Skip to content
Part 29 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Cikin abin da bai fice minti ashirin ba suka isa Police station ɗin. Da ƙyar aka ƙyale Salim ya sami ganinsa anan yake gaya masa barrister ɗin da yake so ya nemo amma abu na farko ya fara nema masa Mukhtar shi zai kai su har gidan da Abba yake. Zai kuma tsaya akan komai.

A waje ya sami Husna ta sa kanta a jikin motarsa tana kuka. Jiki asanyaye ya ƙaraso yana bata baki.

Kai tsaye Gwaggo suka koma suka ɗauka wacce take cikin matsananciyar damuwa. Tana jin damuwar rashin sauraren ɗanta da bata yi ba, tana jin tamkar bata yi masa adalci ba.

Da taimakon Mukhtar suka sami isowa gidan. Wani farin ciki ya tsirga a zuciyar Gwaggo, wanda ta rasa shi a tsawon lokuta masu tsawo.

Abba yana zaune a falon ya yi tagumi. Ya rasa dalilin da yake jin gabansa yana faɗiwa. Ɗaga idanun da zai yi suka yi ido huɗu da Gwaggo da ke tsaye ta kafe shi da nata idanun.

Husna ta zuba masu idanu cike da ƙaunarsu tana ji a zuciyarta da ace za su sami soyayyar juna kamar yadda iyayenmu na da suke yi da mutuwar aure ta zama tarihi.

“Hafsatu!”

Ya kira sunanta yana ƙoƙarin ƙarasowa gareta. Da sauri ta ƙaraso gareshi babu kunya irin wacce akasan Fulani da ita, ta rungume shi tsam. Dukkansu hawaye suke yi, dukkansu suna jin tamkar basu taɓa samun farin ciki irin na yau ba.

Hatta Salim da Mukhtar sai da suka murmusa. Sai bayan sun saki juna ne kunya ta ziyarci Gwaggo ta nemi wuri ta zauna tana dubansa.

“Ina Mu’azzamu? Maza ka zo ka ga ƙoƙarin da kayi, maza ka zo ka ga farin cikin da ka sa iyayenka a ciki. Da wannan kaɗai idan muka barka ba zaka taɓa taɓewa ba.”

Kalaman Abba kenan a lokacin da yake baza idanu yana neman ɗansa. Gwaggo ta goce da sabon kuka ta ce,

“Mu’azzamu yana can hannun ‘yan sanda sun kama mana shi.”

Abba ya zabura ya miƙe tsaye yana girgiza kai,

“Maza ku kaini gun ‘yan sandan ni zan yi shaidarsa zan kare shi insha Allahu babu wani abu da zai same shi.”

Yadda suka ga ya gigice ne yasa Husna ta yi saurin ƙarasowa ta maida shi ya zauna tana goge hawayenta,

“Abba kada ka damu bincike suke yi za su sake shi insha Allahu.”

Daga haka ta kasa ci gaba da magana saboda yadda hawaye ke sauka a kuncinta babu ƙaƙƙautawa. Abba ya zuba mata idanu yana hango tsantsar ƙaunar ɗansa a cikin idanunta.

“Allah ya yi maki albarka Husna.

Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru. Duk suka yi shiru aka rasa mai ƙarfin halin fara magana. Can Husna ta miƙe tana girgiza kai,

“Ba zan taɓa barinsa ya daɗe a hannun hukuma ba. Bai cancanci wurin da suke ajiye da shi ba.”

Da sauri ta yi hanyar waje su Mukhtar suka mara mata baya.

“Yanzu kina ganin ta ina ya kamata a fara?

Bata kai ga basu amsa ba ta hango Yunusa. Jikinta yana kyarma ta ƙarasa gare shi,

“Yunusa ina ka shiga ka bari suka tafi da Uncle?”

“Kiyi haƙuri ba nisa na yi ba. Yanzu menene abin yi?”

Ajiyar zuciya ta sauke,

“Ina son ka kaini dajin da muka sauka da Uncle zan yi bincike cikin kayansa. Sai kuma gidan da su Oga Saleh suke zama.”

