Da sauri ta wuce banɗakinsa ta wanke fuskarta. Gaba ɗaya ta gigice ta fita hayyacinta. Sai ta yi kamar zata fice sai kuma ta sake komawa. Shi kuwa tuni ya sa kai ya fice zuwa falon.
Da gudu ta ƙanƙameta, sai kuma ta kasa jurewa ta fasa kuka mai ban tausayi. Dalilan kukan nata suna da yawa, ita kaɗai tasani sai kuwa M.Y da ke zaune shiru. Kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar da yana cikin wani hali.
Gwaggo ta ɗauke ƙwallan idanunta tana bubbuga bayanta alamun lallashi. A hankali kuma sai kukan Husna ya koma ɗaure mata kai, domin da farko ta yi zaton kukan farin ciki ne, a yanzu kuma sai ta fara fahimtar akwai matsala, musamman yadda shi kansa M.Y ɗin ya sauya mata. Ga shi Husna ta rame sosai.
“Husna!”
Ta ɗan kira sunanta a wani yanayi. Husna ta yi saurin goge hawayenta tana ƙoƙarin tsaida su amma sun ƙi tsayawa. Ta sake sa kuka ta rungumeta tsam tana jin kamar wani zai ƙwace mata ita.
“Gwaggo don Allah kada ki sake yin nesa da ni.”
Ta faɗa cikin sarƙewar murya, da kuka mai taɓa zuciya. Shi kansa M.Y jikinsa ya yi sanyi.
Gwaggo ta dinga lallashinta amma zuciyarta cike da saƙe-saƙe.
Ɗaya bayan ɗaya suka dinga zuwa suna gaida surukarsu. Gwaggo ta jawo hannun Husna, hakan yasa M.Y shima ya bi bayansu gudun kada ta gayawa Gwaggo zancen da zai iya kasheta.
Husna ta dinga yin nan nan da Gwaggo. Tana neman inda zata je ta ɓoye ta yi kukan da ya tsaya mata a maƙoshi ko zata samu natsuwa. Amma sai Gwaggo ta dinga binta da kallo a duk inda tasa ƙafafu.
M.Y bai sake bin ta kan Husna ba, tunda ya tabbatar ba zata iya tarwatsa farin cikin Gwaggo ba. Haka zalika ko ya ce zai tsaya su yi magana ba lallai ta fahimce shi ba.
Husna ce kwance a cinyar Gwaggo ta yi magana cikin sanyi,
“Gwaggo wai me ya kashe Abba ne? Na ji ana cewa kashe shi akayi.”
Gwaggon ta shafi kanta ta ce,
“Bana son tunawa Husna. Malam Yusuf ya kasance yana aiki a ƙarƙashin wani mutum, mai kuɗi. Shi ne direban Alhajin don haka suka kasance masu yawan tafiye-tafiye. A shekarun baya kafin mutuwar iyayenki, aka zo har gida aka ɗauki Malam Yusuf. Kuma a ranar ya dawo gida ya gaya min ya ajiye aikinsa bansan dalili ba, kuma cikin damuwa ya dawo gidan. Da farko waɗanda suka ɗauke shi sun ce a biyasu kuɗaɗe har miliyan goma sannan za su sake shi. Shi ne muka siyar da komai namu, da ƙyar muka haɗa miliyan biyar. Shi kansa Babban mutum a lokacin karatu yake yi. Bayan mun bayar da miliyan biyar wanda Babban mutum yakai masu dan kowa ya ce ba zai je ba. Kawai sai suka sake kiranmu suka ce sun kashe shi. Gawansa ma suka hana mu. Ba zan taɓa yafewa mutanan nan ba. Mun shiga wani hali na ƙuncin rayuwa da babu. Ga babban mutum ya yi ta ciwo ina jinyarsa, kowa ya guje mu. Dama mahaifinki shi ne ƙanina shi yakan taimaka mana. Shima kuma daga baya ya yi hatsari shi da mahaifiyarki duk suka rasu. Mun sha wahala kafin Allah yasa Babban mutum ya sami aiki har zuwa tahowarsa Kaduna. Itama Salma ƙanwata ta haifeta wato ƙanwar mahaifinki, nasan kinsan hakan. Zumuncin yanzu ne anwatsar da shi abin sai addu’a.”
Husna ta sake ɗagowa tana kallon yadda Gwaggo take goge hawayenta. Ta yi shiru tana nazarin dalilin talauci zai sa M.Y ya shiga mummunan aiki? Aikin da har agun Allah babu uzuri?
A take tunaninta ya koma baya, da ta tsinci bindiga a jakarsa, da irin ƙaryar da ya yi wa Gwaggo.
“Gwaggo menene asalin aikin Uncle?”
Bakinta ya suɓuce ta yi tambayar da bata san lokacin da ta fito ba.
“Ma aikacin banki ne, acan yake aiki. Me ya sa kike yawan yi min tambayar nan?”
Gwaggo ta mayar mata da martani tare da tambaya a jere. Girgiza kai kawai ta yi,
“Babu komai.”
