Skip to content
Part 20 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Tun ƙarfe biyar ya fice daga gidan, don ita kanta sai da ta so makara wajen tashi. A hanzarce ta yi Sallah, sannan ta gyara masa ko ina ta sa kai ta fice. Gwaggo tana zaune tana lazimi ta ƙaraso ta kwanta a jikinta. Kamar wasa ta koma barcinta. Gwaggo dai ta zuba mata idanu zata so da tana da iko da ta buɗe zuciyar Husna domin ta ga abin da ke damunta.

Ƙarfe tara Husna ta tashi daga barci, lokacin masu aiki sun gaji da zaman jiranta sun haɗa abin karyawa. Har falon ta rako Gwaggo sannan ta koma ɗaki ta fasa kukan da yake ta cinta a rai. Tana tsananin ƙyamar kanta idan ta tuna wanda ta ɗauke shi a matsayin mai share mata hawaye, yau shi ne da kansa ya keta mata haddi sai ta ji me ya sa ma ta rayu?

Duk da haka tausayin Gwaggo ya danne komai a zuciyarta. Kukanta take yi tsakaninta da Allah. Wannan karon ta ji motsin buɗe ƙofa don haka ta ɗago a razane. Shi ɗinne ya jingina kansa a jikin ƙofar, bayan ya rufe yana binta da kallo cike da tausayawa.

“Husna me ya sa kike kuka? Me ya sa ba zaki karɓi ƙaddararki kamar yadda na karɓi nawa ba?

A hankali ta yi magana idanunta suna zubar da hawaye,

“Uncle kai kayi min fyaɗe? Ka gaya min abin da zuciyata zata sami natsuwa don Allah. Ka gaya min gaskiya Uncle ka ƙaryata zuciyata da take kwana da baƙin ciki. Da gaske kai kayi wa marainiya fyaɗe a daji? Ba zan mance ba mutane uku na gani tsaye akaina me ya sa ban ganeka daga cikin su ba?”

Idan da Husna tasan yadda yake ji a zuciyarsa da ta tausaya masa ta daina furta masa kalaman nan. Bai san me zai ce mata ba, bai san yadda za ayi ta fahimta ba. Bai san ta ina zai fara ba. Har yanzu kallon ƙanƙanuwar yarinya yake mata wacce ba zata iya ɗaukan tashin hankalin da yake ɓoye da shi ba. Da ace zata iya ɗauka, da babu ko shakka sai ya raba tashin hankalinsa wuri biyu ya bata rabi. Sai dai kuma miƙa mata daidai yake da tarwatsa duk wani farin cikinta.

Husna ta sharce hawayenta ta miƙe tsaye tana dubansa,

“Shikenan ka sa na gazgata zuciyata akan abin da bana son gazgatata. Ina ta ƙaryata kaina akan ba kai kayi wannan aikin ba, amma a yanzu na gama amincewa.”

Ta ja wani irin ajiyar zuciya da yasa ya juyo cikin tashin hankali,

“Uncle… Ko menene dalilin da yasa ka shiga cikin wannan masifar, Allah babu ruwansa ba zai taɓa yi maka uzuri ba. Idan ya ɗauki ranka a yanzu kasan makomarka wuta ne.”

Tana gama faɗa masa hakan, ta shiga banɗaki da gudu tana ci gaba da wani irin kuka mai taɓa zuciya. A hankali ya dafa bango ya nemi wuri ya zauna yana jin kansa yana sara masa. Tabbas idan ya mutu yanzu wuta zai shiga. Ya yi magana a hankali,

“Indai mahaifina zai shiga Aljanna, na amince inshiga wutan. Indai Gwaggo da Abba za su shiga aljannah burina ya cika.”

Wata zuciyarsa ta fizgo shi da ƙarfi ta ce,

‘Mu’azzam ka dawo hayyacinka. Wutan Allah na dabanne. Har yanzu kana da sauran dama da zaka kusanto kanka ga Allah. Har yanzu kana da sauran daman neman yafiyar mahaifiyarka.’

Girgiza kansa ya yi tare da miƙewa,

‘Idan na nemi yafiyar Gwaggo su kuma iyayen da na bada gudumawa akan rayukansu fa?’

Har zai fice ya waiwayo ya dubi Husna da ta wanko fuskarta tana gogewa. Jikinsa a mace ya ce,

“Ki je Gwaggo tana kiranki.”

Bayansa ta bi suka fito tare. Hakan yasa duk matan suka zuba masa ido. Salima kuwa tunda ya shiga take duban lokaci a ƙalla ya yi mintuna talatin a cikin ɗakinta.