Girgiza kansa ya yi,

“Idan kika je gidan su Oga Saleh tsautsayi yasa suka hangoki kasheki za su yi.”

Murmushin takaici ta yi,

“Ni dai kayi abin da na gaya maka.”

Ta dawo da dubanta ga su Mukhtar,

“Kuyi ƙoƙarin haɗa mu da hukuma gudun samun matsala. Sai kuma a sami barrister. Domin ina da tabbacin ranar monday za a tura su kotu.”

Duk suka amince da abin da ta ce, a gefe guda kuma suna jinjinawa Husna, da wahala a sami mace mai sadaukarwa kamarta.

Dajin nan suka nufa ta isa har bukkan ta shiga. Ba wasu abubuwa ta samu ba, sai wayar nan da Jamilu ya bashi don haka ta ɗauko harda wayar. Bayan sun fito ne suka sami isowa gidan su Alhaji Saleh, sai dai a cikin rashin sa’a wani ya hango su ya biyo su garin gudu ne ta saki wayar a ƙasa ta ci gaba da gudu.

Dole ta haƙura ta koma police station ɗin da kuka da magiya suka barta ta ganshi.

Hannayenta ya kama yana dubanta,

“Tunda kinsan ni mai gaskiya ne me zai sa ki dinga ɗaga hankalinki haka? Insha Allah zan fito.”

Girgiza kai ta yi da ƙarfi,

“Ta ina zamu sami shaidu? Bamu da wata shaida Uncle.”

Murmushi ya sakar mata,

“Ki je ki nemo Yunusa ya kaiki dajin nan, akwai waya da Jamilu ya bani. Duk da ban buɗe ba ina kyautata zaton akwai wani abu mai mahimmanci a ciki wanda zai iya taimakon mu. Kuma ranar da muka bar gidanmu naga wayar tana recording bansani ba ko nine na danna recording ɗin na dai san tabbas daga ƙarshe na danna saving. Ki ɗauko wayar ki sa a caji ƙila Allah ya taimake mu.”

Husna ta buɗe baki tana dubansa,

“Innalillahi… Na saki wayar garin gudu. Walh na saki wayar.”

Idanu ya sake watsa mata ganin yadda duk ta ruɗe. Dole tana buƙatar ƙarfin guiwa, don haka ya ce,

“Ki natsu sosai za ki iya tuna a daidai inda kika saki, sai ki je ki ɗauko. Idan kina irin wannan ruɗewan ba zaki samo komai ba.”

Ya fita gaskiya, kafin ta kai ga yin magana andatse hakan ta hanyar gaya mata lokaci ya yi. Dole ta fito tana sanar da Yunusa. Duk jikinsu ya yi sanyi.

*****

A yau aka gurfanar da M.Y a gaban kotu, wanda kotun ta cika da mutane saboda ganin yadda Shari’ar zata kasance.

Bayan dogon fafatawa kotun ta sake ɗaga ƙaran. Husna duk ta rame ta lalace. Da farko bata taɓa tunanin za su kai irin wannan lokacin ba a sakar mata mijinta ba. Sai dai ta ƙudurce insha Allahu a zama na gaba zai zamana anwanke shi ne.

*****

Wannan karon fafatawan ya fi zafi. Shiru-shiru babu Husna babu dalilinta. Can sai gata ta shigo da gudun gaske. Ita ce shaida ta gaba da ake nema, don haka ta ƙara so ta gabatar da kanta tare da wayar da ke hannunta. Abun mamaki hatta video ɗin ayyukan da su Saleh suke aikatawa sai da Jamilu ya ɗauka, har zuwa ranar da suka kashe shi.

Mu’azzam ya saki ajiyar zuciya, ya sani indai Husna tana raye ba zata taɓa bari ya wulakanta ba. Tarin hujjoji sun tabbatar da M.Y bai da laifin komai sai ma kuɗi da za a biya shi na ɓata masa suna da akayi, da kuma ɓata masa lokaci.

Kotu kuma ta bayar da umarnin a nemo duk inda su Alhaji Saleh suke a kamo su.