Da daddare duk suna tare a falo, ana kallon film. A lokacin M.Y ya shigo hannunsa riƙe da ledoji. Falon fes! Husna ta gyara ta sanya turaren wuta. Duk da zazzaɓin da yake ji, hakan bai hanashi jin farin ciki da wannan ƙamshi da ya shaƙa ba.
A gaban Gwaggo ya ajiye ledojin ya wuce ɗaki domin watsa ruwa. Gwaggo ta juyo tana kallon matan ɗaya bayan ɗaya.
“A cikinku wacece ke da girki?”
Duk suka yi shiru, kasancewar girkin ya birkice masu. Kuma shi babu ruwansa kullum yana tare da Salimarsa.
Carab Salima ta ce,
“Nice Gwaggo.”
Ta ɗan dubeta sheƙeƙe,
“To ki tashi ki bi mijinki.”
Salima ta miƙe ta bi bayan M.Y. Yana nan zaune ya yi tagumi. Ya zubawa sarƙan Husna idanu baya mance yadda akayi sarƙan yazo hannunsa. Ga hijabinta wanda akayi mata fyaɗe, bayan Kabir ya tabbatar mata ba aga Hijabinta ba, hakannan suka kawota cikin mota babu hijabi babu ɗankwali. Shi kaɗai yasan dalilin ajiye kayayyakin nan. Ya kai Hijabin hanci ya shinshina.
“M.Y menene wannan kuma a hannunka?”
Salima ta katse masa tunani. Ya dubeta kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce,
“Bana buƙatan kowa a kusa da ni.”
Ta girgiza kai,
“Gwaggo ce ta tambayi waye ke da girki, nace mata nice. Don haka ta turo ni dole sai na zo.”
Bai sake magana ba, ya tattara kayan ya sauya masu wuri zuwa cikin jakarsa, ya shige banɗaki ya sakarwa kansa ruwa.
Husna kuwa miƙewa ta yi ta ce tana zuwa, ta shiga ɗaki ta zauna kawai tare da tagumi. Can ta fasa kuka mai ban tausayi, tana jin wutar tsanar M.Y yana sake ruruwa a zuciyarta. Idan har saboda talauci yasa M.Y ya faɗa cikin halaka babu wanda zai taɓa yi masa uzuri daga irin cin amanar da ya yi wa mahaifiyarsa. Ta sake fasa kuka tana cusa hijabi a cikin bakinta.
Ji ta yi andafata hakan yasa ta ɗago da jajayen idanunta a firgice duk a tunaninta Gwaggo ce. M.Y ta gani cikin jallabiyarsa. Duk da baida walwala yana nan da kyansa na Fulani. Gaba ɗaya sai ya cika mata idanu hakan yasa ta sunkuyar da kai. Tana son yi masa rashin kunya amma bakinta ya yi nauyi, dole ta yi shiru.
“Ki tashi Gwaggo tana nemanki. Ki goge hawayen nan.”
Baki a sake take kallonsa har ya juya. Da sauri ta nufi banɗaki ta wanke idanunta. Duk yadda Husna ta kai ga ɓoye damuwarta tuni Gwaggo ta gano akwai matsala, sai dai ta yi alkawarin zata bi komai a hankali har ta gane komai.
Anan falon suka yi ta hira da ciye-ciye har sha ɗayan dare, sannan suka yi Sallama kowa ya wuce makwancinsa. Dama Gwaggo a ɗakin Husna ta sauka. Ta kalli ko ina ta ce,
“Shi babban mutum ba zai gyara maki ɗakin bane?”
Sai Husna ta ji kamar ta ce mata bata buƙatan kuɗin haram. Sai kuma ta yi shiru.
Ƙarfe ɗayan dare idanunsu biyu, sai hira Gwaggo take yi mata, ita kuma ta dinga daurewa tana bata amsa. A lokacin ta miƙe tana hamma,
“Zanje insha ruwa a falo.”
Gwaggo ta bita da kallo har ta fice. A falon ta ɗebi ruwa tana sha, ta ji muryar M.Y yana magana a hankali,
“Eh kada ku damu ku fara tafiya gani nan zuwa.”
Ta waiwayo tana kallonsa. Bindiga ce a hannunsa yana dubawa. Ƙirjinta ya buga da ƙarfi. A lokaci guda suka haɗa idanu, sai dai babu alamun razana a idanunsa.
“Uncle kaji tsoron Allah.”
Ta furta masa, tare da shigewa da sauri tana jin ƙirjinta kamar ansanya guduma.
A can ƙarshen katifar ta maƙale tana jin zuciyarta tana suya.
“Husna zo nan ki gaya min abin da ke damunki.”
Tana son yin magana kuka ya ƙwace mata, ta sakko da sauri ta rungume Gwaggo tana ci gaba da kukanta. Gaba ɗaya Gwaggo take tausayi. Duk irin halayyar da ta tsani mutum da su, ga sunan kwance a jikin ɗanta ɗan da ta fi so fiye da komai.
“Gwaggo Uncle ne…”
Ta furta bakinta yana karkarwa.
“Me ya yi?”
Gwaggo ta tambaya cikin razana da tashin hankali..
Mu je zuwa dai..