A hankali ta janye jikinta daga na Gwaggo ta ce,
“Gwaggo ba ƙaran Uncle zan kawo maki ba. Amma ina roƙonki da ki roƙe shi ya bani wayata ina ƙaruwa da wayar, ko da ba zai barni in koma Makaranta ba.”
Gwaggo ta saki ajiyar zuciya ta sake janyo Husna jikinta. Sai a lokacin hawayen fuskarta ya sauka.
“Husna kin bani tsoro, kin firgitani. A zatona babban mutum yana cutar da ke ne, ko kuma yana aikata ba daidai ba. Tunda nake babu wanda ya taɓa kawo min ƙaran babban Mutum sai dai ma azo a gode min akan aikin alkhairin da ya yi. Idan saboda wannan ne ki kwantar da hankalinki.”
Husna ta sa hannu ta goge hawayen fuskar Gwaggo tana ƙara jin sonta yana ratsata.
“Husna ina son ki taimakeni ki yi min alƙawarin wani abu.”
Yarr! Husna ta ji tsigan jikinta ya tashi. Babu abinda Gwaggo zata nema a duniya ko menene bata yi mata ba. Don haka ta dubi fuskar Gwaggo ta ce,
“Na yi maki alƙawarin ko menene zan yi maki. Insha Allahu ko baki yi alfahari da kowa a cikin ‘ya’ya ba, zaki yi alfahari da ni Gwaggo.”
Gwaggo ta ɗan musƙuta ta ce,
“Ina son duk rintsi duk wuya kada ki guji babban mutum, kada ki juya masa baya a duk lokacin da yake neman taimakonki. Domin kin fi kowa kusa da shi a yanzu tunda mijinki ne.”
Abu mai wahala. Ta tsani M.Y ba zata taɓa yafe masa ba, ba zata taɓa zama da shi a matsayin miji ba, duk daren daɗewa. Kalaman Bilki suka daketa a lokacin da take tunawa M.Y abin da ya gaya masu akan aurenta. Ita kuwa me zata ci da mutunin da ya ci amanar mahaifiyarsa? Ita wacece da ba zai ci nata ba?
“Gwaggo na yi maki alƙawari.”
Ta tsinci bakinta wajen furtawa Gwaggo abin da ita kanta ta sani ba zai taɓa faruwa ba. Ta tabbata a lokacin da ta karya alƙawarinta Gwaggo ba zata taɓa yi mata kallon maci amana ba. Sai dai kuma wani ɓangare na zuciyarsa da yake ankarar da ita girman alƙawari.
Haka kowannensu ya kwanta cike da saƙe-saƙe.
Washegari Gwaggo take tambayarsu kwana nawa suke yi a girkinsu? Bilki ta ce kwanaki bibbiyu. Hakan yasa tasa idanu sosai, har kwanakin girkin Husna ya zagayo.
A lokacin Amina ta ji daɗin zuwan Gwaggo kasancewar sun sami kulawan mijinsu da suka rasa shekaru masu yawa.
Gwaggo ta dubi Husna ta ce,
“Maza jeki ki gyara ɓangaren mijinki ki tsaftace masa komai.”
Jiki a sanyaye Husna ta shiga ɗakinsa. Banɗaki ta fara wankewa, sannan ta ɗauke komai ta maida ma’adanansa, ta goge masa takalma, ta duba taga sabon tawul ta fitar masa ta ɗauke wancen da ya yi datti. Ta cire zanen gado ta shimfiɗa wankakke. Ta share ko ina ta goge. Nan da nan ɗakin ya sauya kamanni. Turaren wuta ta sanya ta turara ko ina sannan ta fice zuwa falo. Da ita da masu aiki suka ƙarasa gyaran, sannan suka faɗa ɗakin girki. Ita take nuna masu abubuwan da za su yanka mata har ta gama haɗa lafiyayyan tuwan shinkafa miyar ɗanyan kuɓewa ya ji ganda da busasshen kifi.
Su kansu kishiyoyin sai da yamunsu ya dinga tsinkewa tun kafin ta gama gidan ya cika da ƙamshi. Shi kuwa M.Y tunda ya fita gabansa ke faɗiwa kasancewar yasan yau Husna zata karɓi girki kuma ya tabbata Gwaggo zata sa idanu akai.
A gajiye ya dawo gidan a lokacin ta gama jere komai a dinning. Gwaggo ta dubeta ta gane abinda take nufi, don haka jiki babu ƙwari ta tashi ta karɓi kayan hannunsa ta yi masa sannu da zuwa. Zubawa juna idanu suka yi, nan da nan idanunta suka kawo ruwa. Ya yi saurin kaucewa tsayuwarsu ya ƙarasa yana gaida Gwaggo.
Ɗakinsa ta wuce ta tara masa ruwan wanka ta zauna shiru tana wani dogon tunani. Har ya shigo yana duban ko ina bata sani ba. Ji ya yi wani abu mai sanyi yana kwaranya a zuciyarsa. Da yana da dama, da yau ya gwadawa Husna matsayinta a wurinsa. Da sauri ya kawar da tunanin da yake ya shiga rage kayan jikinsa. Tuni ta duƙar da kai tana Allah-Allaah ya shige banɗakin.