Farin ciki tsantsa ya bayyana a fuskar Husna, ta ƙaraso ta rungume shi tana dariya tare da hawaye. Ya ɗaga kanta suna kallon juna, ya yi murmushi ya sa hannu ya ɗauke mata hawayen yana girgiza kai,

“Godiya zamu yi wa Allah ba kuka ba. Daga yau hawayen nan naki sun ƙare.”

Hannunta ya kama suka samu suka fito waje. Sai a lokacin ya haɗa idanu da Gwaggo. Da sauri ya ƙarasa yana ƙoƙarin durƙusawa ta hana shi, sai kawai ya rungumeta yana jin rauni a zuciyarsa,

“Gwaggo ki yafe min, ki yafe…”

Anan ma ta hana shi ta hanyar rufe masa baki,

“Kada ka furta wata magana zo mu je gida.”

Sai a lokacin idanunsa suka hasko masa Abbansa. Ya dubi Abban ya dubi Gwaggo ya dawo da dubansa ga Husna. Ta gyaɗa masa kai alamun haka ne. Suka yi murmushi.

Raba kawunansu suka yi, M.Y da Husna suna cikin motar Mukhtar, Gwaggo kuma da Abba suna motar Salim.

Bayan sun iso gida ne duk suka amincewa juna akan kowa ya je ya huta.

M.Y ya shiga ɗaki Husna ta bi bayansa. Har ya shiga wanka ya fito tana zaune ta yi tagumi. Tunani take yi na irin zaman da zata yi da M.Y yau jin zuciyarta take fes kamar ba a taɓa halittar wata damuwa a zuciyarta ba.

Ruwan hannunsa ya watsa mata, ta shafi kumatunta tana murmushi. A gabanta ya zauna kasancewar yana kula da yadda take duƙar da kanta.

“Zo ki shafa min mai a bayana.”

Ta ɗan zaro idanu, ya ɗaga mata gira. A hankali ta lakaci man ta fara shafa masa kamar ba zata shafa ba. Gaba ɗaya sai ya ji kamar tana yi masa waiwayi don haka ya juyo da sauri ya riƙe hannayenta.

Da ƙirjinsa ya haɗata wanda duk ruwan wankan ne bai goge ba. Tana jin wani irin saƙo da yake sakar mata a cikin ɗanƙaramin bakinta. Hannunsa yakai yana laluban dukiyar fulaninta, a lokacinne suka ji kiran Sallah a tsakiyar kunnensu. Sakinta ya yi yana faɗin,

“Na yi alwala kin karya min.”

Ita dai tunda ta kwanta a gadon, gaba ɗaya gaɓoɓinta suka daina aiki. Duk jikinta ya mutu. Haka ya koma ya yi alwala ya fito yana dubanta,

“Ragguwa kawai. Ki tashi ki je ki yi alwala ni zan wuce masallaci.”

Shiru ta yi tana duban gefen fuskarsa. Ya ɗan dawo da baya ya ce,

“Oh kirana kike yi kenan.. bari inzo.”

Ganin ya nufota da gaske yasa ta tashi zaune ta ce,

“Yanzu zan je inyi Allah. Kada ka zo.”

Gaba ɗaya yadda take shagwaɓar yasa ya lalace a kallonta. Da sauri ya fice itama ta samu ta wuce banɗakin.

Bayan duk sun natsa suka zauna. M.Y ya dubi iyayensa farin ciki ya ƙara kama shi. Dama ya yi alƙawarin muddin yana raye sai ya sake dawo da farin cikinsa. Sai ga shi Husna ta taimaka masa, irin taimakon da har abada ba zai manceta ba. Iyayen hirarsu kawai suke yi cike da barkwanci. M.Y ya zauna kusa da Gwaggo yasa kansa a kafaɗarta gaba ɗaya kewarta yake yi. Hannu tasa ta shafi kansa,

“Ka yafe min Babban mutum na aikata maka kuskure.”

Murmushi ya wadaci fuskarsa,

“Gwaggo baki taɓa yi min laifi ba.”

Salim da Mukhtar suka shigo harma da Yunusa. Godiya sosai suka yi wa Salim, haka ma Mukhtar da Yunusa.