Kallo ɗaya Gwaggo ta yi mata ta gane ta yi kuka, amma sai ta yi kamar bata gane ba.

A ranar har Gwaggo aka shiga kitchen. Kishiyoyinta kuwa sun ci burin sai dai idan Gwaggo bata tafi ba, don tabbas sai sun raba duk wata alaƙa da ke tsakanin M.Y da Husna. Mugun baƙin kishi har ya sa Salima tana tunanin ta hanyar da zata bi don ganin ta kauda Gwaggo.

Yau ma sai da Husna ta yi gardama wajen shiga makwancin M.Y. wannan karon da kukanta ta shigo wiwi kamar wacce akayi wa mutuwa. Yana zaune bai ce mata komai ba. Har sha biyun dare bata daina kuka ba, shi kuma bai iya rintsawa ba.

A lokacin ne suka ji harbe-harbe ko ta ina. Tsananin tsoro da firgici suka shigeta, ta tashi da gudu ta rungume shi tsam jikinta babu inda baya rawa.

M.Y ya rintse idanunsa yana jin ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi, yana jin shikenan ranar tonon asirinsa ya zo. Sai dai ko da wasa ba zai bari wani ya taɓa masa uwa ba. A hanzarce ya miƙe, bai yi yunƙurin raba Husna da jikinsa ba, don ko ya yi yunƙurin yin hakan ba zata yarda ba. Bindigarsa ya ɗauko yana zuba mata harsashi. Ta sake ƙanƙame shi tana jin zufa yana keto mata. Zai buɗe ƙofa ta riƙe hannunsa sosai jikinta yana kyarma,

“Kada ka buɗe kada ka buɗe.”

Abin da bakinta yake iya furtawa kenan cikin tsoro. Ya girgiza kai ya shafi kanta,

“Husna koma ki zauna dole zan fita. Rayuwar mahaifiyata yana cikin hatsari, da inrasata gara ni ta fara rasani. Ba zan jure rashin Gwaggo ba.”

 A lokaci ɗaya ta ji tsoron zuciyarta ya ragu, ta ce,

“Muje tare a rasamu. Nima ba zan jure rashin Gwaggo ba, idan suka kashe min ita nima mutuwa zanyi.”

Bai yi wata wata ba ya buɗe ƙofar. Tuni antattara su a falon harda Gwaggo da jikinta yake kyarma. M.Y ya ɗaga bindigarsa kenan ya ji wata murya tana magana,

“M.Y ka sauke bindigar nan ko kuma mu kashe ‘yar tsohuwar nan.”

Husna tana maƙale a jikinsa ya sauke bindigar yana kallon mahaifiyarsa a cikin halin da ba zai iya taimakonta ba.

Oga Saleh yana ƙoƙarin ƙwace Husna daga jikinsa, ya yi saurin kawar da ita gefe yana nuna shi da yatsa,

“Kada ka kuskura ƙazamin hannunka ya taɓa min mata.”

Oga Saleh ya tuntsure da dariya ya ce,

“Dama an gaya min kafi son amaryarka fiye da sauran. Sai dai yau zamu kawo ƙarshen taurin kanka.”

Sai yanzu Gwaggo ta samu ta ɗago kanta. Idanunta a kafe akan Saleh. Bakinta na rawa ta ce,

“Alhaji Saleh?”

Shima ya juyo, sai dai shi murmushi yake yi mata.

“Tsohuwa menene abin mamaki dan kin ganni a cikin mutanan nan? Ga abin mamaki nan ɗanki da kika amincewa.”

Kwata-kwata Gwaggo bata fahimci me yake cewa ba. Mamakin ganin Alhaji Salen yafi komai ɗaga mata hankali. A lokaci guda ta fara wani tunani.

“Saleh kada ka taɓa min mahaifiyata.”

M.Y ya furta yana jin yau shikenan abin da ya jima yana ɓoyewa zai fito fili. Ya tabbata yau asirinsa zai tonu. Yau kowa zai guje shi. A yau mahaifiyarsa zata tsine masa. Sai dai abin da suke son ya yi ko da za su kashe shi ne ba zai iya aikatawa ba. Ɗaga idanunsa ya yi yana neman Jamilu, babu shi a cikinsu. Ya sani Jamilu ba zai jure ganin anayi masa irin wannan cin mutuncin ba.

Tohhh muje zuwa.

<< Mu’azzam 19Mu’azzam 21  >>

1 thought on “Mu’azzam 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.