kai alamun eh. Har yanzu yarinyar tana cigaba da bashi mamaki. Sai kace ba Samha dai mara kunya da ya sani ba. Samhar da babu mai kayar da ita a magana. Yarinyar da duk girmanka take iya kallon idanunka ta wankeka tas!

Ya mika mata hannu,

“Taso mu je.”

Ta mika masa ya dagata. Gaba daya ya mayar da ita jikinsa.

Hawaye suka cigaba da gudu a bisa takalin fuskarta.

Ya dagota yana dauke mata hawayen tare da cewa,

“Ki daina kuka kada kishiya ta rainaki.”

Nan da nan kuwa ya nemi hawayen ya rasa. Yayi ta murmushi kawai ya kamo hannunta suka kama hanyar sakkowa. Tunda Sakina ta ji takun sakkowa kuma ba karar takalmin Zayyad kadai bane ta zurawa matattakalan idanu.

Abinda take zato shi ta gani. Sunyi bala’in kyau kamar a sure su a gudu da su. Yadda ya rike hannunta yafi komai daga mata hankali. Kuka take so tayi amma ta dake kada yarinyar ta ga faduwarta.

A kujera daya suka zauna. Ya dubi Sakina sannan ya dubi Samha ya ce,

“Ina so injawo hankulanku ne. Dukkanku nan soyayya ce ta saka na aureta. Babu wacce akayi min dole. Dan haka ya zama dole ku hada kanku ku girmama juna.”

Sakina ta yi tsalam ta ce,

“Ta dai girmamani.”

Kallo daya yayi mata tayi saurin dawowa hayyacinta.

<< Miskilin Namiji 6Miskilin Namiji 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×