Sun jima suna hira akan lalacewar ƙasarmu. Daga bisani suka yi sallama kowa ya kama kansa.

A ɗakin ta gama shiryawa da nufin kwanciya Gwaggo ta ƙwala mata kira. Da sauri ta fito tana amsawa. Dubanta ta yi sosai sannan ta ce,

“Saura ki saki jikinki da babban mutum. Akwai gyaran da zan yi maki ki ja ajinki agunsa.”

M.y da ya ji kamar ta watsa masa ruwan zafi ya nemi wuri ya zauna tare da dafe kai.

‘Wai sai yaushe Gwaggo zata barni insami abin da nake da buƙata ne?’

Gabansa ya faɗi da ƙarfi da ya tuna bai gayawa iyayensa shi ne ya aikatawa Husna abin da ya aikata ba. Dole shima ba zai kusanceta ba har sai iyayensa sun san wannan laifin. Ba zai iya gaya masu ba amma zai kira Dakta Salim ya yi masa bayani.

Husna ta shigo tana sunkuyar da kai, yana kallonta ta kwanta bai nemi matsowa kusa da ita ba, yana ganin kamar zai yi kuskure ne.

*****

Bayan Dakta ya gama yi masu bayani Gwaggo ta yi murmushi,

“Wannan ikon Allah ne. Ba zamu taɓa ƙullatan babban mutum ba, tunda a yanzu haka matarsa ce. Kuma ƙaddararsu kenan. Mu ma gobe zamu koma insha Allahu.”

Haka suka tattauna da Dakta Salim ya koma ya sanar da M.Y hakan yasa ya ji daɗi matuƙa. Idan iyayensa suna hira suna zolayar juna Husna da M.y sai su dubi juna su saki murmushi. Abin yana matuƙar burgesu.

M.Y bai koma gidansa ba sai ma yasa a kasuwa aka siya ya gyara ɗayan gidan ya zuba komai. Ya ɗauki su Gwaggo suka koma Gombe ‘yan uwa da abokan arziki sai farin ciki suke.

Ana gobe za su dawo Abba ya zauna ya yi masu nasiha mai tsawo. A daren ta sake komawa gidan Salma sun daɗe suna tattaunawa daga bisani ta dawo gida. Gwaggo ta dinga bata wasu jiƙe-jiƙe ita dai karɓa kawai take yi tana sha.

Washegari suka bar garin zuwa Kaduna..

Gidan ya ƙawatu matuƙa ta yadda ta dinga kallo tana yabawa. Tun Magrib da ya fita bai sake dawowa ba ya tafi wurin Mukhtar suna tattaunawa akan sabuwan kasuwancin da za su fara yi. Sai bayan isha’i ya dawo da kaji.

Tana zaune ta idar da Sallah tana jan carbi ta dube shi kamar za ta yi kuka. Ya gane abin da take nufi don haka ya sakar mata murmushi,

“Tuba nake yi.”

Ta yi murmushi ta ce,

“Sannu da zuwa.”

Ya amsa. Da kansa ya je kitchen ya ɗauko plate ya zuba kajin ya tura mata akan ta ci kafin ya fito wanka. Yadda ya shiga wankan ya bar kajin haka ya fito ya same su. Da rigima ya samu ta ci kaɗan sannan ta sake yin brush suka yi Sallar nafila, ya yi mata addu’a sosai sannan ya jawota zuwa ɗakinsa.

Jikinta ya fara rawa, tuni ta lalubo ƙarya ta ce,

“Yanzu naga jinin al’adata.”

Da farko ya ɗan firgita, sai can ya kama lissafi sai kuma ya yi murmushi.

“Ina ruwana da al’adarki? Ko na ce maki zan yi maki wani abu ne?”

Shiru ta yi tana juya yatsunta. Yasa hannu ya jawota gadon gaba ɗaya ta yi kwanciyarta a ƙirjinsa. Ya kashe masu wuta tare da raɗa mata a kunne,

“Rufe idonki ki yi barci sai da safe.”