Babu ɓata lokaci ya faɗa wanka ya barta tana tattara kayan da ya cire.
Yana fitowa ya sami wurin ya ƙara yi masa kyau da haske. Lallai tsafta abu ne mai kyau. Zai so ya kasance da Husna ita kaɗai babu ko shakka zata ɗauke masa matsayin mata ukun nan da ya tara.
Har ya gama shiri kanta a ƙasa, sannan ya dubeta,
“Muje ki kai min abincina kusa da Gwaggo zan ci.”
Bata tanka masa ba, ta bi bayansa. A gaban Gwaggo ya zauna wanda itama tuwan take ci. Yana fara ci ya yi hamdala. Husna har ta so ta ɗara Gwaggo iya girki.
Gwaggo tana kula da yadda gaba ɗaya Husna ta takura, don haka ta dinga sakota a cikin hirarta. A hankali ta haɗa masa kan iyalan suna samun lokacinsa har ayi ɗan hira da shi. Duk da idan Gwaggo ta yi magana yafi bata amsa akan sauran.
Misalin ƙarfe goman dare ya shigo da kayan ciye-ciye. Ya zubewa Gwaggo a gaba.
“Gwaggo so nake kiyi ƙiba sosai kafin ki koma.”
Duk suka yi dariya. Ita kuwa Husna a duk lokacin da ta ganshi sai ta kafe shi da idanunta tana al’ajabin yadda ya rufe mummunan fuskarshi ya fiddowa mahaifiyarsa mai kyan. A duk lokacin da ta tuna Gwaggo zata iya mutuwa muddin tasan ɗayan fuskar ɗanta, sai ta ji hawaye.
Tana yi masa fatan ya shiryu kafin lokacin tonon asirinsa, don tabbas lokacin nan yana nan zuwa.
“Gwaggo sai da safe barci nake ji.”
Gwaggo ta amsa masa ya sa kai ya wuce. Salima ta miƙe tsalam da ninyan binsa, tunda tasan Husna bata zuwa kwana da shi. Hasalima bata da girki a gidan.
“Ke Salima zo nan.”
Salima ta dawo cike da sanyin guiwa tana duban Gwaggo.
“Ɗakinki zaki shiga ki daina shiga hurumin wasu.”
Duk suka dubi Salima,yadda ta yi kamar ta yi kuka. Ba ƙaramin takurata Gwaggo ta yi a kwanakin nan ba, ta yadda bata samun mijinta yadda ya kamata. A fusace ta shige ɗakinta ta rufe. Husna kuma ta tashi ta shiga ɗakinta.
Gwaggo ta bi bayanta tana kallonta,
“Kinyi wanka?”
Ta tambayeta tana dubanta. Gyaɗa kai ta yi a sanyaye. Gwaggo bata bi ta kanta ba, ta jeho Mata rigar barci ta ce,
“Maza kisa, ki kuma tabbatar kin shafa Humra ki wuce wurin mijinki.”
Bata da ƙarfin guiwar yin musu da Gwaggo dole ta aiwatar da hakan. A zuciyarta tana cewa a falo zata kwana, ko kuma ta ƙwanƙwasawa Amina ta turata wurin mijin.
Sai dai tana gama shiryawa Gwaggo ta rakota har bakin ƙofar M.Y ta ce maza ta shiga. Jiki babu ƙwari ta shiga da Sallama Gwaggo ta juya ta koma.
Yana zaune yana danna Laptop ɗinsa ya ɗago ya dubeta, ita bata ƙaraso ba, ita kuma bata koma ba. Bai ce mata komai ba har ta gaji da tsayuwa ta yi zamanta a ƙasa a bakin ƙofar.
Shi gaba ɗaya tsoronta yake ji, dan ta zame masa dodo.
Kwanciya ya yi akan gadon kamar ya yi barci hakan yasa itama ta kwanta anan bakin ƙofar. Yana kallon yadda ta takure kanta cikin hijabi, har barci ya saceta. A hankali ya sakko ya ɗauketa cak ya ajiye akan gadon, ya jawo masu bargo tare da rungumeta.
Ajiyar zuciya ya ƙwace masa. Humran mai sanyin ƙamshi yasa shi kai hancinsa yana shinshinanta. Ganin zata tashi ya yi saurin dainawa. A hankali ya zare hijabin jikinta gaba ɗaya sai ya kafe ƙirjin da idanu. Yarinyar Allah ya yi mata halitta. Ɗan bakin ya kaiwa duba yana tuna kalamanta akansa. Ya ɗan rintse idanu.
Saukan hannunta ya ji a jikinsa ta shige masa sosai. Hakan yasa shima ya shigewa tattausan fatarta yana ƙara jin wani irin natsuwa.
Tsoro yake ya yi abin da zai tasheta don haka ya yi masu addu’a yaja bargon har cikin kansu ta yadda suke shaƙar numfashi.
Sai ince sai da safe Husna da Mu’azzam.
Very good