Ta yi saurin rintse idanunta tana sakin numfashi mai cike da tsoro. Tun daga wuyanta yake sakar mata sumba mai rikita jiki, har ya samu daman sauka kan laɓɓanta. Harshensa ya zura mata wanda ya sake tafiya da duk wani tunaninta. A hankali yasa hannu ya ɗaga karamin rigar barcin hannunsa suka sauka a inda yafi jan hankalinsa. Ya zare bakinsa ya ɗora akan ƙirjinta wanda ya ƙarasa gigitata,

“Uncle…”

Bai daina abinda yake yi ba ya amsa da wata irin murya mai nuni da mamallakin muryar ya fita hayyacinsa. Sannu a hankali ta dinga tura masa ƙirjin hakan ya ƙara haukata shi.

Sai da ya tabbatar da ta gama kamuwa sannan ya yi addu’a. Abin da ya bashi mamaki kamar ba a taɓa shigarta ba, ji yake kamar yau ya fara saninta. Za a iya haɗa mata goma ba a sami mai rabin baiwanta ba.

Kuka kawai take yi masa tana cewa,

“Uncle zafi.”

Amma ina, hakan baisa ya rangwanta mata ba har sai da ya tabbatar da ya sami gamsuwar da yake buƙata.

Jini bai fito ba, sai ɗan tsagewa da ta yi. Azaba kawai take ji kamar barkono. Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, kasancewar ya tsani kwanciya da janaba, musamman yanzu da yake jin kansa kamar jinjiri wanda bai taɓa aikata zunubi ba.

A kunne ya raɗa mata ta je ta watsa ruwa. Kanta a ƙasa ta wuce banɗakin ta shiga ruwan zafin kenan ta ganshi tsaye akanta yana kallon ƙirjinta. Ta yi saurin rufe ƙirjin tana cewa,

“Zan yi maka ihu idan baka fita ba.”

Da shagwaɓarta ta yi maganar, hakan yasa ya gyara tsayuwa ya ce,

“Don Allah yi min ihun inga wanda zai sha kunya.”

Bata san lokacin da ta sa tafukan hannayenta ta rufe fuskar ba. A lokacin ya sami daman ƙarewa ƙirjin idanu. Sai can kuma ta ankara da wautar da ta zabga ta yi saurin buɗe fuskar tana kallonsa. Wurin yake kallo hakan yasa ta maido hannayen ta sake kare ƙirjin tare da fasa kuka. Murmushi kawai ya yi ya fice abinsa. Bayan ta fito ne tana ɗaure da tawul, tasa hijab. Ya jawota har kan gadon ya cire mata Hijabin ya zare tawul ɗin ya rungumeta a ƙirjinsa tare da jawo masu bargo. Yaso ta ƙyale shi ya yi wasa da abubuwansa yadda yake so, sai dai ta sa masa rikici dole ya ƙyaleta.

*****

Salima da ke kaiwa da komowa a ɗakin wata ƙawarta ta dubi ƙawar tana huci,

“Muddin sunana Salima bayarbiya Wallahi Wallahi Sai M.Y ya dawo hannuna kuma na juya shi kamar waina. Sai na tarwatsa duk wani farin ciki da yake ciki da tsinanniyar yarinyar nan. Babu wata ‘ya mace da ta isa ta raba ni da M.Y.”

Ƙawarta ta dubeta cike da kishi ta ce,

“Me ya sa kike ɓata min rai ne? Yanzu na gama gamsar da ke me zai sa ki dinga tuna tsohon saurayinki a gabana? Don Allah ki ƙyale shi.”

Salima ta dubi ƙawarta Shukra duba na ɓacin rai,

“Kinsan me kike cewa kuwa? Ban taɓa haɗa son M.Y da na wata ba. Da na yi tunanin zan iya rayuwa babu shi amma yanzu kam ba zan iya ba. Ki shirya gobe zaki rakani Mina akwai wurin malamin da zanje. Sai na dawo gidana ko ta wani irin hanya ne.”

To masu karatu.. Muje zuwa dai mu ji yadda zata kaya.

Taku har kullum ‘yar mutan Borno.

<< Mu’azzam 28Mu’azzam 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×